Allah Yana Kula da Tsofaffi
WULAKANTA tsofaffi da ya zama ruwan dare a yau ba abin mamaki ba ne. Da daɗewa Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa a “kwanaki na ƙarshe” na wannan zamanin marar bin Allah, mutane za su zama “masu-son kansu, . . . marasa-ƙauna irin na tabi’a.” (2 Timothawus 3:1-3) Kalmar Helenanci da aka fassara “ƙauna irin na tabi’a” ta ƙunshi ƙauna da take kasancewa tsakanin iyali. Cikin jituwa da annabcin Littafi Mai Tsarki, irin wannan ƙaunar hakika babu ita a yau.
Jehobah Allah ya bambanta da waɗanda suke wulakanta tsofaffi ƙwarai, yana ɗaukansu da muhimmanci ƙwarai kuma yana kula da waɗanda suka tsufa. Ka yi la’akari da yadda aka nuna wannan cikin Littafi Mai Tsarki.
‘Mai-Yin Shari’a Domin Gwamraye’
Damuwar Jehobah ga tsofaffi ya bayyana cikin Nassosin Ibrananci. Alal misali, a Zabura 68:5, Dauda ya ce da Allah “Mai-yin shari’a ne kuma domin gwamraye,” waɗanda yawancinsu tsofaffi ne.a A wasu fassaran Littafi Mai Tsarki, kalmomin nan “mai-shari’a” an fassara su “mai-kāre,” da kuma “gwarzo.” A bayane yake cewa Jehobah yana kula da gwauraye. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya ce idan aka wulakanta su yakan yi fushi ƙwarai. (Fitowa 22:22-24) Gwauraye, da kuma dukan tsofaffi masu aminci, Allah da kuma bayinsa suna ɗaukansu da muhimmanci. Misalai 16:31 ta furta ra’ayin Jehobah Allah da kuma mutanensa sa’ad da ta ce: “Furfura rawanin daraja ce, idan an iske ta cikin hanyar adalci.”
Saboda haka, ba abin mamaki ba ne da daraja tsofaffi ya kasance ɓangare mai muhimmanci a Dokar da Jehobah ya bai wa Isra’ilawa. An umurci Isra’ila: “Za ka tashi tsaye a gaban mai-furfura, a bada girma ga fuskar dattijo, ka ji tsoron Allahnka: ni ne Ubangiji.” (Leviticus 19:32) Saboda haka, daraja tsofaffi a Isra’ila ta shafi dangantakar mutum da Jehobah Allah. Mutum ba zai iya cewa yana ƙaunar Allah ba idan yana wulakanta tsofaffi.
Kiristoci ba sa ƙarƙashin Dokar Musa. Amma, suna ƙarƙashin “shari’ar Kristi,” da ya shafi halayensu, da ya haɗa da ƙauna da kuma damuwa da iyaye da tsofaffi. (Galatiyawa 6:2; Afisawa 6:1-3; 1 Timothawus 5:1-3) Kiristoci suna ƙauna ne ba domin kawai an umurce su su yi ba, amma domin zuciyarsu ta motsa su su yi haka. “Ku yi ƙaunar junanku daga zuciya mai-gaskiya” in ji manzo Bitrus.—1 Bitrus 1:22.
Almajiri Yaƙub ya ba da ƙarin dalilin kula da tsofaffi. Ya rubuta: “Addini mai-tsarki marar-ɓāci a gaban Allah Ubanmu ke nan, mutum shi ziyarci marayu da gwauraye cikin ƙuncinsu, shi tsare kansa marar-aibi daga duniya.” (Yaƙub 1:27) Abin da Yaƙub ya faɗa yana da muhimmanci. Ya tuna mana yadda waɗannan suke da tamani ga Jehobah.
Saboda haka, ba kawai batun kada a wulakanta tsofaffi ba ne. Maimakon haka, ya kamata mu nuna damuwarmu a gare su ta wajen yin kyawawan ayyuka. (Dubi akwatin nan “Nuna Ƙauna ta Wajen Ayyuka,” a shafi na 6-7.) Yaƙub ya rubuta: “Bangaskiya ba tare da ayyuka matacciya ce.”—Yaƙub 2:26.
Yi Musu Ta’aziyya “Cikin Ƙuncinsu”
Da wani darasi kuma da za mu koya daga kalmomin Yaƙub. Ka lura cewa Yaƙub ya gaya wa Kiristoci su ziyarci gwauraye ‘cikin ƙuncinsu.’ Kalmar Helenanci da aka fassara “ƙunci” tana nufin wahala, takaici domin matsayi da yanayin rayuwarmu. Babu shakka cewa da yawa tsakanin tsofaffi suna fuskantar irin wannan wahala. Wasu sun kaɗaita. Wasu suna baƙin ciki domin kasawa na tsufa. Har waɗanda suke da ƙwazo ma a hidimarsu ga Allah suna iya baƙin ciki. Yi la’akari da John,b wanda ya yi shelar Mulkin Allah cikin aminci na fiye da shekaru arba’in, kuma a ƙarshe ya yi shekaru uku a hidimar cikakken lokaci. Yanzu a shekarunsa na 80, John ya ce wani lokaci yana yin baƙin ciki. Ya ce: “Sau da yawa ina tuna baya kuma in tuna da kurakurai na, kurakurai masu yawa. Sau da yawa ina ce wa kaina da ba yi ba haka.”
Ana iya ƙarfafa irin waɗannan ta wajen sanar da su cewa Jehobah ko da yake kamili ne ba kamilta yake bukata ba. Ko da yake ya san kurakuranmu, Littafi Mai Tsarki ya ce game da shi: “Idan kai, ya Ubangiji, za ka ƙididdiga laifofi, wa za ya tsaya, ya Ubangiji?” (Zabura 130:3) Hakika, Jehobah zuciyarmu yake dubawa ba kurakuranmu ba. Ta yaya muka san wannan?
Sarki Dauda kansa ba baƙo ba ne wajen yin kuskure, amma Allah ya hure shi ya rubuta kalmomin da suke rubuce cikin Zabura 139:1-3: “Ya Ubangiji, kā bincike ni, kā kuwa san ni. Zamana da tashina ka sani, kā fahimci tunanina tun daga nesa. Kā bincike tafarkina da kwanciyata, kā san dukan al’amurana.” A nan kalmar nan “bincike” na nufin “rairaya,” irin wanda manomi yake yi ya fitar da hatsi. Jehobah ya huri Dauda ya tabbatar mana cewa shi ya san yadda zai rairaye kuma ya zaɓi ayyukanmu nagari.
Ubanmu na samaniya mai jinƙai yana nuna kuma yana ƙaunar ayyukanmu na kirki sa’ad da muka kasance da aminci a gare shi. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya ce idan ya mance da ayyukanmu da kuma ƙauna da muka yi masa ya zaman rashin adalci ne a gare shi.—Ibraniyawa 6:10.
“Al’amura na Fari Sun Shuɗe”
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa matsalolin tsufa ba nufin Allah ba ne ga ’yan adam. Sai da iyayenmu, mutane na farko Adamu da Hauwa’u suka yi tawaye wa mahaliccinsu kafin dukan waɗannan matsaloli na tsufa suka zama abin da mutane suke fuskanta. (Farawa 3:17-19; Romawa 5:12) Wannan ba zai ci gaba har abada ba.
Kamar yadda aka faɗa, yawancin mugayen yanayi da muke fuskanta a yau, haɗe da wulakanta tsufaffi, sun ba da tabbacin cewa muna rayuwa a “kwanaki na ƙarshe” na wannan zamani. (2 Timothawus 3:1) Nufin Allah shi ne ya kawar da dukan sakamokon zunubi, haɗe da motsalolin tsufa da kuma mutuwa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Allah] za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin zuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.”—Ru’ya ta Yohanna 21:4.
A sabuwar duniya ta Allah, raɗaɗi da azaba na tsufa za su kasance abubuwa da suka shuɗe. Haka nan kuma wulakanta tsofaffi. (Mikah 4:4) Har waɗanda suka mutu waɗanda Allah ya tuna da su za a tashe su, saboda su ma su sami damar rayuwar har abada a aljana a duniya. (Yohanna 5:28, 29) A wannan lokacin, zai bayyana ƙwarai fiye da dā cewa Jehobah Allah yana kula da tsofaffi da kuma dukan waɗanda suka yi masa biyyaya.
[Hasiya]
a Hakika, wasu gwauraye ba tsofaffi ba ne. Amma Leviticus 22:13 ta nuna cewa Allah yana kula da gwauraye matasa.
b Ba sunansa ba ne na ainihi.
[Box/Hotuna a shafuffuka na 6, 7]
Nuna Ƙauna ta Wajen Ayyuka
A tsakanin Shaidun Jehobah, dattawa na ikilisiya suna ja-gora wajen daraja tsofaffi. Sun ɗauki gargaɗin manzo Bitrus da muhimmanci: “Ku yi kiwon garken Allah wanda ke wurinku.” (1 Bitrus 5:2) Kula da tsofaffi hanya ce ɗaya ta kiwon garken Allah. Amma menene wannan ya ƙunsa?
Wannan yana bukatar haƙuri da ziyarta da kuma taɗin da zai tabbatar da bukatun tsofaffin. Wataƙila suna bukatar a yi musu cefane, shara, ko kuma a kai su tarurruka na Kirista, da kuma karatun Littafi Mai Tsarki da kuma wasu littattafan Kirista, da kuma wasu abubuwa. Duk yadda ya yiwu, a yi tsari mai kyau, kuma a yi aiki da shi.c
To, yaya idan wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa da ya ko ta tsufa ya ko ta faɗa cikin matsala kuma yana ko tana bukatar taimako na kuɗi? Da farko, yana da kyau a duba ko yana da yara ko kuma dangi da za su yi taimako. Wannan zai jitu da abin da ke rubuce cikin 1 Timothawus 5:4: “Amma idan kowacce gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, bari su koya su fara gwada ibada wajen iyalin gida nasu, su sāka ma iyayensu: gama wannan abin karɓa ne a wurin Allah.”
Wataƙila kuma tsohon zai bukaci taimako ya sani ko ya cancanci ya karɓi taimako daga wurin gwamnati. Wataƙila wasu daga ikilisiya za su iya taimako. Idan babu wani cikin waɗannan da zai yi taimako, dattawa za su duba su gani ko wannan mutumin ya cancanci taimako daga ikilisiya. A wasu yanayi, an yi wannan a ikilisiyar farko, domin manzo Bulus ya rubuta wa abokin aikinsa Timothawus: “Kada a rubuta kowa gwauruwa ce in ta kasa shekara sattin, ta kasance matar namiji ɗaya, ana kuwa shaidatta da kyau domin kyawawan ayyukanta; idan ta goye ’ya’ya, idan ta yi garan bāƙi, idan ta wanke ƙafafun tsarkaka, idan ta yi ma ƙuntattu gudunmuwa, idan ta tsare kowane kyakkyawan aiki da naciya.”—1 Timothawus 5:9, 10.
[Hasiya]
c Domin ƙarin bayani, dubi talifin nan “Meeting the Needs of Our Older Ones—A Christian Challenge,” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 1988 ta Turanci.
[Hoto a shafi na 5]
Dorcas ta kula da gwauraye masu bukata.—Ayukan Manzanni 9:36-39