Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 3/1 pp. 4-9
  • Ku Yi Alfahari—ku Kiristoci Ne!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Yi Alfahari—ku Kiristoci Ne!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sanin ko Su Wanene Mu
  • Ƙalubalen
  • Muma Muna Fuskantar Ƙalubale
  • Sun San Kansu Sosai
  • Ka Yi Alfahari da Halinka
  • Mu Kiyaye Halinmu Na Kirista
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 3/1 pp. 4-9

Ku Yi Alfahari—ku Kiristoci Ne!

“Duk mai yin taƙama yā yi taƙama da Ubangiji.”—1 KORANTIYAWA 1:31.

1. Wane abu ne ya bayyana a halin da mutane suke nunawa game da addini?

“RASHIN damuwa da addini.” Wani mai sharhi game da harkokin addinai ya yi amfani da kalaman nan domin ya kwatanta halayen da mutane suke nunawa ga addininsu. Ya yi bayani: “Ci gaba mafi girma da aka samu a addini na zamani ba na addini ba ne, hali ne na ‘rashin damuwa da addini.’ ” Ya lura cewa mutane da yawa “sun gaskata da Allah . . . amma suna nuna masa halin ko in kula.”

2. (a) Me ya sa ba abin mamaki ba ne cewa mutane suna nuna rashin damuwa da ruhaniya? (b) Wane haɗari ne wannan rashin damuwa yake haddasa wa Kiristoci na gaskiya?

2 Wannan rashin damuwa da addini ba abin mamaki ba ne ga ɗaliban Littafi Mai Tsarki. (Luka 18:8) Kuma idan aka zo batun dukan addini, dole ne a yi tsammanin irin wannan halin. Addinin ƙarya ya yaudari mutane kuma ya ba su kunya na lokaci mai tsawo. (Wahayin Yahaya 17:15, 16) Amma, ga Kiristoci na gaskiya, rababben zuciya da kuma rashin ƙwazo haɗari ne. Za mu sami sakamako marar kyau idan muka nuna rashin damuwa da addininmu kuma za mu yi hasarar ƙwazon da muke da shi na yi wa Allah hidima da kuma gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Yesu ya yi gargaɗi game da irin wannan rashin ƙwazo sa’ad da ya yi wa Kiristoci na ƙarni na farko da suke zaune a Lawudikiya kashedi: ‘Ba ku da sanyi, ba ku kuwa da zafi. Da ma a ce kuna da sanyi, ko kuwa kuna da zafi . . . ku tsakatsaki ne.’—Wahayin Yahaya 3:15-18.

Sanin ko Su Wanene Mu

3. Waɗanne sassa na halinsu ne ke sanya Kiristoci alfahari?

3 Domin su yaƙi halin rashin damuwa da ruhaniya, Kiristoci suna bukatar su fahimci ko su wanene su, kuma su yi alfaharin haka. A matsayinmu na bayin Jehobah da kuma almajiran Kristi, za mu iya samun kwatancin ko su wanene mu a cikin Littafi Mai Tsarki. Mu ‘shaidun’ Jehobah ne, kuma “abokan aiki ne na Allah” domin muna faɗa wa mutane ‘bishara.’ (Ishaya 43:10; 1 Korantiyawa 3:9; Matiyu 24:14) Mu mutane ne da suke ‘ƙaunar juna.’ (Yahaya 13:34) Kiristoci na gaskiya mutane ne “waɗanda hankalinsu ya horu yau da kullum, su rarrabe nagarta da mugunta.” (Ibraniyawa 5:14) Mu “fitilu [ne] a duniya.” (Filibiyawa 2:15) Muna ƙoƙarin mu nuna “halin yabo a cikin al’ummai.”—1 Bitrus 2:12; 2 Bitrus 3:11, 14.

4. Ta yaya ne mai bauta wa Jehobah da gaske zai iya sanin abin da ba zai iya yi ba?

4 Masu bauta ta gaskiya ga Jehobah sun san abin da ba za su iya yi ba. “Su ba na duniya ba ne,” kamar yadda Shugabansu, Yesu Kristi, ba na duniya ba ne. (Yahaya 17:16) Sun raba kansu da “al’ummai,” waɗanda “duhun zuciya gare su, bare suke ga rai wanda Allah ke bayarwa.” (Afisawa 4:17, 18) A sakamakon haka, mabiyan Yesu sun ‘ƙi rashin bin Allah da mugayen sha’awace-sha’awacen duniya, sun kuma yi zamansu a duniyan nan da natsuwa, da adalci, da kuma bin Allah.’—Titus 2:12.

5. Menene wannan furci “yi taƙama da Ubangiji” yake nufi?

5 Domin mun san ko su wanene mu da kuma dangantakar da muke da ita da Mamallakin sararin samaniya, hakan ya motsa mu mu “yi taƙama da Ubangiji.” (1 Korantiyawa 1:31) Wane irin taƙama ke nan? Mu Kiristoci na gaskiya, muna alfahari cewa Jehobah shi ne Allahnmu. Muna bin gargaɗin nan: “Bari wanda zai yi fariya, ya yi fariya a kan cewa ya fahimce ni, ya kuma san ni. Ni ne Ubangiji mai yin alheri, da gaskiya, da adalci a duniya.” (Irmiya 9:24) Muna “taƙama” domin gatar da muke da ita ta sanin Allah da kuma yadda yake amfani da mu domin mu taimaki mutane.

Ƙalubalen

6. Me ya sa yake yi wa wasu wuya su kasance da bambancinsu na Kirista?

6 A gaskiya, kasancewa da bambancinmu na Kiristoci ba abu ba ne mai sauƙi. Wani matashi wanda Kirista ne tun yana ɗan ƙarami ya tuna cewa ya taɓa fuskantar sanyin gwiwa a ruhaniya na ɗan lokaci: “A wasu lokatai, na kan ji cewa ban san dalilin da ya sa ni Mashaidin Jehobah ba ne. Ina cikin gaskiya tun ina ɗan ƙarami. A wasu lokatai na kan ji cewa wannan wani addini ne kawai da aka amince da shi.” Wataƙila wasu sun ƙyale nishaɗi, hanyar watsa labarai, hanyoyi na rayuwa da ba su jitu da Allah ba sun shafi tunaninsu. (Afisawa 2:2, 3) A wani lokaci, wasu Kiristoci suna kasancewa cikin shakka kuma suna sake bincika ɗabi’a da makasudinsu.

7. (a) Wane irin bincika kai ne ya dace da bayin Allah? (b) A ina ne haɗarin ke ɓoyewa?

7 Laifi ne mu bincika kanmu lokaci-lokaci? A’a. Kana iya tuna cewa manzo Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su ci gaba da bincika kansu: “Ku jarraba kanku ku gani, ko har yanzu kuna raye da bangaskiya.” (2 Korantiyawa 13:5) A nan, manzon yana ƙarfafa Kiristoci ne su duba ko akwai wani sanyin gwiwa na ruhaniya da ya taso kuma su ƙuduri aniyar ɗaukan matakin da ya dace domin magance matsalolin. Kirista da zai bincika ko yana da bangaskiya, dole ne ya duba ya gani ko kalmominsa da halayensa sun jitu da abin da ya gaskata. Amma, idan ba mu mai da hankali ba, bincika kanmu game da “halayenmu” ko kuwa neman amsoshin da ba su jitu da dangantakarmu da Jehobah ko ikilisiyar Kirista ba, za su zame mana marasa amfani kuma suna iya lalata ruhaniyarmu.a Ba ma so mu ‘lalata bangaskiyarmu’!—1 Timoti 1:19.

Muma Muna Fuskantar Ƙalubale

8, 9. (a) Ta yaya Musa ya yi shakkar kansa? (b) Ta yaya Jehobah ya amsa rashin cancanta da Musa yake ji? (c) Ta yaya tabbacin Jehobah ya shafe ka?

8 Kiristoci da suke shakka a wasu lokatai ya kamata su yi tunanin cewa sun kasa ne? Ko kaɗan! Hakika, suna iya samun ƙarfafa daga sanin cewa irin waɗannan motsin zuciya ba sabon abu ba ne. Amintattun bayin Jehobah na dā sun fuskanci irin haka. Alal misali, Musa ya nuna bangaskiya mai girma, da aminci, da kuma ba da kai. Sa’ad da ya sami wani aiki mai girma, cikin tsoro Musa ya yi tambaya: “Wane ni?” (Fitowa 3:11) Hakika, abin da yake nufi a zuciyarsa shi ne, ‘Ni ba kome ba ne!’ ko kuwa ‘Ba zan iya ba!’ Wataƙila asalin Musa na iya sanya shi ya ji cewa bai cancanci yin aikin ba: Shi ɗan al’umma ne da suke bauta. ’Yan Isra’ila sun ƙi shi. Kuma shi ba mai lafazi ba ne. (Fitowa 1:13, 14; 2:11-14; 4:10) Shi makiyayi ne, irin aikin da abin ƙyama ne ga Masarawa. (Farawa 46:34) Ba abin mamaki ba ne ya ji cewa bai cancanci ya ceci mutanen Allah da suke bauta ba!

9 Jehobah ya ba Musa tabbaci wajen yi masa alkawura guda biyu masu iko: “Zan kasance tare da kai, wannan kuwa zai zama alama a gare ka, cewa ni ne na aike ka. Sa’ad da ka fito da jama’ar daga Masar, za ku bauta wa Allah a bisa dutsen nan.” (Fitowa 3:12) Allah ya gaya wa bawansa da ba ya son zuwa aikin cewa Zai kasance tare da shi a kowane lokaci. Bugu da ƙari, Jehobah na nuna cewa zai ceci mutanensa. Cikin ƙarnuka, Allah ya yi irin waɗannan alkawura na taimako. Alal misali, ta wurin Musa ya gaya wa al’ummar Isra’ila sa’ad da suke gab da shiga Ƙasar Alkawari cewa: “Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, . . . gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.” (Maimaitawar Shari’a 31:6) Jehobah kuma ya tabbatar wa Joshuwa: “Ba mutumin da zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. . . . Zan kasance tare da kai, ba zan kunyatar da kai ba, ba kuwa zan yashe ka ba.” (Joshuwa 1:5) Kuma ya yi wa Kiristoci alkawari: ‘Har abada ba zan bar ku ba. Har abada kuma ba zan yashe ku ba.’ (Ibraniyawa 13:5) Tun da yake muna da irin wannan alkawari za mu yi alfahari cewa mu Kiristoci ne!

10, 11. Ta yaya aka taimaka wa Balawe Asaf ya riƙe halin da ya dace game da muhimmancin hidimarsa ga Jehobah?

10 Kusan shekaru ɗari biyar bayan mutuwar Musa, wani amintaccen Balawe mai suna Asaf ya rubuta gaskiya game da shakkarsa na muhimmancin bin tafarkin gaskiya. Sa’ad da yake ƙoƙarin bauta wa Allah duk da tsanani da jarraba, Asaf ya ga wasu da ke ba’anta Allah suna ta samun iko kuma suna bunƙasa. Ta yaya hakan ya shafi Asaf? Ya ce: “Amma ina gab da fāɗuwa, ƙafafuna sun kusa zamewa. Saboda na ji kishin masu girmankai, sa’ad da na ga mugaye suna arziki.” Sai ya fara shakkar muhimmancin zama mai bauta wa Jehobah. Asaf ya yi tunani cewa: “Ashe, a banza nake kiyaye kaina da tsarki, hannuwana kuma a tsabtace daga zunubi. Ya Allah, ka sa ina shan wahala dukan yini.”—Zabura 73:2, 3, 13, 14.

11 Ta yaya Asaf ya magance irin waɗannan tunanin? Ya ɓoye su a zuciyarsa ne? A’a. Ya furta su ga Allah a addu’a, kamar yadda muka gani a Zabura ta 73. Asaf ya yi muhimmin canji a tunaninsa sa’ad da ya ziyarci mazaunin haikali. Sa’ad da yake wurin, ya fahimci cewa bauta wa Allah shi ne tafarkin da ya fi dacewa. Bayan ya sabonta muhimmancin ruhaniyarsa, sai ya fahimci cewa Jehobah ya ƙi mugunta kuma nan ba da daɗewa ba zai halaka masu yin mugunta. (Zabura 73:17-19) Domin haka, Asaf ya ƙarfafa azancinsa domin ya fahimci cewa shi bawa ne mai girma na Jehobah. Ya ce wa Allah: “Ina tare da kai kullayaumin, kana riƙe da hannuna. Shawararka, tana bi da ni, daga ƙarshe kuma za ka karɓe ni da daraja.” (Zabura 73:23, 24) Sai Asaf ya koma yana alfahari da Allahnsa.—Zabura 34:2.

Sun San Kansu Sosai

12, 13. Ka ba da misalai na wasu mutane na cikin Littafi Mai Tsarki waɗanda suka yi alfahari domin dangantakarsu da Allah.

12 Wata hanya da za ta ƙarfafa halinmu na Kirista ita ce yin nazari da kuma bin bangaskiyar amintattu masu bauta, waɗanda duk da wahala suna alfahari domin dangantakar da suke da ita da Allah. Yi la’akari da Yusufu, ɗan Yakubu. Sa’ad da yake matashi, an sayar da shi bauta zuwa ƙasar Masar, ƙasa mai nisa wadda ta bambanta da ta su, kuma wadda take ɗarurruwan mil daga inda mahaifinsa mai tsoron Allah yake da zama. Sa’ad da yake Masar, Yusufu ba shi da wani mutumin da zai iya ba shi shawara ta ibada, ban da haka, ya fuskanci yanayi masu ƙalubale da suka jarraba ɗabi’arsa da kuma tawakkalinsa ga Allah. Amma, ya yi ƙoƙari sosai ya nuna kyakkyawar hali na bawan Allah, kuma ya riƙe aminci ga abin da ya sani cewa daidai ne. Ya yi alfahari domin yana bauta wa Jehobah har ma a mahalli mai haɗari, kuma bai ji kunyar furta yadda yake ji ba.—Farawa 39:7-10.

13 Ƙarni takwas bayan haka, wata yarinya Ba’isra’iliya ’yar bauta wadda ta zama baiwar janar na Suriya Na’aman, ba ta manta cewa ita baiwar Jehobah ba ce. Da zarafi ya taso, ta yi shaidar Jehobah da gaba gaɗi sa’ad da ta sanar da cewa Elisha shi ne annabin Allah na gaskiya. (2 Sarakuna 5:1-19) Shekaru da yawa bayan haka, duk da cewa yana zaune a cikin mahalli da babu ɗabi’a mai kyau, Sarki Yosiya matashi, ya ba da doka na sabonta tsarin addini, ya gyara haikalin Allah, kuma ya sa al’ummar ta koma ga Jehobah. Ya yi alfahari da bangaskiyarsa da kuma bautarsa. (2 Tarihi, surori 34, 35) Daniyel da Ibraniyawa uku a Babila ba su taɓa mantuwa ba cewa su bayin Jehobah ne, sun riƙe amincinsu cikin matsi da gwaji. Babu shakka, suna alfahari cewa su bayin Jehobah ne.—Daniyel 1:8-20.

Ka Yi Alfahari da Halinka

14, 15. Menene yin alfahari domin halinmu na Kirista ya ƙunsa?

14 Waɗannan bayin Jehobah sun yi nasara domin sun gina hali mai kyau a gaban Allah. Mu kuma fa a yau? Menene yin alfahari domin halinmu na Kirista ya ƙunsa?

15 Hanya ta farko, ta haɗa da godiya ta musamman na zama mutanen Jehobah masu ɗauke da sunansa, albarkarsa, da kuma yardarsa. Allah ba ya shakkar nasa. Manzo Bulus wanda ya rayu a ƙarnin da aka sami ɗimaucewa na addini, ya rubuta: “Ubangiji ya san nasa.” (2 Timoti 2:19; Littafin Ƙidaya 16:5) Jehobah yana yin alfahari a ‘waɗanda ke nasa.’ Ya sanar da cewa: “Wanda ya tabe ku, ya taɓi ƙwayar idona.” (Zakariya 2:8) Babu shakka, Jehobah yana ƙaunarmu. Saboda haka, dangantakarmu da shi dole ne ta kasance a kan ƙaunar da muke masa. Bulus ya ce: “In kuwa wani na ƙaunar Allah, to, Allah ya san shi.”—1 Korantiyawa 8:3.

16, 17. Me ya sa Kiristoci, manya da yara, ya kamata su yi fariya da gadōnsu na ruhaniya?

16 Matasa waɗanda aka rene su suka tashi Shaidun Jehobah ya kamata su bincika su gani ko halinsu na Kirista yana kyautata domin dangantakarsu da Allah. Kada su dogara a kan bangaskiyar iyayensu kawai. Game da kowane bawan Allah, Bulus ya rubuta: “Ko dai ya tsaya ko ya faɗi, ai, ruwan maigidansa ne.” Saboda haka, Bulus ya ci gaba: “Kowannenmu zai faɗi abin da shi da kansa ya yi, a gaban Allah.” (Romawa 14:4, 12) Hakika, bin addinin iyali ba da zuciya ɗaya ba ba zai iya ƙarfafa dangantaka da Jehobah ba.

17 Duk cikin tarihi, an sami Shaidun Jehobah masu yawa. Sun fara ne tun daga lokacin amintaccen mutum Habila—kusan ƙarnuka 60 da suka wuce—zuwa “ƙasaitaccen taro” na Shaidu na zamani da kuma masu bauta wa Jehobah masu yawa da za su ji daɗin rayuwar marar ƙarewa a nan gaba. (Wahayin Yahaya 7:9; Ibraniyawa 11:4) Mu ne rukuni na zamani na waɗannan amintattun masu bauta masu yawa. Hakika, muna da gadō na ruhaniya!

18. Ta yaya ne halayenmu da tarbiyya suka bambanta mu daga duniya?

18 Ɗabi’armu ta Kirista ta haɗa da, halaye, mizanai, tarbiyya, da kuma abubuwan da suke bayyana cewa mu Kiristoci ne. Ita ce “wannan hanya,” wadda ita kaɗai ce hanyar rai da kuma faranta wa Allah zuciya. (Ayyukan Manzanni 9:2; Afisawa 4:22-24) Kiristoci suna “jarraba kome” kuma su “riƙi abin da ke nagari kankan”! (1 Tasalonikawa 5:21) Muna da fahimi na bambanci mai girma da ke tsakanin Kiristanci da kuma duniyar da take bare daga Allah. Jehobah ya bambanta sarai tsakanin bauta ta gaskiya da ta ƙarya. Ta wurin annabinsa Malakai, ya sanar: “Sa’an nan za ku ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, da tsakanin mutumin da ke bauta mini da wanda ba ya bauta mini.”—Malakai 3:18.

19. Menene Kiristoci na gaskiya ba za su taɓa yi ba?

19 Tun da yake yin alfahari da Jehobah yana da muhimmanci a wannan duniya da ta riga ta ɗimauce, menene zai taimaka mana mu yi alfahari da Allahnmu da kuma halinmu na Kirista? Za a sami shawarwari masu taimakawa a talifi na gaba. Sa’ad da kake bincika su, ka tabbata da wannan: Kiristoci na gaskiya ba za su taɓa nuna rashin damuwa da addininsu ba.

[Hasiya]

a A nan an yi magana ne kawai game da halinmu na ruhaniya. Ga wasu, batun lafiyar hankalinsu zai bukaci taimakon masana.

Ka Tuna?

• Ta yaya Kiristoci za su yi “taƙama da Ubangiji”?

• Menene ka koya daga misalin Musa da Asaf?

• Waɗanne mutane ne a cikin Littafi Mai Tsarki suka yi alfahari da hidimarsu ga Allah?

• Menene yin alfahari domin halinmu na Kirista ya ƙunsa?

[Hoto a shafi na 6]

A wani lokaci, Musa ya yi shakkar kansa

[Hotuna a shafi na 7]

Bayin Jehobah na dā masu yawa sun yi alfahari domin halinsu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba