Mu Kiyaye Halinmu Na Kirista
“Ku ne shaiduna, [in ji Jehobah].”—ISHAYA 43:10.
1. Waɗanne irin mutane ne Jehobah yake jawowa kusa da shi?
SA’AD da kake cikin Majami’ar Mulki, ka duba ko’ina da kyau. Su waye ka gani a wannan wuri na yin bauta? Kana iya ganin yara masu himma suna saurarawa kuma suna ɗaukan hikima ta Ruhaniya. (Zabura 148:12, 13) Hakazalika, kana iya ganin shugabannin iyalai suna ƙoƙarin su faranta wa Allah rai duk da cewa suna zaune a duniyar da ba ta daraja rayuwa ta iyali. Wataƙila, kana ganin wasu tsofaffi ƙaunatattu da suka manne wa keɓe kai da suka yi ga Jehobah duk da matsalar tsufa. (Karin Magana 16:31) Dukansu suna ƙaunar Jehobah sosai. Kuma ya ga cewa ya dace ya kafa dangantaka da su. “Ba mai iya zuwa wurina,” in ji Ɗan Allah, “sai dai in Uba wanda ya aiko ni ne ya jawo shi.”—Yahaya 6:37, 44, 65.
2, 3. Me ya sa zai iya zama ƙalubale a nuna kyakkyawan hali na Kirista?
2 Ba ma farin cikin mu kasance cikin mutanen da suka sami amincewar Jehobah da kuma albarkarsa? Duk da haka, manne wa halinmu na Kirista a wannan lokaci na ‘shan wuya,’ ƙalubale ne. (2 Timoti 3:1) Haka wannan yake musamman ma ga matasa waɗanda aka haifa a cikin iyalan Kirista. “Ko da yake ina zuwa tarurruka na Kirista,” in ji wani matashi, “ba ni da wani cikakken makasudi na ruhaniya, kuma a gaskiya, ba ni da wani sha’awa na bauta wa Jehobah.”
3 Wasu da suke sha’awar bauta wa Jehobah, ana iya janye musu hankali ta wurin matsi na tsara, tasiri na duniya, da kuma muradin yin zunubi. Sa’ad da muka fuskanci matsi, a sannu-sannu hakan na iya sa mu yi hasarar halinmu na Kirista. Alal misali, da yawa a yau suna ɗaukan ɗabi’ar mizanan Littafi Mai Tsarki a kan tsohon yayi ne ko kuma marasa tabbaci a wannan zamani. (1 Bitrus 4:4) Wasu suna jin cewa ba dole ba ne a bauta wa Allah yadda ya ce. (Yahaya 4:24) A cikin wasiƙarsa ga Afisawa, Bulus ya ce wannan duniyar tana da “ruhu” ko kuma hali na musamman. (Afisawa 2:2 Litafi Mai-Tsarki) Wannan ruhun yana matsa wa mutane domin tunaninsu ya daidaita da na mutanen da ba su san Jehobah ba.
4. Ta yaya ne Yesu ya nanata muhimmancin kiyaye halinmu na Kirista?
4 Amma, mu keɓaɓɓu bayin Jehobah, mun fahimci cewa zai zame mana haɗari—matashi ko tsoho—idan muka yi hasarar halinmu na Kirista. Kyakkyawan hali na Kirista ya dangana ne kawai a kan mizanan Jehobah da kuma abubuwan da yake bukata a garemu. Balle ma, an halicce mu ne a siffarsa. (Farawa 1:26; Mika 6:8) Littafi Mai Tsarki ya kwatanta halinmu na Kirista da tufafin da ake sawa, don kowa ya gani. Game da lokacinmu, Yesu ya yi gargaɗi: “Ga ni nan tafe kamar ɓarawo! Albarka tā tabbata ga wanda ke zaune a faɗake, yana sanye da tufafinsa, don kada ya tafi tsirara, a ga tsiraicinsa.”a (Wahayin Yahaya 16:15) Ba ma son mu ɓata halinmu na Kirista da kuma tarbiyyarmu kuma mu ƙyale duniyar Shaiɗan ta mulmula mu. Idan muka ƙyale hakan ya faru, za mu yi hasarar ‘tufafinmu.’ Irin wannan yanayin zai sa mu yi da na sani kuma ya ba mu kunya.
5, 6. Me ya sa ruhaniya mai ƙarfi ke da muhimmanci?
5 Halin Kirista zai iya shafan irin rayuwar da yake yi. Ta yaya? Idan mai bauta wa Jehobah ya ɓata halinsa, yana iya zama mai zuciya biyu, marar cikakken makasudi. Sau da yawa Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi a kan irin wannan hali na zuciya biyu. Almajiri Yakubu ya yi gargaɗi: “Mai shakka, kamar raƙuman ruwan teku yake, waɗanda iska ke korawa tana tuttunkuɗawa. Kada irin mutumin nan mai zuciya biyu, wanda bai tsai da zuciyarsa gu ɗaya a dukan al’amuransa ba, ya sa rai da wani abu a gun Ubangiji.”—Yakubu 1:6-8; Afisawa 4:14; Ibraniyawa 13:9.
6 Ta yaya za mu iya kiyaye halinmu na Kirista? Menene zai taimaka mana mu daɗa fahimtar gata mai girma da muke da ita ta zama masu bauta wa Maɗaukaki Duka? Don Allah ka yi la’akari da hanyoyin da ke gaba.
Ka Ƙarfafa Halinka na Kirista
7. Me ya sa yake da amfani mu roƙi Jehobah ya bincika mu?
7 Ka ci gaba da ƙarfafa dangantakarka da Jehobah. Abu mafi muhimmanci da Kirista ke da shi, shi ne dangantakarsa da Allah. (Zabura 25:14; Karin Magana 3:32) Idan muka fara yin tambayoyi masu dama hankali game da halinmu na Kirista, ya kamata mu binciki halinmu sosai da kuma zurfin wannan dangantakar. Mai Zabura ya yi wannan roƙon: “Ka jarraba ni ka auna ni, ya Ubangiji, ka gwada muradina da tunanina.” (Zabura 26:2) Me ya sa irin wannan jarrabawa ke da muhimmanci? Domin ba ma iya zama tabbataccen mufutin muradinmu da kuma nufe-nufenmu masu zurfi ba. Jehobah kaɗai ne zai iya fahimtar zuciyarmu—muradinmu, tunaninmu, da kuma yadda muke ji.—Irmiya 17:9, 10.
8. (a) Ta yaya ne jarrabawa daga wurin Jehobah za ta amfane mu? (b) Ta yaya ka sami taimako na samun ci gaba na Kirista?
8 Ta roƙon Jehobah ya bincika mu, muna gayyatarsa ya jarraba mu ke nan. Yana iya ƙyale wasu yanayi su taso da za su bayyana muradinmu na gaskiya da kuma yanayin zuciyarmu. (Ibraniyawa 4:12, 13; Yakubu 1:22-25) Dole ne mu marabci irin wannan jarraba domin suna ba mu daman mu nuna zurfin amincinmu ga Jehobah. Za su nuna ƙila mun “zama kamilai cikakku kuma, ba [mu] gaza da kome ba.” (Yakubu 1:2-4) Ta haka, za mu daɗa ruhaniya.—Afisawa 4:22-24.
9. Tilas ne mu tabbatar wa kanmu gaskiyar Littafi Mai Tsarki? Ka ba da bayani.
9 Ka tabbatar wa kanka gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Yadda muke ji game da halinmu mu bayin Jehobah na iya raunana idan bai kafu sosai ba bisa cikakken sani na Nassosi. (Filibiyawa 1:9, 10) Kowane Kirista—babba ko ƙarami, ya kamata ya tabbatar wa kansa cewa abin da ya gaskata shi ne gaskiya da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Bulus ya aririci ’yan’uwa masu bi: “Sai dai ku jarraba kome, ku riƙi abin da ke nagari kankan.” (1 Tasalonikawa 5:21) Dole ne Kiristoci matasa da suke cikin iyalan da suke tsoron Allah su fahimci cewa ba sa iya zama Kiristoci na gaskiya domin bangaskiyar iyayensu. Baban Sulemanu, Dauda, ya aririce shi, ‘ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya.’ (1 Tarihi 28:9) Duba yadda ubansa ke gina bangaskiya a Jehobah ba zai ishe Sulemanu ba. Yana bukatar ya san Jehobah shi da kansa, kuma ya yi hakan. Ya roƙi Allah: “Ka ba ni yanzu hikima da sani, domin in fita, in shiga gaban wannan jama’a.”—2 Tarihi 1:10.
10. Me ya sa babu laifi a yi sahihan tambayoyi da nufi mai kyau?
10 Ana gina bangaskiya mai ƙarfi ne bisa sani. “Bangaskiya ta wurin jawabin da ake ji take samuwa,” inji Bulus. (Romawa 10:17) Menene yake nufi da haka? Yana nufin cewa idan Kalmar Allah ta ciyar da mu, za mu gina bangaskiyarmu da tabbaci a Jehobah, alkawuransa, da ƙungiyarsa. Idan muka yi tambayoyi na gaskiya game da Littafi Mai Tsarki hakan zai iya kai ga amsoshi masu ƙarfafawa. Bugu da ƙari, a Romawa 12:2, mun sami wannan shawara ta Bulus: “Ku tabbatar da abin da Allah ke so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.” Yaya za mu cim ma hakan? Ta ‘inganta sanin gaskiya.’ (Titus 1:1) Ruhun Jehobah zai iya taimaka mana mu fahimci darussa masu wuya. (1 Korantiyawa 2:11, 12) Dole ne mu yi addu’a don taimakon Allah sa’ad da muka sami matsalar fahimtar wani abu. (Zabura 119:10, 11, 27) Jehobah yana son mu fahimci Kalmarsa, mu yarda da ita, kuma mu yi mata biyayya. Yana son sahihan tambayoyi da ake yi da nufi mai kyau.
Ka Ƙuduri Aniyar Faranta wa Allah Rai
11. (a) Wace sha’awa ce za ta iya zame mana tarko? (b) Ta yaya za mu iya kauce wa matsi na tsara da gaba gaɗi?
11 Ka faranta wa Allah rai, ba mutum ba. Ba baƙon abu ba ne mutane su so su kasance cikin wani rukuni na mutane. Kowa na son abokai, kuma idan muka zama karɓaɓɓu, hakan zai sa mu farin ciki. A lokacin ƙuruciya, da kuma rayuwa ta gaba, matsi na tsara na da ƙarfi, domin yana ta da sha’awar bin sawun wasu ko faranta musu rai. Amma abokai da tsararraki a wasu lokatai ba su da marmari mai kyau a gare mu a zuciyarsu. A wasu lokatai suna son wanda zai bi su ne kawai a yin abin da ba shi da kyau. (Karin Magana 1:11-19) Sa’ad da Kirista ya faɗa cikin matsi na tsara marar kyau, ya kan yi ƙoƙarin ɓoye halinsa. (Zabura 26:4) Manzo Bulus ya yi gargaɗi: “Kada ku biye wa halin duniyar da ke zagaye da ku.” (Romawa 12:2, The Jerusalem Bible) Jehobah yana ba mu ƙarfi da muke bukata domin mu yaƙi dukan wani matsi na waje.—Ibraniyawa 13:6.
12. Wane mizani da kuma misali ne za ta ƙarfafamu mu tsaya tsayin daka idan wani abu zai shafi amincinmu ga Allah?
12 Sa’ad da matsi na waje yake yin barazanar lalata halinmu na Kirista, yana da kyau mu tuna cewa amincinmu ga Allah ya fi ra’ayin mutane ko halayensu muhimmanci sosai. Kalmomin Farawa 23:2 mizani ce mai kyau: “Kada ku yi mugunta domin galibin mutane na yi.” Sa’ad da yawancin ’yan Isra’ila suka yi shakkar iyawar Jehobah ya cika alkawuransa, da gaba gaɗi, Kalibu ya ƙi ya bi halin da mutanen suka nuna. Yana da tabbacin cewa alkawuran Allah gaskiya ne, kuma ya sami sakamako mai kyau domin matakin da ya ɗauka. (Littafin Ƙidaya 13:30; Joshuwa 14:6-11) Kai ma kana da niyyar yin tsayayya da matsin ra’ayin jama’a domin ka kiyaye dangantakarka da Allah?
13. Me ya sa abin hikima ne mu sa wasu su san matsayinmu na Kirista?
13 Ka sa a sani ta halinka cewa kai Kirista ne. Karin maganan nan da ke cewa, kai hari shi ne kāriya mafi kyau ya zama gaskiya a yanzu da muke kiyaye halinmu na Kirista. Sa’ad da suka fuskanci hamayya game da ƙoƙarin da suke yi na yin nufin Jehobah a zamanin Ezra, Isra’ilawa masu aminci suka ce: “Mu bayin Allah ne wanda ke da sama da ƙasa.” (Ezra 5:11) Idan muka bari aikatawa da sūka na mutane masu haɗari ya shafe mu, tsoro na iya karya mana lago. Son mu faranta wa kowa rai zai rage ingancinmu. Saboda haka, kada ka tsorata. Zai fi kyau ka sa mutane su sani cewa kai Mashaidin Jehobah ne. Ka bayyana wa mutane a hanya mai kyau abubuwan da kake so, abin da ka gaskata, da kuma matsayinka na Kirista. Ka sa mutane su fahimci cewa ka riga ka ƙudurta ka manne wa mizanai masu girma na Jehobah game da ɗabi’a. Ka fayyace musu cewa amincinka na Kirista ba abin da za a yi jayayyarsa ba ne. Ka nuna cewa kana alfahari da mizanan ka na ɗabi’a. (Zabura 64:10) Kasancewa Kirista na gaskiya zai ƙarfafa ka, zai kāre ka, kuma zai sa wasu su yi tambaya game da Jehobah da mutanensa.
14. Ya kamata ba’a ko hamayya ya sa mu sanyin gwiwa ne? Ka ba da bayani.
14 Hakika, wasu suna iya yi maka ba’a ko kuma su yi hamayya. (Yahuza 18) Idan ka yi wa mutane bayani game da ɗabi’arka kuma suka ƙi sauraronka, kada ka yi sanyin gwiwa. (Ezekiyel 3:7, 8) Komin ƙoƙarin da ka yi, ba za ka iya sha kan mutanen da ba sa son a yi musu huɗuba ba. Ka tuna Fir’auna. Babu annoba ko mu’ujiza—har ma mutuwar ɗansa na fari—da ya sa Fir’auna ya yarda cewa Musa yana magana ne a madadin Jehobah. Saboda haka, kada ka yarda tsoron mutum ya karya maka lago. Gaskatawa da kuma nuna bangaskiya ga Allah za su iya taimaka mana mu sha kan tsoro.—Karin Magana 3:5, 6; 29:25.
Ka Koya Daga Abin da Ya Shige, Ka Gina Rayuwarka ta nan Gaba
15, 16. (a) Menene gadōnmu na ruhaniya? (b) Ta yaya za mu iya amfana daga yin bimbini a kan gadōnmu na ruhaniya da taimakon Kalmar Allah?
15 Ka daraja gadōnka na ruhaniya. Ta wurin hasken Kalmar Allah, Kiristoci za su amfana daga yin bimbini a kan gadōnsu na ruhaniya mai tamani. Wannan gadōn ya haɗa da gaskiyar Kalmar Jehobah, begen rai madawwami, da kuma gatan wakiltan Allah na masu shelar bishara. Kana iya ganin kasancewarka a tsakanin Shaidunsa kuwa, a cikin rukunin mutane masu gata waɗanda aka ba umurnin aikin ceto na yin wa’azin Mulki? Ka tuna cewa, Jehobah ne ya tabbatar cewa: “Ku ne shaiduna.”—Ishaya 43:10.
16 Kana iya yi wa kanka waɗannan tambayoyin: ‘Wannan gadōn na ruhaniya yana da tamani a gare ni kuwa? Ina ɗaukansa da girma sosai domin nufin Allah ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwata? Godiyata ga wannan tana da ƙarfi sosai don ta ƙarfafa ni in yi tsayayya wa jarabar bin tafarkin da zai sa in ƙi shi?’ Gadōnmu na ruhaniya zai iya ba mu kāriya na ruhaniya mai ƙarfi wadda cikin ƙungiyar Jehobah kaɗai ne za mu iya samun ta. (Zabura 91:1, 2) Binciken aukuwa na ban mamaki daga tarihin ƙungiyar Jehobah zai saka mana a zuciya cewa babu mutum ko wani abu da zai iya kawar da mutanen Jehobah daga wannan duniyan.—Ishaya 54:17; Irmiya 1:19.
17. Me kuma ake bukata fiye da dangana a kan gadōnmu na ruhaniya?
17 Hakika, ba za mu iya dangana a kan gadōnmu na ruhaniya kaɗai ba. Dole ne kowannenmu ya gina dangantaka na kud da kud da Allah. Bayan Bulus ya yi ƙoƙari sosai ya gina bangaskiyar Kiristoci a Filibi, ya rubuta musu: “Saboda haka ya ƙaunatattuna, kamar yadda kullum kuke biyayya, haka yanzu kuma, ku yi ta yin aikin ceton nan naku da halin bangirma tare da matsananciyar kula, ba wai sai ina nan kawai ba, har ma fiye da haka in ba na nan.” (Filibiyawa 2:12) Ba za mu dangana a kan wani ba domin cetonmu.
18. Ta yaya ayyukan Kirista za su iya kyautata halinmu na Kirista?
18 Ka nitsar da kanka a cikin ayyuka na Kirista. An lura cewa “aiki yana rinjayar halin mutum.” A yau an ba Kiristoci umurnin su yi aiki mai muhimmanci na yin wa’azin bisharar Mulkin Allah da aka kafa. Bulus ya ce: “Tun da ya ke ni manzo ne ga al’ummai, ina taƙama da aikina.” (Romawa 11:13) Aikin mu na yin wa’azi ya bambanta mu a duniya, kuma saka hannu a cikin aikin na kyautata halinmu na Kirista. Nitsar da kanmu a cikin ayyuka na tsarin Allah, kamar su halartan tarurruka, tsarin ayyuka na gina wuraren yin ibada, taimaka wa waɗanda suke da bukata, da sauransu, za su zurfafa azancin halin mu na Kirista.—Galatiyawa 6:9, 10; Ibraniyawa 10:23, 24.
Halin Kirki na Kawo Albarka Mai Yawa
19, 20. (a) Waɗanne albarka ka taɓa samu na zama Kirista? (b) Menene tushen halinmu na gaskiya?
19 Ka ɗauki lokaci ka yi bimbini a kan dukan albarka da fa’idodin da muke morewa domin mu Kiristoci ne na gaskiya. Muna da gatar cewa Jehobah da kansa ya san da mu. Annabi Malakai ya ce: “Mutane waɗanda ke tsoron Ubangiji suka yi magana da junansu, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya ji abin da suke cewa. A gabansa aka rubuta a littafin tarihin waɗanda ke tsoron Ubangiji, suna kuwa girmama shi.” (Malakai 3:16) Allah na iya ɗaukanmu abokansa. (Yakubu 2:23) Rayuwarmu na cike ne da manufa, ma’ana mai zurfi, da kuma makasudai masu kyau. Kuma an ba mu begen madawwamin rayuwa.—Zabura 37:9.
20 Ka tuna cewa matsayinka da ɗabi’arka sune suka fi muhimmanci a yadda Allah yake ɗaukarka, ba abin da mutane suke tunani game da kai ba. Wasu suna iya kimanta mu a kan mizanai na mutane. Amma ƙaunar Allah da kuma yadda yake kula da mu, ya sa mu ji cewa muna da tamani—domin mu nasa ne. (Matiyu 10:29-31) A sakamakon haka, ƙaunar da muke yi wa Allah na iya sa mu nuna hali mafi kyau kuma ya yi mana ja-gora a rayuwarmu. “In kuwa wani na ƙaunar Allah, to, Allah ya san shi.”—1 Korantiyawa 8:3.
[Hasiya]
a Wataƙila waɗannan kalamai suna nuni ne ga ayyukan shugaban haikalin da ke Urushalima. A lokacin gadi cikin dare, yana zagayawa ya ga ko Balawe da suke gadin suna a faɗake ko suna barci a inda aka saka su. Duk wanda ya ga yana barci zai buge shi da sanda, kuma ana iya kona masa tufafinsa wanda horo ne mai ban kunya.
Ka Tuna?
• Me ya sa yake da amfani Kiristoci su kiyaye halinsu na ruhaniya?
• Ta yaya za mu iya tabbatar da halinmu na Kirista?
• Sa’ad da muka fuskanci tambayar ko waye za mu faranta wa rai, waɗanne fasaloli ne za su taimaka mana mu yanke shawarar da ta dace?
• A matsayinmu na Kirista, yaya ne tunaninmu zai iya shafar rayuwarmu ta nan gaba?
[Hotuna a shafi na 13]
Nitsar da kanmu a cikin ayyukan Kirista na iya kyautata halinmu na Kirista