Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 5/1 pp. 21-25
  • Wa Za A Ta Da Daga Matattu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wa Za A Ta Da Daga Matattu?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ina Matattu Suke?
  • ‘Aka Kai Su ga Jama’arsu’
  • Marasa Adalci Suna Cikin Sheol Ne?
  • Su Waye ne Suke Jahannama?
  • Tashin Matattu na “Farko” Kuma “Mafi Kyau”
  • Menene Sheol da kuma Hades?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Ikon Begen Tashin Matattu
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 5/1 pp. 21-25

Wa Za A Ta Da Daga Matattu?

“Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk waɗanda ke kaburbura za su ji murya tasa, su kuma fito.”—YAHAYA 5:28, 29.

1. Wace sanarwa ta musamman Musa ya ji a kurmi mai cin wuta, kuma wanene ya sake maimaita waɗannan kalmomi?

WANI abin mamaki ya faru fiye da shekaru 3,500 da suka shige. Musa yana kiwon tumakin Yetro uban iyali. Kusa da Dutsen Horeb, mala’ikan Jehobah ya bayyana wa Musa cikin harshen wuta da ke cin kurmi. “Da Musa ya duba, sai ga kurmin yana cin wuta, amma duk da haka bai ƙone ba,” in ji labarin Fitowa. Sai murya ta kira shi daga cikin kurmin. Muryar ta ce “ni ne Allah na kakanninka, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.” (Fitowa 3:1-6) A ƙarni na farko A.Z., Ɗan Allah Yesu ya maimaita waɗannan kalmomi.

2, 3. (a) Wane bege ne Ibrahim, Ishaku, da Yakubu suke da shi? (b) Waɗanne tambayoyi ne aka yi?

2 Yesu yana magana ne da wasu Sadukiyawa da ba su gaskata da tashin matattu ba. Yesu ya sanar: “Game da tashin matattu kuwa, ai, Musa ma ya faɗa, a labarin kurmin, inda ya kira Ubangiji, Allahn Ibrahim, da Allahn Ishaku, da Allahn Yakubu. Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba. Don a wurinsa duka rayayyu ne.” (Luka 20:27, 37, 38) Ta wajen faɗan hakan, Yesu ya ba da tabbacin cewa a ra’ayin Allah, Ibrahim, Ishaku, da Yakubu da suka mutu da daɗewa har ila Allah na tunawa da su. Kamar Ayuba, suna jiran ƙarshen “lokacin wahala,” wato mutuwarsu. (Ayuba 14:14) Za a tashe su daga matattu a sabuwar duniya ta Allah.

3 Mutane biliyoyi da suka mutu a duk tarihin ’yan adam fa? Su ma za a tashe su kuwa? Kafin mu sami amsa mai gamsarwa ga wannan tambayar, bari mu bincika daga Kalmar Allah abin da yake faruwa da mutane idan suka mutu.

Ina Matattu Suke?

4. (a) Ina ne mutane suke zuwa idan suka mutu? (b) Menene Sheol?

4 Littafi Mai Tsarki ya ce matattu “ba su san kome ba.” Idan mutum ya mutu ba ya shan wahala a cikin wutar jahannama ko kuma a Limbo (wajen jira), amma ya koma turɓaya. Shi ya sa, Kalmar Allah ta ba masu rai shawara: “Duk abin da kake iya yi, ka yi shi da iyakar iyawarka, domin ba aiki, ko tunani, ko ilimi, ko hikima a lahira [Sheol, NW ], gama can za ka.” (Mai Hadishi 9:5, 10; Farawa 3:19) Mutane da yawa ba su san wannan kalma “Sheol” ba. Kalmar Ibrananci ce da ba a san asalinta ba. Addinai da yawa suna koyar da cewa matattu har ila suna da rai, amma hurarriyar Kalmar Allah ta nuna cewa waɗanda suke cikin Sheol matattu ne da ba su san kome ba. Sheol inda matattu suke ne.

5, 6. Da Yakubu ya mutu, ina ya tafi, sawun su waye ya bi?

5 Kalmar nan [Sheol] Lahira ta bayyana da farko a Farawa 37:35 cikin Littafi Mai Tsarki. Da ya yi rashin Yusufu ɗansa ƙaunatacce, Yakubu uban iyali ya ƙi ta’azantuwa yana cewa: “[Sheol] Lahira zan tafi wurin ɗana, ina baƙin ciki.” Da yake ya gaskata cewa ɗansa ya mutu, Yakubu ya so ya mutu ya kasance cikin Sheol. Bayan haka, da yaran Yakubu tara suka so su tafi Masar da autansu, Biliyaminu, don su nemi abinci. Amma, Yakubu ya ƙi yana cewa: “Ɗana ba zai gangara tare da ku ba, ga ɗan’uwansa ya rasu, shi kaɗai kuwa ya ragu. Zai yiwu a kashe shi a hanya. Na tsufa ƙwarai ba zan iya ɗaukar wannan baƙin ciki ba, zai kashe ni.” (Farawa 42:36, 38) Waɗannan misalai biyu sun nuna dangantakar mutuwa da Sheol ba da rayuwa ba bayan mutuwa.

6 Labarin Farawa ya bayyana cewa Yusufu ya zama shugaban masu ba da abinci a Masar. Domin haka Yakubu ya tafi can domin farin cikin sake saɗuwa da Yusufu. Bayan haka, Yakubu ya zauna a ƙasar har ya tsufa sosai ya mutu yana da shekara 147. Da yake son ya mutu ya gaya wa ’ya’yansa su kai gawarsa ƙasar Kan’ana su binne a kogon Makfela. (Farawa 47:28; 49:29-31; 50:12, 13) Aka binne Yakubu tare da Ishaku babansa, da kuma Ibrahim, kakansa.

‘Aka Kai Su ga Jama’arsu’

7, 8. (a) Ina ne Ibrahim ya tafi da ya mutu? Ka ba da bayani. (b) Menene ya nuna cewa wasu sun shiga Sheol da suka mutu?

7 Da farko, sa’ad da Jehobah ya tabbatar wa Ibrahim alkawarinsa kuma ya ce zuriyarsa za su yi yawa, ya faɗi abin da zai sami Ibrahim. Jehobah ya ce: “Kai kuwa, cikin salama za ka koma ga iyayenka, da kyakkyawan tsufa za a binne ka.” (Farawa 15:15) Kuma abin da ya faru ke nan. Farawa 25:8 ta ce: “Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe ya kuwa rasu cikin kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa, aka kai shi ga jama’arsa.” Su wanene jama’ar? Farawa 11:10-26 sun lissafa kakanninsa tun daga lokacin ɗan Nuhu Shem. Waɗanda suke barci cikin Sheol ne jama’ar Ibrahim da aka kai shi gare su.

8 Furcin nan “aka kai shi ga jama’arsa” ta bayyana sau da yawa a cikin Nassosin Ibrananci. Da haka, daidai ne a kammala cewa Isma’ilu, ɗan Ibrahim da kuma Haruna ɗan’uwan Musa sun tafi Sheol da suka mutu suna jiran tashin matattu. (Farawa 25:17; Littafin Ƙidaya 20:23-29) Musa shi ma ya tafi Sheol, ko da ba wanda ya san inda kabarinsa yake. (Littafin Ƙidaya 27:13; Maimaitawar Shari’a 34:5, 6) Hakanan ma, Joshua magajin Musa da ya shugabanci Isra’ila, tare da dukan mutanen sun je Sheol da suka mutu.—Littafin Mahukunta 2:8-10.

9. (a) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa kalmar Ibrananci “Sheol” da ta Helenanci “Hades” suna zancen wuri ɗaya? (b) Wane bege waɗanda suke cikin Sheol, ko kuma Hades suke da shi?

9 Ƙarnuka da yawa bayan haka, Dauda ya zama sarki na ƙabilu 12 na Isra’ila. Da ya rasu “aka binne shi” da kakanninsa. (1 Sarakuna 2:10) Shi ma yana cikin Sheol ne? A ranar Fentakos na 33 A.Z., manzo Bitrus ya yi maganar rasuwar Dauda kuma ya yi ƙaulin Zabura 16:10: “Ba za ka bar wanda kake ƙauna a [Sheol] ba.” Bayan ya ambata cewa har ila Dauda yana cikin kabari, Bitrus ya yi amfani da waɗannan kalmomi ga Yesu kuma ya ce Dawuda “ya hango, ya kuma yi faɗi kan tashin Almasihu daga matattu, cewa ba za a yashe shi a Hades ba, jikinsa kuwa ba zai ruɓa ba. Yesun nan kam, Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa duk shaidu ne ga haka.” (Ayyukan Manzanni 2:29-32) Bitrus a nan ya yi amfani da kalmar nan “Hades,” kalmar Helenanci ne da ta yi daidai da ta Ibrananci “Sheol.” Da haka waɗanda suke cikin Hades suna cikin yanayi ɗaya da waɗanda suke cikin Sheol. Suna barci, suna jiran tashin matattu.

Marasa Adalci Suna Cikin Sheol Ne?

10, 11. Me ya sa za mu iya faɗi cewa wasu marasa adalci suna zuwa Sheol, ko kuma Hades idan suka mutu?

10 Bayan Musa ya ja-goranci al’ummar Isra’ila suka bar Masar, wasu sun yi tawaye a cikin daji. Musa ya gaya wa mutanen su ware kansu daga shugabannin—Kora, Datan, da kuma Abiram. Za a katse ransu. Musa ya ba da bayani: “Idan mutanen nan sun mutu kamar yadda mutane ke mutuwa, idan abin da yakan sami kowa shi ne ya sa same su, to, ba Ubangiji ne ya aiko ni ba. Amma idan Ubangiji ya aikata wani abu sabo, ya sa ƙasa ta buɗe bakinta, ta haɗiye su da dukan abin da suke da shi, suka gangara zuwa cikin [Sheol] lahira a raye, sa’an nan za ku sani mutanen nan sun raina Ubangiji.” (Littafin Ƙidaya 16:29, 30) Saboda haka ko ƙasa ce ta buɗe baki ta haɗiye su ko kuwa wuta ce ta ci su yadda ya faru da Kora da Lawiyawa 250 da suka goyi bayansa, duk waɗannan ’yan tawaye sun shiga Sheol ko Hades.—Littafin Ƙidaya 26:10.

11 Sulemanu magajin Dauda ne ya hukunta Shimai da ya yi wa Sarki Dauda mugun zagi. Dauda ya ba da umurni: “Dole ka hukunta shi, ka dai san abin da za ka yi da shi, lalle ne kuma [ka tura shi Sheol].” Sulemanu ya sa Benaiya ya zartar da hukuncin. (1 Sarakuna 2:8, 9, 44-46) Wani kuma da Benaiya ya kashe shi ne Yowab, shugaban sojojin Isra’ila ta dā. Da tsufansa bai gangara Sheol “ta hanyar lafiya” ba. (1 Sarakuna 2:5, 6, 28-34) Duk waɗannan misalan sun nuna gaskiyar hurarriyar waƙar Dauda: “[Sheol ne] maƙarar dukan mugaye, da dukan waɗanda suke ƙin Allah.”—Zabura 9:17.

12. Wanene Ahitofel, ina ya tafi da ya mutu?

12 Ahitofel mashawarcin Dauda ne. Ana ɗaukan shawararsa tamkar daga Jehobah ce. (2 Sama’ila 16:23) Abin baƙin ciki, wannan amintaccen bawa ya zama maci amana kuma ya bi Absalom ɗan Dauda a yin tawaye. Wataƙila Dauda yana maganar wannan amana da aka ci masa sa’ad da ya rubuta: “Da a ce maƙiyina ne ke mini ba’a, da sai in jure. Da a ce abokin gābana ne ke shugabancina, da sai in ɓuya masa.” Dauda ya ci gaba: “Allah ya sa mutuwa ta auko wa maƙiyana ba labari, Allah ya sa su gangara [Sheol] da ransu! Mugunta tana cikin gidajensu da zukatansu.” (Zabura 55:12-15) Da suka mutu, Ahitofel da abokansa sun tafi Sheol.

Su Waye ne Suke Jahannama?

13. Me ya sa aka kira Yahuza “halakakken nan”?

13 Ka gwada yanayin Dauda da abin da Dauda Babba, Yesu ya fuskanta. Ɗaya cikin manzannin Kristi 12, Yahuza Iskariyoti ya zama maci amana kamar Ahitofel. Amana da Yahuza ya ci ya fi na Ahitofel tsanani. Yahuza ya ci amanar Ɗan Allah makaɗaici ne. Da yake addu’a a ƙarshen hidimarsa a duniya, Ɗan Allah ya ba da rahoto game da manzanninsa: “Duk sa’ad da nake tare da su, na kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni. Na kare su, ba kuwa waninsu da ya hallaka, sai dai halakakken nan, domin Nassi ya cika.” (Yahaya 17:12) Ta wajen kiran Yahuza “halakakken nan,” Yesu ya nuna cewa sa’ad da Yahuza ya mutu, ba shi da begen sake tashi kuma. Ba ya cikin waɗanda Allah yake tunawa da su. Ya tafi Jahannama ba Sheol ba. Mecece Jahannama?

14. Jahannama tana wakiltan menene?

14 Yesu ya hukunta shugabannan addinai na zamaninsa domin suna mai da kowanne cikin almajiransu “ɗan [Jahannama].” (Matiyu 23:15) A lokacin nan, mutane suna sane da Kwarin Hinnom, wurin zuba juji ne inda ake saka gawar masu laifi da aka kashe da ba su cancanci a yi musu jana’iza ba. Can dama Yesu ya ambata Jahannama a Hudubarsa a kan Dutse. (Matiyu 5:29, 30) Masu sauraronsa sun fahimci abin da take nufi a alamance. Jahannama halaka ce gabaki ɗaya ba tare da begen tashi ba kuma. Ban da Yahuza Iskariyoti na zamanin Yesu, wasu sun tafi Jahannama da suka mutu kuwa, maimakon Sheol, ko Hades?

15, 16. Su waye suka tafi Jahannama da suka mutu, me ya sa suka je can?

15 An halicci mutane na farko Adamu da Hauwa’u kamiltattu. Sun yi zunubi da gangan. A gabansu suna da zaɓe na rai madawwami ko kuma mutuwa. Sun yi wa Allah rashin biyayya suka goyi bayan Shaiɗan. Da suka mutu ba su da begen amfana daga hadayar fansa ta Kristi. Maimakon haka, sun tafi Jahannama.

16 Kayinu, ɗan fari na Adamu, ya kashe ɗan’uwansa Habila, bayan haka ya yi rayuwa na ɗan gudun hijira. Manzo Yahaya ya kwatanta Kayinu da “wanda yake na Mugun.” (1 Yahaya 3:12) Daidai ne a kammala cewa kamar iyayensa, ya tafi Jahannama sa’ad da ya mutu. (Matiyu 23:33, 35) Wannan dabam yake da yanayin adali Habila! “Ta bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadaya mafi kyau a kan ta Kayinu, ta wannan bangaskiya ce ya kuma sami yardar Allah a kan shi mai adalci ne, domin Allah ma ya shaide shi, da ya karɓi abubuwan da ya bayar,” in ji Bulus, kuma ya daɗa cewa, “ya mutu kam, amma ta bangaskiyan nan tasa har yanzu yana magana.” (Ibraniyawa 11:4) Hakika, Habila yana cikin Sheol yana jiran tashin matattu.

Tashin Matattu na “Farko” Kuma “Mafi Kyau”

17. (a) A wannan “lokaci na ƙarshe,” su wa za su tafi Sheol? (b) Wane bege ne waɗanda suke cikin Sheol da kuma waɗanda suke cikin Jahannama suke da shi?

17 Waɗanda suka karanta wannan bayani za su so su san abin da zai faru da waɗanda suka mutu a wannan “lokaci na ƙarshe.” (Daniyel 8:19) Wahayin Yahaya sura ta 6 ta kwatanta ayyukan mahayan doki huɗu a wannan lokacin. Sunan mahayin doki na ƙarshe Mutuwa ne, kuma Hades na biye da shi. Da haka mutane da yawa da suka mutu lokacin da bai kamata ba domin ayyukan mahayan doki suna cikin Hades, suna jiran tashin matattu a sabuwar duniya ta Allah. (Wahayin Yahaya 6:8) To, menene begen waɗanda suke cikin Sheol, (Hades) da waɗanda suke Jahannama? Za a tashi waɗanda suke cikin Hades; kuma an halaka waɗanda ke Jahannama da madawwamiyar halaka, ba za su sake wanzuwa ba.

18. Wane bege ake samu ta “tashin nan na farko.”

18 Manzo Yahaya ya rubuta: “Duk wanda yake da rabo a tashin nan na farko mai albarka ne, tsattsarka ne. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kan irin waɗannan, amma za su zama firistocin Allah da na Almasihu, su kuma yi mulki tare da shi har shekara dubu.” Waɗanda za su zama abokan sarauta da Kristi ne suke samun “tashin nan na farko,” amma wane bege sauran ’yan adam suke da shi?—Wahayin Yahaya 20:6.

19. Ta yaya wasu za su amfana daga “rayuwa mafi kyau.”

19 Daga zamanin Iliya da Elisha bayin Allah, an ta da mutane zuwa rai da mu’ujizar ta da matattu. Bulus ya ce: “An mayar wa mata da matattunsu da aka tasar. Waɗansu mutane kuma an azabta su har suka mutu, amma sun ƙi yarda da irin ’yancin da za a ba su, domin tashe su su rayu da rayuwa mafi kyau.” Hakika, waɗannan mutane masu aminci suna jiran tashin matattu da zai sa su yi rayuwa ba na ’yan shekaru ba su sake mutuwa, amma na rai madawwami! Hakika, zai zama “rayuwa mafi kyau.”—Ibraniyawa 11:35.

20. Menene za a bincika a talifi na gaba?

20 Idan mun mutu da aminci kafin Jehobah ya kawo ƙarshen wannan zamani, za mu sami tabbataccen begen “rayuwa mafi kyau,” domin za ta zama ta har abada. Yesu ya yi alkawari: “Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk waɗanda ke kaburbura za su ji murya tasa, su kuma fito.” (Yahaya 5:28, 29) Talifinmu na gaba zai ƙara ba da bayanin nufin tashin matattu. Zai nuna yadda begen tashin matattu yake ƙarfafa mu mu zama masu aminci, kuma mu koyi halin sadaukar da kanmu.

Ka Tuna?

• Me ya sa aka ce Jehobah Allah ne ‘rayayye’?

• Menene yanayin waɗanda suke cikin Sheol?

• Menene begen waɗanda suke Jahannama?

• Ta yaya wasu za su amfana daga “rayuwa mafi kyau”?

[Hoto a shafi na 23]

Kamar Ibrahim za a tashi waɗanda suke cikin Sheol

[Hotuna a shafi na 24]

Me ya sa Adamu da Hauwa’u, Kayinu, da kuma Yahuza Iskariyoti suka je Jahannama?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba