Yadda Za Ka Yi Nasara Sosai A Rayuwa
“Za ka sa hanyarka ta yi albarka, . . . kuma za ka yi nasara.” —JOSH. 1:8.
MECE CE AMSARKA?
A waɗanne hanyoyi ne Sulemanu ya yi nasara?
A waɗanne hanyoyi ne Bulus ya yi nasara sosai a rayuwa?
Ta yaya za ka yi nasara da gaske?
1, 2. (a) Yaya mutane da yawa suke ɗaukan nasara? (b) Mene ne zai taimake ka ka san ra’ayinka game da wanda ya yi nasara?
MENE NE yake nuna cewa mutum ya yi nasara a rayuwa? Idan ka yi wa mutane wannan tambayar, za ka ji amsoshi dabam-dabam. Alal misali, wasu suna ɗaukan cewa mutum ya yi nasara sosai a rayuwa idan yana da kuɗi ko sana’a mai kyau ko kuma ilimi. Wasu kuma sun ce, idan mutum yana son ya yi nasara, dole ne ya samu dangantaka mai kyau da iyalinsa da kuma dukan abokansa. Wasu bayin Jehobah suna iya zato cewa gatan da suke da shi a cikin ikilisiya ko abin da suke cim ma a wa’azi ne zai sa su yi nasara.
2 Amma, mene ne ra’ayinka? Kana ganin mece ce alamar cewa mutum mai nasara ne? Da farko, ka rubuta sunayen mutanen da kake zato cewa sun yi nasara a rayuwa kuma kana daraja su sosai. Sunan wane ne ka rubuta? Shin mawadaci ne ko kuwa shahararre ne sosai? Abin da ka rubuta zai iya bayyana abin da ya fi muhimmanci a rayuwarka. Abin da ka daraja zai iya shafan zaɓin da kake yi da maƙasudin da kake kafa wa kanka.—Luk 6:45.
3. (a) Mene ne aka umurci Joshua ya yi don ya yi nasara? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
3 Abin da ya fi muhimmanci a gare mu shi ne ra’ayin Jehobah game da nasara. Sai idan Jehobah ya ce mun yi nasara ne kawai za mu iya yin rayuwa ta har abada. Sa’ad da Jehobah ya ce wa Joshua ya ja-goranci Isra’ilawa zuwa Ƙasar Alkawari, ya gaya masa ya karanta littafin shari’a “dare da rana,” kuma ya bi dokar. Jehobah ya yi masa alkawari: “Za ka sa hanyarka ta yi albarka, da hakanan kuma za ka yi nasara.” (Josh. 1:7, 8) Kuma mun san cewa Joshua ya yi nasara. Mu kuma fa? Me zai taimaka mana mu san ko yadda muke ɗaukan nasara ya jitu da ra’ayin Jehobah? Don samun amsoshin waɗannan tambayoyin, za mu tattauna misalin maza biyu da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki.
SULEMANU YA YI NASARA KUWA?
4. Me ya sa Sulemanu ya yi nasara?
4 Sulemanu ya yi nasara sosai a hanyoyi da yawa. Me ya sa? Domin ya yi shekaru da yawa yana bauta wa Jehobah kuma ya sāka masa sosai. Akwai wani lokacin da Jehobah ya ce Sulemanu ya roƙi duk abin da yake so, sai ya ce Jehobah ya ba shi hikima don ya shar’anta Isra’ilawa. A sakamako, Jehobah ya ba shi hikima da kuma wadata. (Karanta 1 Sarakuna 3:10-14.) Hikimar Sulemanu ta ɗara na “dukan mutanen gabas, da dukan hikimar Masar.” Mutanen “dukan al’ummai na kewaye” sun san game da Sulemanu. (1 Sar. 4:30, 31) Sulemanu mai arziki ne sosai. Kowace shekara yana samun tan 25 na zinariya! (2 Laba. 9:13) Ya yi gine-gine masu kyau. Ya yi tarayya da kuma kasuwanci da wasu ƙasashe. Hakika, Sulemanu ya yi nasara sa’ad da ya kasance da aminci ga Allah.—2 Laba. 9:22-24.
5. Mene ne Sulemanu ya kammala game da yin nasara ta gaske?
5 Abin da Sulemanu ya rubuta a littafin Mai-Wa’azi ya nuna cewa yana da ra’ayin da ya dace game da yin nasara. Bai yi tunanin cewa yin nasara da farin ciki sun dangana ga samun arziki da kuma iko ba. Shi ya sa ya ce: “Na sani babu abin da ya fi masu, kamar su yi murna, su kāma aika nagarta dukan kwanakin ransu. Kowane mutum kuma shi ci, shi sha, shi ji daɗi cikin dukan aikinsa; wannan kyautar Allah ne.” (M. Wa. 3:12, 13) Sulemanu ya kuma fahimci cewa waɗannan abubuwa za su sa mutum farin ciki sosai, idan yana da dangantaka ta kud da kud da Allah. Ya ce: “To yanzu dai bari mu ji ƙarshen duk zancen da an rigaya an yi: Ka ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa; gama wannan kaɗai ne wajibin mutum.”—M. Wa. 12:13.
6. Mene ne misalin Sulemanu ya koya mana game da yin nasara?
6 Sulemanu ya ji tsoron Allah kuma ya yi masa biyayya. Littafi Mai Tsarki ya ce “yana ƙaunar Ubangiji, yana tafiya a cikin farillai na Dauda ubansa.” (1 Sar. 3:3) Hakan ya nuna cewa ya yi nasara sosai. Da taimakon Allah, Sulemanu ya gina haikali mai girma don bauta ta gaskiya kuma ya rubuta littattafai uku a cikin Littafi Mai Tsarki. Hakika, ba za mu iya yin abubuwan da Sulemanu ya cim ma ba. Duk da haka, misalinsa mai kyau ya koya mana yadda za mu yi nasara sosai. Alal misali, Allah ya hure Sulemanu ya rubuta cewa arziki da hikima da iko da kuma yin suna da mutane da yawa suke ɗauka da muhimmanci aikin banza ne. Waɗannan abubuwan ba su da amfani, duk ‘cin iska ne kawai.’ Masu son kuɗi ba sa gamsuwa. Kullum suna ƙoƙari su kāre abubuwan da suka tara. Amma, wata rana wasu za su gāji waɗannan abubuwan.—Karanta Mai-Wa’azi 2:8-11, 17; 5:10-12.
7, 8. Yaya Sulemanu ya yi rashin aminci, kuma da wane sakamako?
7 Sulemanu ya daina yin biyayya ga Jehobah sa’ad da ya tsufa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama ya zama, lokacin da Solomon ya tsufa, matansa suka juyar da zuciyatasa zuwa bin waɗansu alloli; zuciyatasa ba ta kamilta zuwa ga Ubangiji Allahnsa kamar zuciyar ubansa Dauda ba . . . Solomon kuwa ya yi abin da ke mugu a idanun Ubangiji.”—1 Sar. 11:4-6.
8 Jehobah bai yi farin ciki ba kuma ya gaya wa Sulemanu sakamakon rashin biyayyarsa, ya ce: “Tun da shi ke . . . ba ka kuwa kiyaye wa’adina da farillaina ba, waɗanda na umurce ka, hakika zan fizge maka mulkinka, in ba bawanka.” (1 Sar. 11:11) Sulemanu ya yi nasara sosai, amma a ƙarshe, ya sa Jehobah baƙin ciki domin bai ci gaba da kasancewa da aminci ba. Ya kamata kowanenmu ya tambayi kansa, ‘Zan yi amfani da darasin da na koya daga misalin Sulemanu don na yi nasara a rayuwa?’
YADDA ZA MU YI NASARA TA GASKE
9. Shin mutane sun ɗauki Bulus a matsayin mutumin da ya yi nasara? Ka bayyana.
9 Rayuwar manzo Bulus ta sha bambam da rayuwar Sarki Sulemanu. Bulus bai yi rayuwar jin daɗi a fada ba ko kuma ta ci da sha tare da sarakuna. Maimakon haka, akwai lokatan da Bulus yana samun ci da sha da kuma sutura da kyar. (2 Kor. 11:24-27) Sa’ad da ya amince da Yesu a matsayin Almasihu, Bulus ya rasa matsayin da yake da shi a addinin Yahudawa. Kuma, shugabanan wannan addinin sun tsane shi, kuma sun saka shi a fursuna. Bulus ya sha bulala da dūka da sanduna kuma an jejjefe shi da duwatsu. Bulus ya ce an zage shi da ’yan’uwansa, kuma an tsane su da kuma tsananta masa. Ya daɗa cewa: “An maishe mu kamar ƙazantar duniya, jibjin kome, har wa yau.”—1 Kor. 4:11-13.
10. Me ya sa mutane suke ganin cewa Bulus ya yi banza da zarafin da ya samu?
10 Sa’ad da Shawulu yake matashi, yana da zarafin cim ma abubuwa da yawa. Ya fito daga iyalin da ake ji da su. Kuma wani sanannen malami mai suna Gamaliel ne ya koyar da shi. Bulus daga baya ya rubuta: “A cikin addinin Yahudawa na wuce waɗansu tsararakina dayawa.” (Gal. 1:14) Ya iya Ibrananci da Helenanci sosai, kuma yana da ’yancin ’yan ƙasar Roma. Waɗannan abubuwa sun sa Bulus ya samu gata da ’yancin yin wasu abubuwa. Da a ce ya yi ƙoƙarin yin nasara a duniya, da wataƙila ya yi arziki da kuma suna sosai. Akasin haka, ya zaɓi tafarkin rayuwa da wasu mutane har ma da danginsa suke ganin wauta ne. Me ya sa?
11. Mene ne ya fi muhimmanci ga Bulus, kuma wane maƙasudi ne ya kafa? Me ya sa ya yi hakan?
11 Bulus ya ƙaunaci Jehobah kuma yana son ya samu amincewarsa, maimakon ya zama mai arziki ko kuma sananne. Sa’ad da Bulus ya koyi gaskiya sosai sai ya soma daraja abubuwa da yawancin mutane a duniya ba su damu da su ba. Waɗannan abubuwa sun haɗa da hadayar fansa ta Kristi da yin wa’azi da kuma begen yin rayuwa a sama. Bulus ya san cewa Shaiɗan ya ce zai iya sa ’yan Adam su daina bauta wa Allah. Kuma ya san cewa shi ma zai iya ƙaryata Shaiɗan. (Ayu. 1:9-11; 2:3-5) Bulus ya ƙudura niyya ya kasance da aminci ga Allah na gaskiya duk da gwaji da zai fuskanta. Yawancin mutane da suke son su yi nasara a duniya ba sa kafa wa kansa irin wannan maƙasudin.
12. Me ya sa kake dogara ga Allah?
12 Ka kafa irin wannan maƙasudin kuwa? Ko da ba shi da sauƙi mutum ya kasance da aminci, amma idan mun yi hakan, Jehobah zai yi farin ciki kuma zai albarkace mu. Wannan ne ke sa mutum ya yi nasara sosai. (Mis. 10:22) Za mu samu albarka yanzu da kuma nan gaba. (Karanta Markus 10:29, 30.) Saboda haka, muna da ƙwaƙƙwarar dalili na dogara ga Allah “wanda ke ba mu kome a yalwace mu ji daɗinsu,” maimakon mu dogara ga “wadata marar-tsayawa.” Mu ‘ajiye wa kanmu tushe mai-kyau domin lokaci mai-zuwa, da za mu ruski rai wanda ya ke hakikanin rai.’ (1 Tim. 6:17-19) Hakika, ko bayan shekaru da yawa, za mu iya kasance da tabbaci cewa mun yi nasara sosai a rayuwa!
INA DUKIYARKA TAKE?
13. Mene ne Yesu ya ce game da tara dukiya?
13 Yesu ya ce game da dukiya: “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa ke cinyewa, inda ɓarayi kuma ke fashi da sata: amma ku tara wa kanku dukiya cikin sama, inda asu da tsatsa ba su cinyewa, ɓarayi kuma ba su fasawa su yi sata: gama wurinda dukiyarka ta ke, can zuciyarka za ta kasance kuma.”—Mat. 6:19-21.
14. Me ya sa bai dace ba mutum ya tara dukiya a duniya?
14 Ba kuɗi ba ne kaɗai mutum ke tarawa ba. Abubuwan da mutane suke daraja su ne yin suna da kuma iko. Yesu ya faɗa abin da Sulemanu ya ce a littafin Mai-Wa’azi. Dukiya da aka tara a duniya ba ta daɗewa. Ana iya halaka su ko kuma su ɓace da ƙyiftawar ido. Wani shehun malami mai suna F. Dale Bruner ya ce, “Suna ba ya waye gari. Kome sunan da mutum ya yi a yau, za a manta da shi. Mutumin da mawadaci ne yau, zai iya zama talaka gobe. Domin Yesu yana ƙaunar ’yan Adam, shi ya sa ya yi musu gargaɗi a kan neman girma da ke saurin ɓacewa kuma ya bar mutum babu bege. A kowace rana, mutane da suka dogara ga kuɗi da kuma zama shahararru suna yin da-na-sani. Yesu ba ya son almajiransa su yi aikin banza.” Yawancin mutane za su yi na’am da abin da wannan marubucin ya ce. Amma, mutane nawa ne za su bi gargaɗin Yesu a rayuwarsu? Kai kuma fa, za ka bi gargaɗin Yesu a rayuwarka?
15. Wace irin nasara ce ya kamata mu yi ƙoƙari mu samu?
15 Wasu limaman addinai sun ce bai dace ba mutum ya yi ƙoƙari ya yi nasara. Amma, ba abin da Yesu yake nufi ba ke nan. Maimakon haka, yana gaya wa almajiransa su yi ƙoƙarin yin nasara da ta dace. Shi ya sa ya ƙarfafa su su tara wa kansu “dukiya a sama,” wadda za ta dawamma. Abin da ya kamata ya fi muhimmanci a gare mu shi ne yin nasara a gaban Jehobah. Hakika, maganar Yesu ta tuna mana cewa kowannenmu zai zaɓi tafarkin da zai bi a rayuwarsa. Gaskiyar ita ce, muna biɗan abin da ke cikin zuciyarmu ko kuma abin da ya fi muhimmanci a gare mu.
16. Wane tabbaci ne za mu kasance da shi?
16 Idan muka zaɓa mu faranta wa Jehobah rai, muna da tabbaci cewa zai ba mu dukan abubuwan da muke bukata. A wasu lokatai, muna iya rashin abin ci da sha kamar manzo Bulus. (1 Kor. 4:11) Amma, ya kamata mu bi shawarar Yesu: “Kada ku yi alhini fa, kuna cewa, Me za mu ci? ko kuwa, Me za mu sha? ko kuwa, Da minene za mu yi sutura? Gama waɗannan abubuwa duka al’ummai suna ta biɗa; gama Ubanku na sama ya sani kuna bukatar waɗannan abubuwa duka. Amma ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abubuwa duka fa za a ƙara maku su.”—Mat. 6:31-33.
YADDA ZA KA YI NASARA A WURIN ALLAH
17, 18. (a) Yin nasara ta gaske ya dangana ga mene ne? (b) Yin nasara bai dangana a kan mene ne ba?
17 Ya kamata mu tuna cewa, nasara ta gaske ba ta dangana ga yawan abubuwan da muka cim ma ba ko kuma suna da muka yi a wannan duniya. Nasara ta gaske ba ta dangana ga gatar da muke da shi a cikin ikilisiya ba. Muna iya samun irin wannan albarka domin mun yi biyayya ga Allah kuma mun kasance da aminci a gare shi. Allah ya gaya mana: “Abin da a ke nema ga wakilai, [shi ne] a iske mutum da aminci.” (1 Kor. 4:2) Kuma ya wajaba mu ci gaba da kasancewa da aminci. Yesu ya ce: “Wanda ya jimre har matuƙa, shi ne za ya tsira.” (Mat. 10:22) Idan mun samu ceto domin mun kasance da aminci, hakan zai nuna cewa mun yi nasara da gaske.
18 Nasara ta gaske ya dangana ga kasancewa da aminci ga Allah, kuma kowannenmu zai iya kasancewa da aminci a gare shi ko da wane irin yanayi muke ciki. Amincinmu bai dangana ga suna ko ilimi ko kuma kuɗin da muke da shi ba, bai kuwa dangana ga basira ko iyawarmu ba. A ƙarni na farko, wasu cikin masu bauta wa Allah mawadata ne wasu kuma talakawa ne. Bulus ya gaya wa Kiristoci masu arziki cewa “su yi alheri, su zama mawadata cikin kyawawan ayyuka, su kasance da niyar babbayaswa, masu-son zumunta.” Mawadata da talakawa za su iya samun “rai wanda ya ke hakikanin rai.” (1 Tim. 6:17-19) Hakan yake a yau ma. Dukanmu muna da zarafi da gata na kasancewa da aminci da kuma “yin alheri.” Idan muka yi hakan, za mu yi nasara a gaban Mahaliccinmu kuma mu yi farin cikin sanin cewa muna faranta masa rai.—Mis. 27:11.
19. Mene ne ka ƙudura niyyar yi a batun yin nasara?
19 Ba za mu iya canja yadda duniya take ɗaukanmu ba, amma muna iya canja yadda muke ɗaukan yanayinmu. Ka yi ƙoƙari ka kasance da aminci duk da yanayi da kake ciki. Yin hakan kwalliya ce da take biyan kuɗin sabulu. Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace ka a yanzu da kuma har abada. Kada ka manta da abin da Yesu ya gaya wa Kiristoci shafaffu: “Ka yi aminci har mutuwa, ni ma in ba ka rawanin rai.” (R. Yoh. 2:10) Wannan ita ce nasara ta gaske!
[Hoto a shafi na 6]
Mutane da yawa suna ganin Shawulu zai yi nasara a duniya
[Hoto a shafi na 7]
Bulus ya yi nasara da gaske