Ka Dogara Ga Jehovah Ƙwarai A Lokacin Wahala
“Allah mafakarmu ne da ƙarfinmu, taimako ne na kurkusa cikin wahala.”—ZABURA 46:1.
1, 2. (a) Wane misali ya nuna bai isa ba kawai mu ce mun dogara ga Allah? (b) Me ya sa muna da abin da za mu yi fiye da mu ce kawai mun dogara ga Jehovah?
YANA da sauƙi mu ce mun dogara ga Allah. Wani abu ne kuma mu nuna hakan ta ayyukanmu. Alal misali, furcin nan “Mun Dogara ga Allah” ya bayyana da daɗewa a kan kuɗin ƙasar Amirka.a A shekara ta 1956, Majalisa ta Amirka ta ba da umurni cewa furcin nan “Mun Dogara ga Allah” ya zama ƙa’idar ja-gora ta ƙasar Amirka. Amma abin mamaki ne cewa mutane da yawa—ba a wannan ƙasar kaɗai ba ma amma a duk cikin duniya—suna dogara sosai ga kuɗi da arzikin abin duniya fiye da yadda suke da Allah.—Luka 12:16-21.
2 Da yake mu Kiristoci na gaskiya ne, muna da abin da za mu yi fiye da mu ce kawai mun dogara ga Jehovah. Yadda “bangaskiya ba tare da ayyuka matacciya ce,” haka ma cewa kawai mun dogara ga Allah ba shi da amfani idan ba mu nuna ta ayyukanmu ba. (Yaƙub 2:26) A cikin talifi na baya, mun koyi cewa sa’ad da muka yi addu’a gare shi, sa’ad da muka nemi ja-gora daga Kalmarsa, kuma sa’ad da muka nemi ja-gora ta ƙungiyarsa, muna nuna mun dogara ga Jehovah ne. Yanzu bari mu bincika yadda za mu yi amfani da waɗannan matakai uku a lokacin wahala.
Sa’ad da Aka Yi Rashin Aiki ko Kuma Kuɗaɗe Sun Kasa
3. Waɗanne wahalar tattalin arziki bayin Jehovah ke fuskanta a waɗannan “miyagun zamanu,” kuma ta yaya muka sani Allah a shirye yake ya taimake mu?
3 A cikin waɗannan “miyagun zamanu” mu Kiristoci muna fuskantar matsi na tattalin arziki yadda sauran mutane ke fuskanta. (2 Timothawus 3:1) Saboda haka, farat ɗaya, sai mu ga mun yi rashin aiki. Ko kuma a ce mu ƙara sa’o’in aiki amma babu ƙarin kuɗi. A cikin irin yanayin nan za mu iske shi da wuya ‘mu yi wa waɗanda ke na iyalinmu tanadi.’ (1 Timothawus 5:8) Allah Mai Iko Duka a shirye yake ne ya taimake mu a irin lokatan nan? Hakika! Alhali, Jehovah ba ya kāre mu daga dukan wahalar rayuwa cikin wannan zamani. Idan mun dogara gare shi, kalmomin Zabura 46:1 sa zama gaskiya a gare mu: “Allah mafakanmu ne da ƙarfinmu, taimako ne na kurkusa cikin wahala.” To, ta yaya za mu nuna mun dogara ga Jehovah ƙwarai a lokacin wahalar kuɗi?
4. Sa’ad da muke fuskantar matsalar kuɗi, me za mu yi addu’arta, kuma yaya Jehovah ke ɗaukan irin addu’o’in nan?
4 Hanya ɗaya ta nuna mun dogara ga Jehovah ita ce ta yin addu’a gare shi. Amma addu’ar me za mu yi? To, idan muna fuskantar matsalar kuɗi, za mu bukaci hikima yanzu fiye da dā. Sai ka yi addu’a ka same ta! Kalmar Jehovah ta ba mu tabbaci: “Idan kowane a cikinku ya rasa hikima, bari shi yi roƙo ga Allah, wanda ya ke bayar ga kowa a yalwace, ba ya tsautawa kuma; za a kuwa ba shi.” (Yaƙub 1:5) E, ka roƙi hikima daga wurin Jehovah—watau iya amfani da sani, fahimi, basira, da kyau—domin ka tsai da shawarwari kuma ka yi zaɓe masu kyau. Ubanmu mai ƙauna na samaniya ya tabbatar da mu cewa zai saurari irin addu’o’in nan. A shirye yake ya ƙarfafa waɗanda suka dogara gare shi da dukan zuciyarsu.—Zabura 65:2; Misalai 3:5, 6.
5, 6. (a) Me ya sa za mu nemi taimako daga Kalmar Allah don mu jure da matsi na tattalin arziki? (b) Me za mu iya yi don mu iya rage alhini sa’ad da muka yi rashin aiki?
5 Neman ja-gorar Kalmar Allah wata hanya ce ta nuna mun dogara ga Jehovah. Tunasarwarsa da ke cikin Littafi Mai Tsarki sun zama “tabbatattu ƙwarai.” (Zabura 93:5) Ko da yake an gama rubutun tun shekaru 1,900 da suka shige, huraren littafin nan na ɗauke da tabbatattun shawarwari da basira masu kyau da sa taimake mu mu jimre da matsaloli na tattalin arziki da kyau. Ka bincika wasu misalai na hikimar Littafi Mai Tsarki.
6 Da daɗewa Sarki Sulemanu mai hikima ya lura: “Barcin mutum ma’aikaci da daɗi ne, ko ya ci kaɗan, ko dayawa; amma koshin mai-arziki ba za ya bar shi ya yi barci ba.” (Mai-Wa’azi 5:12) Muna bukatar lokaci da kuma kuɗi mu yi gyara, mu tsabtace, mu adana, kuma mu kāre mallakarmu. Saboda haka, idan muka yi rashin aiki, za mu iya amfani da zarafi mu sake bincika yayin rayuwarmu, mu yi ƙoƙarin sanin abubuwan da muke bukata daɗai da waɗanda ba ma bukata. Don mu rage alhini, zai yi kyau mu yi wasu canje-canje. Alal misali, zai yiwu mu sauƙaƙa rayuwarmu ƙila ta ƙaura zuwa ƙaramin gida ko rage abubuwan mallaka da ba ma bukata?—Matta 6:22.
7, 8. (a) Ta yaya Yesu ya nuna ya san cewa ’yan Adam ajizai suna da halin damuwa game da abin duniya? (Duba hasiya.) (b) Wace shawara ta hikima Yesu ya bayar game da yadda za a guje wa yawan alhini?
7 A cikin Huɗuba ta Bisa Dutse, Yesu ya yi gargaɗi: “Kada ku yi alhini saboda ranku, abin da za ku ci, ko kuwa abin da za ku sha; ko saboda jikinku, abin da za ku yafa.”b (Matta 6:25) Yesu ya sani cewa mutane ajizai dama suna damuwa da samun abubuwan biyan bukata. Amma, ta yaya za mu iya daina yin “alhini” game da irin waɗannan abubuwa? “Ku fara biɗan mulkin” in ji Yesu. Duk da irin matsalolin da muke fuskanta, dole mu ci gaba da bauta wa Jehovah abu na farko a rayuwarmu. Idan muka yi haka, Ubanmu na samaniya zai “ƙara” mana dukan abubuwan yau da kullum da muke bukata. A wata sassa, zai sa mu ci gaba da samun na ci da sha.—Matta 6:33.
8 Yesu ya daɗa ba da shawara: “Kada fa ku yi alhini a kan gobe: gama za ya yi alhini don kansa.” (Matta 6:34) Ba hikima ba ce mu damu ainun game da abin da ƙila zai faru gobe. Wani manazarci ya lura: “Tsoron da muke ji game da nan gaba da ƙyar ya yi daidai da ainihin batun.” Ta bin shawarar Littafi Mai Tsarki na mu sa abubuwa masu muhimmanci a rayuwa kuma mu yi rayuwa ta kowacce rana yadda take na taimakonmu mu guje wa yawan alhini.—1 Bitrus 5:6, 7.
9. Sa’ad da muke fuskantar matsalar kuɗi, waɗanne taimako za mu samu a littattafan “bawan nan mai-aminci, mai-hikima”?
9 Sa’ad da muke fuskantar wahalar kuɗi za mu iya nuna kuma cewa mun dogara ga Jehovah ta wurin karanta littattafan “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” domin taimako. (Matta 24:45) A wasu lokatai, jaridar Awake! ta fito da talifofi da suke ɗauke da shawarwari na yadda za a bi da matsalar tattalin arziki. Talifin nan [Out of a Job—What Are the Solutions?] “Rashin Aiki—Menene Maganinsa?” a fitar 8 ga Agusta, 1991, jaridar ta tsara tafarki takwas da sun taimaka wa mutane da yawa su daidaita a batun matsalar kuɗi da kuma jiye-jiyensu sa’ad da suka yi rashin aiki.c Hakika dole a daidaita irin tafarkin nan da muhimmancin kuɗi yadda ya dace. An tattauna a cikin talifin nan [Something More Vital Than Money] “Abin da Ya Fi Kuɗi Muhimmanci,” har ila cikin jaridar.—Mai-Wa’azi 7:12.
Sa’ad da Muke Wahala Domin Rashin Lafiya
10. Ta yaya misalin Sarki Dauda ya nuna cewa daidai ne mu dogara ga Jehovah sa’ad da muke rashin lafiya mai-tsanani?
10 Daidai ne mu dogara ga Jehovah sa’ad da muke rashin lafiya mai tsanani? Babu shakka! Jehovah yana juyayin marasa lafiya tsakanin mutanensa. Ban da haka, a shirye yake ya yi taimako. Ka yi la’akari da misalin Sarki Dauda. Ƙila yana rashin lafiya mai tsanani lokacin da ya rubuta yadda Allah yake bi da adali da ke rashin lafiya. Ya ce: “Ubangiji za ya toƙara shi a bisa shimfiɗarsa ta rashin lafiya: kana gyarta masa shimfiɗa cikin cutarsa.” (Zabura 41:1, 3, 7, 8) Dogarar Dauda ga Allah ta kasance da ƙarfi sosai, daga baya sarkin ya sami sauƙin ciwonsa. Ta yaya za mu nuna mun dogara ga Allah sa’ad da muke wahalar rashin lafiya?
11. Sa’ad da muke rashin lafiya, me za mu roƙa wurin Ubanmu na samaniya?
11 Sa’ad da muke rashin lafiya, hanya ɗaya da za mu nuna mun dogara ga Jehovah ita ce ta roƙonsa don ya taimake mu mu jimre. Muna iya roƙonsa ya taimake mu mu yi amfani da “sahihiyar hikima” domin mu sami sauƙi da zai yi daidai da yanayinmu. (Misalai 3:21) Muna iya roƙonsa ma ya taimake mu mu yi haƙuri kuma mu jimre da rashin lafiya. Fiye da kome, za mu so mu roƙi Jehovah ya kiyaye mu, ya ba mu ƙarfi mu kasance da aminci gare shi kuma kada mu yi rashin aminci ko da me ya faru. (Filibbiyawa 4:13) Riƙe amincinmu ga Allah ma ya fi muhimmanci da cetar da ranmu na yanzu. Idan muka kasance da aminci, Mai Sakawa mai girma zai ba mu kamiltaccen rai da lafiya har abada.—Ibraniyawa 11:6.
12. Waɗanne ƙa’idodi na Nassi za su iya taimakonmu mu tsai da shawara mai kyau game da magani?
12 Dogararmu ga Jehovah ma na motsa mu mu bincika Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki domin ja-gora mai kyau. Ƙa’idodin da ke cikin Nassosi suna iya taimakonmu mu tsai da shawarwari masu kyau game da magani. Alal misali, da sanin Littafi Mai Tsarki ya haramta “sihiri,” za mu guje wata hanyar sanin wani ciwo da ta shafi sihiri. (Galatiyawa 5:19-21; Kubawar Shari’a 18:10-12) Ga wani misali na tabbatacciyar hikima ta Littafi Mai Tsarki: “Marar-wayo yana gaskata kowacce magana: amma mai-hankali ya kan lura da al’amuransa da kyau.” (Misalai 14:15) Saboda haka, sa’ad da muke tunanin jinya, za mu yi hikima mu nemi tabbataccen bayani maimakon “gaskata kowacce magana.” Irin wannan “hankali” zai taimake mu mu bincika zaɓenmu sosai kuma mu tsai da shawara mai kyau.—Titus 2:12.
13, 14. (a) A wace hanya ce za mu iya nuna dogararmu ga Jehovah, kuma ta yaya jaridun Hasumiyar Tsaro da kuma Awake!? suka taimaka a batun nan? (b) Wace shawara ce aka bayar cikin Awake! fitar 22 ga Janairu, 2001 game da ciwo masu tsanani?
13 Za mu kuma nuna dogararmu ga Jehovah ta bincika littattafan bawa mai aminci. A wasu lokaci, jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake! sun fito da talifofi dabam dabam a kan matsalolin rashin lafiya da cututtuka.d Wasu lokatai, sun fito da talifofi game da mutane da suka yi nasara a jimre da cututtuka dabam dabam da kuma naƙasa. Ban da haka, wasu talifofi sun ba da shawarwari na Nassi a kan yadda za a bi da matsalolin rashin lafiya masu tsanani.
14 Alal misali, fitar Awake! na 22 ga Janairu, 2001 tana ɗauke da talifofi a kan [Comfort for the Sick] “Ta’aziyya ga Masu Ciwo.” Talifofin sun gabatar da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da kuma bayani da aka samu daga ganawa da mutane da suke ciwon da ya raunana su na shekaru da yawa. Talifin nan [Living Successfully With Your Ailment—How?] “Ta Yaya Za Ka Yi Nasara a Rayuwa da Ciwonka?” ya ba da wannan shawara: Ka koya game da ciwonka yadda ya yiwu. (Misalai 24:5) Ka kafa muƙasudai, har da na taimakon wasu, amma ka san cewa mai yiwuwa ba za ka iya cim ma muƙasudanka yadda wasu suka cim ma nasu ba. (Ayukan Manzanni 20:35; Galatiyawa 6:4) Ka guje ware kanka. (Misalai 18:1) Sa’ad da wasu suka ziyarce ka ka sa su yi farin ciki. (Misalai 17:22) Fiye da kome, ka riƙe gami na kurkusa da Jehovah da kuma ikilisiyar. (Nahum 1:7; Romawa 1:11, 12) Ba ma farin ciki ne game da tabbatacciyar ja-gorar da Jehovah ya tanadar ta wurin ƙungiyarsa?
Sa’ad da Raunana ta Jiki ta Nace
15. Ta yaya manzo Bulus ya yi nasara a yaƙinsa da jiki ajizi kuma wane tabbaci muke da shi?
15 “Cikin jikina ba wani abin kirki ke zaune ba,” in ji manzo Bulus. (Romawa 7:18) Bulus ya sani daga abin da ya faru masa yadda yake da wuya a yi kokawa da sha’awoyi da raunana ta jiki ajizi. Amma Bulus ya tabbata zai yi nasara. (1 Korinthiyawa 9:26, 27) Ta yaya? Ta wurin dogara ƙwarai ga Jehovah. Shi ya sa Bulus ya ce: “Kaitona, ga ni mutum, abin tausayi! wanene za ya tsamo ni daga cikin jikin nan na mutuwa? Na gode ma Allah ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.” (Romawa 7:24, 25) Mu kuma fa? Mu ma muna yaƙi da raunanan jiki. Yayin da muke kokawa mu bi da irin wannan raunana, yana da sauƙi mu yi rashin gaba gaɗi, mu ce ba za mu taɓa yin nasara ba. Amma Jehovah zai taimake mu idan kamar Bulus mun dogara gare shi ba ga namu ƙarfi ba.
16. Sa’ad da raunana ta jiki ta ci gaba, me za mu yi addu’arsa, kuma me ya kamata mu yi idan muka kasa?
16 Idan raunana ta jiki ta ci gaba, za mu iya nuna mun dogara ga Jehovah ta wurin roƙonsa cikin addu’a. Muna bukatar mu biɗa, mu kuma roƙi, Jehovah domin taimakon ruhunsa mai tsarki. (Luka 11:9-13) Za mu iya biɗi musamman kamewa, wadda ɗaya ce cikin ’yar ruhun Allah. (Galatiyawa 5:22, 23) Me ya kamata mu yi idan muka kasa a wani lokaci? Kada mu fid da rai, ko yaya take. Kada ka taɓa gajiya a yin addu’a ga Allahnmu mai jinƙai, muna neman gafararsa da kuma taimako. Jehovah ba zai ƙi da ‘karyayyar zuciya mai tuba’ wadda take damuwa game da wani laifi ba. (Zabura 51:17) Idan muka roƙe shi da sahihiyar zuciya, mai tuba, Jehovah zai taimake mu mu tsayayya wa jaraba.—Filibbiyawa 4:6, 7.
17. (a) Me ya sa abin taimako ne mu yi tunanin yadda Jehovah yake ji game da wata kasawa da muke kokawa da ita? (b) Waɗanne nassosi za mu iya haddacewa idan muna kokawar mu kame fushinmu? mu kame harshenmu? kuma mu ƙi sha’awar mugun nishaɗi?
17 Za mu kuma nuna mun dogara ga Jehovah ta bincika Kalmarsa don taimako. Yin tunani game da yadda Jehovah yake ji game da al’amarin zai ƙarfafa sha’awarmu mu faranta masa rai. Ta haka, za mu soma ji yadda yake ji, muna ƙin abin da ya ƙi. (Zabura 97:10) Wasu sun ga ya fi musu sauƙi su haddace ayoyin Littafi Mai Tsarki da suke game da wasu kasawa da suke kokawar cim ma. Muna kokawar mu sha kan saurin fushi ne? Sai mu haddace ayoyi irin su Misalai 14:17 da kuma Afisawa 4:31. Muna iske shi da wuya mu tsare harshenmu ne? Muna iya haddace ayoyi kamar Misalai 12:18 da kuma Afisawa 4:29. Muna da son wani mugun nishaɗi ne? Muna iya tuna da ayoyi kamar su Afisawa 5:3 da kuma Kolossiyawa 3:5.
18. Me ya sa ba za mu yarda kunya ta hana mu neman taimako daga wurin dattawa mu sha kan kasawarmu ba?
18 Neman taimako ta wajen dattawa da ruhu ya naɗa su a ikilisiya muna nuna mun dogara ga Jehovah. (Ayukan Manzanni 20:28) Ballantana ma, waɗannan “kyauta ga mutane” tanadi ne daga wurin Jehovah ta wurin Kristi su kāre kuma kula da tumakinsa. (Afisawa 4:7, 8, 11-14) Hakika ba zai yi sauƙi ba mu biɗi taimako don bi da kasawa. Wataƙila za mu ji kunya, muna tsoron cewa dattawan ba za su amince da mu ba. Waɗannan mutane da suka ƙware a ruhaniya za su daraja mu domin gaba gaɗi da muke da shi na biɗan taimako. Ƙari ga haka, dattawan suna ƙoƙari su bi halayen Jehovah a yin sha’ani da garken. Ta’aziyyar da suke bayarwa, gargaɗi, da koyarwa daga Kalmar Allah na iya zama abin da muke bukata don mu sha kan kasawarmu.—Yaƙub 5:14-16.
19. (a) Wace hanya ce Shaiɗan yake nema ya yi amfani da banzanci na wannan rayuwa? (b) Mecece dogara ta ƙunsa, kuma me ya kamata mu ƙudura aniyar yi?
19 Kada ka manta Shaiɗan ya san zarafinsa kaɗan ne. (Ru’ya ta Yohanna 12:12) Yana son ya yi amfani da banzancin rayuwar wannan duniya ya raunana mu mu yi suwu. Bari mu kasance da cikakken gaba gaɗi a abin da aka furta a Romawa 8:35-39: “Wa za ya raba mu da ƙaunar Kristi? ko ƙunci, ko raɗaɗi, ko tsanani, ko yunwa, ko huntanci, ko hatsari, ko takobi? . . . Labudda, cikin dukan waɗannan al’amura mun fi gaban masu-nasara a wurin wanda ya ƙaunace mu. Gama na kawar da shakka, ba mutuwa, ba rai, ba mala’iku, ba sarautai, ba al’amuran yanzu, ba al’amura na zuwa, ba ikoki, ba tsawo, ba zurfi, ba kuwa wani halittaccen abu, da za ya iya raba mu da ƙaunar Allah, wadda ke cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.” Lallai furci ne na dogara ga Jehovah! Amma irin wannan dogarar ba tsotsuwar zuciya ba ce kawai. Maimako, dogara ce da ta ƙunshi shawarwari masu kyau da muke yi a rayuwa. Bari mu ƙudura aniya mu dogara ga Jehovah ƙwarai a lokacin wahala.
[Hasiya]
a A wata wasiƙa zuwa ga Maƙerar Kuɗi na Amirka, mai kwanan wata 20 ga Nuwamba, 1861 da Sakataren Ma’aji, Salmon P. Chase ya rubuta: “Babu wata al’umma da za ta yi ƙarfi idan ba tare da ikon Allah ba, ko kuma a ce bai toƙara mata ba. Ya kamata a rubuta dogarar mutanenmu a kan kuɗaɗen ƙasarmu.” Saboda haka, ƙa’idar ja-gorar nan “Mun Dogara ga Allah” ta bayyana da farko a shekara ta 1864 a kan kuɗin ƙasar Amirka.
b Alhini da aka kwatanta a nan, an ce “damuwa da tsoro da ke hana farin ciki a rayuwa” ne. Wasu fassara suka ce “kada ku yi alhini” ko kuma “kada ku damu.” Amma irin juyin nan ‘kada ku yi alhini’ ko kuma ‘kada ku damu’ na nuna cewa kada ma a soma yin alhinin ko damuwar. Amma wata majiya ta ce: “Aikatau na Helenanci mai nuna sa’in da ake ciki, yana ba da umurnin da ke nuna cewa a daina wasu ayyukan da aka soma.”
c Ga tafarki takwas ɗin: (1) Kada ka yi fargaba; (2) ka kasance da ra’ayi mai kyau; (3) ka yarda ka koyi sabon aiki; (4) ka yi rayuwa daidai da aljihunka—ba tare da ƙyashin na wani ba; (5) ka mai da hankali da cin bashi; (6) ka sa iyalinka su kasance da haɗin kai; (7) ka riƙe mutuncinka; (8) ka tsara yadda za ku kashe kuɗi.
d Waɗannan jaridu masu tushe daga Littafi Mai Tsarki ba sa yaba wa ko kuma gabatar da wani magani musamman ba, sun sani cewa wannan zaɓen mutum ne. Maimako, talifofin da ke tattauna wasu cututtuka ainihi domin a sanar da masu karatu ne yadda cututtukan suke a yanzu.
Ka Tuna?
• Sa’ad da muke fuskantar matsalolin tattalin arziki, a waɗanne hanyoyi za mu nuna mun dogara ga Jehovah?
• Ta yaya za mu nuna mun dogara ga Allah sa’ad da muke rashin lafiya?
• Sa’ad da raunana ta jiki ta ci gaba, ta yaya za mu nuna da gaske cewa mun dogara ga Jehovah?
[Hoto a shafi na 27]
Idan muka yi rashin aiki zai yi kyau mu sake bincika yayin rayuwarmu
[Hoto a shafi na 28]
Labarin Loida ya nuna yadda dogara ga Jehovah ke taimake mutum yin jimiri. (Duba fitar “Awake!” 8 ga Mayu, 2000, Turanci)
[Hoto a shafi na 30]
Ba ma bukata mu ji kunyar neman taimako don mu sha kan kasawarmu ba