Abin Da Ya Sa Mutane Da Yawa Suke Shakkar Cewa Addini Zai Haɗa Kan ’Yan Adam
“KA ƘAUNACI ɗan’uwanka.” (Matiyu 22:39) Addinai da yawa suna yaba wa wannan kyakkyawar ɗabi’a. Idan waɗannan addinai suna ƙoƙari wajen koyar da mabiyansu su ƙaunaci ’yan’uwansu, da mabiyansu sun kasance da haɗin kai. Amma, abin da ka lura ke nan? Addini yana kawo haɗin kai kuwa? A wani bincike da aka yi a Jamus a baya bayan nan, an yi wannan tambayar: “Shin addini yana haɗa kan mutane ne, ko kuma dai yana raba su ne?” Kashi 22 cikin ɗari sun amsa cewa addini yana haɗa kan mutane, kashi 52 kuma suka ce addini yana raba mutane ne. Wataƙila a ƙasarku mutane suna da irin wannan ra’ayin.
Me ya sa mutane kalilan ne suke da tabbacin cewa addini zai iya haɗa kan mutane? Wataƙila saboda abubuwa da suka sani daga tarihi. Maimakon haɗa kan mutane, sau da yawa addini ya raba su. A wani lokaci, baƙar mugunta da aka yi an yi ta ne domin addini. Ka yi la’akari da wasu misalai daga shekaru 100 da suka shige.
Da Sunan Addini
A lokacin yaƙin duniya na biyu, Kuroshiyawa ’yan Katolika da Sabiyawa ’yan Otodos a Gabashin Turai suka yi ta kashe juna. Kowanensu yana da’awar yana bin Yesu, wanda ya koya wa mabiyansa su ƙaunaci ’yan’uwansu. Duk da haka, yaƙinsu ya kai ga “kisan ƙare dangi mafi muni da aka sani a tarihi,” in ji wani mai bincike. Adadin waɗanda suka mutu ya tsorata duniya, fiye da maza, mata, da yara 500,000 suka mutu.
A shekara ta 1947 Indiya ƙasa ce ta mutane miliyan 400, da suka ƙunshi Hindu, Musulmai, da Sikhawa kashi biyar na dukan ’yan adam. Da aka raba Indiya aka sami ƙasar Musulmai ta Pakistan. A wannan lokaci, an ƙona ɗarurruwan dubban masu gudun hijira daga ƙasashen biyu, wasu an yi musu duka, wasu an gana masu azaba, wasu kuma an harbe su a jerin farmakin kisan ƙare dangi na addini.
Kamar dai waɗannan ba su isa ba, shigowar sabon ƙarnin nan ya fito da barazanar ta’addanci. A yau, ta’addanci ya ta da hankalin dukan duniya, kuma da yawa cikin rukunonin ’yan ta’adda suna da’awar cewa suna da goyon bayan addini. Ba a ɗauki addini magami mai haɗa kai ba. Maimakon haka, sau da yawa ana haɗa shi da zubar da jini da rabewar kai. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne da jaridar labarai na Jamus wadda ake kira Focus ta kwatanta manyan addinai na duniya—Buddanci, Kristanci, Kofishiyanci, Hindunci, Musulunci, Yahudanci, da kuma Tawonci—da albarushi.
Jayayya a Cikin Gida
Sa’ad da wasu addinai suke yaƙi da junansu, wasu kuma suna fama da jayayya a cikin gida. Alal misali, a shekarun baya bayan nan, cocin Kiristandam ya rabu domin jayayya a kan abin da ake koyarwa. Malamai da mabiya suka yi tambaya: Shin an amince a ƙa’ida iyali? An yarda a zubar da ciki? Ya kamata ne a naɗa mata su zama firistoci? Yaya matsayin luwaɗi a coci? Ya kamata ne addini ya aminci da yaƙi? Domin irin waɗannan rashin jituwa, mutane da yawa suke mamaki, ‘Ta yaya addini zai haɗa kan mutane idan ba zai iya haɗa kan mabiyansa ba?’
A bayyane yake cewa galibi addini ya gaza wajen haɗa kan mutane. Amma dukan addinai ne suke da rarrabuwar kai? Akwai addinin da ya bambanta ne—wanda zai iya haɗa kan ’yan adam?
[Hoto a shafi na 3]
’Yan sanda da suka ji rauni sa’ad da addinai suka yi taho mu gama a Indiya a shekara ta 1947
[Inda aka Dauko]
Photo by Keystone/Getty Images