Ku Ƙarfafa Juna
“Waɗanda suka yi mini ta’aziyya [“da suka ƙarfafa ni,” NW ].”—KOLOSSIYAWA 4:11.
1, 2. Duk da haɗarin, me ya sa abokan Bulus suka ziyarce shi a kurkuku?
HAƊARI ne ka yi abokantaka da wanda yake kurkuku—ko da ba domin ya yi wani laifi ba ne aka saka shi a kurkukun. ’Yan yari sai su yi kame kame game da kai suna bin sawunka ƙila kai ma mai laifi ne. Saboda haka, kana bukatar gaba gaɗi ka ji daga wurin abokinka ko kuma ka ziyarce shi a kurkuku.
2 Amma, abin da wasu abokan manzo Bulus suka yi ke nan shekara 1,900 da suka shige. Ba su yi jinkiri su ziyarci Bulus lokacin da yake kurkuku ba kuma suka yi masa ta’aziyya suka ƙarfafa shi a ruhaniya. Su waɗannene abokan nan aminai? Kuma me za mu iya koya daga gaba gaɗinsu, amincinsu, da kuma abokantakarsu?—Misalai 17:17.
Waɗanda Suke Ba da Ƙarfafa
3, 4. (a) Su waɗanne ne abokan Bulus guda biyar, kuma me suka zama a gare shi? (b) Menene “ba da ƙarfafa”?
3 Bari mu koma baya zuwa shekara ta 60 A.Z. Manzo Bulus yana kurkuku a Roma domin tuhumar ƙarya da aka yi masa. (Ayukan Manzanni 24:5; 25:11, 12) Bulus ya ambata Kiristoci biyar da suka tallafa masa: Tikikus, wakilinsa daga gundumar Asiya kuma “abokin bauta cikin Ubangiji”; Unisimus, “ɗan’uwa mai-aminci, ƙaunatace” daga Kolosiya; Aristarkus, mutumin Makidoniya daga Tassaluniki wanda a wani lokaci “abokin sarƙa” ne na Bulus; Markus, ɗan uban Barnaba, abokin wa’azi na ƙasashen waje na Bulus, marubucin Lingila mai sunansa; da kuma Yustus, ɗaya cikin abokin aiki na manzon zuwa “mulkin Allah.” Bulus ya ce game da su biyar: “Mutane waɗanda suka yi mini ta’aziyya [“da suka ƙarfafa ni,” NW ].”—Kolossiyawa 4:7-11.
4 Bulus ya yi magana mai kyau game da taimakon da abokansa aminai suka yi masa. Ya yi amfani da kalmar Helenanci (pa·re·go·riʹa) da aka fassara ‘ba da ƙarfafa,’ wadda a wannan ayar ce kawai take cikin Littafi Mai Tsarki. Kalmar nan tana da ma’ana da yawa da ake amfani da su a mahallin jinya.a Ana iya fassara ta ‘kawar da baƙin ciki, sauƙaƙawa, ta’aziyya, ko kuma samun sauƙi.’ Irin wannan ƙarfafa ce Bulus yake bukata kuma mutane biyar ɗin sun yi haka nan.
Abin da Ya Sa Bulus Yake Bukatar Ƙarfafa
5. Ko da yake shi manzo ne, menene Bulus yake bukata, kuma menene dukanmu ke bukata a wasu lokatai?
5 Wasu za su iya mamakin cewa Bulus wanda shi manzo ne har yana bukatar a ƙarfafa shi. Kuma yana bukatar a ƙarfafa shi. Gaskiya ne cewa Bulus yana da ƙarfafan bangaskiya kuma ya tsira wa wahala da yawa, “buge-buge gaba da misali,” “cikin mutuwa iri iri so nawa,” da wasu azaba kuma. (2 Korinthiyawa 11:23-27) Amma har ila shi bil adama ne, dukan mutane a wani lokaci a rayuwarsu suna bukatar ta’aziyya da kuma ƙarfafa bangaskiyarsu ta wurin samun taimakon wasu. Wannan haka ne a batun Yesu ma. A darensa na ƙarshe, mala’ika ya bayyana masa a Jathsaimani don ya “ƙarfafa shi.”—Luka 22:43.
6, 7. (a) A Roma, su wa suka kunyatar da Bulus, kuma su wa suka ƙarfafa shi? (b) Waɗanne hidimomi ’yan’uwa Kiristoci suka yi wa Bulus a Roma da suka zama abin ‘ƙarfafa’?
6 Bulus shi ma yana bukatar a ƙarfafa shi. Lokacin da ya zo Roma shi fursuna, mutanensa ba su marabce shi ba. Waɗannan Yahudawa ba sa son saƙon Mulkin ma gabaki ɗaya. Bayan da manyan mutanen Yahudawa suka ziyarci Bulus a inda aka tsare shi, labarin Ayukan Manzanni ya ce: “Waɗansu suka gaskata abin da aka faɗi, waɗansu ba su gaskata ba. Sa’anda ba su yi muwafaka da junansu ba, suka tashi.” (Ayukan Manzanni 28:17, 24, 25) Rashin godiyarsu ga alherin Jehovah lallai ya dami Bulus ƙwarai! Yadda ya ji game da wannan batun yana cikin wasiƙar da ya rubuta da farko wa ikilisiyar Roma: “Ina da baƙinciki mai-zafi da ciwo marar-hucewa cikin zuciyata. Gama kamar in so ni da kaina in zama la’annane ga Kristi sabili da ’yan’uwana [Yahudawa], dangina na wajen jiki.” (Romawa 9:2, 3) A Roma har ila, ya sami amintattun abokai, da gaba gaɗinsu da soyayya suka sanyaya masa rai. Sune ’yan’uwansa tabbatattu a ruhaniya.
7 Ta yaya waɗannan ’yan’uwa biyar ɗin suka kasance masu ba da ƙarfafa? Ba su yarda kasancewar Bulus a kurkuku ya sa su ji kunyarsa ba. Maimako, da son rai suka yi wa Bulus tanadi, suna yi masa ayyuka da ba zai iya yin su ba domin yana kurkuku. Alal misali, sun zama ’yan saƙo sun idar da wasiƙun da Bulus ya rubuta da kuma saƙonsa ga ikilisiyoyi da yawa; sun kawo masa labarai masu daɗi game da lafiyar ’yan’uwa a Roma da kuma a wasu wurare. Ƙila sun sayo kayayyakin da yake bukata, su rigar sanyi, takardu, da kuma kayan rubuta. (Afisawa 6:21, 22; 2 Timothawus 4:11-13) Dukan taimakon nan sun ƙarfafa manzon nan da yake kurkuku don shi ma ya zama ‘wanda yake ƙarfafa’ wasu har da dukan ikilisiyoyin.—Romawa 1:11, 12.
Yadda Za Mu Zama Masu Ba da Ƙarfafa
8. Wane darasi za mu iya koya daga yadda Bulus cikin tawali’u ya yarda yana bukatar ‘ƙarfafawa’?
8 Menene za mu koya daga wannan labarin Bulus da abokan aikinsa biyar? Bari mu ɗauki misali ɗaya musamman: Ana bukatar gaba gaɗi da kuma sadaukar da kai a taimaki mutane a lokacin wahala. Ban da haka, muna bukatar tawali’u don mu yarda cewa muna bukatar taimako a lokacin wahala. Ba kawai Bulus ya yarda yana bukatar taimako ba amma kuma ya yi godiya ga taimakon da ya samu ya yaba wa waɗanda suka ba da taimakon. Bai ɗauka cewa taimakon da ake masa ya sa shi ya zama kumami ko kuma abin kunya ne gare shi ba, mu ma bai kamata mu yi haka ba. Idan muka ce ba ma bukatar ƙarfafa lallai mu kamiltattu ne. Ka tuna cewa misalin Yesu ya nuna cewa kamili ma wani lokaci zai bukaci taimako.—Ibraniyawa 5:7.
9, 10. Wane sakamako mai kyau za a iya samu sa’ad da mutum ya yarda yana bukatar taimako, kuma wane tasiri wannan zai kasance da shi wajen wasu cikin iyali da kuma cikin ikilisiya?
9 A kan samu sakamako mai kyau idan waɗanda suke matsayi mai girma suka yarda suna da iyaka kuma cewa suna bukatar taimako daga wasu. (Yaƙub 3:2) Irin amincewar nan tana ƙarfafa dangantaka da ke tsakanin waɗanda suke matsayi mai girma da waɗanda suke ƙarƙashinsu, tana jawo ’yancin magana kuma tana daɗaɗawa. Tawali’un waɗanda suka yi na’am da taimako, darasi ne ga wasu da suke cikin irin wannan yanayin. Yana nuna cewa waɗanda suke ja-gora su ma mutane ne kuma cewa ana iya zuwan wajensu.—Mai-Wa’azi 7:20.
10 Alal misali, zai yi wa yara sauƙi su amince da taimakon iyayensu don warware matsaloli da kuma jaraba idan sun sani cewa iyayensu ma sun fuskanci ƙalubale sa’ad da suke yara. (Kolossiyawa 3:21) Ta haka, yin taɗi tsakanin yaro da iyaye zai zama da sauƙi. Zai kasance da sauƙi a magance matsala ta yin amfani da Nassosi kuma a amince da shawarar. (Afisawa 6:4) Haka ma zai kasance da sauƙi wa waɗanda suke cikin ikilisiya su yi na’am da taimakon dattawa sa’ad da suka fahimci cewa dattawan su ma suna da matsaloli, suna fargaba, kuma suna da abubuwan da suke damunsu. (Romawa 12:3; 1 Bitrus 5:3) Haka zai sa ya zama da sauƙi a yi amfani da gargaɗin Nassi, kuma a ƙarfafa bangaskiya da kyau ta wurin iya magana da juna. Ka tuna, ’yan’uwanmu suna bukatar ƙarfafawa yanzu fiye da dā.—2 Timothawus 3:1.
11. Me ya sa mutane da yawa a yau suke bukatar ‘ƙarfafawa’?
11 Duk inda muke zama, ko mu waye, duk da yawan shekarunmu, a wasu lokatai dukanmu na fuskantar wahala a rayuwa. Haka duniyarmu take a yau. (Ru’ya ta Yohanna 12:12) Irin waɗannan yanayi na jiki ko na tsotsuwar zuciya suna gwada ingancin bangaskiyarmu. Yanayin gwaji zai iya tasowa a wajen aiki, a makaranta, a cikin iyali, ko a cikin ikilisiya ma. Wataƙila sanadin wani ciwo mai tsanani ko kuma fargaban wani abin da ya faru ne dā. Idan kana da abokiyar aure, ko wani dattijo, ko aboki da zai ƙarfafa ka da kalmomi masu daɗi da ayyukan taimako—abar wartsakewa ce ƙwarai! Kamar mai ne da aka shafa a busashen jiki! Saboda haka, idan ka ga wani ɗan’uwanka a irin yanayin nan ka ƙarfafa shi. Ko kuma idan kana da matsala da take maka nauyi ƙwarai, ka biɗi taimakon waɗanda suka inganta a ruhaniya.—Yaƙub 5:14, 15.
Yadda Ikilisiya Za ta Taimaka
12. Menene kowa cikin ikilisiya zai iya yi don ya ƙarfafa ’yan’uwansa?
12 Duka a cikin ikilisiya har da yara ma za su iya ƙarfafa mutane. Abu ɗaya shi ne, idan kana halartan taro kullum kuma kana fitar hidimar fage zai ƙarfafa bangaskiyar wasu ƙwarai. (Ibraniyawa 10:24, 25) Kasancewarka kullum a hidima tabbaci ne cewa ka amince da Jehovah kuma yana nuna cewa a faɗake kake a ruhaniya duk da wahalar da kake jimrewa. (Afisawa 6:18) Wannan kasancewa kullum yana ƙarfafa wasu sosai.—Yaƙub 2:18.
13. Me ya sa wasu suke raunana, kuma me za a iya yi don a taimake su?
13 A wasu lokatai, matsi na rayuwa ko kuma wasu matsaloli suna sa wasu su rage himma ko kuma su daina fitar hidimar fage gabaki ɗaya. (Markus 4:18, 19) Ƙila ba za mu ga waɗanda suka raunana a taron ikilisiya ba. Amma, mai yiwuwa ne suna ƙaunar Allah har ila a zuciyarsu. Me za a iya yi don a ƙarfafa bangaskiyarsu? Dattawa za su iya taimakawa ta wurin yi musu ziyara. (Ayukan Manzanni 20:35) Za a iya ce wasu cikin ikilisiya su taimaka su ma. Irin wannan ziyara takan zama daidai abin da ake bukatarsa ne don a maido da waɗannan da suka raunana a bangaskiya.
14, 15. Wane gargaɗi Bulus ya bayar game da ƙarfafa wasu? Ka ba da misalin wata ikilisiya da suka yi amfani da gargaɗinsa.
14 Littafi Mai Tsarki ya yi mana kashedi mu “ƙarfafa masu-raunanan zukata, [mu] tokare marasa-ƙarfi.” (1 Tassalunikawa 5:14) Wataƙila “masu-raunanan zukata” sun ga cewa ba su da gaba gaɗi da za su ci gaba ba kuma suna jin suna bukatar taimako domin cikas da suke fuskanta. Za ka iya taimakawa? An fassara furcin nan, a “tokare marasa-ƙarfi” yana nufin “riƙe da ƙarfi” ko kuma “manne wa” marasa ƙarfi. Jehovah yana so kuma yana ƙaunar dukan tumakinsa. Yana daraja su sosai, kuma ba ya son wani cikinsu ya bijire. Za ka iya taimakon ikilisiya ta “manne wa” marasa ƙarfi har sai sun yi ƙarfi?—Ibraniyawa 2:1.
15 Wani dattijo ya ziyarci wasu ma’aurata da suka raunana na shekaru shida. Dattijon ya rubuta: “Alheri da kuma kulawar dukan ikilisiyar ta taɓa su sosai har suka motsa su dawo cikin garken.” Yaya ’yar’uwa da dā ta raunana ta ji game da ziyarar da waɗanda suke cikin iklisiyar suka yi mata? Yanzu ta ce: “Abin da ya taimake mu shi ne cewa babu wani cikin ’yan’uwan da suka ziyarce mu ko waɗanda suka bi su da ya hukunta mu ko kuma ya soke mu. Amma sun fahimce mu kuma sun ƙarfafa mu ta wurin Nassi.”
16. Waye yake a shirye kullum ya ba da taimako ga waɗanda suke bukatar ƙarfafawa?
16 Hakika, Kirista sahihi zai yi farin ciki ya zama mai ƙarfafa wasu. Kuma yadda yanayi yake canjawa a rayuwarmu, mu ma za mu iya samun ƙarfafa daga ’yan’uwanmu. Amma, mai yiwuwa ne cewa a lokacin bukata, ba za a sami mutanen da za su ba da taimako ba. Duk da haka, akwai wani Tushen samun ƙarfi da koyaushe za a same shi, wanda a shirye yake ya ba da taimako—Jehovah Allah ne.—Zabura 27:10.
Jehovah—Mafificin Tushen Ƙarfi
17, 18. A waɗanne hanyoyi ne Jehovah ya ƙarfafa Ɗansa, Yesu Kristi?
17 Lokacin da aka kafa shi a kan gungume, Yesu ya yi kuka: “Uba, a cikin hannuwanka ni ke bada ruhuna.” (Luka 23:46) Sai ya mutu. Sa’o’i kafin lokacin, an tsare shi kuma abokansa na kud da kud suka yashe shi suka gudu. (Matta 26:56) An bar Yesu shi kaɗai da wani Tushen ƙarfi—Ubansa na samaniya. Duk da haka, dogararsa ga Jehovah ba banza ba ne. An albarkaci amincin Yesu ga Ubansa ta yadda Jehovah kansa ya tallafa masa.—Zabura 18:25; Ibraniyawa 7:26.
18 Duk cikin hidimar Yesu a duniya, Jehovah ya yi wa Ɗansa tanadin abin da yake bukata don ya riƙe aminci har lokacin da ya ja numfashinsa na ƙarshe. Alal misali, sa’in da aka yi wa Yesu baftisma, alamar soma hidimarsa, ya ji muryar Ubansa da yake tabbatar da amincewarsa da ƙaunar Uban gare shi. Lokacin da Yesu yake bukatar tallafawa, Jehovah ya aiki mala’iku su ƙarfafa shi. Sa’ad da Yesu ya fuskanci gwajinsa mafi tsanani a ƙarshen rayuwarsa a duniya, Jehovah ya ji addu’o’insa da roƙe roƙe. Hakika dukan wannan abin ƙarfafa ne wa Yesu.—Markus 1:11, 13; Luka 22:43.
19, 20. Ta yaya za mu tabbata cewa Jehovah zai ƙarfafa mu a lokacin bukata?
19 Jehovah yana son ya zama ainihin Tushen ƙarfinmu. (2 Labarbaru 16:9) Tushe na gaske na dukan ƙarfi da iko, abin ƙarfafa ne gare mu a lokacin bukata. (Ishaya 40:26) Yaƙi, talauci, ciwo, mutuwa, ko ma ajizancinmu suna iya matsa mana ƙwarai. Sa’ad da gwaji a rayuwa ya zama kamar ‘abokin gāba mai ƙarfi’ Jehovah yakan zama ƙarfinmu da kuma iko. (Zabura 18:17; Fitowa 15:2) Yana da taimako mai iko dominmu—ruhunsa mai tsarki. Ta wurin ruhunsa, Jehovah yana ba da “ƙarfi ga masu-kasala” don su iya ‘tashi sama da fukafukai kamar gaggafa.’—Ishaya 40:29, 31.
20 Ruhun Allah ne iko mafi ƙarfi cikin sararin samaniya. Bulus ya ce: “Na iya yin abu duka a cikin wannan da ya ke ƙarfafata.” Hakika, Ubanmu na samaniya zai iya ba mu “mafificin girman iko” don mu iya jimre wa dukan matsaloli har sai ya “sabonta dukan abu” cikin Aljannar da ya yi alkawarinsa wadda yanzu ta yi kusa.—Filibbiyawa 4:13; 2 Korinthiyawa 4:7; Ru’ya ta Yohanna 21:4, 5.
[Hasiya]
a Ƙamus nan Vine’s Complete Expository Dictionary of Old and New Testament Words, na W. E. Vine ya ce: “Ma’anar kalmar nan [pa·re·go·riʹa] a zaman aikatau tana nufin maganin da ke kawar da ƙaiƙayi.”
Ka Tuna?
• Yaya ’yan’uwan da suke a Roma suka zama abin ƙarfafa ga Bulus?
• A waɗanne hanyoyi za mu iya zama masu ba da ƙarfafa cikin ikilisiya?
• Ta yaya yake cewa Jehovah ne mafificin Tushen ƙarfinmu?
[Hoto a shafi na 27]
’Yan’uwa suka zama abin ƙarfafa ga Bulus ta wurin tallafa masa, ƙarfafa shi, kuma ta yi masa wasu hidimomi
[Hoto a shafi na 29]
Dattawa suna ja-gora a ƙarfafa garken