Maganar Jehobah Rayayya Ce
Darussa Daga Littafin Mai-Wa’azi
AYUBA uban iyali ya ce: “Mutum, haihuwar mace kwanakinsa kaɗanna ne, cike da wahala kuma.” (Ayuba 14:1) Yana da muhimmanci kada mu ɓata rayuwarmu ta wurin damuwa da kuma yin ayyuka marasa amfani! Waɗanne irin abubuwa ne ya kamata mu biɗa da lokacinmu, kuzari da kuma dukiyarmu? Waɗanne ne ya kamata mu kauce wa? Kalmar hikima da ke cikin littafin Mai-Wa’zai na Littafi Mai Tsarki ta ba da tabbatacciyar shawara game da wannan batun. Saƙon da yake ciki yana da “hanzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta,” kuma zai iya taimaka mana mu yi rayuwa mai ma’ana.—Ibraniyawa 4:12.
Sarki Sulemanu na Isra’ila ta dā, wanda ya yi suna wajen nuna hikima ne ya rubuta littafin Mai-Wa’azi, littafin yana ɗauke da shawara game da abin da ke da amfani da kuma marar amfani a rayuwa. Tun da yake Sulemanu ya ambata wasu gine ginen da ya yi, ya rubuta littafin Mai-Wa’azi bayan da ya gama ginin ne, kuma kafin ya bijire wa bauta ta gaskiya. (Nehemiah 13:26) Shi ya sa aka ce ya kammala rubutun a shekara ta 1000 K.Z., a kusan ƙarshen Mulkinsa na shekara 40.
MENENE BA BANZA BA?
(Mai-Wa’azi 1:1–6:12)
Mai-wa’azi ya ce: “Dukan abu banza ne,” ya kuma yi tambaya: “Wace irin riba mutum ya samu daga cikin dukan aikinsa wanda ya ke aiki a ƙarƙashin rana?” (Mai-Wa’azi 1:2, 3) Sau da yawa an yi amfani da furcin nan “banza” da kuma “ƙarƙashin rana” a littafin Mai-Wa’azi. Kalmar nan “banza” a Helenanci tana nufin “lumfashi” ko “tiriri” ko kuma abubuwa marasa jimrewa. Furcin nan “ƙarƙashin rana” tana nufin “a duniya.” Hakika, duka abubuwan da mutane suke yi da bai yi daidai da nufin Allah ba, duk banza ne.
Sulemanu ya ce: “Lura da ƙafarka sa’anda ka tafi gidan Allah; gama zuwa garin ji ya fi.” (Mai-Wa’azi 5:1) Yin bauta ta gaskiya ta Jehobah Allah ba banza ba ne. Hakika, idan muka kula da dangantakarmu da shi, hakan zai sa mu yi rayuwa mai ma’ana.
Tambayoyin Nassi da aka Amsa:
1:4-10—Menene ke ‘gajiyarwa’ game da zagaya ta rayuwa? Mai wa’azi ya ce rana, iska, da kuma shirin da Allah ya yi don a yi ruwan sama a ko’ina a duniya, sune abubuwa uku na musamman da suke sa a rayu a duniya. Hakika, waɗannan zagayar ta rayuwa suna da yawa, kuma suna da wuyan fahimta. Mutum zai iya yin bincike har zuwa ƙarshen rayuwarsa, amma ba zai fahimce su sosai ba. Hakan kuwa zai iya ‘gajiyar’ da mutum. Ba zai yiwu ba mu kwatanta gajeren rayuwarmu da waɗannan zagayar marar ƙarewa ba. Ƙoƙarin gano wani sabon abu ma yana kawo gajiya. Ƙirƙiro sababbin abubuwa yin amfani ne da mizanan da Allah na gaskiya ya riga ya kafa kuma ya yi amfani da su a lokacin da yake halitta.
2:1, 2—Me ya sa aka ce dariya “hauka” ne? Dariya za ta iya taimaka mana mu mance da damuwarmu na ɗan lokaci, nishaɗi kuwa zai iya sauƙaƙa mana wahalar da muke fuskanta. Duk da haka, dariya ba ta cire mana wahala. Shi ya sa aka ce, neman farin cikin ta wurin yin dariya “hauka” ne.
3:11—Menene Allah ya sa ya yi “jamali a lokacinsa”? A cikin abubuwan da Allah ya sa suka yi “jamali” a lokacin da ya dace su ne halittar Adamu da Hauwa’u, alkawari ta wurin bakan gizo, alkawarinsa da Ibrahim, alkawarinsa da Dauda, zuwan Almasihu, da kuma lokacin da za a naɗa Yesu Kristi Sarki na Mulkin Allah. Amma, akwai wani abu da Jehobah zai sa ya yi “jamali” a nan gaba. Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa sabuwar duniya mai adalci za ta tabbata a lokacin da ya dace.—2 Bitrus 3:13.
5:9—Ta yaya ne “ribar ƙasa ta kowa ce”? Duka mutanen da ke cikin duniya suna dogara ga “ribar ƙasa,” wato, amfanin gona. Har da sarakuna. Su ma ana yi masu noma.
Darussa Dominmu:
1:15. Ba shi da amfani mutum ya ɓata lokacinsa da kuzari don ya daidaita zalunci da rashin gaskiya da muke gani a yau. Saboda Mulkin Allah ne kawai zai kawar da mugunta.—Daniel 2:44.
2:4-11. Yin zanen gida, yin lambu, kaɗe-kaɗe, da kuma holewa, duk “cin iska” ne, saboda ba za su iya kawo mana farin ciki na dindindin ba.
2:12-16. Hikima ta fi wauta muhimmanci, saboda tana taimaka wa wajen warware wasu matsaloli. Amma game da mutuwa, hikimar mutum ba ta da amfani. Ko idan mutum ya yi suna saboda hikimar da yake da shi, a nan gaba za a manta da shi.
2:24; 3:12, 13, 22. Ba laifi ba ne idan mutum ya ci moriyar aikin da yake yi.
2:26. Allah yana ba da hikima da ke kawo farin ciki ga ‘wanda yake ƙauna.’ Ba zai yiwu mutum ya sami wannan hikimar idan ba shi da dangantaka mai kyau da Allah ba.
3:16,17. Ba zai yiwu a sami adalci a kowane yanayi ba. Maimakon mu yi alhini game da abubuwan da ke faruwa a duniya a yau, ya kamata mu dogara ga Jehobah wanda shi ne zai daidaita al’amura.
4:4. Aiki mai kyau na kawo gamsarwa. Aikin da mutum yake yi don ya fi wasu yana kawo gāsa, baƙin ciki da kishi. Shi ya sa ya kamata hidimarmu na Kirista ta kasance da manufa mai kyau.
4:7-12. Dangantaka tsakanin mutane ta fi abin duniya muhimmanci , saboda haka, kada mu daina dangantakarmu da mutane don neman arziki.
4:13. Matsayi da shekaru ba sa kawo daraja. Waɗanda suke da matsayi su kasance da hikima.
4:15,16. “Sarmayin, na biyu” wato, wanda ya gaji sarki, da farko zai samu goyon baya daga “waɗanda ya zama shugabansu,” amma “waɗanda za su zo daga baya ba za su yi murna da shi ba.” Hakika, yin suna abu ne da ba ya daɗewa.
5:2. Ya kamata addu’armu ta kasance mai ma’ana da kuma daraja, ba tare da amfani da kalamai masu yawa ba.
5:3-7. Damuwa da abubuwan duniya zai iya sa mutum ya soma sha’awarsu. Wannan kuwa yana iya sa mutum tunani cikin dare, wanda zai iya hana barci. Yawan maganganu kuma sukan sa mutum ya zama wawa a gaban mutane kuma sukan iya sa shi ya yi alkawari ga Allah ba tare da yin tunaninsa ba. ‘Jin tsoron Allah’ yakan kāre mu daga yin waɗannan abubuwa.
6:1-9. Menene amfanin arziki, suna, tsawon rai, da kuma iyali mai girma, idan yanayi bai bari mu ji daɗinsu ba? “Gwamma abin da ido ke gani, da a yi sha’awa barkatai,” na abin da mutum ba zai iya samu ba. Abin da ya fi muhimmanci a rayuwa shi ne, mutum ya sami “abinci da sutura,” sa’ad da yake jin daɗin rayuwarsa ya kuma kasance da dangantaka na kud da kud da Jehobah.—1 Timothawus 6:8.
SHAWARA GA MASU HIKIMA
(Mai-Wa’azi 7:1–12:8)
Ta yaya za mu kāre sunanmu? Menene ya kamata ya za ma ra’ayinmu game da masu mulki da kuma rashin adalci da za mu iya gani? Tun da yake matattu ba su san komi ba, yaya ya kamata mu yi amfani da rayuwarmu yanzu? Ta wace hanya ce ya kamata matasa su yi amfani da lokacinsu da kuma ƙarfinsu? Shawarar da mai-wa’azi ya bayar a kan waɗannan batutuwa suna rubuce a littafin Mai-Wa’azi surori 7 zuwa 12.
Tambayoyin Nassi da aka Amsa:
7:19—Ta yaya ne hikima ta fi “masu mulki goma”? Idan aka yi amfani da wannan furcin a alamance a cikin Littafi Mai Tsarki, goma na nufin abin da ya cika. Sulemanu yana nufin cewa muhimmancin hikima ta fi na cikakkun adadin mayaka masu tsaron birni.
10:2—Menene ake nufi idan aka ce zuciyar mutum tana ‘hannunsa na dama’ ko kuma ‘hannunsa na hagu’? Tun da yake a kowane lokaci hannun dama tana nufin yin abubuwa masu kyau, zuciyar mutum a hannun dama tana nufin cewa zuciyarsa ta motsa shi ya yi abu mai kyau. Amma idan ta motsa shi ya yi abu marar kyau, ana cewa zuciyarsa tana hannunsa na hagu.
10:15—Ta yaya ne ‘aikin wawaye yakan gajiyadda su’? Idan mutum ba shi da tunanin kirki, ayyukansa ba za su yi kyau ba. Ba zai kuwa gamsu da aikinsa ba. Irin wannan aikin yakan sa mutum ya gaji.
11:7, 8—Menene ma’anar wannan furcin: “Haske yana da daɗi; abu mai-daɗi kuma ga ido shi dubi rana.” Haske da rana suna sa mu ji daɗin rayuwa. Sulemanu yana nufin cewa abin farin ciki ne muna da rai, saboda haka, mu ‘ji daɗi’ kafin tsufa ta ɗauke ƙarfinmu.
11:10—Ta yaya ne “ƙuruciya da zaman mutum” duk banza ne? Idan ba a yi amfani da su yadda ya kamata ba, dukansu ba su da amfani, saboda kamar raɓa, ƙuruciya tana wucewa da sauri.
Darussa Dominmu:
7:6. Dariya a lokacin da bai kamata ba tana sa mutum ya ji haushi, kuma ba ta da amfani kamar ƙarar icen ƙaya da ke ƙonewa a ƙarƙashin tukunya. Ya kamata mu guji irin wannan dariyar.
7:21,22. Kada mu damu da abin da wasu suka faɗa game da mu.
8:2, 3;10:4. Idan shugaban aikinmu ya zarge mu ko kuma ya yi mana gyara, zai yi kyau mu natsu. Hakan ya fi da mu ce za mu bar aikin don haushi.
8:8; 9:5-10,12. Muna iya mutuwa babu zato ba tsammani kamar kifayen da a kan kama da taru, ko kuma tsuntsayen da a kan kama da tarko. Bugu da ƙari, babu mutumin da zai iya hana mutuwa, ko kuma ya guje wa mutuwa. Saboda haka, kada mu lalata rayuwarmu. Jehobah yana son mu daraja rai kuma mu more rayuwa a hanya mai kyau. Ya kamata mu sa hidimar Jehobah ta zama na farko a rayuwarmu.
8:16,17. Ko da mun hana kanmu yin barci don bincike, ba za mu iya fahimtar duka abubuwan da Allah ya yi da kuma abubuwan da ya bari su faru ba. Idan muka damu da abubuwan da suke faruwa, za su hana mu jin daɗin rayuwarmu.
9:16-18. Ya kamata a daraja hikima, har ma a wurin da ba a ɗauke ta da muhimmanci ba. Maganar da mai hikima yake yi cikin natsuwa ta fi ihun wawa.
10:1. Ya kamata mu kula da maganarmu da kuma halinmu. Shaye-shaye, hasala, da kuma jima’i, za su iya lalata suna mai kyau da mutum ke da shi.
10:5-11. Kada a yi kishin mutumin da bai ƙware ba a wurin aiki. Idan mutum ya kasa yin aikin da aka ba shi, hakan na iya kawo mugun sakamako. Maimakon haka, ‘nuna hikima’ yana da muhimmanci. Yana da muhimmanci sosai idan muka ƙware a aikin yin wa’azin Mulki da almajirantarwa!
11:1, 2. Mu kasance masu bayarwa da zuciya ɗaya. Domin hakan na jawo karimci.—Luka 6:38.
11:3-6. Kada mu bari rashin tabbaci na rayuwa su hana mu tsai da shawara.
11:9; 12:1-7. Matasa za su ba da amsa ga Jehobah. Saboda haka, ya kamata su yi amfani da lokacinsu da kuma kuzarinsu a hidimar Allah kafin tsufa ta ɗauke ƙarfinsu.
“KALMAR MASU HIKIMA” DA ZA SU YI MANA JA-GORA
(Mai-Wa’azi 12:9-14)
Yaya ya kamata mu ɗauki “magana masu daɗin ji” da mai-wa’azi ya nema kuma ya rubuta? Dabam da “littatafai” waɗanda suke ɗauke da hikimar mutane, “Kalmomi masu-hikima kamar ƙirmi su ke; zantattukan da a ke tattarawa kuma kamar kafaffun ƙusoshi ne, daga bakin makiyayi ɗaya su ke fitowa.” (Mai-Wa’azi 12:10-12) Kalmomi masu hikima da “makiyayi ɗaya,” Jehobah yake furtawa, suna da muhimmanci a rayuwarmu.
Idan muka yi amfani da shawarar da ke cikin littafin Mai-Wa’azi, za su taimake mu mu yi rayuwa mai ma’ana kuma mu ji daɗin rayuwarmu. Bugu da ƙari, an tabbatar mana cewa: “Waɗanda ke tsoron Allah za su zama lafiya.” Bari mu manne wa ƙudurinmu na ‘jin tsoron Allah, mu kiyaye dokokinsa; gama wannan kaɗai ne wajibin mutum.’—Mai-Wa’azi 8:12; 12:13.