Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 12/1 pp. 4-7
  • Ta Yaya ne Mutane a Dukan Duniya Suke Haɗa Kai?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya ne Mutane a Dukan Duniya Suke Haɗa Kai?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Tsoron Makaman Nukiliya Yana Yi wa Haɗin Kai Barazana
  • Tushen Haɗin Kai na Gaskiya
  • Kalmar Allah Ce ta Haɗa Kansu
  • “Ƙauna ga Junanku”
  • Ana Gane Masu Bauta Ta Gaskiya Ta Haɗin Kansu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Bauta Cikin Haɗin Kai a Lokacinmu—Menene Take Nufi?
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Haɗin Kai Na Kiristoci Yana Ɗaukaka Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 12/1 pp. 4-7

Ta Yaya ne Mutane a Dukan Duniya Suke Haɗa Kai?

TA YAYA za ka ba da ma’anar “haɗin kai”? Ga wasu mutane kalmar tana nufin rashin jayayya. Alal misali idan ƙasashe biyu ko fiye da haka suka ƙulla yarjejeniya kuma suka yarda cewa za su kasance da salama za a iya cewa suna da haɗin kai. Amma hakan gaskiya ne? A yawancin lokaci hakan ba gaskiya ba ce.

Alal misali: Tarihi ya nuna cewa an ƙulla yarjejeniya da yawa na zaman lafiya amma an kasa cim ma hakan. Me ya sa? Domin a yawancin lokaci shugabannin duniya sun fi damuwa ne kawai da nasu ikon fiye da zaman lafiya ko kuma haɗin kai. Sa’an nan kuma wasu ƙasashe suna jin tsoron abin da zai faru idan sojojinsu ba su da ƙarfi kamar ta sauran ƙasashen.

Saboda haka, idan ƙasashe biyu ba sa yaƙi da juna hakan ba ya nufin cewa suna da haɗin kai. Za a iya cewa mutane biyu da suke son su harbi kansu suna da haɗin kai ne don kawai ba su yi hakan ba? Yin tunanin haka wawanci ne! Irin wannan yanayin ne ƙasashe da yawa suke ciki a yau. Rashin yarda da juna da ke ƙaruwa ya sa mutane da yawa suke jin tsoro cewa wata rana za a yi amfani da waɗannan mugayen makaman. Menene aka yi don a hana haɗarin faruwa?

Tsoron Makaman Nukiliya Yana Yi wa Haɗin Kai Barazana

Yawancin mutane sun dogara da Yarjejeniyar Hana Yaɗuwar Makaman Nukiliya da aka yi, (Nuclear Non-Proliferation Treaty). Wannan yarjejeniya da aka amince da ita a shekara ta 1968 ta hana ƙera makaman nukiliya a ƙasashen da ba su da makaman kuma ta hana yaɗuwarsu a ƙasashen da suke da shi. Makasudin wannan yarjejeniyar wadda ƙasashe fiye da 180 suka yi na’am da ita, shi ne hana ƙera makamai gabaki ɗaya.

Ko da wannan makasudin kamar yana da kyau, wasu masu sūka suna ganin cewa an kafa wannan yarjejeniyar ce don a hana wasu ƙasashe ƙera makaman nukiliya. Saboda haka, ana tsoron cewa waɗanda suka saka hannu a wannan yarjejeniya suna iya canja ra’ayinsu. Hakika, wasu ƙasashe suna ganin cewa bai dace a hana su su ƙera makaman da za su kāre kansu da shi ba.

Abin da ya ƙara rikirkitar da batun har ya ƙara haɗarin shi ne babu ƙasar da aka hana ta ƙera makamashin nukiliya. Wannan ya sa wasu mutane suke jin tsoron cewa ƙasashen da suke amfani da makamashin nukiliya don zaman lafiya suna iya soma ƙera makaman nukiliya a ɓoye.

Ƙasashen da suke da makaman nukiliya suna iya yin watsi da wannan yarjejeniya na zaman lafiya. Masu sūka sun ce wawanci ne a yi tsammanin cewa ƙasashen da suke da makaman nukiliya sosai su halakar da su ko kuma su rage su. In ji wata majiya, “don a cim ma hakan . . . ana bukatar abota na kud da kud da kuma aminci tsakanin ƙasashen da suke faɗa da juna [kuma yana da wuya a gaskata] cewa wannan zai taɓa faruwa.”

Ƙoƙarin ’yan adam na kawo haɗin kai ya zama aikin banza. Wannan ba abin mamaki ba ne ga ɗaliban Littafi Mai Tsarki domin Kalmar Allah ta ce: “Mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.” (Irmiya 10:23) Littafi Mai Tsarki ya kuma faɗi sarai cewa: “Akwai wata hanya wadda ta ke da alamar kirki ga mutum, amma matuƙatta tafarkun mutuwa ce.” (Misalai 16:25) Gwamnatin ’yan adam ba su iya kawo haɗin kai na dindindin ba. Duk da haka, muna da bege.

Tushen Haɗin Kai na Gaskiya

Littafi Mai Tsarki na ɗauke da alkawarin Allah cewa duniya za ta kasance da haɗin kai amma ba ta ƙoƙarin ’yan adam ba. Mahalicci wanda nufinsa shi ne cewa ’yan adam za su yi zaman lafiya a dukan duniya zai cim ma abin da ’yan adam ba za su iya ba. Wasu suna ganin hakan ba zai yiwu ba. Duk da haka, nufin Allah tun da farko shi ne cewa ’yan adam su zauna lafiya da juna.a Ayoyi da yawa cikin Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa har ila nufin Allah ne ya haɗa kan ’yan adam. Ga wasu misalai:

• “Ku zo, ku duba ayukan Ubangiji, Irin risɓewa da ya yi cikin duniya. Ya sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya; Ya karya baka, ya daddatse māshi; Ya ƙoƙone karusai cikin wuta.”—ZABURA 46:8, 9.

• “Ba za su yi ciwutaswa ba; ba kuwa za su yi ɓarna ko’ina cikin dutsena mai-tsarki ba: gama duniya za ta cika da sanin Ubangiji, kamar yadda ruwaye su ke rufe teku.”—ISHAYA 11:9.

• “Ya haɗiye mutuwa har abada: Ubangiji Yahweh za ya shafe hawaye daga dukan fuskoki: za ya kuma kawarda zargin mutanensa daga dukan duniya: gama Ubangiji ya faɗi.”—ISHAYA 25:8.

• “Bisa ga alkawarinsa, muna sauraron sabobin sammai da sabuwar duniya, inda adalci yake zaune.”—2 BITRUS 3:13.

• “[Allah] za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin zuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.”—RU’YA TA YOHANNA 21:4.

Waɗannan alkawura tabbatattu ne. Me ya sa? Domin Mahalicci Jehobah Allah yana da iko da iyawa na haɗa kan ’yan adam. (Luka 18:27) Yana sha’awar ya yi hakan. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya yarda ya “tattara dukan abu cikin Kristi, abubuwan da ke cikin sammai, da abubuwan da ke bisa duniya.”—Afisawa 1:8-10.

Alkawarin Allah cewa zai kawo “sabuwar duniya” inda “adalci yake zaune” ba wasiƙar jaki ba ne. (2 Bitrus 3:13) Game da abin da ya alkawari, Jehobah Allah ya ce: “Ba za ta koma wurina wofi ba, amma za ta cika abin da na nufa, za ta yi albarka kuma a cikin saƙona.”—Ishaya 55:11.

Kalmar Allah Ce ta Haɗa Kansu

Kamar yadda aka ambata a talifin da ya gabata, sau da yawa addini ne ke raba kawunan mutane maimakon ya haɗa su. Ya dace mu bincika wannan sosai, don idan mun yarda cewa akwai Mahalicci, zai dace mu masu bauta masa mu zauna lafiya da juna kuma mu haɗa kanmu.

Rarrabuwar da addini yake jawowa tsakanin mutane bai jitu da ra’ayin Jehobah Allah da Kalmarsa ba. Maimakon haka, addini ne ke da laifi domin suna amfani da dabarun mutane wajen haɗa kan mutane maimakon ɗaukaka nufin Allah. Yesu ya kira shugabannin addini na zamaninsa “masu-riya” kuma ya ce musu: “Daidai Ishaya ya yi annabci a kanku, da ya ce, Wannan al’umma tana girmamana da leɓunansu; Amma zuciyarsu tana nesa da ni. Amma banza su ke yi mani sujada, koyarwa da su ke yi dokokin mutane ne.”—Matta 15:7-9.

Akasin haka, bauta ta gaskiya tana haɗa kan mutane. Annabi Ishaya ya annabta: “Za ya zama a cikin kwanaki na ƙarshe, dutse na gidan Ubangiji za ya kafu a ƙwanƙolin duwatsu, ya ɗaukaka bisa kan tuddai; al’ummai duka kuma za su zubo wurinsa. Za ya raba shari’a kuma tsakanin al’ummai, ya tsauta ma dangogi dayawa: za su kuma bubbuge takubansu su zama garmuna, māsunsu kuma su zama lauzuna: al’umma ba za ta zāre ma al’umma takobi ba, ba kuwa za a ƙara koya yaƙi nan gaba ba.”—Ishaya 2:2, 4.

A ƙasashe 230 a yau, Shaidun Jehobah suna bin umurnin da Jehobah Allah ya bayar game da hanyoyin kasancewa da haɗin kai. Menene tushen haɗin kansu? Manzo Bulus ya rubuta: “Ku yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.” (Kolossiyawa 3:14) Kalma ta asali da Bulus ya yi amfani da ita na “magami” tana iya nufin jijiyoyin jikin mutum. Waɗannan jijiyoyin suna da ƙwari kamar igiya kuma suna yin ayyuka biyu masu muhimmanci. Suna riƙe gaɓoɓin jiki da ƙasusuwa.

Haka ƙauna take. Wannan halin ba kawai yana hana mutane kashe juna ba. Ƙauna irin ta Kristi tana sa mutane daga wurare dabam dabam su yi aiki tare cikin lumana. Alal misali, tana sa mutane su yi rayuwar da ta jitu da abin da ake kira Ƙa’idar Ja-gora. Kamar yadda aka rubuta a Matta 7:12, Yesu Kristi ya ce: “Dukan abu fa iyakar abin da ku ke so mutane su yi maku, ku yi musu hakanan kuma.” Bin wannan ja-gorar ya taimaki mutane da yawa su sha kan wariya.

“Ƙauna ga Junanku”

Shaidun Jehobah sun ƙuduri su nuna su almajiran Kristi ne ta wajen yin abin da Yesu ya ce: “Mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yohanna 13:35) An nuna irin wannan ƙauna a hanya ta musamman a lokacin wariya da kuma faɗan siyasa. Alal misali, sa’ad da aka yi kisan ƙare dangi a Ruwanda a shekara ta 1994, Shaidun Jehobah sun nuna ƙauna ga juna. Shaidu ’yan ƙabilar Hutu sun kasadar da ransu domin su kāre ’yan’uwansu ’yan Tutsi!

Hakika, ba zai yiwu ba al’umman duniya su ƙaunaci maƙwabtansu da har zai kawo haɗin kai na duniya. Bisa ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, Allah ne zai cim ma wannan a lokacinsa. A yanzu ma mutane suna iya ƙaunar juna kuma su haɗa kansu.

A shekarar da ta shige, Shaidun Jehobah sun ba da fiye da sa’o’i biliyan ɗaya suna ziyarar mutane kuma suna gaya musu game da Littafi Mai Tsarki da amfaninsa a rayuwa ta yanzu. Cikakken sani na Kalmar Allah ya haɗa kawunan miliyoyin mutane da wasu cikinsu a dā suna ƙiyayya da junansu. Waɗannan sun haɗa da Larabawa da Yahudawa, Armeniyawa da ’yan Turkiya, ’yan Jamus da ’yan Rasha da sauransu.

Za ka so ka ƙara koya game da yadda Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki take haɗa kan mutane? Idan kana so, ka tuntuɓi Shaidun Jehobah da ke yankinku, ko kuma ka rubuta zuwa ga adireshi da ya dace da ke shafi na 2.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani game da nufin Allah ga ’yan adam, ka duba babi uku na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Hoto a shafi na 4]

An ƙulla yarjejeniya da yawa kuma an yi watsi da su

[Hoto a shafi na 7]

Bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ya cim ma abin da gwamnatocin ’yan adam ba za su iya ba

[Hoto a shafi na 5]

Kalmar Allah ta nuna Tushen haɗin kai na gaskiya

[Hoto a shafi na 7]

Shaidun Jehobah ’yan Hutu da Tutsi suna gina wajen yin bauta tare

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba