Ka Tsare Kanka Cikin Ƙaunar Allah!
“Ƙaunatattu, . . . ku tsare kanku cikin ƙaunar Allah, . . . zuwa rai na har abada.”—YAHUDA 20, 21.
1, 2. Ta yaya za ka iya kasancewa a cikin ƙaunar Allah?
JEHOBAH yana ƙaunar duniya sosai har ya ba da makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi ya sami rai madawwami. (Yohanna 3:16) Abu ne mai kyau mu shaida irin wannan ƙaunar! Idan kai bawan Jehobah ne, babu shakka, za ka so ka more wannan ƙaunar har abada.
2 Almajiri Yahuda ya bayyana yadda za ka iya kasancewa a cikin ƙaunar Allah. “Cikin gina kanku bisa bangaskiyarku maficin tsarki, kuna addu’a cikin Ruhu Mai-tsarki,” in ji Yahuda, “ku tsare kanku cikin ƙaunar Allah, kuna sauraron jinƙan Ubangijinmu Yesu Kristi zuwa rai na har abada.” (Yahuda 20, 21) Yin nazarin Kalmar Allah da kuma wa’azin bishara zai taimake ka ka manyanta a ‘bangaskiyarka maficin tsarki’ wato, koyarwar Kirista. Domin ka kasance a cikin ƙaunar Allah, dole ne ka yi addu’a “cikin Ruhu Mai-tsarki,” ko kuwa a ƙarƙashin ikonsa. Idan kana son ka sami rai madawwami, dole ne ka ba da gaskiya ga hadayar fansa na Yesu Kristi.—1 Yohanna 4:10.
3. Me ya sa wasu ba Shaidun Jehobah ba ne kuma?
3 Wasu da suka ba da gaskiya a dā sun ƙi su kasance a cikin ƙaunar Allah. Domin sun zaɓi tafarkin zunubi, ba su ci gaba da kasancewa Shaidun Jehobah ba. Ta yaya za ka iya guje wa irin wannan al’amari? Yin bimbini a kan bayanai na gaba zai iya taimaka maka ka guje wa zunubi kuma ka kasance a cikin ƙaunar Allah.
Ka Nuna Ƙaunarka ga Allah
4. Menene muhimmancin yin biyayya ga Allah?
4 Ka nuna ƙaunarka ga Allah ta wajen yi masa biyayya. (Matta 22:37) “Ƙaunar Allah ke nan,” in ji manzo Yohanna, “mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.” (1 Yohanna 5:3) Yin biyayya ga Allah zai iya ƙarfafa ka ka ƙi gwaji kuma hakan zai sa ka farin ciki. Mai zabura ya ce: “Mai-albarka ne mutum wanda ba ya bi ta shawarar miyagu ba, . . . Amma marmarinsa cikin shari’a ta Ubangiji ya ke.”—Zabura 1:1, 2.
5. Ƙaunarka ga Jehobah za ta motsa ka ka yi me?
5 Ƙaunarka ga Jehobah za ta motsa ka ka guje wa yin mugun zunubin da zai ɓata sunansa. Agur ya yi addu’a: “Kada ka ba ni ko talauci ko wadata: Ka ciyasda ni da abincin da ke daidai bukatata: Kada in ƙoshi, in musance ka, in ce, Wanene Ubangiji? Kada kuma in yi talauci har in yi sata, In kama sunan Allahna banza.” (Misalai 30:1, 8, 9) Ka ƙudurta cewa ba za ka ‘kama sunan Allah a banza ba’ ta wajen ɓata masa suna. Maimakon haka, ka ci gaba da yin abubuwa masu kyau da za su kawo yabo ga sunansa.—Zabura 86:12.
6. Menene zai iya faruwa idan ka yi zunubi da sane?
6 Ka dinga yin addu’a a kowane lokaci ga Ubanka na samaniya mai ƙauna don ya taimaka maka ka guje wa jarabar yin zunubi. (Matta 6:13; Romawa 12:12) Ka ci gaba da bin umurnin Allah don kada addu’o’inka su hanu. (1 Bitrus 3:7) Idan ka yi zunubi da gangan, sakamakon na iya kasancewa mai haɗari, domin a alamance Jehobah yana tare addu’ar ’yan tawaye da girgije don kada addu’arsu ta zarce zuwa gare shi. (Makoki 3:42-44) Saboda haka, ka nuna tawali’u, kuma ka yi addu’a kada ka yi abin da zai hana ka yin addu’a ga Allah.—2 Korinthiyawa 13:7.
Ka Nuna Ƙauna ga Ɗan Allah
7, 8. Ta yaya ne bin umurnin Yesu zai iya taimaka wa mutum ya ƙi tafarki na zunubi?
7 Ka nuna ƙauna ga Yesu Kristi ta wajen yin biyayya ga dokokinsa, domin hakan zai taimaka maka ka ƙi tafarkin zunubi. “Idan kun kiyaye dokokina,” in ji Yesu, “za ku zauna cikin ƙaunata: kamar yadda na kiyaye dokokin Ubana, ina zaune kuwa cikin ƙaunatasa.” (Yohanna 15:10) Ta yaya ne yin amfani da kalaman Yesu zai taimaka maka ka kasance a cikin ƙaunar Allah?
8 Mai da hankali ga kalaman Yesu zai iya taimaka maka ka manne wa mizanai na ɗabi’a. Dokar Allah ga Isra’ila ta ce: “Ba za ka yi zina ba.” (Fitowa 20:14) Amma Yesu ya bayyana wani mizani da ke tattare da wannan dokar, ya ce: “Dukan wanda ya duba mace har ya yi ƙyashinta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.” (Matta 5:27, 28) Manzo Bitrus ya ce wasu a cikin ikilisiya na ƙarni na farko suna da ‘idanu cike da zina’ kuma ‘sun jarabci mutane marasa-tsayawa.’ (2 Bitrus 2:14) Akasin haka, kana iya guje wa yin lalata idan kana ƙauna da yin biyayya ga Allah da kuma Kristi, idan kuma ka ƙudurta ka kāre dangantakarka da su.
Bari Ruhun Jehobah Ya Yi Maka Ja-gora
9. Game da ruhu mai tsarki, menene zai iya faruwa idan mutum ya ci gaba da yin zunubi?
9 Ka yi addu’a don samun ruhu mai tsarki na Allah, kuma ka bari ya yi maka ja-gora. (Luka 11:13; Galatiyawa 5:19-25) Idan ka ci gaba da yin zunubi, Allah yana iya janye ruhunsa mai tsarki daga wurinka. Bayan Dauda ya yi zunubi da Bath-sheba, ya roƙi Allah: “Kada ka yashe ni daga gabanka; kada kuma ka ɗauke mini ruhunka mai-tsarki.” (Zabura 51:11) Domin ya ƙi ya tuba daga zunubinsa, Sarki Saul ya rasa ruhun Allah. Saul ya yi zunubi ta wajen yin hadaya da kuma ƙin halaka tumaki, da shanu, da kuma sarkin Amalakawa. Bayan haka, Jehobah ya janye ruhunsa mai tsarki daga Saul.—1 Samuila 13:1-14; 15:1-35; 16:14-23.
10. Me ya sa ya kamata ka guji ainihin tunanin yin zunubi?
10 Ka guji tunanin yin zunubi. “Idan muna yin zunubi da nufin zuciyarmu bayanda mun karɓi sanin gaskiya,” in ji manzo Bulus, “babu sauran wata hadaya domin zunubai.” (Ibraniyawa 10:26-31) Abu ne mai haɗari idan ka yi zunubi da gangan!
Ka Nuna Ƙauna ga Mutane
11, 12. A waɗanne hanyoyi ne ƙauna da daraja za su hana mutum yin zina?
11 Ƙauna ga mutane zai hana ka yin lalata. (Matta 22:39) Irin wannan ƙaunar za ta taimaka maka ka kāre zuciyarka domin kada ta motsa ka ka yi sha’awar matar wani. Domin hakan na iya sa mutum yin kwartanci. (Misalai 4:23; Irmiya 4:14; 17:9, 10) Ka kasance kamar Ayuba, wanda ya ƙi ya mai da hankali ga wasu mata sai matarsa kaɗai.—Ayuba 31:1.
12 Daraja tsarkakar aure zai iya taimaka maka ka guje wa yin mugun zunubi. Nufin Allah ne cewa aure mai daraja da kuma jima’i su kasance hanyar haihuwa. (Farawa 1:26-28) Ka tuna cewa amfanin al’aure shi ne haihuwa, wanda abu ne mai tsarki. Mazinata da kwartaye suna yin rashin biyayya ga Allah, suna raina tsarin jima’i, suna kuma raina tsarkakar aure, kuma suna yin zunubi ga jikinsu. (1 Korinthiyawa 6:18) Amma ƙauna ga Allah da kuma maƙwabta da kuma yin biyayya ga Allah za su hana mutum ya yi abin da zai sa a yi masa yankan zumunci daga ikilisiyar Kirista.
13. Ta wace hanya ce mazinaci ke “lalatadda arzikinsa”?
13 Ya kamata mu danne tunanin yin lalata saboda kada mu jawo wa masu ƙaunarmu baƙin ciki. “Wanda yana tara zamansa da karuwai yana lalatadda arzikinsa,” in ji Misalai 29:3. Kwarton da ya ƙi tuba yana lalata dangantakarsa da Allah da kuma gamin iyali. Matarsa tana da ikon kashe aure. (Matta 19:9) Ko da mata ko mijin ne ya yi zunubi, kashe auren na iya sa marar zunubin, da yaran, da kuma wasu baƙin ciki. Ka yarda cewa sanin haɗarin lalata ya kamata ya motsa mu mu guje wa gwajin da zai sa mu yin ta?
14. Wane darassi ne za a koya game da yin laifi daga Misalai 6:30-35?
14 Sanin cewa babu yadda za a daidaita yin zina ya kamata ya motsa mutum ya guje wa wannan zunubin. Misalai 6:30-35 sun nuna cewa mutane suna iya jin tausayin ɓarawon da ya yi sata domin yana jin yunwa, amma ba sa daraja mazinaci domin ba shi da muradi mai kyau. “Ransa ya ke nema ya hallaka.” Za a kashe irin wannan mutumin ne a ƙarƙashin Dokar Musa. (Leviticus 20:10) Wanda ya yi zina na jawo wa wasu baƙin ciki domin yana son ya biya bukatarsa na lalata, kuma mazinacin da ya ƙi tuba ba zai kasance a cikin ƙaunar Allah ba, amma za a kore shi daga ikilisiyar Kirista mai tsabta.
Ka Kasance da Lamiri Mai Kyau
15. Menene yanayin lamirin da ya zama “lalas sai ka ce da ƙarfe mai-wuta”?
15 Idan muna so mu kasance cikin ƙaunar Allah, ba za mu ƙyale lamirinmu ya daina damuwa da yin zunubi ba. Babu shakka, ba za mu yi na’am da irin mizanai na ɗabi’a da ke taɓarɓarewa a duniya ba, kuma muna bukatar mu mai da hankali da irin abokanmu, abubuwan da muke karantawa, da kuma nishaɗi. Bulus ya yi gargaɗi: “Cikin kwanaki na ƙarshe waɗansu za su ridda daga imani, suna maida hankali ga ruhohi na ruɗami da koyarwar aljanu, ta wurin riyar mutane masu-faɗin ƙarya, waɗanda an yi ma lamirinsu lalas sai ka ce da ƙarfe mai-wuta.” (1 Timothawus 4:1, 2) An kwatanta lamirin da ya zama “lalas sai ka ce da ƙarfe mai-wuta” da tabo a jiki, wanda idan aka taɓa ba za a ji zafi ba. Irin wannan lamirin ba zai yi mana kashedi mu guje wa ’yan ridda da kuma yanayin da zai sa mu yi watsi da imaninmu ba.
16. Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da lamiri mai kyau?
16 Cetonmu ya dangana ne a kan kasancewa da lamiri mai kyau. (1 Bitrus 3:21) Ta wurin imaninmu da jinin da Yesu ya zubar, an tsabtace lamirinmu daga matattun ayyuka, don mu “bauta ma Allah mai-rai.” (Ibraniyawa 9:13, 14) Idan muka yi zunubi da gangan, lamirinmu zai zama marar tsabta, kuma ba za mu kasance mutane masu tsabta da suka dace da hidimar Allah ba. (Titus 1:15) Amma, da taimakon Jehobah, za mu iya kasancewa da lamiri mai kyau.
Wasu Hanyoyin da Za a Kauce wa Mugun Hali
17. Menene muhimmancin ‘bin Ubangiji sarai’?
17 Ka “bi Ubangiji sarai,” kamar yadda Kaleb na Isra’ila ta dā ya yi. (Kubawar Shari’a 1:34-36) Ka yi abin da Allah yake bukata a gare ka, kuma kada ka yi tunanin ci daga taburin “aljanu.” (1 Korinthiyawa 10:21) Ka ƙi ridda. Cikin godiya ka ci daga abinci na ruhaniya da ke kan teburin Jehobah kawai, kuma malaman ƙarya ko mugayen ruhohi ba za su rinjaye ka ba. (Afisawa 6:12; Yahuda 3, 4) Ka mai da hankali ga abubuwa na ruhaniya, kamar su nazarin Littafi Mai Tsarki, halartar taro, da kuma hidimar fage. Kana da tabbacin kasancewa da farin ciki idan ka bi Jehobah yadda ya kamata kuma ka yawaita a cikin aikin Ubangiji.—1 Korinthiyawa 15:58.
18. Ta yaya ne tsoron Jehobah zai shafi halinka?
18 Ka ƙudurta ka “yi ma Allah sujjada . . . tare da ladabi da saduda.” (Ibraniyawa 12:28) Tsoron Jehobah zai motsa ka ka ƙi duk wani tafarki marar kyau. Zai taimaka maka ka bi da kanka daidai da umurnin Bitrus ga shafaffu: “Idan kuma kuna kira bisa gareshi kamar Uba, shi wanda ya ke hukumtawa, ba da tara ba, amma gwalgwadon aikin kowane mutum, sai ku yi zaman baƙontarku da tsoro.”—1 Bitrus 1:17.
19. Me ya sa ya kamata ka dinga yin amfani da abubuwan da ka koya daga Kalmar Allah?
19 Ka dinga yin amfani da abubuwan da kake koya daga Kalmar Allah a kowane lokaci. Hakan zai taimaka maka ka guje wa yin mugun zunubi domin za ka kasance cikin “waɗanda suna da hankulansu wasassu bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.” (Ibraniyawa 5:14) Maimakon yin sakaci da furcinka da ɗabi’a, ka mai da hankali domin ka yi tafiya a matsayin mutum mai hikima, kana “rifta zarafi” a wannan mugun zamanin. Ka “fahimci abin da ke nufin Ubangiji,” kuma ka ci gaba da yin sa.—Afisawa 5:15-17; 2 Bitrus 3:17.
20. Me ya sa ya kamata mu guje wa ƙyashi?
20 Ka guje wa yin kwaɗayin abin wasu. Ɗaya daga cikin Dokoki Goma ta ce: “Ba za ka yi ƙyashin gidan makusancinka ba, ba za ka yi ƙyashin matar makusancinka ba, ko bawansa, ko baiwassa, ko sansa, ko jākinsa, ko kowane abin da ke na makusancinka.” (Fitowa 20:17) Wannan dokar ta kāre gidan mutum, matarsa, bayi, tumakinsa, da sauransu. Amma abu mafi muhimmanci shi ne furcin da Yesu ya yi cewa kwaɗayi na ƙazantar da mutum.—Markus 7:20-23.
21, 22. Waɗanne matakai ne Kirista zai iya ɗauka don ya guje wa zunubi?
21 Ka ɗauki matakai da za su hana sha’awar da za ta sa ka yin zunubi. Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Kowanne mutum ya jarabtu, sa’anda sha’awatasa ta janye shi, ta yi masa tarko. Sa’annan, lokacinda sha’awa ta habala, ta kan haifi zunubi: zunubi kuwa, sa’anda ya ƙasaita, ya kan fidda mutuwa.” (Yaƙub 1:14, 15) Alal misali, idan mutum yana da matsalar yin maye a dā, yana iya yanke shawarar cewa ba zai ajiye giya a gidansa ba. Don guje wa gwaji game da kishiyar jinsi, Kirista na iya canja inda yake aiki ko aikinsa.—Misalai 6:23-28.
22 Kada ka ɗauki matakin da zai kai ka ga yin zunubi. Yin kwarkwasa da kuma tunanin yin lalata za su iya kai ga zina ko kwartanci. Yin ƙananan ƙarya na iya ba mutum gaba gaɗin yin babbar ƙarya, wanda hakan na iya kai wa ga zunubin yin ƙarya. Yin ƙananan sata na iya kashe lamirin mutum har ya soma yin babbar sata. Mutum na iya amincewa da wani ƙaramin abu daga kalaman ’yan ridda, kuma hakan na iya sa mutum ya zama ɗan ridda.—Misalai 11:9; Ru’ya ta Yohanna 21:8.
Idan Ka Yi Zunubi Fa?
23, 24. Wane ƙarfafa ne za a iya samu a cikin 2 Labarbaru 6:29, 30; Misalai 28:13?
23 Mutane duka ajizai ne. (Mai-Wa’azi 7:20) Amma idan ka yi mugun laifi, kana iya samun ƙarfafa daga addu’ar da Sarki Sulemanu ya yi a wajen keɓe haikalin Jehobah. Sulemanu ya yi addu’a ga Allah: “Komi addu’a ko gado da kowa za ya yi, ko da dukan jama’arka Isra’ila za su yi, kowa yana ciki, ya kuwa miƙe hannuwansa yana fuskanta wannan gida; sai ka ji daga sama wurin zamanka, ka gafarta, ka sāka ma kowane mutum bisa ga dukan aikinsa, kana sane da zuciyassa; (gama kai, i, kai kaɗai ka san zukatan ’ya’yan mutane).”—2 Labarbaru 6:29, 30.
24 Hakika, Allah ya san zuciya kuma yana gafartawa. Misalai 28:13 ta ce: “Wanda ya rufe laifofinsa ba za ya yi albarka ba: Amma dukan wanda ya faɗa su ya kuwa rabu da su za ya sami jinƙai.” Ta wajen tuba da kuma furta zunubi, mutum zai iya samun tagomashin Allah. Duk da haka, idan ka raunana a ruhaniya, menene kuma zai iya taimaka maka ka kasance a cikin ƙaunar Allah?
Yaya Za Ka Amsa?
• Yaya za mu iya kasancewa a cikin ƙaunar Allah?
• Ta yaya ne ƙaunar Allah da Kristi suke taimaka mana mu ƙi tafarki na zunubi?
• Me ya sa ƙauna ga mutane zai hana mu yin lalata?
• Ta waɗanne hanyoyi ne za a guje wa yin lalata?
[Hoto a shafi na 3]
Yahuda ya nuna mana yadda za mu kasance a cikin ƙaunar Allah
[Hoto a shafi na 5]
Rabuwar aure na iya jawo wa abokin aure marar laifi da yaran baƙin ciki
[Hoto a shafi na 6]
Kamar Kaleb, ka ƙudurta cewa za ka “bi Ubangiji sarai”?
[Hoto a shafi na 7]
Ka ci gaba da yin addu’a a kowane lokaci don samun taimakon ƙin gwaji