Nasara a Hanya ta Musamman
KANA fuskantar hamayya ga imaninka, wataƙila a wajen aiki, a makaranta, a iyali, ko kuma domin wani hani da Gwamnati ta yi? Idan haka ne kada ka yi sanyin gwiwa. Shaidun Jehobah da yawa sun fuskanci irin wannan gwaji, duk da haka sun yi nasara. Ka yi la’akari da misalin Erna Ludolph.
An haifi Erna a Lübeck ta Jamus, a shekara ta 1908. Ita kaɗai ce cikin iyalinsu take bauta wa Jehobah. A shekara ta 1933, da Hitler ya soma sarauta, Shaidun Jehobah suka soma fuskantar gwaji da yawa. Abokan aikin Erna suka zarge ta domin ta ƙi ta sara wa Hitler, wannan ya sa ’yan Nazi suka kama ta. Ta yi shekara takwas a kurkuku dabam dabam da kuma sansanoni da suke Hambuk-Fusbuttel, Moringen, Liktenbuk, da kuma Rabensbruk. Sa’ad da Erna take garin Rabensbruk, wani abu ya faru da ya sa ta yi nasara.
Mai Kula da Gida na Musamman
Farfesa Fredrik Holt da matarsa Alice, suna da zama a birnin Berlin. Ba sa cikin rukunin Nazi kuma ba su goyi bayan ra’ayinsa ba. Amma su dangi ne na wani babban ma’aikaci na Hitler da yake kula da wasu fursunoni na sansanin. Saboda haka, sa’ad da farfesan da matarsa suke neman mai kula da gida, wannan ma’aikaci ya sa su zaɓi fursuna ta mace. A Maris na shekara ta 1943, Alice ta ziyarci garin Rabensbruk ta zaɓi mai kula da gida. Wa ta zaɓa? Ta zaɓi Erna Ludolph. Erna ta soma zama da iyalin Holt, kuma sun kula da ita sosai. Bayan yaƙin, ta ƙaura da iyalin zuwa birnin Halle na Zāle. A wajen ta fuskanci hamayya, daga ma’aikatan mulkin kama-karya na Jamus ta Gabas. A shekara ta 1957 an tilasta wa iyalin ta koma Jamus ta Yamma, kuma Erna ta bi su. A ƙarshe Erna ta sami ’yancin bin imaninta.
Ta yaya Erna ta yi nasara a hanya ta musamman? Domin halin Erna mai kyau da kuma yin wa’azin saƙon Littafi Mai Tsarki sosai, Alice Holtz da yaranta biyar suka zama Shaidun Jehobah da suka yi baftisma. Ƙari ga haka, jikokin Alice guda 11 Shaidu ne. Biyu cikinsu yanzu suna hidima a ofishin reshe na Shaidun Jehobah a Selters ta Jamus. “Iyalinmu tana cikin gaskiya domin misalin Erna,” in ji Susanne, ɗaya cikin ’ya’ya mata na Alice. Erna ta sami albarka sosai domin jimirinta. Kai kuma fa? Idan ka jimre a yanayi mai wuya kai ma za ka iya samun irin wannan sakamakon. Hakika, hali mai kyau da yin wa’azi sosai zai iya taimakonka ka yi nasara a hanya ta musamman.a
[Hasiya]
a Erna Ludolph ta rasu sa’ad da ake shirya wannan talifin, tana da shekara 96. Ta kasance da aminci har ƙarshe.
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 15]
Erna Ludolph (a zaune) da waɗanda suke cikin iyalin Holtz