Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 1/1 pp. 4-6
  • ƘAUNAR ALLAH ta Haɗa Kansu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ƘAUNAR ALLAH ta Haɗa Kansu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Menene Ya Jawo Kiristoci a Ikilisiya Kusa da Juna?
  • Sun Ci Gaba da Haɗa Kai
  • Haɗa Kai Cikin Bauta a Zamani
  • Haɗin Kai na Jawo Mutane
  • Ana Gane Masu Bauta Ta Gaskiya Ta Haɗin Kansu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Haɗin Kai Na Kiristoci Yana Ɗaukaka Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Bauta Cikin Haɗin Kai a Lokacinmu—Menene Take Nufi?
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 1/1 pp. 4-6

ƘAUNAR ALLAH ta Haɗa Kansu

SA’AD da aka kafa ikilisiyar Kirista a ƙarni na farko na zamaninmu, wani abu ɗaya da ya sa ta yi fice shi ne cewa—duk da bambance-bambance na mabiyanta—tana da haɗin kai. Waɗanda suke bauta wa Allah na gaskiya sun fito daga al’ummai dabam dabam, Asiya, Turai, da kuma Afirka. Mutane ne iri-iri—firistoci, sojoji, bayi, ’yan gudun hijira, ’yan tireda, masana, da kuma manyan ’yan kasuwa. Wasu Yahudawa ne wasu kuma ’Yan Al’ummai ne. Da yawa a dā mazinata ne, ’yan luwaɗi, mashaya, ɓarayi, masu kwaɗayi. Duk da haka, sa’ad da suka zama Kiristoci, sun yi watsi da miyagun ɗabi’unsu suka zama da haɗin kai cikin bangaskiya.

Me ya sa Kiristoci na ƙarni na farko suka haɗa kan dukan waɗannan mutane? Me ya sa suka yi zaman lafiya da juna da kuma galibin mutane? Me ya sa ba su saka hannu ba cikin hargitsi da yaƙe-yaƙe? Me ya sa Kiristoci na farko suka bambanta haka sosai da manyan addinai na yau?

Menene Ya Jawo Kiristoci a Ikilisiya Kusa da Juna?

Aba da ta haɗa kan mabiya a ƙarni na farko ita ce ƙaunar Allah. Waɗannan Kiristoci sun fahimci ainihin wajibin su ƙaunaci Allah na gaskiya, Jehobah, da zuciya ɗaya. Alal misali, an umurci manzo Bitrus, Bayahude, ya ziyarci gidan ɗan al’umma, mutumin da a dā ba wani abin da zai haɗa su. Aba da ta sa ya yi biyayya, ita ce ƙaunar Jehobah. Bitrus da wasu Kiristoci na farko sun more dangantaka mai kyau da Allah wadda take bisa cikakken sanin halayen Allah, abin da yake ƙauna da abin da yake ƙyama. Da shigewar lokaci, dukan masu bauta suka fahimci cewa nufin Jehobah ne a gare su su ‘haɗa kai, suna da nufi ɗaya, ra’ayinsu ɗaya.’—1 Korantiyawa 1:10; Matiyu 22:37; Ayyukan Manzanni 10:1-35.

Mabiya kuma suka sake kusantar juna domin bangaskiyarsu ga Yesu Kristi. Suna so su bi sawunsa da kyau. Ya umurce su: “Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku . . . Ta haka kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.” (Yahaya 13:34, 35) Wannan ba kawai zai kasance motsin zuciya ba ne, amma ƙauna ce na sadaukar da kai. Menene zai kasance sakamakon haka? Yesu ya yi addu’a game da waɗanda suka ba da gaskiya a gare shi: “[Na] roƙa . . . domin dukansu su zama ɗaya, kamar yadda kai, ya Uba, kake cikina, ni kuma nake cikinka, haka su ma su kasance cikinmu.”—Yahaya 17:20, 21; 1 Bitrus 2:21.

Jehobah ya zubo da ruhunsa mai tsarki, ko kuma ikon aikinsa ga bayinsa na gaskiya. Wannan ya kawo haɗin kai a tsakaninsu. Ya sa suka fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki yadda aka amince da ita a dukan ikilisiyoyi. Masu bauta wa Jehobah suna shelar saƙo ɗaya ne—tsarkake sunan Jehobah ta wajen Mulkin Allah na Almasihu, gwamnatin samaniya da za ta yi sarauta bisa dukan ’yan adam. Kiristoci na farko sun fahimci wajibinsu su kasance “ba na duniya ba.” Saboda haka, sa’ad da hargitsi ko kuma yaƙi ya tashi, Kiristoci ba sa saka hannu. Suna zaman lumana da kowa.—Yahaya 14:26; 18:36; Matiyu 6:9, 10; Ayyukan Manzanni 2:1-4; Romawa 12:17-21.

Dukan mabiya suna cika hakkinsu na kyautata haɗin kai. Ta yaya? Ta wajen tabbata cewa halayensu sun jitu da Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci: “Ku yar da halinku na dā, wanda dā kuke ciki,” kuma “ku ɗauki sabon halin.”—Afisawa 4:22-32.

Sun Ci Gaba da Haɗa Kai

Hakika, mabiya a ƙarni na farko ba kamiltattu ba ne, kuma yanayi sun taso da suka ƙalubalanci haɗin kansu. Alal misali, a Ayyukan Manzanni 6:1-6 an ba da labarin rashin jituwa da ya taso tsakanin Kiristoci Yahudawa masu jin Helenanci da waɗanda suke jin Ibrananci domin waɗanda suke jin Helenanci suna jin cewa ana nuna musu wariya. Da aka sanar da manzanni batun, sun magance shi cikin hanzari babu wariya. Daga baya batun koyarwa ya jawo rashin jituwa game da wajibin ’yan al’ummai a ikilisiyar Kirista. An yanke shawara bisa ga mizanan Littafi Mai Tsarki, kuma duka suka yarda da wannan shawarar.—Acts 15:1-29.

Waɗannan misalan sun nuna cewa rashin jituwa bai kai ga tsatsaguwa na ƙabila ko kuma rashin haɗin kai wajen koyarwa ba a ikilisiyar Kirista a ƙarni na farko. Me ya sa? Domin abubuwa da suke sa haɗin kai—ƙaunar Jehobah, bangaskiya ga Yesu Kristi, ƙauna ta sadaukar da kai ga juna, bin ja-gorar ruhu mai tsarki, fahimta iri ɗaya na Littafi Mai Tsarki, da kuma kasancewa a shirye a yi canji a halaye—suna da isashen ƙarfi su haɗa kan ikilisiya ta farko kuma ta kasance da salama.

Haɗa Kai Cikin Bauta a Zamani

Ana iya samun haɗin kai a wannan hanyar a yau? Waɗannan abubuwa za su iya jawo mabiya waje ɗaya kuma su sa su su yi zaman lumana da dukan launukan mutane a dukan ɓangarorin duniya? Ƙwarai kuwa! Shaidun Jehobah suna da haɗin kai a ’yan’uwantaka na dukan duniya da ya ƙunshi fiye da ƙasashe 230, tsibirai, da kuma yankuna. Kuma waɗannan abubuwa da suka haɗa kan Kiristoci na farko ne suka haɗa kan na zamani.

Aba da ta fi haɗa kan Shaidun Jehobah ita ce bautarsu ga Jehobah Allah. Wannan yana nufin cewa suna ƙoƙari su kasance da aminci a gare shi a dukan yanayi. Shaidun Jehobah kuma sun ba da gaskiya ga Yesu Kristi da kuma koyarwarsa. Waɗannan Kiristoci suna nuna ƙauna ta sadaukar da kai ga ’yan’uwansu masu bi kuma suna wa’azin bishara iri ɗaya ta Mulkin Allah a dukan ƙasashe da suke. Suna farin cikin gaya wa mutanen dukan addinai, launuka, da ƙasashe, game da wannan Mulki. Shaidun Jehobah babu ruwansu da al’amuran wannan duniya, wanda yake taimakonsu su tsayayya wa matsi na siyasa, al’ada na mutane, da na kasuwanci da suke da yawa a tsakanin mutane. Dukan Shaidun sun karɓi wajibinsu su ɗaukaka haɗin kai ta wajen halaye da suka jitu da mizanan Littafi Mai Tsarki.

Haɗin Kai na Jawo Mutane

Wannan haɗin kai sau da yawa yana jawo hankalin mutane da ba Shaidun Jehobah ba ne. Alal misali Ilse,a ta taɓa zama mace mai-zaman zuhudu na Katolika a Jamus. Menene ya jawo ta ga Shaidun Jehobah? Ilse ta ce: “Su ne mutanen kirki da na taɓa saduwa da su. Ba sa zuwa yaƙi, ba sa yin wani abu domin su cuci wani. Suna so su taimaki mutane su rayu cikin farin ciki a aljanna a duniya a ƙarƙashin Mulkin Allah.”

Günther ma wani misali ne, sojan Jamus ne da aka aika Faransa a lokacin yaƙin duniya na biyu. Wata rana firist na Frotastan ya limanci bauta a rukunin sojoji na Günther. Firist ɗin ya roƙi albarka, kāriya, da kuma nasara. Bayan bautar, Günther ya koma bakin aikinsa wajen gadi. Ta madubinsa mai jawo nesa kusa, ya lura cewa abokan gabansu ma firist yana yi musu ja-gora a wajen bauta a ɗayan gefen daga. Günther ya ce: “Wataƙila wannan firist ma ya roƙa musu albarka, kāriya, da kuma nasara. Na yi mamaki, me ya sa cocin Kiristoci za su kasance abokan gaba a yaƙi.” Wannan abu ne da Günther ba zai manta ba. Sa’ad da ya sadu da Shaidun Jehobah daga baya, ya ga ba sa saka hannu a yaƙi, sai Günther ya shiga ’yan’uwantakansu na dukan duniya.

Ashok da kuma Feema sun taɓa kasancewa a cikin addinin Gabas. A gidansu, suna da bagadin bauta ga allahnsu. Sa’ad da cuta mai tsanani ta faɗa wa iyalinsu, sai suka sake bincika addininsu. Da suke taɗi da Shaidun Jehobah, koyarwar Littafi Mai Tsarki da kuma ƙauna da take tsakanin Shaidun suka burge Ashok da Feema su ma yanzu masu shelar bisharar Mulkin Jehobah ne da ƙwazo.

Ilse, Günther, Ashok, da Feema suna da haɗin kai da miliyoyin Shaidun Jehobah a ’yan’uwantaka na dukan duniya. Sun gaskata alkawarin Littafi Mai Tsarki cewa abubuwa da suka haɗa kansu a yau ba da daɗewa ba za su haɗa kan dukan ’yan adam masu biyayya. Sa’an nan ba za a sake samun mugunta ba, da rarrabuwar kawuna, da kuma tsatsaguwa cikin sunan addini. A dukan duniya za a haɗa kai wajen bauta wa Jehobah Allah na gaskiya shi kaɗai.—Wahayin Yahaya 21:4, 5.

[Hasiya]

a An canja wasu sunaye da aka yi amfani da su cikin wannan talifin.

[Hotuna a shafuffuka na 4, 5]

Ko da yake sun fito daga wurare dabam dabam, Kiristoci na farko suna da haɗin kai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba