“Sayenku Aka Yi Da Tamani”
“Sayenku aka yi da tamani. To, sai ku ɗaukaka Allah.”—1 KORANTIYAWA 6:20.
1, 2. (a) In ji Dokar Musa, yaya za a bi da Isra’ilawan da suka zama bayi? (b) Wane zaɓi ne bawan da ke ƙaunar ubangijinsa yake da shi?
“BAUTA aba ce da ta wanzu kuma ta zama karɓaɓɓiya a duniyar dā,” inji littafin nan Holman Illustrated Bible Dictionary. Ya daɗa cewa: “Tattalin arzikin Masar, Hellas, da Roma ya dangana ne a kan bayi. A ƙarni na farko na Kiristoci, ɗaya cikin mutane uku da ke ƙasar Italiya da kuma ɗaya cikin biyar a sauran ƙasashe bayi ne.”
2 Ko da yake bauta ta wanzu a Isra’ila ta dā, Dokar Musa ta tabbata cewa Ibraniyawa da suka zama bayi sun sami kāriya. Alal misali, Dokar ta ce, Ba’isra’ile na iya yin bauta da ba ta wuce ta shekaru shida ba. A shekara ta bakwai kuwa, a “yantar da shi kyauta.” Amma umurnai game da yadda za a bi da bayi suna da kyau har ya sa Dokar Musa ta yi tanadin abin da ke gaba: “Idan hakika bawa ya hurta ya ce, yana ƙaunar ubangijinsa, da matarsa, da ’ya’yansa, ba ya son ’yancin, to, sai ubangijinsa ya kawo shi a gaban Allah a ƙofa ko a madogarar ƙofa, sa’an nan ubangijinsa ya huda kunnensa da abin hudawa. Zai bauta wa ubangijinsa muddin ransa.”—Fitowa 21:2-6; Littafin Firistoci 25:42, 43; Maimaitawar Shari’a 15:12-18.
3. (a) Wace irin bauta ce Kiristoci na ƙarni na farko suka yarda da ita? (b) Me ke motsa mu mu bauta wa Allah?
3 Tanadin bauta na son rai na kwatanta irin bautar da Kiristoci na gaskiya ke ƙarƙashinsa. Alal misali, marubutan Littafi Mai Tsarki, Bulus, Yakubu, Bitrus, da Yahuza sun ƙira kansu bayin Allah da Kristi. (Titus 1:1; Yakubu 1:1; 2 Bitrus 1:1; Yahuza 1) Bulus ya tuna wa Kiristocin da ke Tasalonika cewa sun ‘rabu da gumaka, sun juyo ga Allah, domin su bauta wa Allah Rayayye na gaskiya.’ (1 Tasalonikawa 1:9) Menene ya motsa waɗannan Kiristocin su zama bayin Allah da son rai? To, menene ke motsa Ba’isra’ile da ke bauta ya ƙi ’yancinsa? Ba domin ƙaunar da yake yi wa ubangijinsa ba ne? Bauta ta Kirista na bisa ƙaunar Allah ne. Sa’ad da muka san Allah mai rai na gaskiya kuma muka ƙaunace shi, mun motsa mu bauta masa ‘da zuciya ɗaya da dukan ranmu.’ (Maimaitawar Shari’a 10:12, 13) Menene zama bawan Allah da na Kristi ya ƙunsa? Ta yaya hakan ya shafi rayuwarmu ta yau da kullum?
“Ku Yi Kome Saboda Ɗaukakar Allah”
4. Ta yaya muka zama bayin Allah da Kristi?
4 An ba da ma’anar bawa cewa “mutum ne wanda ya zama dukiyar wani ko wasu kuma dole ya yi cikakkiyar biyayya.” Mun zama dukiyar Jehobah sa’ad da muka keɓe rayuwarmu a gare shi kuma muka yi baftisma. Manzo Bulus ya ce: “Ku ba mallakar kanku ba ne. Sayenku aka yi da tamani.” (1 Korantiyawa 6:19, 20) Wannan aba mai tamani ita ce fansar hadaya ta Yesu Kristi, wannan dalilin ne ya sa Allah ya karɓe mu a matsayin bayinsa, ko mu shafaffun Kiristoci ne ko abokansu da ke da begen zama a duniya. (Afisawa 1:7; 2:13; Wahayin Yahaya 5:9) Saboda haka, tun a lokacin da muka yi baftisma, “na Ubangiji ne mu.” (Romawa 14:8) Tun da yake an fanshe mu da jinin nan mai daraja na Yesu Kristi, mun zama bayinsa ke nan, kuma dole ne mu bi umurninsa.—1 Bitrus 1:18, 19.
5. A matsayinmu na bayin Jehobah, menene ainihin farillan da muke da shi, kuma yaya za mu iya cim ma hakan?
5 Dole ne bawa ya yi wa ubangijinsa biyayya. Bautarmu ta son rai ce kuma ƙaunar da muke yi wa Ubangijinmu ne ke motsa ta. “Domin ƙaunar Allah,” in ji 1 Yahaya 5:3, “ita ce mu bi umarninsa, umarninsa kuwa ba matsananta ba ne.” Biyayyarmu tana nuna miƙa kanmu da kuma ƙaunarmu. Tana bayyana a dukan abin da muke yi. “Duk abin da kuke yi, ko ci, ko sha,” in ji Bulus, “ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.” (1 Korantiyawa 10:31) A rayuwa ta yau da kullum, har ma a ƙananan abubuwa, muna so mu nuna cewa muna “bauta wa Ubangiji.”—Romawa 12:11.
6. Ta yaya ne zama bawan Allah ke shafan shawarwarin da muke yi a rayuwa? Ka kwatanta wannan da wani misali.
6 Sa’ad da muke yanke shawarwari, ya kamata mu mai da hankali, mu yi tunani sosai a kan ra’ayin Ubangijinmu na sama, Jehobah. (Malakai 1:6) Shawarwari masu wuya suna iya gwada biyayyarmu ga Allah. Za mu bi shawararsa maimakon bin tunanin zuciyarmu mai “rikici” kuma mai “cuta?” (Irmiya 17:9) Melisa, wata Kirista marar aure ce da ba ta daɗe da yin baftisma ba, sai wani saurayi ya fara sha’awarta. Ya yi kamar shi mutumin kirki ne, kuma yana nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Duk da haka, wani dattijo ya gaya wa Melisa game da hikimar bin umurnin Jehobah wajen aurar “mai bin Ubangiji.” (1 Korantiyawa 7:39; 2 Korantiyawa 6:14) “Bin wannan shawarar ba ta da sauƙi,” in ji Melisa. “Amma sai na yanke shawarar cewa tun da na riga na keɓe kaina ga Jehobah domin in yi nufinsa, zan yi biyayya ga dukan umurninsa.” Sa’ad da take tunani a kan abin da ya faru daga baya, sai ta ce: “Na yi farin ciki da na bi wannan shawarar. Ba da daɗe wa ba mutumin ya daina nazari. Da a ce mun ci gaba da wannan dangantaka, da na auri marar bi.”
7, 8. (a) Me ya sa bai kamata mu cika damuwa da faranta wa mutane zuciya ba? (b) Ka kwatanta yadda za a iya kawar da tsoron mutane.
7 A matsayinmu na bayin Allah, ba za mu zama bayin mutane ba. (1 Korantiyawa 7:23) Hakika, babu wani cikinmu da ba ya so ya zama sananne, amma dole ne mu tuna cewa mizanan Kiristoci sun bambanta da na mutanen duniya. Bulus ya yi tambaya: “Ƙoƙari nake yi in faranta wa mutane zuciya?” Ya ƙarasa da cewa: “Da har yanzu mutane nake faranta wa zuciya, ai, da ban zama bawan Almasihu ba.” (Galatiyawa 1:10) Ba za mu faɗa wa matsi na tsara kuma mu zama masu faranta wa mutane zuciya ba. Saboda haka, me za mu yi idan muka fuskanci matsi na daidaita da mutane?
8 Yi la’akari da misalin Elena wata Kirista matashiya a ƙasar Spain. Akwai abokan ajinta da yawa da suke ba da jini. Sun san cewa Elena Mashaidiyar Jehobah ce, ba za ta ba da jini ba kuma ba za ta karɓi ƙarin jini ba. Sa’ad da zarafi ya taso ta bayyana matsayinta ga dukan ’yan ajinta, Elena ta yi gabatarwa. “A gaskiya, hakan ya sa ni rawar jiki,” in ji Elena. “Amma na yi shiri sosai kuma na sami sakamako mai kyau. Yawancin abokan ajina suka fara daraja ni, kuma malaminmu ya gaya mini cewa yana yaba wa aikin da nike yi. Fiye da haka, na sami gamsuwa cewa na kāre sunan Jehobah kuma na bayyana sarai dalilai na imanina na Nassi.” (Farawa 9:3, 4; Ayyukan Manzanni 15:28, 29) Hakika, mu bayin Allah da Kristi, mun bambanta. Amma fa, mutane za su daraja mu idan muna a shirye mu kāre imaninmu a cikin biyayya.—1 Bitrus 3:15.
9. Menene muka koya daga wani mala’ika da ya bayyana ga manzo Yahaya?
9 Tuna cewa mu bayin Allah ne zai taimaka mana mu kasance da tawali’u. A wani lokaci, manzo Yahaya ya sami wahayi na Urushalima na samaniya kuma hakan ya burge shi sosai har ya faɗi a gaban mala’ikan da ya wakilci Allah wurin magana domin ya yi masa sujada. Sai mala’ikan ya ce masa: “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ’yan’uwanka annabawa, da kuma waɗanda ke kiyaye maganar littafin nan. Allah za ka yi wa sujada.” (Wahayin Yahaya 22:7-9) Wannan mala’ikan ya kafa wa dukan bayin Allah misali mai kyau! Wataƙila wasu Kiristoci suna da hakki na musamman a cikin ikilisiya. Duk da haka, Yesu ya ce: “Duk wanda ke son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku. Wanda duk kuma ke so ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawanku.” (Matiyu 20:26, 27) Mu mabiyan Yesu, dukanmu bayi ne.
“Mun dai Yi Abin da ke Wajibinmu Kurum.”
10. Ka ba da misalai na Nassi da suka nuna cewa yin nufin Allah bai yi wa amintattun bayinsa sauƙi ba.
10 Yin nufin Allah ba abu ba ne mai sauƙi ga mutane ajizai. Annabi Musa ya yi jinkiri ya yi biyayya sa’ad da Jehobah ya gaya masa ya je ya fito da ’ya’yan Isra’ila daga bauta a ƙasar Masar. (Fitowa 3:10, 11; 4:1, 10) Sa’ad da ya sami aikin shelar hukunci ga mutanen Nineba, Yunusa “ya gudu daga wurin Ubangiji zuwa Tarshish.” (Yunusa 1:2, 3) Baruk, wanda shi ne magatakardan annabi Irmiya ya yi kukan gajiya. (Irmiya 45:2, 3) Me ya kamata mu yi sa’ad da burinmu ko abin da muke so ya yi saɓani da nufin Allah? Misalin da Yesu ya ba da ya amsa wannan tambayar.
11, 12. (a) Ka ɗan taƙaita misalin da Yesu ya ba da, da ke Luka 17:7-10. (b) Wane darasi ne muka koya daga misalin Yesu?
11 Yesu ya yi magana game da wani bawa wanda ke kula da tumakin ubangijinsa tun da safe a jeji. Sa’ad da ya dawo da yamma a gajiye, ubangijinsa bai gayyace shi ya zo ya ci abinci ba. Maimakon haka, sai ubangijinsa ya ce: “Shirya mini jibi, ka kuma yi ɗamara, ka yi mini hidima, har in gama ci da sha, daga baya kai kuma ka ci ka sha.” Bawan na iya kula da na shi bukatun ne kawai, idan ya gama kula da na ubangijinsa. Yesu ya kammala wannan misalin yana cewa: “Haka ku ma, in kuka bi duk abin da aka umarce ku, sai ku ce, ‘Mu bayi ne marasa amfani. Mun dai yi abin da ke wajibinmu kurum.’ ”—Luka 17:7-10.
12 Ba wai Yesu ya ba da wannan misalin ba ne domin ya nuna cewa, Jehobah bai yaba wa abin da muke yi a hidimarsa. Littafi Mai Tsarki ya ce dalla-dalla: “Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi.” (Ibraniyawa 6:10) Maimako, abin da misalin Yesu ke nufi shi ne, bawa ba zai so kansa ba ko kuma ya mai da hankali a kan holewarsa. Sa’ad da muka keɓe kanmu ga Allah kuma muka zama bayinsa, mun yarda ke nan mu saka nufinsa a gaba da namu. Dole ne mu saka nufin Allah a gaban namu.
13, 14. (a) A waɗanne yanayi ne ya kamata mu kawar nufe-nufenmu? (b) Me ya sa za mu ƙyale nufin Allah ya kasance?
13 Yin nazarin Kalmar Allah a kowane lokaci da kuma littattafan “amintaccen bawan nan mai hikima” na iya bukatar ƙoƙari matuƙa a gare mu. (Matiyu 24:45) Wannan na iya faruwa musamman idan yana yi mana wuya mu yi karatu ko kuwa idan littafin na tattauna “zurfafan al’amuran Allah.” (1 Korantiyawa 2:10) Bai kamata mu nemi lokacin yin nazari na kai ba? Wataƙila muna bukatan mu horar da kanmu don mu zauna kuma mu ba da lokaci wajen nazarin. Idan ba mu yi haka ba, ta yaya za mu yi marmarin “abinci mai tauri, . . . na manya”?—Ibraniyawa 5:14.
14 A lokatai da muka dawo gida kuma muka ji cewa mun gaji bayan dogon aiki fa? Wataƙila za mu same shi da wuya mu halarci tarurruka na Kirista. Ko kuwa ba za mu so mu yi wa baƙi wa’azi ba. Bulus da kansa ya fahinci cewa akwai wasu lokatai da muke shelar bishara ‘ba da son ranmu ba.’ (1 Korantiyawa 9:17) Amma fa, muna yin waɗannan abubuwa ne domin Jehobah—Ubangijinmu na sama wanda muke ƙauna, shi ya umurce mu mu yi hakan. Ba ma jin daɗi da kuma wartsakewa bayan mun yi iyakacin ƙoƙarinmu mu yi nazari, mu halarci tarurruka, da kuma wa’azi?—Zabura 1:1, 2; 122:1; 145:10-13.
Kada ka ‘Duba Baya’
15. Ta yaya Yesu ya kafa misali na yin biyayya ga Allah?
15 Yesu Kristi ya nuna biyayyarsa ga Ubansa na samaniya a mafificin hanya. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Na sauko daga sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.” (Yahaya 6:38) Sa’ad da yake cikin baƙin ciki a lambun Gatsemani, ya yi addu’a: “Ya Ubana, in mai yiwuwa ne, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalan nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.”—Matiyu 26: 39.
16, 17. (a) Yaya ya kamata mu ɗauki abubuwa da muka bari a baya? (b) Ka nuna yadda Bulus ainihi ya ɗauki abubuwa na duniya “hasara.”
16 Yesu Kristi yana so mu kasance da aminci ga shawarar da muka yanke na zama bayin Allah. Ya ce: “Wanda ya fara huɗa da keken noma, yana duban baya, bai dace da Mulkin Allah ba.” (Luka 9:62) Yin tunani a kan abin da muka bari a baya ba abin da ya dace ba ne sa’ad da muke bauta wa Allah. Maimakon haka, mu daraja abin da muka samu na zama bayin Allah. Ga Filibiyawa, Bulus ya rubuta: “Na ɗauki dukkan abubuwa hasara ne, a kan mafificiyar darajar sanin da nake yi na Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shi ne na zaɓi yin hasarar dukkan abubuwa, har ma na mai da su tozari domin Almasihu yā zama nawa.”—Filibiyawa 3:8.
17 Ka yi tunani a kan dukan abubuwa da Bulus ya ɗauka abin hasara kuma ya yi watsi da su domin lada na ruhaniya a matsayinsa na bawan Allah. Ya yi watsi da holewa na duniya, wataƙila, tare da zama shugaban addinin Yahudawa. Da Bulus ya ci gaba da bin addinin Yahudanci, ƙila da ya sami irin maƙamin Siman, ɗan malaminsa, Gamaliyal. (Ayyukan Manzanni 22:3; Galatiyawa 1:14) Siman ya zama shugaban Farisiyawa kuma ya ja-goranci tawayen da Yahudawa suka yi ga Romawa a shekara ta 66-70 A.Z., duk da cewa suna da shakka. Ya mutu a wannan hargitsin, wataƙila a hannun Bayahude ko sojojin Roma.
18. Ka ba da wani misali da ya nuna yadda abubuwa da aka cim ma na ruhaniya ke kawo lada.
18 Yawancin Shaidun Jehobah sun bi misalin Bulus. “Bayan wasu ’yan shekaru da gama makaranta, na sami aikin babban magatakarda na wani sanannen lauya a Landan,” in ji Jean. “Ina jin daɗin aikina ina kuma samun isashen kuɗi, amma a zuciya ta na san cewa zan iya ƙara ƙoƙari a bauta wa Jehobah. A ƙarshe, sai na yi murabus kuma na zama majagaba. Na yi farin ciki cewa na ɗauki wannan matakin shekaru 20 da suka shige! Hidima ta ta cikakken lokaci ta wadatar da raina fiye da yadda kowane irin aikin magatakarda zai yi. Babu abin da zai iya ba da gamsarwa kamar ganin yadda Kalmar Jehobah ta canja rayuwar mutum. Saka hannu a wannan aikin abu ne mai ban al’ajabi. Ba ma iya kwatanta abin da muka samu daga hannun Jehobah da abin da muka ba shi.”
19. Menene ya kamata ya zama ƙudurinmu, kuma me ya sa?
19 Yanayinmu na iya canjawa. Amma, keɓewarmu ga Allah ba zai canja ba. Har yanzu mu bayin Jehobah ne, kuma ya ƙyale mu mu zaɓi yadda za mu yi amfani da lokacinmu, ƙarfi, baiwa, da kuma dukiya a hanya mai kyau. Saboda haka, zaɓin da muka yi na iya nuna ƙaunar da muke yi wa Allah. Kuma suna nuna ko muna da niyyar sadaukar da kanmu. (Matiyu 6:33) Ko yaya yanayinmu, bai kamata mu ƙudurta za mu bai wa Jehobah abu mafi kyau ba? Bulus ya rubuta: “In mutum na da niyyar bayarwa, bayarwa tasa za ta zama abar karɓa ce bisa ga yawan abin da ya ke da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.”—2 Korantiyawa 8:12.
Kuna Samun “Sakamakonku”
20, 21. (a) Wane irin hali ne bayin Allah suke nuna wa? (b) Yaya ne Jehobah yake yin albarka ga waɗanda suka ba shi abu mafi kyau?
20 Zama bayin Allah ba zalunci ba ne. Akasarin haka, tana kāre mu daga wata irin bauta da za ta hana mu farin ciki. “Yanzu da aka ’yanta ku daga bautar zunubi, kun zama bayin Allah,” Bulus ya rubuta, “sakamakonku shi ne tsarkakewa, ƙarshenta kuwa rai madawwami.” (Romawa 6:22) Zama bayin Allah na kawo sakamako a tsarkakkiyar hanya domin muna amfana daga tsarkakken ɗabi’a. Ƙari ga haka, za ta kawo rai madawwami a nan gaba.
21 Jehobah na nuna karimci ga bayinsa. Sa’ad da muka yi iyakacin ƙoƙarinmu a hidimarsa, yana buɗe mana “taskokin sama” kuma ya zubo mana “albarka mai yawan gaske.” (Malakai 3:10) Zai zama abin farin ciki mu ci gaba da kasancewa bayin Jehobah har abada!
Ka Tuna?
• Me ya sa muka zama bayin Allah?
• Ta yaya muke nuna biyayyarmu ga nufin Allah?
• Me ya sa ya kamata mu kasance a shirye mu saka nufin Jehobah a gaban namu?
• Me ya sa bai kamata mu “duba baya” ba?
[Hoto a shafi na 16]
Tanadin bauta na son rai a Isra’ila na kwatanta irin bautar da Kiristoci ke yi
[Hoto a shafi na 18]
Musa ya yi jinkiri wajen karɓan aikin da aka ba shi