Me Ya Sa Mutane Suke yin Miyagun Abubuwa?
ABU ɗaya da mutane kalilan ba za su iya musanta ba shi ne cewa: Dukanmu ajizai ne kuma saboda haka muna yin kuskure muna kuma yin abubuwa da daga baya mu yi da-na-sani. Ko da hakan gaskiya ne, dalilin da ya sa miyagun ayyuka manya ko kuma ƙanana, da muke gani ko ji kusan kullum, a zahiri ko daga kafofin yaɗa labarai suke faruwa kuwa?
Duk da ajizanci ’yan Adam, mutane gabaki ɗaya sun amince cewa akwai ɗabi’o’i da bai kamata mu karya su ba kuma ’yan Adam za su iya ƙin yin miyagun ayyuka. Yawancin mutane kuma za su amince cewa akwai bambanci tsakanin faɗin abu da ba daidai ba da kuma yin tsegumi kai tsaye, da kuma jawo wa wani rauni ba da gangan ba da kuma yin kisa da gangan. Sau da yawa, mutanen da ba a yi tsammani ba ne suke aikata abubuwa masu ban tsoro. Me ya sa mutane suke yin miyagun abubuwa?
Littafi Mai Tsarki ya ba da ƙarin haske a kan wannan batun. Ya shaida dalilai na musamman da suke sa mutane su yi abubuwan da suka san cewa ba su da kyau. Ka yi la’akari da abin da ya ce.
▪ “Zalunci ya kan maida mai-hikima wawa.”—MAI-WA’AZI 7:7.
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a wasu lokatai, mutane sukan yi abubuwan da a ainihi ba za su so su yi ba. Wasu ma sukan yi miyagun ayyuka don su yi ƙoƙari su daidaita yanayi da suke ganin yake kawo wahala da rashin gaskiya. “A yanayi da yawa,” in ji littafin nan Urban Terrorism, “ainihin dalilin da ya sa ake ta’addanci shi ne don fushin abubuwan da suke faruwa a siyasa, zaman jama’a da tattalin arziki.”
▪ “Son kuɗi asalin (tushen) kowace irin mugunta ne.”—1 TIMOTAWUS 6:10.
Wani tsohon karin magana ya ce, Wasu sun ce har ma mutane masu aminci za su ƙi yin nagarta idan an ba su kuɗi mai yawa. Waɗansu da suke yi kamar su masu fara’a ne kuma suna da kirki suna canja halayensu idan zancen kuɗi ya taso, sai su canja halayensu zuwa masu faɗace-faɗace. Ka yi tunani a kan yawancin laifuffuka da ake yi don haɗama, kamar su, sharri, zamba, sace mutum, da kuma kisa.
▪ “Saboda ba a aika shari’a da aka hukunta a bisa mugunta da sauri ba, shi ya sa zuciyar ’yan adam ta kan ji ƙarfin aika mugunta.”—MAI-WA’AZI 8:11.
Wannan nassin ya nuna halin ’yan Adam na yin tunani cewa mutum zai iya karya doka idan hukuma ba ta kallo. Hakan yake da mutane da suke mugun gudu a kan babbar hanyar mota, masu yin sata a jarabawa, masu sata kuɗin jama’a da masu yin abin da ya fi hakan tsanani. Idan ba a yawan hukunta masu laifi, ko kuma mutane ba sa jin tsoron cewa za a kama su, mutanen da suke bin doka za su samu gaba gaɗin yin abin da ba za su so su yi ba. “Yadda masu laifi suke kuɓuce wa horo da sauƙi” in ji jaridar Arguments and Facts “yakan sa talakawa su aikata laifuffuka da suka fi tsanani.”
▪ “Kowane mutum yakan jarabtu, sa’anda sha’awatasa ta janye shi, ta yi masa tarko. Sa’annan, lokacin da sha’awa ta habala, ta kan haifi zunubi.”—YAƘUB 1:14, 15.
Dukan ’yan Adam suna yin tunani marar kyau. Kullum, ana cika mu da shawarwari masu yawa da kuma ana jarraba mu mu yi laifi. A zamanin da aka rubutun Littafi Mai Tsarki, an gaya wa Kiristoci: “Babu wata jaraba ta same ka sai irin da mutum ya iya jimrewa.” (1 Korintiyawa 10:13) Duk da haka, sakamakon ya dangana ga zaɓin da mutumin ya yi, wato, ko ya ƙi mugun tunani da sauri ko kuma ya ƙyale shi ya yaɗu a cikin zuciyarsa. Nassin da aka yi ƙaulinsa a sama daga hurarriyar wasiƙar Yaƙub ya ba da gargaɗi cewa idan mutum ya ƙyale mugun sha’awa ta “habala,” munanan ayyuka za su bi baya.
▪ “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima, amma abokin tafiyar wawaye za ya cutu dominsa.”—MISALAI 13:20.
Abokanmu za su iya rinjayarmu a hanya mai kyau ko marar kyau. A yawancin lokaci, mutane sukan yi abin da ba niyyarsu ba, saboda matsi na tsara ko kuma kamar yadda mutane da yawa suke cewa, domin sun yi abokai marar kyau. A harshen da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “wawaye” ba ta nufin waɗanda ba su da basira, amma tana nufin waɗanda suka ƙi bin shawara mai kyau da ke cikin Kalmar Allah. Ko da mu yara ne ko kuma manya, idan ba mu zaɓa abokanmu ba da kyau, wato, ta wurin yin amfani da mizanai masu kyau da ke cikin Littafi Mai Tsarki, dole za mu “cutu.”
Wannan da ayoyi dabam dabam na Littafi Mai Tsarki sun bayyana dalla-dalla dalilin da ya sa mutane, har waɗanda ba sa laifi suke yin miyagun ayyuka. Duk da cewa yana da kyau a fahimci dalilin da ya motsa mutane su yi miyagun ayyuka, amma akwai bege cewa za a iya samun sauƙi kuwa? E, gama Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalilai da ke sa mutane su yi miyagun ayyuka kuma ya yi alkawari cewa ayyukan nan ba za su ƙara kasancewa kuma ba. Mene ne waɗannan alkawuran? Shin dukan mugunta da ke duniya za su zo ga ƙarshe kuwa? Talifi na gaba zai ba da amsoshin.