Za a Taɓa Samun Haɗin Kai a Duniya Kuwa?
ZA A sami zaman lafiya a duniyarmu ko kuwa tana gab ne da halaka? Kamar dai akwai abubuwa da suka nuna cewa ɗaya daga cikinsu zai iya faruwa.
Wasu shugabannin duniya sun ce da gaba gaɗi cewa za a iya samun salama a dukan duniya, domin idan ba a samu salama ba yanayin duniya zai kasance da ban tsoro. A wata sassa kuma mutane da yawa suna yin irin waɗannan tambayoyin cikin tsoro cewa: Waɗanne ƙasashe ne suke da makaman da za su iya kashe mutane da yawa a take? Za su taɓa amfani da su kuwa? Menene zai faru idan suka yi amfani da su?
Tarihi ya nuna cewa tun da daɗewa kiyayya da wariya sune ainihin batutuwan da suke hana haɗin kai, kuma addini ya ci gaba da rura wutar maimakon ya kashe ta. Ɗan jarida James A. Haught ya rubuta: “Duk wani abin da zai iya raba kawunan mutane yana iya kawo kiyayya, kuma addini shi ne ainihin abin da ke raba kawunan mutane. Duk da imanin da dukan mutane suka yi cewa addini yana sa mutane su zama mutanen ‘kirki,’ a bayyane yake cewa yana sa wasu mutane su yi mugayen ayyuka.” Wani marubuci mai suna Steven Weinberg yana da irin wannan ra’ayin domin ya rubuta cewa: “Addini ne ke sa mutanen kirki su yi mugunta.”
Za a taɓa samun haɗin kai a duniyarmu kuwa? Kwarai kuwa! Amma kamar yadda za mu gani, ba mutane ko kuwa addinai ba ne za su kawo haɗin kai a duniya ba.
[Hoto a shafi na 3]
Duniyar nan tana kama ne da nakiyar da take gab da fashewa?