Kristi Yana Ja-gorar Ikilisiyarsa
“Ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.”—MATTA 28:20.
1, 2. (a) Sa’ad da yake ba da umurnin a almajirantar da mutane, menene Yesu da ya tashi daga matattu ya yi alkawari ga mabiyansa? (b) Ta yaya Yesu ya ja-goranci ikilisiya ta Kiristoci na farko da ƙwazo?
KAFIN ya tafi sama, Yesu Kristi, Shugabanmu da aka ta da daga matattu, ya bayyana ga almajiransa kuma ya ce: “Dukan hukunci a cikin sama da ƙasa an bayar gareni. Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku: ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.”—Matta 23:10; 28:18-20.
2 Yesu bai bai wa almajiransa aikin ceton rai kawai ba, na ƙara almajirantarwa amma kuma ya yi musu alkawarin zai kasance tare da su. Tarihin Kiristanci na farko, da ke rubuce cikin littafin Ayukan Manzanni na Littafi Mai Tsarki, ya tabbatar da cewa Kristi ya yi amfani da iko da aka ba shi ya ja-goranci ikilisiyar da aka kafa ba da daɗewa ba. Ya aiko da “mai-taimakon” da ya yi alkawari—ruhu mai tsarki—ya ƙarfafa mabiyansa kuma ya yi musu ja-gora a ƙoƙarce-ƙoƙarcensu. (Yohanna 16:7; Ayukan Manzanni 2:4, 33; 13:2-4; 16:6-10) Yesu da ya tashi daga matattu ya yi amfani da mala’iku da suke ƙarƙashinsa ya taimaki almajiransa. (Ayukan Manzanni 5:19; 8:26; 10:3-8, 22; 12:7-11; 27:23, 24; 1 Bitrus 3:22) Bugu da ƙari, Shugabanmu ya yi ja-gorar ikilisiyar wajen shirya ƙwararrun mutane su yi hidima ta hukumar mulki.—Ayukan Manzanni 1:20, 24-26; 6:1-6; 8:5, 14-17.
3. Waɗanne tambayoyi ne za a tattauna a wannan talifin?
3 To, game da lokacinmu fa, ‘ƙarshen zamanu’? Ta yaya Yesu Kristi yake ja-gorar ikilisiyar Kirista a yau? Kuma ta yaya za mu nuna cewa muna na’am da shugabancinsa?
Ubangiji Yana da Bawa Mai Aminci
4. (a) Su wa ke cikin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima”? (b) Menene Ubangijin ya danka a hannun bawan?
4 Sa’ad da yake annabta game da alamar bayyanarsa, Yesu ya ce: “Wanene fa bawan nan mai-aminci, mai-hikima wanda ubangijinsa ya sanya shi bisa iyalin gidansa, domin shi ba su abincinsu a lotonsa? Wannan bawa mai-albarka ne, wanda ubangijinsa sa’anda ya zo za ya iske shi yana yin haka. Hakika, ina ce muku, za ya sanya shi bisa dukan abin da ya ke da shi.” (Matta 24:45-47) ‘Ubangijin’ shi ne Shugabanmu, Yesu Kristi, kuma ya naɗa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima”—rukunin Kiristoci shafaffu a duniya—bisa dukan abu da yake da shi a duniya.
5, 6. (a) A wahayin da manzo Yohanna ya gani, menene “fitilu bakwai na zinariya” da kuma “taurari bakwai” suke alamtawa? (b) Mecece gaskiyar cewa “taurari bakwaiɗin” suna cikin hannun dama na Yesu yake nufi?
5 Littafin Ru’ya ta Yohanna na Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa bawa mai aminci, mai hikima na ƙarƙashin ja-gorar Yesu Kristi. A cikin wahayi na “ranar Ubangiji,” manzo Yohanna ya ga “fitilu guda bakwai na zinariya; a cikin tsakiyar fitilu kuma ga wani mai-kama da ɗan mutum” wanda “cikin hannunsa na dama kuma yana da taurari bakwai.” Da yake bayani game da wahayin Yohanna, Yesu ya ce: “Asirin taurarin nan bakwai waɗanda ka gani cikin hannuna na dama, da fitilu bakwaiɗin kuma. Taurari bakwaiɗin mala’iku ne na ikilisiyan nan bakwai; fitilu bakwaiɗin kuma ikilisiya bakwai ne.”—Ru’ya ta Yohanna 1:1, 10-20.
6 “Fitilu bakwai na zinariya” alama ce na dukan ikilisiyoyi na Kiristoci na gaskiya da suke wanzuwa a “ranar Ubangiji,” wadda ta fara a shekara ta 1914. To, “taurari bakwaiɗin” kuma fa? Da farko, suna alamta dukan waɗanda aka haifa ta ruhu, masu kula shafaffu da suke kula da ikilisiyoyi na ƙarni na farko.a Masu kula suna cikin hannun Yesu—ƙarƙashin ja-gorarsa. Hakika, Kristi Yesu yake ja-gorar wannan haɗaɗen ajin bawa. Amma a yanzu, shafaffu masu kula adadinsu kaɗan ne. Ta yaya shugabancin Kristi ya kai bisa fiye da ikilisiyoyi 93,000 na Shaidun Jehovah a dukan duniya?
7. (a) Ta yaya Yesu yake amfani da Hukumar Mulki ya ba da ja-gora cikin ikilisiya a dukan duniya? (b) Me ya sa za a ce dattawa Kiristoci ruhu mai tsarki ne yake naɗa su?
7 Kamar yadda yake a ƙarni na farko, ƙaramin rukunin na ƙwararrun mutane daga tsakanin masu kula shafaffu yanzu suna hidima cikin Hukumar Mulki, suna wakiltan bawa mai aminci, mai hikima. Shugabanmu yana amfani da Hukumar Mulki ya naɗa ƙwararrun mutane—ko waɗanda ruhu ya shafe su ko babu—su zama dattawa a cikin ikilisiya. A wannan hanyar, ruhu mai tsarki, wanda Jehovah ya bai wa Yesu iko ya yi amfani da shi, yana aiki mai muhimmanci. (Ayukan Manzanni 2:32, 33) Da farko, waɗannan masu kula dole ne su cika bukatun da aka kafa a cikin Kalmar Allah, wanda aka hure shi da ruhu mai tsarki. (1 Timothawus 3:1-7; Titus 1:5-9; 2 Bitrus 1:20, 21) Zaɓa da kuma naɗawa ana yin su ne bayan addu’a kuma ta ja-gorar ruhu mai tsarki. Bugu da ƙari, waɗanda aka naɗa suna ba da tabbacin ba da ’ya’yan ruhu. (Galatiyawa 5:22, 23) Saboda haka, gargaɗin Bulus ya shafi dukan dattawa, ko shafaffe ne ko babu: “Ku tsare kanku, da dukan garke kuma, wanda Ruhu Mai-tsarki ya sanya ku shugabannai a ciki.” (Ayukan Manzanni 20:28) Waɗannan mutane da aka naɗa suna samun ja-gora daga Hukumar Mulki kuma suna kiwon ikilisiya da son rai. A wannan hanyar, Kristi yana tare da mu yanzu kuma yana ja-gorar ikilisiyarsa da ƙwazo.
8. Ta yaya Kristi yake amfani da mala’iku wajen ja-gorar mabiyansa?
8 Yesu yana amfani da ainihin mala’iku ya ja-goranci mutanensa a yau. A misali na alkama da zawa, lokacin girbi zai zo a “matuƙar zamani.” Su waye Ubangijin zai yi amfani da su wajen girbin? “Masu-girbi mala’iku ne,” in ji Kristi. Ya daɗa cewa: “Ɗan mutum za ya aike mala’ikunsa, su kuma za su tattara abin da ke sa tuntuɓewa duka, da masu-aika mugunta, su cicire daga cikin mulkinsa.” (Matta 13:37-41) Bugu da ƙari, kamar yadda mala’ika ya ja-goranci sawun Filibbus ya sadu da Habashi bābān, da tabbaci mai yawa a yau cewa Kristi yana amfani da mala’iku su ja-goranci aikin Kiristoci na gaskiya wajen neman masu zukatan kirki.—Ayukan Manzanni 8:26, 27; Ru’ya ta Yohanna 14:6.
9. (a) Ta wace hanya ce Kristi yake ja-gorar ikilisiyar Kirista a yau? (b) Waɗanne tambayoyi za mu yi idan muna so mu amfana daga shugabancin Kristi?
9 Yana ba da tabbaci mu sani cewa Yesu Kristi ya yi tanadin ja-gora ga mabiyansa a yau ta wajen Hukumar Mulki, ruhu mai tsarki, da kuma mala’iku! Idan ma wasu bayin Jehovah an raba su na ɗan lokaci da Hukumar Mulki domin tsanantawa ko kuma wasu yanayi kamar hakan, Kristi zai yi musu tanadin shugabanci ta wajen ruhu mai tsarki da kuma taimakon mala’iku. Amma dai, muna amfana ne daga shugabancinsa kaɗai idan muka karɓe shi. Ta yaya za mu nuna cewa mun karɓi shugabancin Kristi?
“Ku Yi Biyayya . . . Ku Sarayadda Kanku”
10. Ta yaya za mu nuna muna daraja dattawa da aka naɗa a cikin ikilisiya?
10 Shugabanmu ya ba wa ikilisiyar “kyauta ga mutane”—“waɗansu, masu-wa’azin bishara; waɗansu, makiyaya da masu-koyarwa.” (Afisawa 4:8, 11, 12) Hali da muke nuna musu yana bayyana ko mun karɓi shugabancin Kristi. Yana da kyau ‘mu nuna muna godiya’ domin mutane ƙwararru na ruhaniya da Kristi ya bayar. (Kolossiyawa 3:15) Kuma sun dace mu ba su daraja. “Dattiɓai waɗanda ke mulki da kyau sai a maishe su sun isa bangirma ninki biyu,” manzo Bulus ya rubuta. (1 Timothawus 5:17) Ta yaya za mu nuna godiyarmu da kuma daraja waɗannan—dattawa, ko kuma masu kula—na ikilisiya? Manzo Bulus ya amsa: “Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabannanku, ku sarayadda kanku.” (Ibraniyawa 13:17) Hakika, muna bukatar yi musu biyayya kuma mu sarayar da kanmu, mu miƙa kai gare su.
11. Me ya sa daraja shirin da dattawa suka yi batu ne na kiyaye baftismarmu?
11 Shugabanmu kamili ne. Mutanen da ya bayar kyauta ba kamilai ba ne. Saboda haka, za su yi kuskure a wasu lokatai. Hakika, yana da muhimmanci mu kasance da aminci ga tsarin Kristi. Babu shakka, aikatawa cikin jituwa da keɓewar kanmu da kuma baftisma yana nufin fahimtar dacewar iko da ruhu ya naɗa a cikin ikilisiya da kuma miƙa kai da son rai ga ikon. Baftismarmu ‘cikin sunan ruhu mai tsarki’ nuni ne a fili cewa mun fahimci ruhu mai tsarki kuma mun san aikinsa a cikin nufin Jehovah. (Matta 28:19) Irin wannan baftisma yana nufin cewa za mu ba da haɗin kai ga ruhun kuma ba za mu yi kome ba da zai hana aikinsa tsakanin mabiyan Kristi. Tun da ruhu mai tsarki yana yin aiki na musamman wajen zaɓan da kuma naɗa dattawa, za mu iya kasancewa da aminci ga keɓewar kanmu da gaske, idan muka ƙi ba da haɗin kai ga abin da dattawa suka shirya a cikin ikilisiya?
12. Waɗanne misalai game da rashin daraja iko Yahuda ya ambata, kuma menene suke koya mana?
12 Nassosi suna ɗauke da misalai da suke koya mana muhimmancin biyayya da kuma sarayar da kai. Da yake maganar waɗanda suke zagin mutane da aka naɗa a cikin ikilisiya, almajiri Yahuda ya yi nuni da misalan gargaɗi guda uku, yana cewa: “Kaitonsu! Gama suka bi hanyar Kayinu, suka tunzura a guje cikin kuskuren Bal’amu domin ijara, suka halaka kuma cikin tayarwa ta Kuraha.” (Yahuda 11) Kayinu ya yi banza da gargaɗin ƙauna na Jehovah kuma da son rai ya bi hanyar ƙiyayya mai kisa. (Farawa 4:4-8) Duk da gargaɗi da Allah ya yi masa a kai a kai, Bal’amu ya yi ƙoƙari ya la’anci mutanen Allah domin dukiya. (Litafin Lissafi 22:5-28, 32-34; Kubawar Shari’a 23:5) Kuraha yana da na sa hakki mai kyau a Isra’ila, amma bai ishe shi ba. Ya ta da tawaye bisa bawan Allah, Musa, mutum da ya fi kowa tawali’u a duniya. (Litafin Lissafi 12:3; 16:1-3, 32, 33) Masifa ta faɗo wa Kayinu, Bal’amu, da Kuraha. Hakika waɗannan misalai sun koya mana mu saurari gargaɗin waɗanda Jehovah yake amfani da su a matsayin hakki kuma mu ba su daraja!
13. Wace albarka annabi Ishaya ya annabta ga waɗanda suka sarayar da kai ga tsarin dattawa?
13 Waye ba zai so ya amfana ba daga irin wannan tsari mai kyau na kulawa da Shugabanmu ya kafa a ikilisiya ta Kirista? Annabi Ishaya ya annabta albarkarta, yana cewa: “Duba, wata rana wani sarki za ya yi mulki cikin adalci, hakimai kuma za su yi mulki da shari’a. Mutum kuma za ya zama kamar maɓoya daga iska, makāri kuma daga hadarin ruwa; kamar koguna cikin ƙeƙasasshiyar ƙasa, kamar inuwar babban dutse cikin ƙasa mai-agazari.” (Ishaya 32:1, 2) Kowanne cikin waɗannan dattawa ya kamata ya zama irin wannan “maɓoya” na kāriya da kuma kwanciyar rai. Ko ma idan miƙa kai ga iko yana yi mana wuya, bari cikin addu’a mu yi ƙoƙari mu ba da kanmu ga yin biyayya da kuma sarayar da kai ga tsarin iko da Allah ya kafa cikin ikilisiya.
Yadda Dattawa Suke Sarayar da Kai ga Shugabancin Kristi
14, 15. Ta yaya waɗanda suke ja-gora a cikin ikilisiya suke nuna cewa sun sarayar da kai ga shugabancin Kristi?
14 Kowane Kirista—musamman ma dattawa—dole ne su bi shugabancin Kristi. Masu kula, ko kuma dattawa, suna da ɗan iko cikin ikilisiya. Amma ba sa neman su zama ‘shugabanni bisa bangaskiyar ’yan’uwansu masu bi’ ta ƙoƙarin su ja-goranci rayuwarsu ba. (2 Korinthiyawa 1:24) Dattawa suna bin maganar Yesu: “Kun sani sarakunan Al’ummai suna nuna musu sarauta, manyansu kuma suna gwada musu iko. Ba haka za ya zama a cikinku ba.” (Matta 20:25-27) Yayin da dattawa suke cika hakkinsu, da gaske suna ƙoƙarin su yi hidima ga wasu.
15 An aririci Kiristoci: “Ku tuna da waɗanda su ke shugabannanku . . . ku yi koyi da bangaskiyarsu, kuna tuna da matuƙar tasarrufinsu.” (Ibraniyawa 13:7) Ba a bukaci wannan ba domin dattawa su suke shugabanci. Yesu ya ce: “Gama ɗaya ne [Shugabanku], Kristi.” (Matta 23:10) Bangaskiya ce abin da za a yi koyi da ita daga dattawa domin suna yin koyi da Shugabanmu na gaske, Kristi. (1 Korinthiyawa 11:1) Ka yi la’akari da wasu hanyoyi da dattawa suke ƙoƙarin su zama kamar Kristi a dangantakarsu da wasu a cikin ikilisiya.
16. Duk da ikon da yake da shi, yaya Yesu ya bi da mabiyansa?
16 Ko da yake Yesu mafifici ne fiye da dukan wani mutum ajizi a kowacce hanya kuma yana da iko babu na biyunsa daga Ubansa, yana da filako a yadda yake bi da almajiransa. Bai sha kan masu sauraronsa da nuna ilimi na ban mamaki ba. Yesu ya nuna ya damu kuma da tausayi ga mabiyansa, ya lura da bukatunsu. (Matta 15:32; 26:40, 41; Markus 6:31) Bai taɓa biɗan abin da almajiransa ba za su iya bayarwa ba, kuma bai taɓa ɗora musu abin da ba za su iya ɗaukawa ba. (Yohanna 16:12) Yesu “mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya kuma.” Saboda haka, ba abin mamaki ba ne, da mutane da yawa suka samu wartsakewa a wurinsa.—Matta 11:28-30.
17. Ta yaya dattawa za su nuna filako irin na Kristi a dangantakarsu da wasu a cikin ikilisiya?
17 Idan Kristi da yake Shugaba ya nuna filako, lallai ya kamata waɗanda suke ja-gora a cikin ikilisiya ma su yi haka! Hakika, suna mai da hankali kada su yi ɓarna da ikon da aka danka musu. Kuma ba sa zuwa da “gwanintar zance,” domin su burge wasu. (1 Korinthiyawa 2:1, 2) Maimako, su yi ƙoƙari su faɗi maganar gaskiya ta Nassi da gaskiya da kuma sauƙin fahimta. Bugu da ƙari, dattawa suna ƙoƙari wajen abin da suke tsammani daga wajen wasu kuma suna la’akari da bukatun wasu. (Filibbiyawa 4:5) Da sanin cewa kowaye yana da nasa iyaka, ta wurin ƙauna suna yin la’akari da wannan a yadda suke bi da ’yan’uwansu. (1 Bitrus 4:8) Kuma dattawa da suke da tawali’u kuma masu sauƙin hali ba sa wartsakarwa ne da gaske? Hakika suna wartsakarwa.
18. Menene dattawa za su koya daga yadda Yesu ya bi da yara?
18 Ana iya zuwa wajen Yesu, har da ƙanana ma. Ka lura da amsarsa sa’ad da almajiransa suka kwaɓi mutane da suke kawo “yara ƙanƙanana” wurinsa. “Ku bar yara ƙanƙanana su zo gareni,” Yesu ya ce, “kada ku hana su.” Sai “ya rungume su, ya sa musu albarka, ya ɗibiya musu hannuwa.” (Markus 10:13-16) Yesu yana da kirki kuma yana daɗaɗa wa wasu rai, kuma wasu suka matsa kusa da shi. Mutane ba sa tsoron Yesu. Har yara sun sake a gabansa. Dattawa ma ana iya zuwa wurinsu, kuma suna nuna ƙauna mai daɗaɗawa da kuma kirki, wasu—har yara—suna sakewa a wajensu.
19. Menene ‘kasancewa da nufin Kristi’ ya ƙunsa, kuma wane ƙoƙari wannan yake bukata?
19 Iyakacin yadda dattawa za su yi koyi da Kristi Yesu ya dangana ne bisa yawan yadda suka san shi. “Wanene ya gane nufin Ubangiji, da za ya koya masa?” in ji tambayar Bulus. Sai ya daɗa: “Amma nufin Kristi yana wurinmu.” (1 Korinthiyawa 2:16) Kasancewa da nufin Kristi ya ƙunshi sanin yadda yake tunani da kuma cikakkiyar mutuntakarsa saboda mu san abin da zai yi a wani yanayi. Ka yi tunanin sanin Shugabanmu haka da kyau! Hakika, wannan yana bukatar mai da hankali ga labaran Linjila da kuma cika zukatanmu a kai a kai da fahimtar rayuwar Yesu da kuma misalansa. Sa’ad da dattawa suka yi ƙoƙari su bi shugabancin Kristi har haka, waɗanda suke cikin ikilisiya za su so su yi koyi da bangaskiyarsu. Dattawa kuma za su gamsu idan suka ga wasu suna bin sawun Shugaba da farin ciki.
Ka Ci Gaba a Ƙarƙashin Shugabancin Kristi
20, 21. Yayin da muke hangar sabuwar duniya ta alkawari, menene ya kamata mu ƙuduri aniyar yi?
20 Yana da muhimmanci dukanmu mu kasance a ƙarƙashin shugabancin Kristi. Yayin da muke dumfarar ƙarshen wannan zamani, muna cikin yanayi daidai da Isra’ilawa a Filayen Mowab a shekara ta 1473 K.Z. Suna bakin Ƙasar Alkawari, kuma ta bakin annabi Musa, Allah ya ce: “Kai [Joshua] za ka tafi tare da mutanen nan cikin ƙasa wadda Ubangiji ya rantse ma ubanninsu za ya ba su ita.” (Kubawar Shari’a 31:7, 8) Joshua ne shugaba da aka naɗa. Domin su shiga cikin Ƙasar Alkawari, Isra’ilawan dole ne su sarayar da kai ga shugabancin Joshua.
21 Littafi Mai Tsarki ya ce mana: “Gama ɗaya ne [Shugabanku], Kristi.” Kristi ne kaɗai zai ja-gorance mu zuwa sabuwar duniya ta alkawari inda adalci yake zaune. (2 Bitrus 3:13) Saboda haka bari mu ƙuduri aniyar sarayar da kanmu ga shugabancinsa a dukan ɓangarorin rayuwa.
[Hasiya]
a “Taurari” a nan ba alamar mala’iku ba ne na zahiri. Yesu ba zai yi amfani da mutum ba ya rubuta bayani domin halittun ruhu da ba su ganuwa. Saboda haka, lallai “taurari” ya kasance alama ta mutane masu kula, ko kuma dattawa, a ikilisiya, waɗanda ake ɗaukar su manzannin Yesu. Tun da adadinsu bakwai ne yana nufin cika da Allah ya ƙudura.
Ka Tuna?
• Ta yaya Kristi ya ja-goranci ikilisiya ta farko?
• Ta yaya Kristi yake ja-gorar ikilisiyarsa a yau?
• Me ya sa za mu sarayar da kanmu ga waɗanda suke ja-gora a cikin ikilisiya?
• A waɗanne hanyoyi ne dattawa za su nuna cewa Kristi ne Shugabansu?
[Hoto a shafi na 17]
Kristi yana ja-gorar ikilisiya kuma yana riƙe da masu kula cikin hannunsa na dama
[Hotuna a shafi na 18]
“Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabannanku, ku sarayadda kanku”
[Hoto a shafi na 20]
Yesu yana da ƙauna kuma ana iya zuwa gare shi. Dattawa Kiristoci ku yi ƙoƙarin zama kamarsa