Tsofaffi—Suna Da Tamani A Cikin ’Yan’uwancinmu Na Kirista
“Su waɗanda an dasa cikin gidan Ubangiji za su yi yabanya. . . . Za su yi ta ’ya’ya da tsufa a kai.”—ZABURA 92:13, 14.
1. Yaya mutane da yawa suke ɗaukan tsofaffi?
JEHOVAH yana ƙaunar dukan bayinsa amintattu, har da waɗanda suka tsufa. Bisa ga wani kimantawa na ƙasa, kowace shekara tsofaffi kusan rabin miliyan a ƙasar Amirka suke shan wahalar zalunci ko kuwa ƙyaliya. Irin wannan rahoto da ake samu a gewayan duniya ya nuna cewa zaluntar tsofaffi matsala ce a dukan duniya. Wata ƙungiya ta kira tushen wannan matsalar “halin mutane da yawa a ko’ina shi ne . . . amfanin tsofaffi ya wuce, ba su da wani amfani kuma suna dangana ga taimako daga wasu ne.”
2. (a) Yaya Jehovah yake ɗaukan bayinsa amintattu tsofaffi? (b) Wane kwatanci mai daɗaɗa rai muka samu a Zabura 92:12-15?
2 Jehovah Allah yana ɗaukan tsofaffin bayinsa amintattu da tamani. Yana mai da hankalinsa ne ga “mutumi namu na ciki”—yanayin ruhaniyarmu—maimakon kasawarmu. (2 Korinthiyawa 4:16) Mun sami tabbaci mai daɗaɗa rai a cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki: “Mai-adalci za shi yi yabanya kamar giginya [Ibrananci tamar da ke nufin “itacen dabino”]: za shi yi girma kamar cedar cikin Lebanon. Su waɗanda an dasa cikin gidan Ubangiji za su yi yabanya cikin harabun Allahnmu. Za su yi ta ’ya’ya da tsufa a kai: Za su kasance cike da romo da ɗanyantaka: Domin a bayyana Ubangiji mai-yi daidai ne.” (Zabura 92:12-15) Tattauna waɗannan ayoyi zai nuna fasalolin gudummawa da ku tsofaffi za ku iya ba da cikin ’yan’uwancinmu na Kirista.
“Za Su Yi ta ’Ya’ya da Tsufa a Kai”
3. (a) Me ya sa aka kamanta masu adalci da itacen dabino? (b) Ta yaya tsofaffi suke “ ’ya’ya da tsufa a kai”?
3 Mai Zabura ya kamanta amintattu da itacen dabino ‘waɗanda aka dasa a cikin harabun Allahnmu.’ Sun “yi ta ’ya’ya da tsufa a kai.” Ba ka yarda ba cewa wannan yana da ban ƙarfafa? Ana ganin kyaun itacen dabino a ko’ina a farfajiyar mutanen Gabas na lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki. Ban da darajar adonta, itacen dabino tana da daraja saboda ’ya’ya masu yawa da take yi, waɗansu suna ba da ’ya’ya fiye da shekara ɗari ma.a Idan ka dasu ƙwarai a cikin ibada ta gaskiya, haka nan kai ma za ka iya “bada ’ya’ya cikin kowane kyakkyawan aiki.”—Kolosiyawa 1:10.
4, 5. (a) Waɗanne irin muhimman ’ya’ya ya kamata Kiristoci su ba da? (b) Ka ba da misalai na Nassi na tsofaffi da suka ba da “ ’ya’yan leɓuna.”
4 Jehovah yana son Kiristoci su yi “ ’ya’yan leɓuna”—kalami da aka yi don yabonsa da kuma manufarsa. (Ibraniyawa 13:15) Wannan ya shafe ka ne kai da ka tsufa? Hakika.
