Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 9/1 pp. 20-25
  • Ka Sa Jehovah Ya Zama Madogararka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Sa Jehovah Ya Zama Madogararka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sha Kan Tangarɗar da ke Hana Dogara ga Jehovah
  • Me Ya Sa Jehovah Ya Ƙyale Wahala?
  • Abin da Yake Nufi a Dogara ga Jehovah
  • Me Ya Sa Allah Ya Kyale Wahala?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Me Ya Sa Muke Shan Wahala Sosai?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Abin Da Ya Sa Dukan Wahala Za Ta Ƙare Ba Da Daɗewa Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Me Ya Sa Akwai Mugunta da Wahala a Ko’ina?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 9/1 pp. 20-25

Ka Sa Jehovah Ya Zama Madogararka

“Kai ne begena, ya Ubangiji Yahweh: kai ne madogarata tun ina yaro.”—ZABURA 71:5.

1. Wane ƙalubale ya fuskanci Dauda, yaro mai kiwo?

MUTUMIN yana da tsayi fiye da kafa tara. Ba abin mamaki ba ne da sojojin Isra’ila suka ji tsoron fuskantarsa! Cikin makonni da yawa, safe da yamma, Goliath, katon nan Bafilisti yana tsokanar rundunar Isra’ila, yana yi musu ba’a su kawo wani mayaƙi da ya isa ya yi yaƙi da shi. Daga baya, wani ƙaramin matashi, ba soja ba ne ya amsa ba’ar. Dauda, yaro mai kiwo, idan aka gwada shi da abokin gābansa, shi ɗan ƙarami ne. Hakika, nauyin makaman yaƙi na Goliath ma sun ɗara nauyinsa! Duk da haka, matashin ya fuskanci katon kuma ya zama sanannen misalin gaba gaɗi.—1 Samu’ila 17:1-51.

2, 3. (a) Me ya sa Dauda ya iya fuskantar Goliath da gaba gaɗi? (b) Waɗanne matakai biyu za mu tattauna domin mu sa Jehovah ya zama madogararmu?

2 Me ya sa Dauda ya yi irin gaba gaɗin nan? Ka yi la’akari da wasu kalmomi da Dauda ya rubuta bayan wasu shekaru: “Kai ne begena, ya Ubangiji Yahweh: kai ne madogarata tun ina yaro.” (Zabura 71:5) Hakika, tun yana matashi, Dauda ya dogara ga Jehovah ƙwarai. Ya fuskanci Goliath yana cewa: “Kai kana zuwa wurina da takobi, da māshi, da kunkeli: amma ni na zo wurinka cikin sunan Ubangiji mai runduna, Allah na rundunan yaƙi na Isra’ila wanda ka zarge.” (1 Samu’ila 17:45) Ko da yake Goliath ya dogara ga yawan ƙarfinsa da makamansa, Dauda ya dogara ga Jehovah. Da yake Ubangiji Mamallakin dukan halitta yana tare da shi, me zai sa Dauda ya ji tsoron ɗan Adam, ko yaya girma da kuma yawan makamansa suke?

3 Yayin da ka karanta game da Dauda, kana sha’awar da a ce dogararka ga Jehovah ta fi haka ƙarfi? Mai yiwuwa, yawancinmu muna sha’awar hakan. Saboda haka, bari mu bincika matakai biyu da za mu bi mu sa Jehovah ya zama madogararmu. Da farko, muna bukatar mu sami kuma mu riƙe yadda za mu sha kan wani hani ga irin dogarar nan. Na biyu, muna bukatar mu koyi daidai abin da dogara ga Jehovah ta ƙunsa.

Sha Kan Tangarɗar da ke Hana Dogara ga Jehovah

4, 5. Me ya sa yake wa mutane da yawa wuya su dogara ga Allah?

4 Menene ke hana mutane su dogara ga Allah? Sau da yawa, domin wasu sun ɗimauce ne game da abin da ya sa munanan abubuwa ke faruwa. An koyar da mutane da yawa cewa Allah ne ke haddasa wahala. Sa’ad da wani bala’i ya auku, limamai sukan ce Allah ya “kwashi” mutanen zuwa wurinsa a sama. Ban da haka, shugabannin addini da yawa suna koyar da cewa Allah ya ƙaddara kowacce aukuwa—har da kowanne bala’i da kuma mugunta—da ke aukuwa a wannan duniyar. Zai yi wuya a dogara ga wani Allah marar tausayi. Shaiɗan wanda ke makantar da hankulan marasa ba da gaskiya, yana ɗokin ya gabatar da dukan irin wannan “koyarwar aljanu.”—1 Timothawus 4:1; 2 Korinthiyawa 4:4.

5 Shaiɗan ba ya son mutane su dogara ga Jehovah. Wannan magabcin Allah ba ya son mu san ainihin dalilin da ya sa mutane suke wahala. Kuma idan mun koyi dalilan Nassi na wahala, Shaiɗan zai so mu manta da su. Saboda haka, yana da kyau mu maimaita a wasu lokaci dalilai uku na musamman da ya sa ake wahala a duniya. Ta yin haka za mu sake tabbatar da zukatanmu cewa ba Jehovah ne ke haddasa wahala da muke fuskanta a rayuwa ba.—Filibbiyawa 1:9, 10.

6. Yaya 1 Bitrus 5:8 ta nuna dalili ɗaya da ya sa mutane suke wahala?

6 Dalili ɗaya da ya sa mutane suke wahala shi ne domin Shaiɗan yana son ya karya imanin mutanen Jehovah masu aminci. Ya yi ƙoƙarin ya karya imanin Ayuba. Shaiɗan ya kasa, amma bai daina ƙoƙari ba. Da yake shi ne mai mulkin wannan duniyar, yana neman ya “cinye” bayin Jehovah masu aminci. (1 Bitrus 5:8) Wannan ya haɗa da kowannenmu! Shaiɗan yana son ya sa mu daina bauta wa Jehovah. Saboda haka, yana iza tsanantawa. Ko da yaya wahalar take da ban azaba, muna da dalili mai kyau mu jimre. Ta yin haka, muna tabbatar da cewa Shaiɗan maƙaryaci ne, ta haka muna faranta wa Jehovah rai. (Ayuba 2:4; Misalai 27:11) Yayin da Jehovah yake ƙarfafa mu mu jimre tsanantawa, dogararmu gare shi tana daɗa ƙarfi.—Zabura 9:9, 10.

7. Wane dalilin wahala Galatiyawa 6:7 ta taimake mu mu sani?

7 Dalili na biyu na shan wahala yana cikin wannan ƙa’idar: “Iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe.” (Galatiyawa 6:7) Wani lokaci mutane sukan girbe sakamakon wahala domin sun yi shuki ta yin munanan zaɓe. Sukan zaɓi su yi tuƙi yadda suka ga dama, ya jawo musu haɗari. Mutane da yawa sukan zaɓi su sha sigari, da ke sa su ciwon zuciya ko kuma dajin huhu. Waɗanda suka zaɓi su yi lalata suna shan wahalar rashin dangantaka mai kyau ta iyali, rashin mutuncin kai, cuta da ake samu ta wajen jima’i, da kuma cikin shege. Mutane sukan ce Allah ne ke da alhakin irin wannan wahalar, amma a gaskiya kam, munanan zaɓensu ne ke jawo musu hakan.—Misalai 19:3.

8. In ji Mai-Wa’azi 9:11, me ya sa mutane ke wahala?

8 An ambata dalilai uku na shan wahala a Mai-Wa’azi 9:11: “Na sake duba kuma, na gani a cikin duniya; tsere, ba mai-sauri ke ci ba; yaƙi kuma, ba ga ƙarfafa ya ke ba; abinci kuma, ba ga masu-hikima ba; arziki kuma, ba ga masu-azanci ba; tagomashi kuma, ba ga masu-gwaninta ba: amma ga dukansu lokacinsu da zarafinsu su kan zo.” Wasu lokatai, mutane sukan kasance a inda tsausayi ke same su. Duk da ƙarfinmu ko raunanarmu, wahala da mutuwa takan same kowannenmu a lokacin da ba ma tsammani. Alal misali, a zamanin Yesu wata hasumiya a Urushalima ta fāɗi ta kashe mutane 18. Yesu ya nuna cewa ba horo Allah yake musu domin zunuban da suka yi dā ba. (Luka 13:4) A’a, ba za a ga laifin Jehovah ba a wannan wahalar.

9. Menene mutane da yawa ba su fahimta ba game da wahala?

9 Yana da muhimmanci a fahimci wasu abubuwa da suke haddasa wahala. Amma, akwai wani sashen batun da mutane suke iske da wuya su fahimta. Shi ne wannan: Me ya sa Jehovah Allah ya ƙyale wahala?

Me Ya Sa Jehovah Ya Ƙyale Wahala?

