Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 11/1 pp. 2-4
  • Duniya Marar Adalci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Duniya Marar Adalci
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Hakan Mugun Lokaci Yakan Auko Farat Ɗaya’
  • Haka Zai Riƙa Faruwa?
  • Da Wanda Zai iya Canja Duniya Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Yadda Za Ka Yi Nasara Sosai A Rayuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Me Ya Sa Mutane Suke yin Miyagun Abubuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Shi Misali Mai Kyau Ne A Gare Ka Ko Kuma Kashedi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 11/1 pp. 2-4

Duniya Marar Adalci

KA YARDA cewa muna raye ne a duniya marar adalci? Babu shakka ka yarda da haka. Hakikanin gaskiya shi ne ko yaya ƙwarewarmu, ko yaya muka tsara rayuwarmu cikin hikima, a ƙarshe ba mu da tabbacin samun dukiya ko nasara ko ma abinci. Sau da yawa yakan kasance kamar yadda Sarki Sulemanu ya ce: “Ba kullum mai hikima ne da abinci ba, ba kullum mai basira ne ke da wadata ba, ba kullum gwani ne ke samun tagomashi ba.” Me ya sa? Sulemanu ya amsa, “sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.”—Mai Hadishi 9:11.

‘Hakan Mugun Lokaci Yakan Auko Farat Ɗaya’

Hakika, “sa’a da tsautsayi” sau da yawa suna kasancewa ne a wurin da bai dace ba, da kuma lokacin da bai dace ba, sau da yawa yana wargaje mana abin da muka tsara cikin hikima da kuma abin da muka sa rai a kai. Sulemanu ya ce, muna kama ne da “kifayen da akan kama da taru, kamar kuma tsuntsayen da akan kama da tarko, hakanan mugun lokaci yakan auko . . . farat ɗaya.” (Mai Hadishi 9:12) Alal misali, miliyoyin mutane, suna aiki tuƙuru su yi noma domin samun abinci ga iyalansu, sai kawai “mugun lokaci” ya faɗa musu, sa’ad da ruwan sama ya yanke, fari ya halaka gonakinsu.

Wasu suna ƙoƙari su yi taimako, amma taimako ma da duniya take yi wa waɗanda “mugun lokaci” ya auko musu sau da yawa sai ya kasance marar adalci. Alal misali, wajen kokawa da yunwa a shekarun baya bayan nan, taimako da aka ba wa “dukan nahiyar [Afirka] kashi ɗaya ne kawai cikin biyar na kuɗaɗen da aka ware domin yaƙin arabiya,” in ji wata ma’aikatar ba da agaji. Adalci ne a ce kuɗaɗe da aka kashe wajen yaƙi da wata ƙasa sun ninka waɗanda aka kashe wajen taimakon dukan nahiya sau biyar? Adalci ne a ce mutane da yawa suna da wadata amma a ce mutum ɗaya cikin huɗu a duniya yana cikin matsanancin talauci ko kuma yara miliyoyi suna mutuwa kowace shekara daga cututtuka da za a iya kāre su? Hakika rashin adalci ne!

Hakika sa’ad da “mugun lokaci” ya auko ya ƙunshi fiye da “sa’a da tsautsayi.” Yanayi kuma da suka fi ƙarfinmu su ma suna mamaye rayuwarmu suna sarrafa abin da yake faruwa da mu. Hakan ya faru a garin Beslan, Alaniya, a lokacin kaka na shekara ta 2004, sa’ad da faɗa ta ɓarke tsakanin ’yan ta’adda da ’yan tsaro kuma aka kashe ɗarurruwan mutane da yawancinsu yara ne a ranarsu ta farko a makaranta. Hakika, a irin wannan yanayi waɗanda suka rayu da waɗanda suka mutu ya dangana ne ga sa’a—amma abin da ya jawo irin wannan mugun lokaci hargitsi ne na mutane.

Haka Zai Riƙa Faruwa?

“Haka rayuwa take,” wasu suke cewa sa’ad da suke magana game da rashin adalci. “Tun dā ma haka take, kuma haka za ta riƙa faruwa.” In ji su, mai ƙarfi zai ci gaba da danne marar ƙarfi, mai arziki zai ci gaba da cutar matalauci. Hakan haɗe da “sa’a da tsautsayi,” za su ci gaba da shafar mutane, suka ce, muddin ɗan adam ya ci gaba da rayuwa.

Amma dole ne ya kasance haka? Zai taɓa yiwuwa kuma a ce waɗanda suka yi amfani da iyawarsu da basirarsu cikin hikima su sami ladar ƙoƙarinsu? Da wanda zai yi wani abu kuma ya kawo ƙarshen wannan matsalar dindindin? Ka bincika abin da talifi na gaba zai ce game da wannan.

[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 2]

BANGO: Mutum da yaro: UN PHOTO 148426/McCurry/Stockbower

[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 3]

MAXIM MARMUR/AFP/Getty Images

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba