Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 3/1 p. 3
  • Bakar Magana Me Ya Sa Take Ɓata Rai?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bakar Magana Me Ya Sa Take Ɓata Rai?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Makamantan Littattafai
  • “Mu Bi Waɗannan Abu fa da ke Nufa Wajen Salama”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Israꞌilawa a Zamanin Dā Sun Yi Yake-Yake​—Me Ya Sa Ba Ma Yi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 3/1 p. 3

Bakar Magana Me Ya Sa Take Ɓata Rai?

“Me ke haddasa gāba da husuma tsakaninku?”—YAKUBU 4:1.

YAKUBU marubucin Littafi Mai Tsarki ya yi wannan tambayar ba ga sojojin Roma da suke yaƙi a lokacinsa ba. Ba kuma tuhumar wani rukunin Yahudawa masu kisankai a yaƙin sari-ka noƙe na ƙarni na farko a zamaninmu yake yi ba. Yakubu yana maganar husuma ce tsakanin mutane biyu. Me ya sa? Domin husuma tana yin ɓarna kamar yaƙi. Ga waɗannan misalai na Littafi Mai Tsarki.

’Ya’yan Yakubu uban iyali sun sayar da Yusufu ɗan’uwansu zuwa bauta domin sun tsane shi sosai. (Farawa 37:4-28) Saul, Sarkin Isra’ila ya yi ƙoƙari ya kashe Dauda. Don me? Domin yana ƙishin Dauda. (1 Sama’ila 18:7-11; 23:14, 15) A ƙarni na farko, Afodiya da Sintiki mata biyu Kiristoci sun dami dukan ikilisiya domin suna jayayya.—Filibiyawa 4:2.

A baya bayan nan, mutane suna warware jayayyarsu ta wajen fuskantar juna da takubba ko kuma bindigogi. Sau da yawa ana kashe ko kuma naƙasa ɗaya cikin masu faɗan. A yau waɗanda suke jayayya na dindindin suna amfani da baƙar magana. Ko da yake ba ta kashe mutum, baƙar magana tana ɓata rai da kuma sunan mutum. Sau da yawa marasa laifi ne suke wahala daga irin wannan ‘baƙar magana.’

Ka yi la’akari da abin da ya faru wasu shekaru da suka shige, sa’ad da wani firist a cocin Angilika ya zargi wani ɗan’uwansa firist da almubazzaranci da kuɗin coci. Jayayyarsu ta fito fili har ta kai ga raba ikilisiya da suke wa hidima zuwa rukuni dabam dabam. Wasu mabiyan ba sa zuwa coci idan firist da suka ƙi ne yake ba da jawabi. Mabiyan suna jayayya sosai har ta kai ga ba sa magana da juna sa’ad da suka je coci don bauta. Sa’ad da aka ce firist da ke zargin ɗayan ya yi lalata, jayayyar ta daɗa tsananta.

Shugaban bishop-bishop na garin Canterbury a Ingila ya roƙi firistoci biyun su bar jayayya. Ya ce jayayyarsu “ciwon daji” ne kuma “abin kunya ne da ba ya ɗaukaka sunan Ubangijinmu.” A shekara ta 1997 ɗaya cikin firistocin ya yarda ya yi murabus. Ɗayan kuwa ya ci gaba da hidimarsa har ya kai shekarar da dole ne ya yi murabus. Amma ya ci gaba har ya yi murabus a ranar 7 ga Agusta, 2001, ranar bikin haihuwarsa na cika shekara 70. Jaridar The Church of England (Cocin Ingila) ta ce ranar da ya yi murabus ranar bikin “Waliyi” Victricius ne. Wanene “Waliyi” Victricius? Wani limami ne a ƙarni na huɗu da aka ce an sha yi masa bulala domin ya ƙi ya yi yaƙi. Jaridar ta yi maganar halaye da suka bambanta waliyin da kuma firist ɗin da ya yi murabus tana cewa: “Firist da ke son ya yi murabus bai guji yin faɗa da wani firist ba.”

Da a ce sun bi gargaɗin da ke Romawa 12:17, 18: “Kada ku rama muguntar kowa da mugunta. Ku yi ta lura al’amuranku su zama daidai a gaban kowa. In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa,” da waɗannan firistoci ɗin ba su baƙanta wa kansu da kuma wasu ba.

Kai kuma fa? Idan wani ya yi maka laifi, ƙiyayya tana sa ka yi baƙar magana? Ko kuwa kana ƙin baƙar magana ka nemi yin salama. Idan ka yi wa wani laifi, kana kauce wa mutumin da zaton cewa idan aka jima kaɗan zai manta da batun? Ko kuwa kana neman gafara? Ko ka nemi gafara ko kuwa ka gafarta wa wani, sulhuntawa za ta sa ka farin ciki. Gargaɗin Littafi Mai Tsarki zai taimake mu mu magance jayayya dindindin.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba