Kada Mu Yi Zaman Ganin Dama
“[Kristi] ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin waɗanda ke raye, kada su yi zaman ganin dama.”—2 KORANTIYAWA 5:15.
1, 2. Wace doka ta Nassi ce ta motsa mabiyan Yesu na ƙarni na farko su kawar da son kai?
ADAREN Yesu na ƙarshe a duniya, kafin ya ba da ransa a madadin dukan waɗanda za su ba da gaskiya a gare shi, Yesu ya gaya wa manzanninsa masu aminci muhimman abubuwa masu yawa. A cikinsu da wata doka game da halin da za ta bambanta mabiyansa, ya ce: “Sabon umarni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma ku ƙaunaci juna. Ta haka kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”—Yahaya 13:34, 35.
2 Kiristoci na gaskiya za su nuna ƙauna ta wajen ba da kai ga junansu kuma za su saka bukatun ’yan’uwansu masu bi gaba da nasu. Ba za su yi shakkar ‘ba da ransu saboda aminansu ba.’ (Yahaya 15:13) Ta yaya ne Kiristoci na farko suka bi wannan sabuwar doka? A cikin sanannen littafinsa Apology, (Kāriya) marubucin ƙarni na biyu Tertulian ya ambata abin da wasu suka ce game da Kiristoci: ‘Dubi yadda suke ƙaunar juna; har ma suna shirye su mutu domin juna.’
3, 4. (a) Me ya sa ya kamata mu ƙi son kai? (b) Menene za mu tattauna a wannan talifin?
3 Dole ne mu ma mu ‘ɗau wahalar juna, ta haka za mu cika shari’ar Almasihu.’ (Galatiyawa 6:2) Amma fa, son kai yana ɗaya daga cikin gargada na yin biyayya ga dokar Kristi da kuma ‘ƙaunar Jehobah Allahnmu da dukan zuciyarmu, da dukan ranmu, da dukan hankalinmu. Da kuma ƙaunar ɗan’uwanmu kamar kanmu.’ (Matiyu 22:37-39) Domin mu ajizai ne, mukan nuna son kai. Ƙari ga wannan shi ne wahalar rayuwa ta yau da kullum, gasa a makaranta ko a wajen aiki, da kuma ƙoƙarin samun abin duniya, waɗannan bukatun sai ƙaruwa suke yi. Wannan tunani na son kai ba raguwa yake yi ba. Manzo Bulus ya yi gargaɗi: “A zamanin ƙarshe . . . Mutane za su zama masu sonkai.”—2 Timoti 3:1, 2.
4 Kusan ƙarshen hidimarsa a duniya, Yesu ya bai wa almajiransa matakai uku da za su taimake su su kawar da son kai. Menene waɗannan, kuma yaya za mu amfana daga umurnansa?
Rigakafi Mai Amfani!
5. Sa’ad da yake wa’azi a arewacin Galili, menene Yesu ya gaya wa almajiransa, kuma me ya sa wannan ya sa su baƙin ciki?
5 Yesu yana wa’azi kusa da Kaisariya Filibi a arewacin Galili. Wannan kyakkyawan wuri mai salama, kamar dai zai fi dacewa da yin nishaɗi ba hana wa kai ba. Sa’ad da yake wurin, sai Yesu ya fara yi wa almajiransa bayani cewa “lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.” (Matiyu 16:21) Wannan abin baƙin ciki ne ga almajiran Yesu, domin a wannan lokacin suna tsammanin cewa Shugabansu zai kafa Mulkinsa a wannan duniya!—Luka 19:11; Ayyukan Manzanni 1:6.
6. Me ya sa Yesu ya tsawata wa Bitrus?
6 Nan da nan Bitrus “ya ja [Yesu] waje ɗaya, ya fara tsawata masa, ya ce, ‘Allah ya sawwaƙe, ya Ubangiji! Wannan har abada ba zai same ka ba!’ ” Wace amsa ce ya ba shi? “Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, ‘Ka yi nesa da ni, ya Shaiɗan! Tarko kake a gare ni. Ba ka tattalin al’amuran Allah, sai na mutane.’ ” Da bambanci a halin mutanen nan biyu! Da son rai Yesu ya karɓi tafarkin sadaukar da kai daga Allah, wanda zai kai ga mutuwarsa a kan gungumen azaba. Amma shawarar da Bitrus ya ba shi ta tafarkin rayuwa ne mai sauƙi. Ya ce, “Allah ya sawwaƙe.” Babu shakka, Bitrus na da manufa mai kyau. Duk da haka, Yesu ya tsawata wa Bitrus domin ya ƙyale Shaiɗan ya rinjaye shi a wannan lokaci. Bitrus ‘ba ya tattalin al’amuran Allah, sai na mutane.’—Matiyu 16:22, 23.
7. Kamar yadda yake a rubuce a Matiyu 16:24, wane tafarki ne Yesu ya lissafa wa almajiransa su bi?
7 Ana iya jin makamancin irin wannan kalami da Bitrus ya yi wa Yesu a yau. Wannan duniyar tana ariritar mutane, ‘su so kansu’ ko ‘su bi tafarkin rayuwa mafi sauƙi.’ A wani ɓangare kuma, Yesu ya ƙarfafa halin da ya bambanta da wannan. Ya gaya wa almajiransa: “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki [gungumen azabarsa], ya bi ni.” (Matiyu 16:24) “Wannan gayyatar ba ga marasa bi ba ne,” inji littafin nan The New Interpreter’s Bible, “amma wannan gayyata ce da ke nuna ma’anar almajiranci ga waɗanda sun riga sun amsa kiran Kristi.” Mabiya ne za su bi matakai uku da Yesu ya lissafa, kamar yadda suke a wannan nassin. Bari mu tattauna dukan matakan da ɗaiɗai da ɗaiɗai.
8. Ka bayyana ma’anar ƙin kai.
8 Na farko, dole ne mu ƙi kanmu. Kalmar Hellenanci ta “ƙin kai” na nufin kawar da son kai ko sukuni. Ƙin kai ba wai yana nufin cewa mu yi watsi da wasu nishaɗi na ɗan lokaci ba, kuma ba wai yana nufin cewa mun zama marasa farin ciki ko muna so mu halaka kanmu ba. Ba mu ‘mallaki kanmu ba’ domin mun miƙa rayuwarmu da dukan abin da muke da shi ga Jehobah da son rai. (1 Korantiyawa 6:19, 20) Maimakon mu zama masu son kai, mun zama masu son Allah. Ƙin kanmu na nuni ga ƙudurinmu na yin nufin Allah, duk da cewa ba ma son yin hakan domin ajizancinmu. Mun nuna cewa mun ba da kanmu gabaki ɗaya ga Allah sa’ad da muka keɓe kanmu a gare shi kuma muka yi baftisma. Sai mu yi ƙoƙarin cika keɓe kanmu har iyaka rayuwarmu.
9. (a) Sa’ad da Yesu yake a duniya, menene gungumen azaba ke nufi? (b) A wace hanya muka ɗauki gungumen azabarmu?
9 Mataki na biyu shi ne cewa dole ne mu ɗauki gungumenmu na azaba. A ƙarni na farko, gungumen azaba na nufin wahala, kunya, da mutuwa. Dama masu laifi ne kawai ake kashewa a kan gungumen azaba ko kuma a rataye su a kan gungumen. Da waɗannan kalaman, Yesu yana nuna cewa dole ne Kirista ya fuskanci tsanani, ƙyama, har ma da mutuwa, tun da shi ba na duniya ba ne. (Yahaya 15:18-20) Halayenmu na Kirista sun bambanta mu, saboda haka duniya take ‘zaginmu.’ (1 Bitrus 4:4) Wannan na iya faruwa a makaranta, a wurin aikinmu, ko kuma a iyali. (Luka 9:23) Duk da haka, mun ƙuduri niyyar jimre wa ƙyamarmu da duniya za ta yi domin ba ma mallakar kanmu. Yesu ya ce: “Albarka tā tabbata gare ku sa’ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta, saboda ni. Ku yi murna da farin ciki matuƙa, domin sakamakonku mai yawa ne a Sama.” (Matiyu 5:11, 12) Hakika, samun tagomashin Allah shi ne abu mafi muhimmanci.
10. Menene bin Yesu ya ƙunsa?
10 Na uku, Yesu ya ce mu ci gaba da bin shi. In ji littafin nan An Expository Dictionary of New Testament Words, na W. E. Vine, bi yana nufin zama aboki—“wanda ke tafiya a hanya ɗaya.” Yahaya na farko 2:6 ta ce: “Kowa ya ce yana zaune cikinsa [Allah], ya kamata shi kansa ma ya yi irin zaman da shi [Kristi] ya yi.” Wane irin zama ne Yesu ya yi? Saboda ƙaunar da Yesu yake yi wa Ubansa na samaniya da almajiransa bai nuna son kai ba. Bulus ya rubuta, “Almasihu ma bai yi sonkai ba.” (Romawa 15:3) Har ma sa’ad da ya gaji kuma yunwa na damunsa, Yesu ya saka bukatun mutane a bisa na sa. (Markus 6:29-34) Yesu ya yi ƙoƙari matuƙa wajen yin wa’azin Mulki da aikin koyarwa. Bai kamata mu ma mu bi sawunsa yayin da muke cika aikinmu da ƙwazo na ‘almajirtar da dukkan al’ummai, muna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da Yesu ya umarce mu’ ba? (Matiyu 28:19, 20) A cikin duka wannan, Kristi ya bar mana gurbi, kuma dole ne mu “bi hanyarsa.”—1 Bitrus 2:21.
11. Me ya sa yake da muhimmanci mu ƙi kanmu, mu ɗauki gungumen azabarmu, kuma mu ci gaba da bin Yesu Kristi?
11 Yana da muhimmanci mu ƙi kanmu, mu ɗauki gungumen azaba, kuma mu ci gaba da bin wanda muke bin Misalinsa. Idan muka yi haka za mu yi rigakafi ga son kai—wanda ke jawo tangarɗa wajen nuna ƙauna ta sadaukar da kai. Bugu da ƙari, Yesu ya ce: “Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi. Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa?”—Matiyu 16:25, 26.
Ba Za mu Iya Bauta wa Iyayengiji Biyu ba
12, 13. (a) Menene ya fi damun wannan saurayi matashi da ya nemi shawara wajen Yesu? (b) Wace shawara ce Yesu ya ba matashin, kuma me ya sa?
12 Watanni sun wuce bayan da Yesu ya nanata muhimmancin ƙin kai ga almajiransa, sai wani masarauci saurayi mai arziki ya matso wurinsa ya ce: “Malam, wane aiki nagari ne da lalle zan yi in sami rai madawwami?” Sai Yesu ya ce masa “ka kiyaye umarnan nan” kuma ya gaya masa wasu daga cikinsu. Sai saurayin ya ce masa: “Ai, duk na kiyaye waɗannan.” Mutumin ya faɗi gaskiya kuma yana iyaka ƙoƙarinsa domin ya bi Doka. Saboda haka, sai ya yi tambaya: “Me kuma ya rage mini?” Sai Yesu ya gaya wa saurayin wani abu mai muhimmanci, yana cewa: “In kana so ka zama kammalalle, sai ka je ka sayar da duk mallakarka, ka bai wa gajiyayyu, ka sami wadata a Sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.”—Matiyu 19:16-21.
13 Yesu ya ga cewa idan saurayin yana son ya bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsa, yana bukatar kawar da manyan abubuwa da za su janye zuciyarsa—wato dukiyarsa. Almajirin gaskiya na Kristi ba zai iya bauta wa iyayengiji biyu ba. Ba dama ya “bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.” (Matiyu 6:24) Yana bukatar ‘lafiyayyen ido’ da ya mai da hankali a kan abubuwa na ruhaniya. (Matiyu 6:22) Kawar da dukiya da kuma yin kyauta da su ga talakawa, na nuna ba da kai. A musanya da dukiyarsa, Yesu ya bai wa wannan saurayi masarauci gata mai tamani na tara dukiyarsa a sama—gatar da za ta zama rai madawwami a gare shi kuma za ta kai ga yin mulki tare da Kristi a sama. Saurayin ba ya son ya ƙi kansa. “Ya tafi, yana baƙin ciki, don yana da arziki ƙwarai.” (Matiyu 19:22) Amma, sauran mabiyan Yesu ba su yi haka ba.
14. Ta yaya ne masūnta huɗu suka amsa gayyatar Yesu?
14 Shekaru biyu kafin wannan, Yesu ya yi irin wannan gayyata ga masūnta huɗu, Bulus, Andarawas, Yakubu, da Yahaya. A lokacin, biyu a cikinsu na yin sū, sauran biyun kuma suna gyara tarunsu. Yesu ya ce musu: “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.” Sai su huɗun suka watsar da aikinsu na sū suka bi Yesu har ƙarshen rayuwarsu.—Matiyu 4:18-22.
15. Ta yaya ne wata Mashaidiyar Jehobah ta zamani ta sadaukar da kai domin ta bi Yesu?
15 Yawancin Kiristoci a yau sun bi misalin masūntan nan huɗu maimakon na saurayin nan masarauci. Sun sadaukar da dukiya da yin suna a wannan duniyar domin su bauta wa Jehobah. “Sa’ad da nike ’yar shekara 22, akwai wata babbar shawara da na fuskanta,” in ji Deborah. Ta ce: “Na yi nazarin Littafi Mai Tsarki na watanni shida, kuma ina son in keɓe kaina ga Jehobah, amma iyalina suna hamayya da haka. Suna da arziki sosai, kuma suna tunanin cewa idan na zama Mashaidiya hakan zai jawo musu kunya. Sun ba ni awa 24 in zaɓi abin da nike so—rayuwa ta jin daɗi ko kuwa gaskiya. Idan ban daina tarayya da Shaidun ba, iyalina za su ƙi ni. Jehobah ya taimaka mini na yi zaɓi mai kyau kuma ya ƙarfafa ni domin in cim ma hakan. Na yi shekara 42 a hidima na cikakken lokaci, kuma hakan bai sa na yi da na sani ba. Ta wajen juya wa son kai da rayuwan jin daɗi baya, na tsira daga rayuwa marar manufa da kuma rashin farin ciki da nike gani a cikin iyalina. Ni da mijina, mun taimaka wa mutane fiye da ɗari su sami gaskiya. Waɗannan ’ya’ya na ruhaniya sun fi duk wani dukiya a gare ni.” Sauran miliyoyin Shaidun Jehobah suna da farin ciki irin nata. Kai fa?
16. Ta yaya za mu iya nuna cewa ba mu ke mallakar kanmu ba?
16 Muradinsu na rashin mallakar kansu ya motsa dubban Shaidun Jehobah su yi hidimar majagaba, ko kuma yin shelar Mulki na cikakken lokaci. Wasu da yanayinsu bai sa sun yi hidima na cikakken lokaci ba, suna da ruhun majagaba kuma sun yi iyakacin ƙoƙarinsu wajen taimakawa a aikin wa’azin Mulki. Iyaye ma sun nuna irin wannan ruhu sa’ad da suka saka yawancin lokacinsu kuma suka sadaukar da abubuwan kansu domin su koyar da ’ya’yansu a ruhaniya. A kowane hali, dukanmu muna iya nuna cewa sha’awar Mulki ita ce abu ta farko a rayuwarmu.—Matiyu 6:33.
Ƙaunar Waye ce ta Motsa Mu?
17. Menene ya motsa mu mu ba da kanmu?
17 Nuna ƙauna ta ba da kai ba tafarki ba ne mai sauƙi da za a bi. Amma ka yi tunani a kan abin da ya motsa mu. Bulus ya rubuta: “Ƙaunar Almasihu gare mu ita ke mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da ya ke wani ya mutu saboda dukan mutane . . . Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin waɗanda ke raye, kada su yi zaman ganin dama nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.” (2 Korantiyawa 5:14, 15) Ƙaunar Kristi ce ta motsa mu kada mu mallaki kanmu. Wannan motsawa ce mai iko ƙwarai! Tun da yake Kristi ya mutu dominmu, ba ma ganin cewa ya kamata ya mallake mu? Hakika, godiya ga ƙauna mai zurfi da Allah da kuma Kristi suka nuna mana ne ya motsa mu mu keɓe rayuwarmu ga Allah, kuma mu zama almajiran Kristi.—Yahaya 3:16; 1 Yahaya 4:10, 11.
18. Me ya sa tafarkin sadaukar da kai ke da amfani?
18 Rashin mallakar kanmu na da wani amfani kuwa? Bayan wannan saurayi masarauci ya ƙi gayyatar da Kristi ya yi masa kuma ya kama gabansa, sai Bitrus ya ce wa Yesu: “To, ai, ga shi mun bar kome, mun bi ka. Me za mu samu ke nan?” (Matiyu 19:15-27) Hakika, Bitrus da sauran manzannin sun riga sun ƙi kansu. Wane lada ne za su samu? Da farko, Yesu ya ambata gatan da za su samu na yin mulki tare da shi a sama. (Matiyu 19:28) Sa’an nan kuma, Yesu ya faɗi albarkatun da kowane almajirinsa zai samu. Ya ce: “Ba wanda zai bar gida, ko ’yan’uwansa mata, ko ’yan’uwansa maza, ko uwa tasa, ko ubansa, ko ’ya’yansa, ko gonakinsa, sabili da ni da kuma bishara, sa’an nan ya kasa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu . . . a [zamani mai zuwa] kuma ya sami rai madawwami.” (Markus 10:29, 30) Mun sami fiye da abubuwan da muka sadaukar. Ubanninmu, da iyayenmu mata, da ’yan’uwa maza da mata, da yara na ruhaniya, ba su fi abubuwa da muka ƙi domin Mulki tamani ba? Wanene ke da rayuwa mai albarka—Bitrus ko wannan saurayi masarauci?
19. (a) Farin ciki na gaskiya ya dangana a kan menene? (b) Menene za mu tattauna a talifi na gaba?
19 Ta kalmominsa da ayyukansa, Yesu ya nuna cewa ana samun farin ciki ne ta wajen bayarwa da kuma yin hidima, ba daga son kai ba. (Matiyu 20:28; Ayyukan Manzanni 20:35) Sa’ad da muka sadaukar da kanmu kuma muka ci gaba da bin Kristi, muna samun gamsuwa na rayuwa a yanzu da kuma begen rai madawwami a nan gaba. Hakika, idan muka ƙi kanmu, Jehobah zai zama Mamallakinmu. Da haka, mun zama bayin Allah. Me ya sa wannan bauta na da muhimmanci? Ta yaya yake shafan shawarwarin da muke yi a rayuwarmu? Talifi na gaba zai tattauna waɗannan tambayoyin.
Ka Tuna?
• Me ya sa ya kamata mu yi rigakafi ga tunaninmu na son kai?
• Menene ma’anar mu ƙi kanmu, mu ɗauki gungumenmu na azaba, da kuma ci gaba da bin Yesu?
• Menene ya motsa mu mu sadaukar da kanmu?
• Me ya sa rayuwa ta sadaukar da kai ke da amfani?
[Hoto a shafi na 11]
“Allah ya sawwaƙe, ya Ubangiji”
[Hoto a shafi na 13]
Menene ya hana wannan saurayi masarauci bin Yesu?