Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 8/1 pp. 3-7
  • Ka Yi Zunubi Ga Ruhu Mai Tsarki ne?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Zunubi Ga Ruhu Mai Tsarki ne?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yana Gafartawa Idan Aka Tuba
  • Sun Yi wa Ruhu Zunubi
  • Ba su Yi wa Ruhu Zunubi Ba
  • Ka Rage Damuwar Cewa Ka Yi Zunubi
  • Mene ne Zunubin da Ba A Gafartawa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ka Amfana Daga Yadda Jehobah Yake Gafarta Mana?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Yi Na’am Da Horon Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 8/1 pp. 3-7

Ka Yi Zunubi Ga Ruhu Mai Tsarki ne?

“Akwai zunubi wanda ya kai ga mutuwa.”—1 YOHANNA 5:16.

1, 2. Ta yaya muka san cewa zai yiwu a yi wa ruhu mai tsarki na Allah zunubi?

“NA DAMU da tunanin cewa na riga na yi wa ruhu mai tsarki zunubi.” Haka wata mata da take zaune a Jamus ta rubuta, ko da yake tana bauta wa Allah. Kirista zai iya yi wa ruhu mai tsarki na Allah, ko ikon aiki zunubi ne?

2 Hakika, zai yiwu a yi wa ruhu mai tsarki na Jehobah zunubi. “Kowane zunubi ko saɓo za a gafarta ma mutane su,” in ji Yesu Kristi, “amma saɓon da a ke yi a kan Ruhun ba za a yi gafarassa ba.” (Matta 12:31) An yi mana gargaɗi: “Idan muna yin zunubi da nufin zuciyarmu bayanda mun karɓi sanin gaskiya, babu sauran wata hadaya domin zunubai, sai sauraro mai-ban tsoro ga shari’a.” (Ibraniyawa 10:26, 27) Kuma manzo Yohanna ya rubuta: “Akwai zunubi wanda ya kai ga mutuwa.” (1 Yohanna 5:16) Amma, wanda ya yi mugun zunubi ne zai yi zaton ko ya yi “zunubi wanda ya kai ga mutuwa”?

Yana Gafartawa Idan Aka Tuba

3. Idan muka nuna damuwa sosai domin zunubin da muka yi, menene hakan ke nunawa?

3 Jehobah ne Mai Shari’a na ƙarshe na masu zunubi. Hakika, dukanmu za mu ba shi lissafin abin da muka yi, kuma yana yin abin da ya dace a kowane lokaci. (Farawa 18:25; Romawa 14:12) Jehobah ne zai yanke shawarar ko mun yi zunubin da ba zai gafarta ba, kuma yana iya janye ruhunsa daga gare mu. (Zabura 51:11) Amma, idan muka nuna damuwa sosai game da zunubin da muka yi, ƙila mun tuba da gaske ke nan. Amma, menene tuba na gaskiya?

4. (a) Menene tuba ke nufi? (b) Menene ke da ban ƙarfafa a Zabura 103:10-14?

4 Tuba na nufin mu canja halinmu game da zunubin da muka yi ko muke shirin yi. Yana nufin mun yi baƙin ciki sosai ko da na sani kuma mun bar tafarkin zunubin. Idan muka yi mugun zunubi kuma muka ɗauki matakan da suka dace da suka nuna cewa mun tuba da gaske, muna iya samun ƙarfafa daga kalaman mai zabura: “[Jehobah] ba ya aika mamu gwalgwadon zunubanmu ba, Ba ya sāka mamu gwalgwadon laifofinmu ba. Gama kamar yadda sama ta yi nisa birbishin duniya, Hakanan kuma jinƙansa yana da girma zuwa ga masu-tsoronsa. Kamar nisan gabas da yamma, hakanan ya kawar da saɓe saɓenmu, ya nisantadda su. Kamar yadda uba ya kan yi juyayin ’ya’yansa, hakanan Ubangiji yana juyayin masu-tsoronsa. Gama ya san tabi’ammu; Ya kan tuna mu turɓaya ne.”—Zabura 103:10-14.

5, 6. Ka faɗi ainihin bayanin da ke 1 Yohanna 3:19-22, kuma ka bayyana ma’anar kalaman manzon.

5 Wani abin ban ƙarfafa shi ne kalaman manzo Yohanna: “Saboda wannan za mu sani muna wajen gaskiya, mu rinjayi zuciyarmu a gabansa kuma, dukan inda zuciyarmu ta kashe mu; gama Allah ya fi zuciyarmu girma, ya kuwa san abu duka. Masoya, idan zuciyarmu ba ta kāshe mu ba, gaba gaɗi mu ke gaban Allah; dukan iyakar abin da mu ke roƙa kuma, muna karɓa daga wurinsa, domin muna kiyaye dokokinsa, muna yin abubuwa da sun gamshe shi.”—1 Yohanna 3:19-22.

6 Mun san “muna wajen gaskiya” domin muna ƙaunar ’yan’uwanmu kuma ba ma zunubi. (Zabura 119:11) Idan muna damuwa sosai domin wasu dalilai, ya kamata mu tuna cewa “Allah ya fi zuciyarmu girma, ya kuwa san abu duka.” Jehobah yana nuna mana tagomashi domin ya san “sahihiyar ƙauna ta ’yan’uwa” da muke nunawa, yaƙin da muke yi da zunubi, da kuma ƙoƙarin da muke yi na yin nufinsa. (1 Bitrus 1:22) Zuciyarmu ba za ta “kashe mu” ba idan muka gaskata da Jehobah, muka nuna ƙauna ga ’yan’uwa, kuma ba mu yi zunubi da sane ba. Za mu kasance da ‘gaba gaɗi a gaban Allah’ a addu’a, kuma zai ji mu domin mun bi dokokinsa.

Sun Yi wa Ruhu Zunubi

7. Menene zai nuna cewa zunubin da mutum ya yi wanda za a gafarta ne ko a’a?

7 Waɗanne zunubai ne ba a gafartawa? Don a amsa wannan tambayar, bari mu tattauna wasu misalai da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Ya kamata wannan ya ƙarfafa mu idan muka tuba amma muna baƙin ciki domin mugun zunubin da muka yi. Za mu ga cewa ba irin zunubin da mutum ya yi ba ne ainihin batun; amma, muradinsa, yanayin zuciyarsa, da kuma son ransa ne zai nuna ko zunubin irin wanda za a gafarta ne ko a’a.

8. Ta yaya ne wasu shugabannin addinai a ƙarni na farko suka yi zunubi ga ruhu mai tsarki?

8 Shugabannin addinan Yahudawa na ƙarni na farko da ke hamayya da Yesu Kristi sun yi wa ruhu mai tsarki zunubi. Sun ga cewa Yesu yana da ruhu mai tsarki sa’ad da yake yin mu’ujizai da ke ɗaukaka Jehobah. Duk da haka, waɗannan maƙiyan Kristi sun ce ya samo ikonsa ne daga Shaiɗan Iblis. In ji Yesu, waɗanda suka saɓa wa ruhu mai tsarki na Allah suna zunubi ne da ba za a gafarta ba a “wannan zamani, ko cikin zamani mai-zuwa.”—Matta 12:32.

9. Menene saɓo, kuma menene Yesu ya ce game da shi?

9 Saɓo na nufin ɓata suna ko baƙar magana. Tun da yake Allah ne Tushen ruhu mai tsarki, faɗin abubuwan da ba su dace ba game da ruhunsa, daidai ne da faɗin abin da bai dace ba game da Jehobah. Ci gaba da yin irin wannan furcin zunubi ne da ba a gafartawa. Abin da Yesu ya faɗa game da irin wannan zunubin ya nuna cewa Yesu yana nuni ne ga waɗanda suke hamayya da ikon ruhu mai tsarki na Allah da sane. Domin Yesu yana da ruhun Jehobah ne ya sa waɗanda suke hamayya da shi suka ce ruhun na Iblis ne, saboda haka, sun yi saɓo ga ruhu. Shi ya sa Yesu ya ce: “Dukan wanda za ya yi saɓon Ruhu Mai-tsarki ba shi da gafara har abada, amma shi mai-laifin zunubi mara-matuƙa ne.”—Markus 3:20-29.

10. Me ya sa Yesu ya kira Yahuda “ɗan lalacewa”?

10 Yi la’akari kuma da batun Yahuda Iskariyoti. Ya bi tafarki na rashin aminci, yana satan kuɗi daga akwatin da aka ba shi ya ajiye. (Yohanna 12:5, 6) Daga baya, Yahuda ya je ya sami shugabannin Yahudawa kuma ya shirya ya ci amanar Yesu a kan zinari 30. Ko da yake Yahuda ya yi da na sani bayan ya ci amanar Yesu, bai tuba ba daga zunubin da ya yi da sane. Saboda haka, Yahuda bai cancanci tashi daga matattu ba. Shi ya sa Yesu ya kira shi “ɗan lalacewa.”—Yohanna 17:12; Matta 26:14-16.

Ba su Yi wa Ruhu Zunubi Ba

11-13. Ta yaya ne Sarki Dauda ya yi zunubi da Bath-sheba, kuma wane ƙarfafa ne za a iya samu daga yadda Allah ya bi da su?

11 A wasu lokatai, Kiristocin da suka faɗi mugun zunubin da suka yi kuma suka sami taimako na ruhaniya daga dattawa Kiristoci, suna iya ci gaba da yin baƙin ciki domin taka dokar Allah da suka yi a dā. (Yaƙub 5:14) Idan muna damuwa a wannan hanyar, babu shakka za mu amfana daga tattauna abubuwan da Nassosi suka ce game da waɗanda aka gafarta wa zunubansu.

12 Sarki Dauda ya yi mugun zunubi da Bath-sheba, matar Uriah. Da ya hangi wannan matar kyakkyawa tana wanka daga inda yake tsaye a saman gidansa, Dauda ya sa aka kawo ta fādarsa kuma ya yi lalata da ita. Bayan ya ji cewa ta yi ciki, ya yi ƙulli don maigidanta, Uriah, ya kwana da ita don hakan ya rufe asirin lalatar da ya yi. Da ya ga cewa ƙullin bai yiwu ba, sarkin ya sa a kashe Uriah a fagen yaƙi. Bayan haka, Bath-sheba ta zama matar Dauda kuma ta haifar masa ɗa wanda ya mutu.—2 Samuila 11:1-27.

13 Jehobah ne ya shari’anta Dauda da Bath-sheba. Allah ya gafarta wa Dauda, wataƙila domin ya tuba da kuma domin alkawarin Mulki da aka yi da shi. (2 Samuila 7:11-16; 12:7-14) Babu shakka, Bath-sheba ta tuba, domin ta sami gatar zama uwar Sarki Sulemanu da kuma kakar Yesu Kristi. (Matta 1:1, 6, 16) Idan muka yi zunubi, yana da kyau mu tuna cewa Jehobah yana lura da halinmu na tuba.

14. Ta yaya aka kwatanta yawan gafartawar Allah a batun Sarki Manassa?

14 An kwatanta yawan gafartawar Jehobah a batun Sarki Manassa na Yahudiya. Ya yi abin da ba shi da kyau a gaban Jehobah. Manassa ya kafa bagadai wa Baal, ya bauta wa “dukan rundunar sama,” kuma ya gina bagadai wa allolin ƙarya a cikin farfajiya biyu na haikali. Ya sa ’ya’yansa su ratsa ta tsakiyar wuta, ya ƙarfafa yin sihiri, kuma ya sa mazauna Yahuda da Urushalima “su yi saɓo, har mugunta da suka yi ta fi ta al’ummai waɗanda Ubangiji ya hallaka a gaban ’ya’yan Isra’ila.” Ya ƙi bin gargaɗin da annabawan Allah suka yi. Daga baya, sarkin Assuriya ya kai Manassa bauta. A lokacin da yake bauta, Manassa ya tuba kuma ya ci gaba da yin addu’a ga Allah cikin tawali’u, Allah ya gafarta masa kuma ya mai da shi kan sarautarsa a Urushalima, a inda ya ɗaukaka bauta ta gaskiya.—2 Labarbaru 33:2-17.

15. Wane aukuwa a rayuwar manzo Bitrus ne ya nuna cewa Jehobah yana gafartawa “a yalwace”?

15 Ƙarnuka bayan haka, manzo Bitrus ya yi mugun zunubi ta wajen musanta Yesu. (Markus 14:30, 66-72) Amma, Jehobah ya gafarta wa Bitrus “a yalwace.” (Ishaya 55:7) Me ya sa? Domin Bitrus ya tuba da gaske. (Luka 22:62) Cikakkiyar alamar gafartawar Allah ta bayyana kwana 50 bayan haka a ranar Fentikos, Bitrus ya sami gatar ba da shaida mai ƙarfi game da Yesu. (Ayyukan Manzanni 2:14-36) Babu wani dalilin da zai sa kada mu yarda cewa Allah zai gafarta wa Kiristocin da suka tuba da gaske a yau. “Idan kai, ya Ubangiji, za ka ƙididdiga laifofi, wa za ya tsaya, ya Ubangiji?” mai zabura ya raira, “amma akwai gafara a wurinka.”—Zabura 130:3, 4.

Ka Rage Damuwar Cewa Ka Yi Zunubi

16. Menene za mu yi kafin Allah ya gafarta mana zunubinmu?

16 Waɗannan misalan da aka ambata ya kamata su taimaka mana mu rage damuwa game da ƙila mun yi wa ruhu mai tsarki zunubi. Sun nuna cewa Jehobah yana gafarta wa masu zunubi da suka tuba. Abu mafi muhimmanci shi ne yin addu’a ga Allah. Idan mun riga mun yi zunubi, muna iya neman gafara bisa hadayar fansa ta Yesu, tagomashin Jehobah, ajizancin da muka gada, da kuma hidimar aminci da muka yi. Sanin alherin Jehobah, zai iya sa mu nemi gafara da tabbacin cewa zai gafarta mana.—Afisawa 1:7.

17. Menene muke bukatar mu yi idan muka yi zunubi kuma muna bukatar taimako na ruhaniya?

17 Idan mun riga mun yi zunubi, kuma mun kasa yin addu’a domin zunubinmu ya sa mun raunana a ruhaniya fa? Game da wannan, almajiri Yaƙub ya rubuta: “[Mutumin ya] kira dattiɓan ikilisiya su yi addu’a a bisansa, suna shafe shi da mai cikin sunan Ubangiji: addu’ar bangaskiya kuwa za ta ceci mai-ciwo, Ubangiji kuwa za ya tashe shi; idan kuma ya yi zunubai, za a gafarta masa.”—Yaƙub 5:14, 15.

18. Me ya sa za a iya gafarta wa mutum ko da an kore shi daga cikin ikilisiya?

18 Idan wanda ya yi zunubi ya ƙi ya tuba kuma aka kore shi daga cikin ikilisiya, hakan ba ya nufin cewa ba za a iya gafarta masa zunubinsa ba. Game da wani shafaffe da ya yi zunubi kuma aka yi masa yankan zumunci a Koranti, Bulus ya rubuta: “Ga irin wannan mutum, hukuncin da aka yi ta bakin mutane dayawa ya isa; gwamma fa ku gafarta masa, ku yi masa ta’aziya kuwa, kada ya zama da ko ƙaƙa irin wannan shi dulmaya domin yawan baƙincikinsa.” (2 Korinthiyawa 2:6-8; 1 Korinthiyawa 5:1-5) Domin su daidaita dangantakarsu da Jehobah, waɗanda suka yi zunubi suna bukatar su yi na’am da taimako na ruhaniya daga dattawa Kiristoci kuma su nuna alamar tuba ta gaskiya. Dole ne su yi abubuwan da zai nuna ‘tubansu.’—Luka 3:8.

19. Menene zai taimaka mana mu kasance “sahihai cikin bangaskiya”?

19 Menene kuma wani abin da zai iya sa mu yi tunanin cewa mun yi wa ruhu mai tsarki zunubi? Yawan damuwa ko kuwa rashin lafiya na iya sa haka. A irin wannan yanayin, addu’a da ƙarin hutu na iya taimakawa. Musamman kada mu yarda Shaiɗan ya jawo mana sanyin gwiwa, domin mu daina bauta wa Allah. Tun da yake Jehobah ba ya son mutuwar mugu, ba ya son ya yi rashin wani daga cikin bayinsa. Saboda haka, idan muna tsoron cewa mun yi wa ruhu zunubi, mu ci gaba da karanta Kalmar Allah, har da irin wuraren nan masu ƙarfafawa kamar Zabura. Muna bukatar mu ci gaba da halartar taron ikilisiya da kuma yin aikin wa’azin Mulki. Yin haka zai taimaka mana mu zama “sahihai cikin bangaskiya” kuma mu daina damuwa ko ƙila mun yi zunubin da ba za a gafarta ba.—Titus 2:2.

20. Wane irin tunani ne zai taimaka wa mutum ya ga cewa bai yi zunubi ga ruhu mai tsarki ba?

20 Duk wani wanda yake tsoron cewa ya yi wa ruhu mai tsarki zunubi yana iya tambayar kansa: ‘Na yi saɓo ga ruhu mai tsarki? Na tuba da gaske daga zunubi na? Idan haka ne, na gaskata cewa Allah yana gafartawa? Ni ɗan ridda ne wanda ya ƙi haske na ruhaniya?’ Hakika, irin waɗannan mutanen za su fahimci cewa ba su yi saɓo ga ruhu mai tsarki na Allah ba, kuma ba su zama ’yan ridda ba. Sun tuba, kuma suna da bangaskiya a gafarar Jehobah. Idan haka ne, ba su yi zunubi ga ruhu mai tsarki na Jehobah ba.

21. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a talifi na gaba?

21 Albarka ne ƙwarai da gaske mu san cewa ba mu yi zunubi ga ruhu mai tsarki ba! Wasu abubuwa kuma da suka shafi wannan batun su ne tambayoyin da za mu tattauna a talifi na gaba. Alal misali, muna iya tambayar kanmu: ‘Ruhu mai tsarki na Allah yana yi mini ja-gora kuwa? Ina nuna alamar haka a rayuwata?’

Mecece Amsarka?

• Me ya sa za mu iya cewa zai yiwu a yi zunubi ga ruhu mai tsarki?

• Menene tuba ke nufi?

• Su waye ne suka yi zunubi ga ruhu sa’ad da Yesu yake duniya?

• Ta yaya za a iya sha kan damuwar yin zunubin da ba za a gafarta ba?

[Hoto a shafi na 4]

Waɗanda suka ce Yesu ya yi mu’ujizai da ikon Shaiɗan sun yi zunubi ga ruhu mai tsarki na Allah

[Hoto a shafi na 5]

Ko da yake ya musanta Yesu, Bitrus bai yi zunubin da ba za a gafarta ba

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba