Tashin Matattu —Koyarwa Da Ta Shafe Ka
“Ina sa zuciya ga Allah . . . za a ta da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.”—AYYUKAN MANZANNI 24:15.
1. Ta yaya tashin matattu ya zama batun mahawara a gaban Majalisa?
MANZO Bulus yana Urushalima a ƙarshen tafiyarsa ta uku ta wa’azi, a shekara ta 56 A.Z. Bayan Romawa sun kama shi, sun tura shi gaban Majalisa, babban kotun Yahudawa. (Ayyukan Manzanni 22:29, 30) Da Bulus ya dubi waɗanda suke cikin kotun, ya lura cewa wasu Sadukiyawa ne, sauran kuma Farisawa ne. Waɗannan rukuni biyu sun bambanta a hanya ta musamman. Sadukiyawa ba su gaskata da tashin matattu ba; amma Farisawa sun yi imani da tashin matattu. Domin ya sanar da imaninsa a kan batun, Bulus ya ce: “Ya ’yan’uwa, ni ma Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ga shi kuwa, saboda na sa zuciya ga tashin matattu ne ake mini shari’a.” Da ya faɗi haka, ya rikitar da taron!—Ayyukan Manzanni 23:6-9.
2. Me ya sa Bulus yake a shirye ya ba da amsar imaninsa game da tashin matattu?
2 Da yake tafiya zuwa Dimashƙu shekaru da suka shige, Bulus ya ga wahayi inda ya ji muryar Yesu. Bulus ya ma tambayi Yesu: “Me zan yi, ya Ubangiji?” Yesu ya amsa: “Tashi, ka shiga Dimashƙu, a can ne za a faɗa maka duk abin da aka ɗora maka ka yi.” Da Bulus ya isa Dimashƙu, Kirista almajiri Hananiya ya same shi, ya bayyana masa: “Allahn kakanninmu ya zaɓe ka ka san nufinsa, ka ga Mai Adalcin nan, [Yesu da ya tashi daga matattu] ka kuma ji jawabi daga bakinsa.” (Ayyukan Manzanni 22:6-16) Shi ya sa Bulus yake a shirye ya ba da amsar imaninsa game da tashin matattu.—1 Bitrus 3:15.
Sanar da Begen Tashin Matattu a Fili
3, 4. Ta yaya Bulus ya zama mai goyon bayan koyarwar tashin matattu sosai, kuma me za mu koya daga misalinsa?
3 An kai Bulus gaban Gwamna Filikus. A lokacin, “wani lauya” mai suna Tartulus ne ya shigar da ƙarar da Yahudawa suke yi game da Bulus, ya zargi Bulus cewa shi ne shugaban ɗarika kuma yana da laifin ta da zaune tsaya. Bulus ya amsa babu ɓata lokaci, yana cewa: “Amma na yarda, cewa bisa ga hanyan nan da suke kira ‘Ɗarika’ nake bauta wa Allahn kakanninmu.” Da yake maganar ainihin batun, ya ci gaba: “Ina sa zuciya ga Allah, yadda su waɗannan ma suke sawa, wato za a ta da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.”—Ayyukan Manzanni 23:23, 24; 24:1-8, 14, 15.
4 Bayan shekara biyu, Borkiyas Festas magajin Filikus ya gayyaci Sarki Hirudus Agaribas su tuhumi Bulus fursuna tare. Festas ya yi bayani cewa masu zargin Bulus sun ƙi shelarsa cewa “wani, wai shi Yesu, wanda ya mutu . . . yana da rai.” Da Bulus yake ba da amsa, ya yi tambaya: “Yaya cewa Allah na ta da matattu ya ƙi gaskatuwa a gare ku?” Sai ya sanar: “Da na sami taimakon Allah kuwa, ga ni nan har yanzu, ina shaida wa babba da yaro, ba na faɗar kome sai abin da annabawa da Musa suka ce zai auku, cewa dai lalle ne Almasihu yā sha wuya, shi ne kuma zai fara tashi daga matattu, ya sanar da jama’an nan da al’ummai haske.” (Ayyukan Manzanni 24:27; 25:13-22; 26:8, 22, 23) Hakika Bulus mai goyon bayan koyarwar tashin matattu ne sosai! Kamar Bulus mu ma za mu iya sanar da tabbaci cewa za a yi tashin matattu. Yaya za mu yi tsammanin mutane za su aikata? Yadda suka yi wa Bulus.
5, 6. (a) Yaya mutane suka aikata sa’ad da manzannin suke gabatar da tashin matattu? (b) Sa’ad da muke furta begenmu na tashin matattu, menene yake da muhimmanci?
5 Ka yi la’akari da abin da ya faru a lokacin tafiyar hidimar Bulus ta biyu (a misalin 49-52 A.Z.) sa’ad da ya ziyarci Atina. Ya yi magana da mutane da suka gaskata da alloli da yawa kuma ya aririce su su fahimci cewa Allah zai yi amfani da mutum da ya zaɓa ya yi wa duniya shari’a cikin adalci. Yesu ne mutumin. Bulus ya yi bayani cewa Allah ya ba da tabbacin wannan ta wajen ta da Yesu daga matattu. Menene suka yi? Labarin ya ce: “Da dai suka ji maganar tashin matattu, sai waɗansu suka yi ba’a, amma waɗansu suka ce, ‘game da wannan magana kam, mā sāke jin abin da za ka faɗa.’ ”—Ayyukan Manzanni 17:29-32.
6 Abin da Bitrus da Yahaya suka fuskanta ne ba da daɗewa ba bayan Fentakos na 33 A.Z. Sadukiyawa ne musamman suka ta da jayayyar. Ayyukan Manzanni 4:1-4 sun faɗi abin da ya faru: “Suna cikin yin magana da jama’a sai firistoci da shugaban dogaran Haikali da Sadukiyawa suka ji haushi ƙwarai, suka aukar musu, wai don suna koya wa jama’a, suna tabbatar da tashi daga matattu, suna misali da Yesu.” Amma wasu sun aikata da kyau. “Da yawa cikin waɗanda suka ji wa’azin sun ba da gaskiya, har jimillarsu ta kai wajen mutum dubu biyar.” Babu shakka, mutane za su aikata abubuwa dabam dabam sa’ad da muka yi magana game da begen tashin matattu. Shi ya sa, yake da muhimmanci mu ƙarfafa imaninmu a wannan koyarwar.
Imani da Kuma Tashin Matattu
7, 8. (a) Kamar yadda aka nuna a wasiƙa ga ikilisiyar Koranti a ƙarni na farko, ta yaya bangaskiya za ta zama banza? (b) Ta yaya fahimtar begen tashin matattu yadda ya dace ya bambanta Kiristoci na gaskiya?
7 Ba dukan waɗanda suka zama Kiristoci ba ne a ƙarni na farko A.Z., suka iske shi da sauƙi su amince da begen tashin matattu. Wasu da suka iske shi da wuya suna tarayya da ikilisiya da ke Koranti. Bulus ya rubuta musu: “Jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, shi ne wanda na karɓo, cewa Almasihu ya mutu domin zunubanmu, kamar yadda Littattafai suka faɗa, cewa an binne shi, an ta da shi a rana ta uku, kamar yadda Littattafai suka faɗa.” Sai Bulus ya ba da tabbacin wannan gaskiya ta cewa Kristi da aka tasar “ya bayyana ga ’yan’uwa fiye da ɗari biyar,” waɗanda ya ce yawancinsu suna da rai a lokacin. (1 Korantiyawa 15:3-8) Ya daɗa tabbatar musu: “Da ya ke ana wa’azin Almasihu kan an tashe shi daga matattu, ƙaƙa waɗansunku ke cewa babu tashin matattu? In dai babu tashin matattu, ashe, ba a ta da Almasihu ba ke nan. In kuwa ba a ta da Almasihu ba, to, ashe, wa’azinmu banza ne, bangaskiyarku kuma banza ce.”—1 Korantiyawa 15:12-14.
8 Hakika, koyarwar tashin matattu tana da muhimmanci da idan ba amince da ita ba, bangaskiya ta Kirista banza ce. Hakika, fahimtar tashin matattu sosai ya bambanta Kiristoci na gaskiya daga na ƙarya. (Farawa 3:4; Ezekiyel 18:4) Shi ya sa Bulus ya haɗa koyarwar tashin matattu a “ka’idodin farko” na Kiristanci. Bari mu ƙudura aniyar ci gaba har “zuwa kammala.” Bulus ya ce “za mu kuwa ci gaba in Allah ya yarda.”—Ibraniyawa 6:1-3.
Begen Tashin Matattu
9, 10. Menene Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya yi maganar tashin matattu?
9 Don mu daɗa ƙarfafa bangaskiyarmu ga tashin matattu, bari mu bincika tambayoyi kamar su: Menene Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya yi maganar tashin matattu? Ta yaya koyarwar tashin matattu take ɗaukaka ƙaunar Jehobah? Amsoshin waɗannan tambayoyi za su sa mu matsa kurkusa da Allah kuma su taimake mu mu koyar da mutane.—2 Timoti 2:2; Yakubu 4:8.
10 “Tashin matattu” fassarar kalmar Helenanci ce da a zahiri take nufin “sake tashiwa.” Menene wannan furcin yake nufi? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa begen tashin matattu tabbaci ne cewa matacce zai sake rayuwa. Littafi Mai Tsarki ya daɗa nuna cewa maido mutumin zuwa rai ko kuma jiki na ruhu, ya dangana ga ko yana da begen zama a duniya ko kuma a sama. Muna mamaki game da ƙaunar Jehobah, hikimarsa, da ikon da ya nuna a wannan begen tashin matattu mai ban al’ajabi.
11. Wane begen tashin matattu bayin Allah shafaffu suke da shi?
11 Yesu da ’yan’uwansa shafaffu sun tashi daga matattu da jiki na ruhu, wannan ya dace don hidima a sama. (1 Korantiyawa 15:35-38, 42-53) Za su yi sarauta na Mulkin Almasihu tare, wannan zai kawo Aljanna a duniya. A ƙarƙashin Yesu Babban Firist, shafaffu za su zama ƙungiyar firistocin babban sarki. Za su sa ’yan adam su amfana daga hadayar fansa ta Kristi a sabuwar duniya ta adalci. (Ibraniyawa 7:25, 26; 9:24; 1 Bitrus 2:9; Wahayin Yahaya 22:1, 2) Kafin nan, shafaffu da har ila suke duniya suna son su ci gaba da samun amincewar Allah. Sa’ad da suka mutu, za su sami ‘sakamakonsu’ ta wurin tashin matattu su yi rayuwa ta ruhu a sama ba tare da sake mutuwa ba. (2 Korantiyawa 5:1-3, 6-8, 10; 1 Korantiyawa 15:51, 52; Wahayin Yahaya 14:13) Bulus ya rubuta: “Tun da ya ke mun zama ɗaya da shi wajen kwatancin mutuwa tasa, ashe kuwa, za mu zama ɗaya ma wajen tashinsa.” (Romawa 6:5) Waɗanda za a tashe su daga matattu su yi rayuwa a duniya kuma fa? Ta yaya begen tashin matattu zai sa su kusaci Allah? Za mu koyi abubuwa da yawa daga misalin Ibrahim.
Tashin Matattu da Kuma Abuta da Jehobah
12, 13. Ibrahim yana da wane ƙarfafan dalili na yin imani da tashin matattu?
12 Ibrahim da aka kwatanta da “aminin Allah,” mutum ne mai bangaskiya na musamman. (Yakubu 2:23) Bulus ya yi maganar bangaskiyar Ibrahim sau uku da yake lissafa maza da mata masu aminci da ke sura ta 11 ta littafin Ibraniyawa. (Ibraniyawa 11:8, 9, 17) Na ukun game da bangaskiyar Ibrahim ne sa’ad da cikin biyayya ya yi shirin miƙa ɗansa Ishaku hadaya. Ibrahim ya tabbata cewa Jehobah zai cika alkawarin zuriya ta wurin Ishaku. Ko idan ma Ishaku ya mutu a hadaya, Ibrahim “ya amince cewa ko daga matattu Allah yana da iko ya ta da mutum.”
13 Sa’ad da Jehobah ya ga yawan bangaskiyar Ibrahim, ya shirya a yi amfani da dabba don hadayar. Duk da haka, abin da Ishaku ya fuskanta misali ne na tashin matattu, yadda Bulus ya yi bayani: “Bisa ga misali sai a ce daga matattu ne [Ibrahim] ya sāke samun Ishaku.” (Ibraniyawa 11:19) Ƙari ga haka, Ibrahim ya daɗa samun ƙarfafan dalili na yin imani da tashin matattu. Shin ba Jehobah ba ne ya maido da ikon haihuwa na Ibrahim lokacin da shi da matarsa Saratu a tsufansu suka haifi ɗansu Ishaku?—Farawa 18:10-14; 21:1-3; Romawa 4:19-21.
14. (a) Bisa ga Ibraniyawa 11:9, 10, menene Ibrahim yake jira? (b) Don ya samu albarkar Mulki a sabuwar duniya, menene dole zai sami Ibrahim tukuna? (c) Ta yaya za mu sami albarkar Mulki?
14 Bulus ya ce Ibrahim ya yi baƙunci kuma yana zama cikin alfarwa yana “jiran birnin nan mai tushe, wanda mai fasarta shi, mai gina shi kuma, Allah ne.” (Ibraniyawa 11:9, 10) Wannan ba birni na zahiri ba ne kamar Urushalima inda haikalin Allah yake. Birni ne na alama. Mulkin samaniya ne na Allah da Kristi Yesu da abokansa na sarauta 144,000 suke ciki. Domin suna da ɗaukaka na samaniya ana kiran mutane 144,000 “tsattsarkan birni . . . , Sabuwar Urushalima,” “amaryar” Kristi. (Wahayin Yahaya 21:2) A shekara ta 1914, Jehobah ya naɗa Yesu Sarki Almasihu na Mulkin samaniya kuma ya umurce shi ya yi sarauta bisa maƙiyansa. (Zabura 110:1, 2; Wahayin Yahaya 11:15) Domin Ibrahim “aminin Allah” ya sami albarkar sarauta na Mulkin, zai sake rayuwa. Haka nan ma, don mu sami albarkar Mulkin, dole ne mu kasance da rai a sabuwar duniya ta Allah ko muna cikin taro mai girma da suka tsira daga Armageddon ko kuma waɗanda aka tashe su daga matattu. (Wahayin Yahaya 7:9, 14) To, menene dalilin kasance da begen tashin matattu?
Ƙaunar Allah Ita ce Tushen Begen Tashin Matattu
15, 16. (a) Ta yaya annabci na farko cikin Littafi Mai Tsarki ya sa begen tashin matattu ya yiwu? (b) Ta yaya gaskata da tashin matattu zai sa mu kusaci Jehobah?
15 Za mu zama adilai kuma Jehobah zai ɗauke mu abokansa idan muna dangantaka na kurkusa da Ubanmu na samaniya mai ƙauna, idan bangaskiyarmu tana da ƙarfi kamar ta Ibrahim kuma muna biyayya ga umurnin Allah. Wannan zai sa mu amfana daga sarautar Mulki. Annabci na farko da aka rubuta cikin Kalmar Allah, a Farawa 3:15 ta ba da dalilin begen tashin matattu da kuma yin abuta da Allah. Ta annabta cewa za a ƙuje kan Shaiɗan kuma za a ƙuje diddigen Zuriyar mace ta Allah. Da yake Yesu ya mutu a kan gungume an ƙuje diddigensa ke nan a alamance. Tashinsa daga matattu a kwana ta uku ya warkar da raunin kuma ya sa ya yiwu a yi maganin “mai ikon mutuwa, wato Iblis.”—Ibraniyawa 2:14.
16 Bulus ya tuna mana cewa “Allah na tabbatar mana da ƙaunar da yake mana, wato tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu dominmu.” (Romawa 5:8) Nuna godiya don wannan alherin zai sa mu matsa kusa ga Yesu da kuma Ubanmu na sama mai ƙauna.—2 Korantiyawa 5:14, 15.
17. (a) Wane bege ne Ayuba ya furta? (b) Menene Ayuba 14:15 ta nuna game da Jehobah, yaya kake ji game da wannan?
17 Ayuba mutum ne mai aminci kafin zamanin Kiristanci, shi ma ya saurari tashin matattu. Ya sha wahala sosai domin abin da Shaiɗan ya yi masa. Ba kamar abokansa na ƙarya da ba su ambata tashin matattu ba, wannan begen ya ƙarfafa Ayuba kuma ya yi tambaya: “Idan mutum ya mutu, zai sāke rayuwa kuma?” Sai Ayuba kansa ya amsa: “Zan jira lokaci mafi kyau, in jira sai lokacin wahala ya wuce.” Da yake wa Allahnsa, Jehobah magana ya ce: “Sa’an nan za ka yi kira, ni kuwa zan amsa.” Game da yadda Mahaliccinmu mai ƙauna yake ji, Ayuba ya ce: “Za ka yi murna da ni, ni talikinka.” (Ayuba 14:14, 15) Hakika, Jehobah yana ɗokin lokacin da dukan masu aminci za su sake rayuwa a lokacin tashin matattu. Sa’ad da muke bimbini a kan ƙauna da alherin da yake mana ko da mu ajizai ne wannan yana sa mu kusace shi!—Romawa 5:21; Yakubu 4:8.
18, 19. (a) Wane bege ne na sake rayuwa Daniyel yake da shi? (b) Menene za mu bincika a talifi na gaba?
18 Mala’ikan Allah ya kwatanta annabi Daniyel ‘mutumin da ake so ƙwarai’ da ya yi rayuwa na hidima da aminci. (Daniyel 10:11, 19) Ya kasance da aminci sosai ga Jehobah a lokacin da yake bauta a shekara ta 617 K.Z., har mutuwarsa bayan ya sami wahayi a shekara ta 536 K.Z., shekara ta uku na Sairus, sarkin Farisa. (Daniyel 1:1; 10:1) Wani lokaci a shekara ta uku na sarautar Sairus, Daniyel ya sami wahayi game da ayyukan masu iko da duniya da zai ƙare a ƙunci mai girma da ke zuwa. (Daniyel 11:1–12:13) Domin bai fahimci wahayin sosai ba, Daniyel ya tambayi mala’ika da ya idar da saƙon: “Ya shugabana, menene ƙarshen waɗannan abubuwa?” (Daniyel 12:8) Mala’ikan ya amsa ya ce sai a “ƙarshen lokaci,” da “masu hikima za su gane.” Wane bege ne Daniyel yake da shi? Mala’ikan ya ce: “[Za] ka huta, a ƙarshen kwanaki za ka tashi ka karɓi naka rabo.” (Daniyel 11:1–12:13) Daniyel zai dawo a “ranar tashin masu adalci” lokacin Sarautar Alif na Kristi.—Luka 14:14.
19 Muna cikin ƙarshen kwanaki kuma mun kusan somawar Sarautar Alif na Kristi fiye da sa’ad da muka zama masu bi. Saboda haka, dole mu tambayi kanmu, ‘Zan kasance kuwa a sabuwar duniya in yi tarayya da Ibrahim, Ayuba, Daniyel, da wasu maza da mata masu aminci?’ Za mu kasance a wajen muddin mun kusaci Jehobah kuma muka yi biyayya ga umarninsa. A talifinmu na gaba za mu ƙara bincika begen tashin matattu dalla-dalla domin mu san waɗanda za su tashi.
Ka Tuna?
• Yaya mutane suka aikata sa’ad da Bulus ya sanar da begensa na tashin matattu?
• Me ya sa begen tashin matattu ya sa Kiristoci na gaskiya suka bambanta da na ƙarya?
• Ta yaya muka sani cewa Ibrahim, Ayuba, da Daniyel suna da bangaskiya ga tashin matattu?
[Hoto a shafi na 17]
Bulus a gaban Gwamna Filikus kuma ya sanar da begen tashin matattu da tabbaci
[Hoto a shafi na 18]
Me ya sa Ibrahim yake da bangaskiya ga tashin matattu?
[Hoto a shafi na 20]
Begen tashin matattu ya ƙarfafa Ayuba
[Hoto a shafi na 20]
Daniyel zai dawo a tashin matattu na masu adalci