Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 10/15 pp. 25-29
  • Menene Za Ka Yi Don Ka Ci Gaba Da Rayuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Menene Za Ka Yi Don Ka Ci Gaba Da Rayuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Kristi Bai Yi Son Kai Ba’
  • Jehobah Yana So Mu Ba Shi Abu Mafi Kyau
  • Ka Yi Amfani da Lokacinka da Kyau
  • “Ina Tare da Ku Kullayaumi”
  • Kada Mu Yi Zaman Ganin Dama
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Me Ya Sa Za Ka Bi “Kristi”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • An Koyar Da Su Domin Su Yi Wa’azi Da Kyau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • ‘Ka Zo Ka Bi Ni’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 10/15 pp. 25-29

Menene Za Ka Yi Don Ka Ci Gaba Da Rayuwa?

“Ina kuwa abin da mutum za ya bayas musanyar ransa?”—MAT. 16:26.

1. Me ya sa Yesu ya ƙi abin da Bitrus ya ce?

MANZO Bitrus ya yi mamakin abin da ya ji. Ƙaunataccen shugabansa Yesu Kristi, ya “faɗi a sarari” cewa ba da daɗewa ba zai sha wuya kuma ya mutu. Sai Bitrus da ra’ayi mai kyau ya tsauta wa Yesu, ya ce: “Allah shi sawaƙa maka, Ubangiji, wannan ba za ya same ka ba daɗai.” Yesu ya waiwaya ya kalli sauran almajiran. Wataƙila su ma sun yarda da wannan shawara marar kyau. Sai ya ce wa Bitrus: “Ka koma bayana, Shaitan: abin tuntuɓe ka ke a gareni; gama ba ka yi tattalin abin da ke na Allah ba, sai na mutane.”—Mar. 8:32, 33; Mat. 16:21-23.

2. Ta yaya ne Yesu ya nuna abin da ake bukata don a zama almajirin gaske?

2 Wataƙila kalaman da Yesu ya yi daga baya ya taimaki Bitrus ya fahimci dalilin da ya sa Yesu ƙi abin da Bitrus ya ce masa. Yesu ya “kirawo taron tare da almajiransa” ya ce: “Idan kowane mutum yana da nufi shi bi ni, sai shi yi musun kansa, shi ɗauki gicciyensa, shi biyo ni. Gama dukan wanda ya ke nufi shi ceci ransa, ɓadda shi za ya yi; amma dukan wanda ya ke ɓadda ransa sabili da ni da bishara, cetonsa za ya yi.” (Mar. 8:34, 35) Hakika, ba saɗaukar da ransa kawai ba ne zai yi amma yana bukatar waɗanda suke binsa su kasance a shirya su saɗaukar da ransu a hidimar Allah. Idan suka yi hakan, za su sami lada mai yawa.—Ka karanta Matta 16:27.

3. (a) Waɗanne tambayoyi ne Yesu ya yi wa masu sauraronsa? (b) Mecece tambayar Yesu ta biyu ta tuna wa masu sauraronsa?

3 A wannan ranar, Yesu ya yi tambaya guda biyu masu motsa zuciya: “Ina abin da mutum ya ribato, shi sami dukan duniya, ya ruɓusadda ransa? Gama ina abin da mutum za ya bayas musanyar ransa?” (Mar. 8:36, 37) Babu shakka, ’yan adam za su san amsar tambaya ta farkon. Ba shi da amfani mutum ya mallaki dukan duniya sannan ya rasa ransa. Abubuwan duniya suna da amfani ne kawai idan mutum yana da rai da zai more su. Tambayar Yesu ta biyu: “Ina abin da mutum za ya bayas musanyar ransa?” wataƙila ya tuna wa masu sauraransa abin da Shaiɗan ya ce a zamanin Ayuba: “Dukan abin da mutum ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa.” (Ayu. 2:4) Ga mutanen da ba sa bauta wa Jehobah, kalaman Shaiɗan za su kasance gaskiya. Wasu mutane za su yi kome, su ƙi bin kowace ƙa’ida don su rayu. Amma Kiristoci sun ɗauki abubuwa dabam.

4. Me ya sa tambayoyin da Yesu ya yi suke da ma’ana sosai ga Kiristoci?

4 Mun san cewa Yesu bai zo duniya don ya ba mu ƙarfin jiki, arziki, da kuma tsawon rai a wannan duniyar ba. Ya zo ne don ya buɗe zarafin yin rayuwa ta har abada a sabuwar duniya, kuma begen wannan rayuwar shi ne muke riƙe da muhimmanci. (Yoh. 3:16) Kirista zai fahimci cewa abin da Yesu yake nufi a tambayarsa ta farko shi ne, “Ina amfani mutum ya mallaki dukan duniya amma ya rasa rai ta har abada?” Amsar ita ce, babu amfani ko kaɗan. (1 Yoh. 2:15-17) Don mu sami amsar tambayar Yesu ta biyu, za mu iya tambayar kanmu, ‘Ina shirye na saɗaukar da kaina sosai yanzu don in tabbata cewa begen yin rayuwa a sabuwar duniya za ta yiwu?’ Muna ba da amsar wannan tambayar ta hanyar rayuwarmu, da take nuna irin begen da muke da shi a zuciyarmu.—Ka gwada Yoh. 12:25.

5. Ta yaya za mu iya samun kyautar rai na har abada?

5 Hakika, ba wai Yesu yana cewa mun cancanci samun rai ba ne. Rayuwarmu a wannan zamanin da ba ta da tsawo ma kyauta ce. Ba za mu iya sayensa ba ko kuma mu yi abubuwan da za su sa mu cancanci samun ta ba. Hanya ɗaya da za mu iya samun rai ta har abada ita ce mu kasance da ‘bangaskiya ta wurin Yesu Kristi’ da kuma Jehobah, “mai-sākawa . . . ga waɗanda ke biɗarsa.” (Gal. 2:16; Ibran. 11:6) Duk da haka, dole ne mu nuna bangaskiyarmu ta ayyuka, tun da “bangaskiya ba tare da ayyuka mataciya ce.” (Yaƙ. 2:26) Amma, idan muka ƙara yin bimbini bisa tambayar da Yesu ya yi, hakan zai sa mu yi tunani sosai game da sadaukar da kai da za mu iya yi a wannan zamanin da kuma abin da za mu iya yi a hidimar Jehobah don mu nuna cewa bangaskiyarmu rayayya ce.

‘Kristi Bai Yi Son Kai Ba’

6. Menene Yesu ya mai da hankali a kai?

6 Maimakon ya sa ido ga abubuwan duniya na zamaninsa, Yesu ya mai da hankali ga abubuwa masu muhimmanci kuma ya ƙi gwajin da zai sa ya tara abubuwan duniya don ya ji daɗin rayuwa. Rayuwarsa ta sadaukar da kai ce da kuma biyayya ga Allah. Maimakon ya gamsar da kansa, ya ce: ‘Ina aikata abin da ya gamshe [Allah].’ (Yoh. 8:29) Menene Yesu ya yi don ya gamshi Allah?

7, 8. (a) Wace sadaukar da kai ne Yesu ya yi, kuma ta yaya ya sami lada? (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu tambayi kanmu?

7 Akwai lokacin da Yesu ya ce wa almajiransa: “Ɗan mutum ya zo ba domin a yi masa bauta ba, amma domin shi bauta ma waɗansu, shi bada ransa kuma abin fansar mutane dayawa.” (Mat. 20:28) A lokacin da Yesu ya gaya wa almajiransa cewa ba da daɗewa ba zai “bada ransa,” Bitrus ya ce masa Allah shi sawaƙa maka. Duk da haka, Yesu ya kasance a faɗake. Ya ba da kamiltaccen ransa da son rai, don mutane. Don ya bi tafarki na rashin son kai, Yesu ya tsare rayuwarsa ta nan gaba. An ta da shi daga matattu kuma an “ɗaukaka shi ga hannun dama na Allah.” (A. M. 2:32, 33) A haka, ya kafa mana misali mai kyau.

8 Manzo Bulus ya shawarci Kiristoci na Roma ‘kada su yi son kai’ ya kuma tuna musu cewa “Kristi kuma ba ya yi son kai ba.” (Rom. 15:1-3) To, ta yaya za mu bi umurnin waɗannan mazannin kuma mu yi koyi da Kristi?

Jehobah Yana So Mu Ba Shi Abu Mafi Kyau

9. Menene Kirista da gaske yake nunawa sa’ad da ya keɓe kansa ga Allah?

9 A Isra’ila ta dā, Dokar Musa ta ce a ba bayin Ibraniyawa ’yancin kai a shekara ta bakwai da suka yi bauta ko kuma a shekarar ’yanci. Amma, suna da wata zaɓi. Idan bawa yana ƙaunar shugabansa sosai, zai iya zaɓi ya ci gaba da bauta a gidan har abada. (Ka karanta Kubawar Shari’a 15:12, 16, 17.) Haka yake sa’ad da muka keɓe kanmu ga Allah. Mun yarda da son ranmu cewa za mu yi nufin Allah ba nufinmu ba. Ta yin haka, muna nuna ƙaunarmu ga Jehobah kuma da muradin bauta masa har abada.

10. A wace hanya ce muka zama kayan Allah, kuma ta yaya sanin haka ya kamata ya shafi tunaninmu da ayyukanmu?

10 Idan kana yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, kana shelar bishara kuma kana halartar taron Kirista, muna yabon ka. Muna sa rai cewa ba da daɗewa ba abin da kake yi zai motsa ka ka keɓe kanka ga Jehobah kuma ka yi irin tambayar da Bahabashen nan ya yi wa Filibus: “Me za ya hana a yi mini baftisma?” (A. M. 8:35, 36) Dangatakarka da Allah za ta zama kamar na Kiristocin da Bulus ya ce musu: “Ku kuwa ba na kanku ba ne; gama aka saye ku da tamani.” (1 Kor. 6:19, 20) Ko begenmu na zuwa sama ne ko na yin rayuwa a duniya, idan muka keɓe kanmu ga Jehobah, mun zama nasa. Abu mai muhimmanci ne mu ƙi son kai kuma mu ƙi “zama bayin mutane.” (1 Kor. 7:23) Gata ne mu zama bayi amintattu ga Jehobah don ya yi amfani da mu yadda yake so.

11. Wace irin hadaya ce aka aririci Kiristoci su ba da, kuma menene hakan yake nufi, kamar yadda aka kwatanta da hadaya a Dokar Musa?

11 Bulus ya aririci ’yan’uwa masu bi: “Ku miƙa jikunanku hadaya mai-rai mai-tsarki, abin karɓa ga Allah, bautarku mai-ruhaniya ke nan.” (Rom. 12:1) Waɗannan kalaman sun tuna wa Kiristoci Yahudawa irin hadayu da suke yi a addininsu na dā kafin su zama mabiyan Yesu. Ya kamata su sani cewa a Dokar Musa ana bukatar a yi amfani da dabbobi masu kyau sosai idan za a yi hadaya a bagadin Jehobah. Ba za a karɓi dabbobi marasa kyau ba. (Mal. 1:8, 13) Haka yake idan muka miƙa jikunanmu “hadaya mai-rai.” Muna ba wa Jehobah abin mu mafi kyau, ba sai mun gamsu kafin mu ba wa Jehobah ba. Idan muka keɓe kanmu ga Allah, za mu ba shi ‘ranmu,’ har da ƙarfinmu, arzikinmu, da kuma ingancinmu. (Kol. 3:23) Ta yaya za mu yi hakan a rayuwarmu?

Ka Yi Amfani da Lokacinka da Kyau

12, 13. Wace hanya ɗaya ce za mu iya ba wa Jehobah abu mafi kyau?

12 Wata hanya da za mu ba Jehobah abu mai kyau ita ce ta yin amfani da lokacinmu da kyau. (Ka karanta Afisawa 5:15, 16.) Hakan na bukatar mu kame kanmu. Rinjaya daga duniya da kuma ajizancinmu suna iya sa mu yi amfani da lokacinmu don jin daɗi. Hakika, “ga kowane abu akwai nasa kwanaki,” hakan ya ƙunshi lokacin nishaɗi da lokacin aiki don mu cika hakkinmu na Kirista. (M. Wa. 3:1) Amma, ya kamata Kirista da ya keɓe kai ya daidaita abubuwa kuma ya yi amfani da lokacinsa da kyau.

13 Sa’ad da Bulus ya ziyarci Atina, ya lura cewa “dukan Athinawa fa da baƙi mazamna a wurin ba su sha’anin komi ba, sai ko su jiyas ko kuwa su ji wani sabon abu.” (A. M. 17:21) A yau, mutane da yawa suna ɓata lokacinsu. Abubuwa na zamani da suke jan hankalin mutane sun ƙunshi kallon talabijin, wasan bidiyo, da kuma yin amfani da Intane. Akwai abubuwa da yawa da suke janye hankalinmu kuma su sa mu ɓata lokacinmu. Idan muka bari suka janye mana hankali, za mu mance da samun ilimin Jehobah. Za mu gaskata cewa ba mu da lokacin yin “mafifitan al’amura” wato, abubuwa da suka shafi bautar Jehobah.—Filib. 1:9, 10.

14. Waɗanne tambayoyi ne suke bukatar mu mai da musu hankali sosai?

14 Saboda haka, idan kai bawa ne da ka keɓe kanka ga Jehobah, ka tambayi kanka, ‘Ayyukata ta kowace rana ta ƙunshi karatun Littafi Mai Tsarki, yin bimbini, da kuma addu’a kuwa?’ (Zab. 77:12; 119:97; 1 Tas. 5:17) ‘Ina keɓe lokaci don in shirya taron Kirista kuwa? Ina ƙarfafa wasu da kalamai na a taro kuwa?’ (Zab. 122:1; Ibran. 2:12) Kalmar Allah ta ce Bulus da abokansa “da daɗewa . . . suna yin magana gaba gaɗi cikin Ubangiji.” (A. M. 14:3) Za ka iya daidaita yanayinka ka yi aikin wa’azi “da daɗewa,” har ma ka zama majagaba?—Ka karanta Ayukan Manzani 14:3.

15. Ta yaya ne dattawa suke amfani da lokacinsu da kyau?

15 Sa’ad da manzo Bulus da wasu maza amintattu suka ziyarci ikilisiyar Kirista a Antakiya, “suka zauna kwanaki ba kaɗan ba tare da masu-bi” don su ƙarfafa su. (A. M. 14:28) A yau dattawa masu ƙauna suna ba da lokacinsu don su ƙarfafa wasu. Ban da hidima ta wa’azi da suke yi, suna aiki tuƙuru don su ƙarfafa tumaki, su nemi tumaki da suka ɓata, su taimaki marasa lafiya, kuma su kula da wasu hakki da yawa a cikin ikilisiya. Idan kai ɗan’uwa ne da ka keɓe kai, yanayinka yana barinka ka cancanci samun waɗannan hakkin kuwa?

16. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya “aika nagarta zuwa ga dukan mutane, . . . waɗanda su ke cikin iyalin imani”?

16 Mutane da yawa suna farin cikin taimaka wa waɗanda suka yi rashin abubuwa don tsarar bala’i. Alal misali, wata ’yar’uwa mai shekara kusan 65 da take hidima a Bethel ta yi tafiya mai nisa sau da yawa don ta ba da kanta a aikin taimakon ba da agaji. Me ya sa ta yi amfani da lokacin hutunta ta wannan hanyar? Ta ce: “Ko da yake ban iya wani aikin hannu ba, gata ne in yi abin da ake bukata. Na sami ƙarfafawa sosai ganin irin bangaskiya mai ƙarfi na ’yan’uwana da suka yi rashin abubuwa sosai.” Bugu da ƙari, mutane da yawa suna taimakawa a wajen gina Majami’un Mulki da Majami’un Taro. Ta wajen saka hannu a irin waɗannan ayyuka, muna “aika nagarta zuwa ga dukan mutane, . . . waɗanda su ke cikin iyalin imani.”—Gal. 6:10.

“Ina Tare da Ku Kullayaumi”

17. Menene za ka ba da don ka yi musanya da rai na har abada?

17 An kusa halaka ’yan adam da suka ware kansu daga Allah. Ba mu san daidai lokacin da hakan zai faru ba. Duk da haka, mun san cewa an “gajertadda kwanaki” kuma “ƙa’idar duniyan nan tana shuɗewa.” (Ka karanta 1 Korinthiyawa 7:29-31.) Wannan ya ƙara ma’ana ga tambayar da Yesu ya yi: “Ina abin da mutum za ya bayas musanyar ransa?” Za mu yi kowane irin sadaukarwa da Jehobah ya ce mu yi don mu sami “hakikanin rai.” (1 Tim. 6:19) Hakika, wajibi ne mu yi biyayya ga umurnin Yesu ‘ku biyo ni’ kuma mu ‘fara biɗan mulki.’—Mat. 6:31-33; 24:13.

18. Wane tabbaci ne ya kamata mu kasance da shi, kuma me ya sa?

18 Hakika, bin Yesu ba shi da sauƙi, kuma kamar yadda Yesu ya ba da umurnin, hakan ya sa wasu sun rasa rayukansu a wannan zamanin. Duk da haka, kamar Yesu, bari mu guji gwajin ‘sawaƙa wa kanmu.’ Mu ba da gaskiya ga tabbacin da ya ba wa shafaffunsa masu bi a ƙarni na farko: “Ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.” (Mat. 28:20) Bari mu yi amfani da lokacinmu da ingancinmu sosai a tsarkakkar hidima. Sa’ad da muke yin haka, muna nuna tabbaci cewa Jehobah zai kāre mu a lokacin ƙunci mai girma ko kuma ya dawo da mu a sabuwar duniya. (Ibran. 6:10) Hakan zai sa mu nuna yadda muka ɗauki kyautar rai da tamani.

Mecece Amsarka?

• Ta yaya ne Yesu ya nuna fitaccen misali na daraja Allah da mutum?

• Ta yaya ne mutum zai sadaukar da kansa, kuma ta yaya zai iya yin hakan?

• A Isra’ila ta dā, wace irin hadaya ce Jehobah yake karɓa, kuma ta yaya hakan yake yi mana ja-gora a yau?

• A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin amfani da lokacinmu da kyau?

[Hotuna a shafi na 26]

A koyaushe Yesu yana yin abin da ke faranta wa Allah rai

[Hoto a shafi na 28]

Isra’ilawa da suka yi farin ciki sun ba da abubuwa mafi kyau don bauta ta gaskiya

[Hotuna a shafi na 29]

Muna faranta wa Allah rai ta wurin yin amfani da lokacinmu a yin abu mai kyau

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba