Wane Addini Ya Kamata Ka Zaɓa?
‘ADDINAI hanyoyi ne dabam dabam da suke da nufi ɗaya. Ballantana ma, Allah ɗaya ne, ko ba haka ba?’ Waɗanda suke jin cewa ko da bin wani addini yana da muhimmanci, babu wata matsala a duk addini da mutum ya zaɓa ya bi ne suka yarda da furcin nan.
A farko kamar wannan daidai ne, da yake Allah ɗaya ne, Maɗaukaki Duka. (Ishaya 44:6; Yohanna 17:3; 1 Korinthiyawa 8:5, 6) Duk da haka, ba za mu iya ƙyale bambance-bambance da ke a bayyane ba—har da saɓani ma—tsakanin yawancin rukunin addinai da ke da’awar bauta wa Allah na gaskiya. Sun bambanta sosai a ayyukansu, imaninsu, koyarwarsu, da farillansu. Bambancin yana da yawa sosai har wasu da suke bin wani addini ko kuma rukuni sun iske shi da wuya su fahimci ko su yarda da abin da wasu suke koyarwa ko yi imani da shi.
A wata sassa, Yesu ya ce: “Allah ruhu ne; waɗanda su ke yi masa sujada kuma, sai su yi sujada cikin ruhu da cikin gaskiya kuma.” (Yohanna 4:24) Bauta wa Allah cikin gaskiya yana ƙyale ra’ayoyi da yawa da suka saɓa da juna game da wanene Allah, nufe-nufensa, da kuma yadda yake son a bauta masa ne? Daidai ne mu yarda cewa yadda muke bauta wa Allah Maɗaukaki Duka bai da muhimmanci gare shi?
Kiristoci na Gaskiya a Dā da Kuma a Yanzu
A wasu lokatai Kiristoci na ƙarni na farko sun kasance da ra’ayoyi dabam dabam game da abubuwa. Alal misali, da yake magana game da waɗanda suke Koranti, manzo Bulus ya ce: “ ’Yan’uwa, an shaida mini a kanku, daga bakin ’yan gidan Kuluwi, wai akwai jayayya tsakaninku. Wato azancina, kowane ɗaya daga cikinku yana cewa, Ni na Bulus ne; Ni na Apollos; Ni na Kefas; Ni na Kristi.”—1 Korinthiyawa 1:11, 12.
Bulus ya ɗauki waɗannan bambance bambancen ra’ayi cewa babu muhimmanci ne? Kowane mutum yana bin nasa ra’ayi ne don ya sami ceto? A’a! Bulus ya yi gargaɗi: “ ’Yan’uwa, ina roƙonku, ta wurin sunan Ubangijinmu Yesu Kristi, dukanku ku yi magana ɗaya, kada tsatsaguwa su kasance a tsakaninku; amma ku zama cikakku cikin hankali ɗaya da shawara ɗaya.”—1 Korinthiyawa 1:10.
Hakika, ba a samun haɗin kai a imani ta wurin tilastawa. Ana iya samunsa sa’ad da mutane sun yi bincike sosai kuma sun yarda su kammala daidai. Saboda haka, nazarin Kalmar Allah da kanka kuma da muradin bin abin da ka koya muhimman matakai ne don ka mori irin haɗin kai da Bulus ya yi maganarsa. Za a iya samun irin wannan haɗin kan kuwa? Kamar yadda aka tattauna, Allah yana sha’ani da mutanensa a rukuni. Yana yiwuwa ne a san wannan rukunin a yau?
Fa’idodin Tarayya da ta Dace
Mai Zabura Dauda ya taɓa tambaya: “Ya Ubangiji, wa za ya sauka cikin tanti naka? Wanene za ya zauna cikin tudunka mai-tsarki?” Hakika wannan tambaya ce mai sa tunani. Dauda ya ba da amsa: “Shi wanda ke tafiya sosai, yana aika adalci, yana kuwa faɗin gaskiya cikin zuciyarsa.” (Zabura 15:1, 2) Cikakken sanin Littafi Mai Tsarki zai taimake mutum ya sami addini na gaskiya da ke bin farillan Allah. Sa’an nan, ta yin tarayya da wannan rukunin, mutum zai ji daɗin tarayya mai ginawa da mutanen da suke bauta wa Allah da haɗin kai “cikin ruhu da cikin gaskiya kuma.”
Shaidun Jehovah sun nuna cewa yana iya yiwuwa a sami haɗin kai a imani da hali har ma a duniya ta yau da babu haɗin kai. A tsakaninsu da akwai wasu da dā suke cikin ɗaruruwan addinai da rukunin ƙabilai. Wasu Shaidu dā waɗanda ba su gaskata akwai Allah ba ne ko kuma masu musun wanzuwar Allah ne. Wasu har ila dai ba ruwansu da addini. An sami mutane daga cikin wannan iri-irin addinai, al’adu, da ussan ilimi waɗanda yanzu ke jin daɗin haɗin kan addini da ba a samunsa a duniya a yau ba.