5 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalan tsofaffi waɗanda da gaba gaɗi suka ba da shaida game da sunan Jehovah da kuma nufe-nufensa. Musa ya riga ya wuce shekaru “hauya uku da goma” sa’ad da Jehovah ya sa ya zama annabinsa da kuma wakilinsa. (Zabura 90:10; Fitowa 4:10-17) Tsufa bai hana annabi Daniel ya ba da shaida game da ikon mallakar Jehovah da gaba gaɗi ba. Wataƙila Daniel yana cikin shekarunsa na 90 sa’ad da Belshazzar ya sammace shi ya fassara rubutun da ba a fahimta ba da hannu yake rubutawa a jikin bango. (Daniel, sura 5) Manzo Yohanna tsoho kuma fa? Kusa da ƙarshen aikinsa na dogon lokaci, ya iske kansa a kurkuku a tsibirin Batmusa “sabili da maganar Allah da shaidar Yesu.” (Ru’ya ta Yohanna 1:9) Wataƙila kana iya tunawa da wasu a cikin Littafi Mai Tsarki da suka ba da “ ’ya’yan leɓuna” a ƙarshen shekarunsu.—1 Samu’ila 8:1, 10; 12:2; 1 Sarakuna 14:4, 5; Luka 1:7, 67-79; 2:22-32.
6. Ta yaya ne Jehovah ya yi amfani da ‘tsofaffi’ su yi annabci a waɗannan kwanaki na ƙarshe?
6 Manzo Bitrus ya ɗauko maganar annabi Joel Ba’ibrane a inda ya sanar: “A cikin kwanakin ƙarshe,” in ji Allah, “zan zuba Ruhuna bisa mai-rai duka [har da “tsofaffi”], . . . za su yi annabci kuma.” (Ayukan Manzanni 2:17, 18; Joel 2:28) Daidai da haka, a wannan kwanaki na ƙarshe, Jehovah ya yi amfani da tsofaffi waɗanda suke cikin rukunin shafaffu da kuma “waɗansu tumaki” domin su yi shelar nufe-nufensa. (Yohanna 10:16) Wasunsu cikin aminci sun ci gaba da ba da ‘ya’ya na Mulki shekaru da yawa.
7. Ka ba da misalin yadda tsofaffi suke yaɗa ’ya’yan Mulki duk da raunanar jikinsu.
7 Yi la’akari da Sonia, da ta zama majagaba na cikakken lokaci wadda take shelar Mulki a shekara ta 1941. Ko da yake ta yi fama da rashin lafiya mai tsanani na da daɗewa, ta ci gaba da tafiyar da nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai a cikin gidanta. “Yaɗa bishara ya zama abin da ba zan iya bari ba a rayuwata,” in ji Sonia. “Hakika, ya zama tafarkin rayuwata. Na ƙi in daina yin wa’azi.” Ba da daɗewa ba, Sonia da ’yar’uwarta, Olive, sun gaya wa Janet mai ciwon ajali wadda suka sadu da ita a asibiti, begen da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Mamar Janet, mai yawan ibada ’yar addinin Katolika ce, ta ji daɗin ƙauna da aka nuna ma ’yarta, wannan ya sa ta yarda a riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki na gida da ita kuma yanzu tana ci gaba mai kyau. Kana iya amfani da irin wannan zarafi ka yaɗa ‘ya’yan Mulki?
8. Ta yaya ne Kaleb tsoho ya nuna cewa ya dogara ga Jehovah, kuma yaya ne Kiristoci tsofaffi za su iya yin koyi da misalinsa?
8 Ta ci gaba da ƙarfin zuciya wajen aikin wa’azi na Mulki duk da raunana ta tsufa, tsofaffin Kiristoci suna bin tafarkin Ba’isra’ile mai-aminci, Kaleb, wanda yake tare da Musa a cikin daji har shekaru arba’in. Kaleb yana ɗan shekara 79 sa’ad da ya ketare Kogin Urdun zuwa Ƙasar Alkawari. Bayan ya yi shekaru shida yana cikin rundunar yaƙi na Isra’ila masu nasara da ya yi murabus kawai. Amma bai yi haka ba, ya ci gaba da aikinsa da gaba gaɗi yana mallakar “birane manya masu ganuwa” a sashen duwatsu na Yahuda, wurin da Anakim ke zaune, mutane ƙatta. Da taimakon Jehovah, Kaleb ya “kore su kuwa kamar yadda Ubangiji ya faɗi.” (Joshua 14:9-14; 15:13, 14) Ka tabbata cewa Jehovah yana tare da kai, yadda ya yi da Kaleb, sa’ad da kake ci gaba da ba da ‘ya’yan Mulki duk da tsufarka. Idan ka kasance mai aminci, zai ba ka wuri a sabuwar duniya da ya yi alkawarinta.—Ishaya 40:29-31; 2 Bitrus 3:13.
“Za Su Kasance da Romo da Ɗanyantaka”
9, 10. Ta yaya ne tsofaffin Kiristoci suka zama sahihai a cikin bangaskiya kuma suka riƙe ƙarfin ruhaniyarsu? (Duba akwati a shafi na 9.)
9 Da yake jawo hankalinmu ga albarkar tsofaffin bayin Jehovah, mai Zabura ya rera: “Mai-adalci za shi yi yabanya kamar giginya [Ibrananci tamar da ke nufin “itacen dabino”]: za shi yi girma kamar cedar cikin Lebanon. Za su yi ta ’ya’ya da tsufa a kai: Za su kasance cike da romo da ɗanyantaka.”—Zabura 92:12,14.
10 Ta yaya ne za ka iya riƙe kuzarinka na ruhaniya duk da tsufarka? Kyaun itacen dabino ya dangana ne ga samun ruwa ko da yaushe. Haka nan, za ka iya samun abinci daga ruwan gaskiya na Littafi Mai Tsarki ta yin nazarin Kalmar Allah da kuma yin tarayya da ƙungiyarsa. (Zabura 1:1-3; Irmiya 17:7, 8) Ƙarfin ruhaniyarka zai sa ka zama mai tamani ga ’yan’uwanka masu bi. Ka yi la’akari da yadda haka ya zama gaskiya game da tsoho Babban Firist Jehoiada.
11, 12. (a) Wane irin aiki ne Jehoiada ya yi a tarihin daular Yahuda? (b) Ta yaya ne Jehoiada ya yi amfani da ikonsa domin ya ɗaukaka bauta ta gaskiya?
11 Wataƙila Jehoiada yana da shekaru fiye da ɗari sa’ad da Sarauniya Athaliah ta ƙwace mulkin ƙasar Yahuda ta wajen karkashe dukan jikokinta. Menene Jehoiada tsoho zai yi? Shi da matarsa suka ɓoye Jehoash wanda shi kaɗai ne ya tsira daga cikin magadan sarautar, har tsawon shekara shida, a cikin haikali. A hanya ta ban mamaki, sai Jehoiada ya bayyana Jehoash ɗan shekara bakwai a matsayin sarki ya kuma halaka Athaliah.—2 Labarbaru 22:10-12; 23:1-3, 15, 21.
12 A matsayinsa na mai kula da sarki, Jehoiada ya yi amfani da ikonsa ya ɗaukaka bauta ta gaskiya. Ya “yi alkawari tsakanin kansa da dukan jama’a da kuma sarki, su zama jama’ar Ubangiji.” Da izinin Jehoiada, mutanen suka rurrushe gidan Ba’al allahn ƙarya suka cire bagadansa, sifofinsa, da firist. Kuma ƙarƙashin ja-gorar Jehoiada ne Joash ya maido ayyukan hidima a haikali kuma ya yi ayyukan da ake bukata wajen gyaran haikali. “Jehoash ya aika nagarta a gaban Ubangiji dukan kwanakinsa, inda Jehoiada firist yana koya masa.” (2 Labarbaru 23:11, 16-19; 24:11-14; 2 Sarakuna 12:2) Sa’ad da ya mutu a shekararsa ta 130, an yi wa Jehoiada biso mai girma tare da sarakuna “domin ya yi aikin nagarta cikin Isra’ila, zuwa ga Allah da gidansa kuma.”—2 Labarbaru 24:15, 16.
13. Ta yaya tsofaffin Kiristoci za su ‘iya yin aikin nagarta ga Allah da gidansa kuma’?
13 Wataƙila rashin lafiya ko kuwa wasu yanayi sun rage abin da za ka iya yi domin ɗaukaka bauta ta gaskiya. Idan haka ne, kai ma kana ‘iya yin aikin nagarta ga Allah da gidansa.’ Kana iya nuna himma ga gidan ruhaniya na Jehovah ta hanyar halarta da yin furci a taron ikilisiya da kuma sa hannu cikin hidimar fage a kowane lokaci da ka samu damar yin hakan. Kasancewarka a shirye ka karɓi shawarar Littafi Mai Tsarki da kuma tallafawarka na aminci ga “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” da kuma ikilisiyar za ta ƙarfafa ’yan’uwanci na Kirista. (Matta 24:45-47) Kana iya tsokanar ’yan’uwa masu-bi “ga ƙauna da nagargarun ayyuka.” (Ibraniyawa 10:24, 25; Filimon 8, 9) Za ka zama albarka ga wasu idan ka bi shawarar da manzo Bulus ya bayar: “Tsofaffi su kasance masu-kamewa, masu kimtsa fuska, masu-hankali, sahihai [“da ƙwazo,” in ji An American Translation] cikin bangaskiya, cikin ƙauna, cikin haƙuri. Haka nan tsofaffin mata kuma su yi ladabi cikin al’amuransu, ba masu-tsegumi ba, ba bayi ne ga yawan ruwan anab ba, masu-koyarda nagarta.”—Titus 2:2-4.
14. Menene tsofaffin Kiristoci masu kula za su yi don su ci gaba da bauta ta gaskiya?
14 Kana hidima na dattijo a cikin ikilisiya na shekaru da yawa? “Ka yi amfani da hikimar da ka samu a duk shekarunka babu son kai,” wannan shi ne shawarar da wani tsohon dattijo na ikilisiya ya faɗi. “Ka ba da aiki, ka kuma ba da labarinka ga waɗanda suke son su yi koyi daga wurinka. . . . Kana ganin wasu za su iya yin wani abu. Ka yi koyi kuma ka faɗaɗa wannan iyawa. Ka yi shiri don nan gaba.” (Kubawar Shari’a 3:27, 28) Marmarinka na ƙwarai a faɗaɗa aikin bisharar Mulki zai kawo albarka mai yawa ga wasu a cikin ’yan’uwancinmu na Kirista.
“Ka Bayyana Ubangiji Mai-Yi Daidai Ne”
15. Ta yaya ne Kiristoci tsofaffi suke “bayyana Ubangiji mai-yi daidai ne”?
15 Tsofaffin bayin Allah suna yin aikinsu da murna “domin a bayyana Ubangiji mai-yi daidai ne.” Idan kai dattijo ne na Kirista, maganarka da ayyukanka za su nuna ma wasu cewa ‘Ubangiji Fa naka ne, a cikinsa kuwa babu rashin adalci.’ (Zabura 92:15) Itacen dabino yana ba da shaidar halaye mafi girma na Mahaliccinsa. Amma Jehovah ya ba ka gatar ba da shaida game da shi ga waɗanda suke na’am da bauta ta gaskiya. (Kubawar Shari’a 32:7; Zabura 71:17, 18; Joel 1:2, 3) Me ya sa wannan yake da muhimmanci?
16. Wane misali na Littafi Mai Tsarki ya nuna muhimmancin “bayyana Ubangiji mai-yi daidai ne”?
16 A lokacin da shugaba Ba’isra’ile Joshua “ya tsufa, shekarunsa sun yawaita,” sai “ya kira dukan Isra’ila da dattiɓansu da manyansu, da alƙalawansu, da magabatansu,” domin ya tuna musu yadda Allah ya yi sha’ani da su cikin gaskiya. Ya ce: “Babu wani abu ɗaya ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku: dukansu sun tabbata a gareku.” (Joshua 23:1, 2, 14) Na ɗan lokaci, waɗannan kalaman sun ƙarfafa mutanen su kasance masu aminci. Bayan mutuwar Joshua, “sai kuma wata tsara ta tashi . . . waɗanda ba su san Ubangiji ba, ko aikin da ya aika domin Isra’ila. ’Ya’yan Isra’ila fa suka aika mugunta a idanun Ubangiji, suka bauta ma Ba’alim.”—Alƙalawa 2:8-11.
17. Ta yaya ne Jehovah ya yi sha’ani da mutanensa a wannan zamanin?
17 Amincin ikilisiyar Kiristoci na yanzu bai dangana a kan rubutaccen labaran tsofaffin bayin Allah na dā ba kawai. Amma, bangaskiyarmu ga Jehovah da alkawuransa yana ƙarfi sa’ad da muka ji labarin “manyan ayyukan” da ya aikata domin mutanensa a waɗannan kwanaki na ƙarshe. (Alƙalawa 2:7; 2 Bitrus 1:16-19) Idan ka fara tarayya da ƙungiyar Jehovah na shekaru da yawa, kana iya tuna lokacin da masu shelar Mulki suke ɗan kaɗan a ƙasarka ko kuma a yankinka ko kuma sa’ad da aikin wa’azi yake fuskantar hamayya mai tsanani. A kwana a tashi, ka ga yadda Jehovah ya cire wasu matsaloli kuma ya “hanzarta” yawan masu bishara. (Ishaya 54:17; 60:22) Ka lura da ƙarin bayanin gaskiya na Littafi Mai Tsarki kuma ka shaida gyaran da aka yi a ƙungiyar Allah da ake gani. (Misali 4:8; Ishaya 60:17) Kana nema ka ƙarfafa wasu ta wurin gaya musu labarinka da ya nuna Jehovah mai-yi daidai ne? Wannan zai motsa ya kuma ƙara ƙarfafa ’yan’uwancinmu na Kirista!
18. (a) Ka ba da misalin sakamakon gaya wa mutane “Ubangiji mai-yi daidai ne.” (b) Ta yaya ne ka taɓa shaida adalcin Jehovah?
18 Lokacin da ka shaida kulawar Jehovah na ƙauna da kuma ja-gorancinsa a rayuwarka kuma fa? (Zabura 37:25; Matta 6:33; 1 Bitrus 5:7) Wata ‘yar’uwa tsohuwa mai suna Martha ta ƙarfafa wasu cewa: “Ko menene ya faru, kada ka ƙyale Jehovah. Domin zai kiyaye ka.” Wannan shawarar ta taɓa Tolmina sosai, ɗaya ce cikin waɗanda Martha ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su, ta yi baftisma a farkon shekarun 1960. “Lokacin da mijina ya mutu,” in ji Tolmina, na yi sanyin gwiwa ƙwarai, amma waɗancan kalmomi ya sa na ƙudura cewa ba zan ƙi halartar taro ko guda ba. Kuma Jehovah ya ƙarfafa ni na ci gaba.” Tolmina ta ba da irin wannan shawarar ga mutane da yawa da take nazarin Littafi Mai Tsarki da su na shekaru da yawa. Hakika, ta wurin ba da ƙarfafa da kuma ba da cikakken labarin yadda Jehovah ya yi daidai, kana iya yin fiye da haka don gina bangaskiyar ’yan’uwa masu bi.
Jehovah Yana Ɗaukar Tsofaffi Amintattu da Tamani
19, 20. (a) Yaya ne Jehovah yake ɗaukan ayyukan bayinsa tsofaffi? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?
19 Wannan duniya ta yau, da ta cika da rashin godiya, ba ta la’akari da tsofaffi. (2 Timothawus 3:1, 2) Sau da yawa abin da ya sa ake tuna da su, domin yadda suke dā ne, ba domin yadda suke a yanzu ba. Akasarinsa, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ba marar-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa, yayinda kuka hidimta ma tsarkaka, kuna kuwa yi har wa yau.” (Ibraniyawa 6:10) Hakika, Jehovah Allah yana tuna amintaccen ayyuka na dā da ka yi. Amma kuma yana daraja ka domin hidimar da ka ke ci gaba da yi masa. Hakika, ya ɗauki amintattun tsofaffi a matsayin masu ba da ’ya’ya, lafiyayyu ta ruhaniya, kuma Kiristoci masu ƙarfi—mutane rayayyu tabbaci na ƙarfinsa.—Filibbiyawa 4:13.
20 Kana ɗaukan tsofaffi waɗanda suke cikin ’yan’uwancinmu na Kirista yadda Jehovah yake ɗaukansu? Idan haka ne, wannan zai sa ka nuna ƙaunarka a gare su. (1 Yohanna 3:18) Talifinmu na gaba zai nuna wasu hanyoyi masu kyau da za mu nuna irin wannan ƙauna ta wajen kula da bukatunsu.
[Hasiya]
a Kowane tarin damin dabino tana yin ’ya’ya kusan dubu, kuma tana iya kai nauyin kilo 8 ko fiye da haka. Wani marubuci ya kimanta cewa “kowane itacen dabino zai iya yin ’ya’ya har tan biyu ko uku na dabino da mai shi zai samu riba sa’ad da take raye.”
Menene Amsoshin Ka?
• Ta yaya ne tsofaffi suke “bada ’ya’ya”?
• Me ya sa ƙarfin ruhaniyar Kiristoci tsofaffi yake da daraja?
• Ta yaya tsofaffi za su iya faɗa cewa “Ubangiji mai-yi daidai ne”?
• Me ya sa Jehovah yake daraja bayinsa tsofaffi?
[Hoto a shafi na 7]
Tsofaffi suna ba da ’ya’yan Mulki masu daraja
[Hoto a shafi na 10]
Ƙarfi na ruhaniyar tsofaffi tamani ne mai daraja