Kana Samun Ƙarfafa Daga Kalmar Allah?
SA’AD da ka fuskanci ƙalubale, yaya kake bi da shi? Lokacin da Yesu ya fuskanci gwaji daga Shaiɗan, ya tuna da nassi da ya dace kuma wannan ya taimake shi. (Matta 4:1-11) Haka ma yake, sa’ad da Sarki Dauda ya fuskanci gwaji, Kalmar Allah ta ƙarfafa shi. Ya ce: “A cikin yawan wuswasi da ke cikina ta’aziyyanka suna ji ma raina daɗi.”—Zabura 94:19.
Hakan nan kuma, idan muka tuna da nassi da muka fi so zai iya yi mana ta’aziyya kuma ya ƙarfafa mu sa’ad da muka fuskanci ƙalubale. Alal misali, Rex, shekararsa 89, yana hidima ta cikakken lokaci tun shekara ta 1931. Duk da haka ya ce: “Sau da yawa nakan ji ban isa a ba ni wani aiki na musamman cikin hidima ba.” Yaya ya bi da wannan? Na tuna da nassi da na fi so, Misalai 3:5 da ta ce: ‘Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi.” Sa’ad da na tuna kuma na yi amfani da wannan nassi yana taimakona na yi aikina da kyau.”
Matasa ma suna amfana ta tuna da nassi da suka fi so. Jack, ɗan shekara shida ya ce nassi da ya fi so shi ne Matta 24:14. Wannan nassi yana motsa shi ya je wa’azi da iyayensa. Ya ce: “Ina son zuwan wa’azi kowacce Asabar da mamata, da babana, da yata.”
Kai ma a wani lokaci kana fuskantar ƙalubalen bangaskiyarka kamar yadda Yesu ya fuskanta ne? Ƙila Filibbiyawa 4:13 za ta zama ɗaya cikin nassi da ka fi so. Kana ji kamar Sarki Dauda sa’ad da yake wahalar “wuswasi” ne? Sai ka tuna da nassi da ke Filibbiyawa 4:6, 7 da zai iya taimakonka. Kana ji ne wani lokaci cewa bautarka ba ta da amfani ga Allah? Idan ka tuna da 1 Korinthiyawa 15:58 zai ƙarfafa ka.
Ta wurin haddace nassosin da suka dace, za mu yarda Kalmar Allah ta kasance da ƙarfi gare mu. (Ibraniyawa 4:12) Irin waɗannan nassosi masu kyau suna ba mu ƙarfi da kuma ta’aziyya. —Romawa 15:4.