Tushen wannan haɗin kai shi ne Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki. Hakika, Shaidun Jehovah sun sani cewa ba za su tilasta wa mutane abin da suke bukatar yi ba. Amma suna godiya ga gatar ƙarfafa mutane su koya daga Littafi Mai Tsarki domin su yi zaɓe bisa wannan tushe mai ƙarfi su yi sujada. A wannan hanyar ce, mutane da yawa za su iya amfana daga bauta wa Allah “cikin ruhu da kuma cikin gaskiya.”
A yau, haɗarin faɗawa cikin mugun tasiri da tarko yana da girma. Zaɓan tarayya da ta dace tana da muhimmanci. Littafi Mai Tsarki ya ce ‘wanda yake tafiya tare da masu-hikima, zai kuwa yi hikima’ kuma “zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.” (Misalai 13:20; 1 Korinthiyawa 15:33) Yin tarayya da ainihin masu bauta wa Allah kāriya ce. Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya tunasar mana: “Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu, kamar yadda waɗansu sun saba yi, amma mu gargaɗadda juna; balle fa yanzu, da kuna ganin ranan nan tana gusowa.” (Ibraniyawa 10:24, 25) Wannan lallai albarka ce sa’ad da abokai na gaske, ’yan’uwa maza da mata a ruhaniya, suna taimakon juna cikin ƙauna domin su cika hakkinsu a gaban Allah!
Ottmar ya tabbatar da wannan ra’ayin. An yi renonsa a Jamus a cikin iyalin Katolika, amma bai daɗe ba ya bar zuwan coci. Ya ce: “Duk lokacin da na je coci, nakan koma gida ban koya kome ba.” Duk da haka, ya riƙe bangaskiyarsa ga Allah. Sai ya sadu da Shaidun Jehovah kuma ya tabbata sune bayin Allah na gaske. Ya ga bukatar yin tarayya da su. Yanzu ya ce: “Ina more salamar zuci da kwanciyar rai domin kasance da himma cikin ƙungiya ta dukan duniya. Ana taimakona a hankali in samu cikakken sani na Littafi Mai Tsarki. Abu ne mai tamani a gare ni.”
Gayya ga Waɗanda Suke Biɗa
Mutane masu nufi ɗaya da suke aiki tare a rukuni suna iya aiki da kyau fiye da waɗanda suke zaman kansu. Alal misali, umurnin da Yesu ya ba wa mabiyansa kafin su rabu shi ne: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” (Matta 28:19, 20) Ta yaya za a cika wannan aiki sosai idan babu ja-gora ko kuma tsari? Ta yaya mutum zai yi biyayya da wannan umurnin Nassin idan yana ƙoƙarin ya bauta ma Allah da kansa kawai ba tare da yin tarayya da wasu ba?
A cikin shekarar da ta shige, Shaidun Jehovah a dukan duniya sun rarraba littattafai na tushe daga Littafi Mai Tsarki, ƙasidu, da mujallu 91,933,280, da jaridu 697,603,247, ta haka sun kai saƙon Kalmar Allah wa miliyoyin mutane a ƙasashe 235. Hakika wannan tabbaci ne cewa yin aiki cikin haɗin kai da ƙoƙarce-ƙoƙarcen rukuni da aka tsara suna aiki sosai fiye da ƙoƙarin mutum ɗaya kawai.
Ƙari ga rarraba littattafai da suke da tushe cikin Littafi Mai Tsarki, Shaidun Jehovah suna tafiyar da nazarin Littafi Mai Tsarki kyauta domin su taimake mutane su sami sani sosai na abin da Allah yake bukata. A shekarar da ta shige, sun tafiyar da wannan nazarin Littafi Mai Tsarki, matsakaicinsu 5,726,509 da mutane ɗai-ɗai ko da rukunin mutane kowane mako. Wannan koyarwar Littafi Mai Tsarki ta taimaki miliyoyin mutane su sami dalili mai kyau da za su yi zaɓensu na bauta. Ana gayyatarka ka koya farillan Allah yadda suke a cikin Littafi Mai Tsarki. Bayan haka sai ka tsai da shawararka.—Afisawa 4:13; Filibbiyawa 1:9; 1 Timothawus 6:20; 2 Bitrus 3:18.
Idan kana son ka faranta wa Allah zuciya, muhimmin abu ne ka bi wani addini—amma ba kowanne addini ko rukuni kawai ba. Duk da haka, ya kamata ka zaɓi addininka bisa cikakken sanin Littafi Mai Tsarki, ba a kan wasu jita-jita ba ko kuma a kan waiwai ba. (Misalai 16:25) Ka koya farillan addini na gaskiya. Ka gwada su da imaninka. Sa’an nan ka yi zaɓe mai kyau.—Kubawar Shari’a 30:19.
[Hotuna a shafi na 5]
Shaidun Jehovah suna more haɗin kai a cikin duniya da babu haɗin kai