10, 11. (a) In ji Romawa 8:19-22, me ya faru da “dukan talikai”? (b) Yaya za mu san wanda ya ƙasƙantar da talikai zuwa banza?

10 Wani waje cikin wasiƙar manzo Bulus zuwa ga Romawa ya ba da ƙarin bayani a kan wannan muhimmin batun. Bulus ya rubuta: “Gama begen talikai yana sauraron bayyanuwar ’ya’yan Allah. Gama aka ƙasƙantadda talikai zuwa banza, ba da yardar kansu ba, amma sanadin shi wanda ya sanya su, ana bege talikai da kansu kuma za su tsira daga bautar ɓācewa zuwa cikin ’yanci na darajar ’ya’yan Allah. Gama mun sani dukan talikai suna nishi suna naƙuda tare da mu har yanzu.”—Romawa 8:19-22.

11 Domin a fahimci waɗannan ayoyi, da farko muna bukatar mu bincika wasu muhimman tambayoyi. Alal misali, Wanene ya ƙasƙantar da talikai zuwa banza? Wasu sun ce Shaiɗan; wasu kuma Adamu. Amma babu wani cikinsu da ya ƙasƙantar da talikai. Me ya sa? Domin wanda ya ƙasƙantar da talikai zuwa banza ya yi hakan ne domin “bege.” Hakika, ya ba da bege cewa a ƙarshe masu aminci za su “tsira daga bautar ɓacewa.” Adamu ko Shaiɗan ba za su iya ba da irin begen nan ba. Jehovah ne kaɗai zai iya. A bayyane yake cewa shi ya ƙasƙantar da talikai zuwa banza.

12. Wane ɗimauci ya taso game da sanin ma’anar “dukan talikai,” kuma ta yaya za a amsa wannan tambayar?

12 Amma, menene “dukan talikai” da aka ambata a wannan ayar? Wasu sun ce “dukan talikai” yana nufin dukan halitta, haɗe da dabbobi da tsiro. Shin dabbobi da tsiro suna begen samun “ ’yanci na darajar ’ya’yan Allah” ne? A’a. (2 Bitrus 2:12) Saboda haka, “dukan talikai” na nufin mutane ne kaɗai. Wannan halittar ce zunubi da mutuwa ta shafe ta saboda tawaye na Adnin kuma da take ɗokin samun bege.—Romawa 5:12.

13. Menene tawaye a Adnin ya yi wa mutane?

13 Shin, menene ainihi tawayen ya yi wa mutane? Bulus ya kwatanta sakamakon a kalma guda: banzanci.a Wani bincike ya ce, wannan kalmar ta kwatanta “banzancin wani abu da ba ya aikin da aka sa shi ya yi.” An halicci mutane don su yi rayuwa ta har abada, suna aiki tare su kamiltattu, iyali masu haɗin kai su kula da duniya ta aljanna. Maimako, sun yi rayuwa ta ɗan lokaci, ta azaba, sau da yawa kuma da baƙin ciki. Kamar yadda Ayuba ya sa shi, “mutum haihuwar mace kwanakinsa kaɗanna ne, cike da wahala kuma.” (Ayuba 14:1) Hakika banzanci kuwa!

14, 15. (a) Wane tabbacin adalci muka gani cikin hukuncin Jehovah a kan ’yan Adam? (b) Me ya sa Bulus ya ce an ƙasƙantar da talikai “ba da yardar kansu ba”?

14 Yanzu mun kai muhimmiyar tambaya: Me ya sa “Mai-shari’an dukan duniya” ya ƙasƙantar da mutane zuwa wannan rayuwar azaba da baƙin ciki? (Farawa 18:25) Ya yi adalci a yin haka? To, ka tuna abin da iyayenmu na farko suka yi. An yi wa Allah tawaye, sun bi Shaiɗan wanda ya tuhumi ikon mallakar Jehovah. Ta wurin ayyukansu sun goyi bayan tuhumar cewa rayuwar ’yan Adam za ta fi kyau ba tare da Jehovah ba, suna sarautar kansu ƙarƙashin ja-gorar halittar ruhu ɗan tawaye. An yi wa ’yan tawayen hukunci, watau, Jehovah ya ba su abin da suka so. Ya ƙyale ’yan Adam su yi sarautar kansa ƙarƙashin ikon Shaiɗan. Cikin yanayin nan, wace shawara ta fi kyau da ƙasƙantar da ’yan Adam zuwa banza amma domin su sami bege?

15 Amma, wannan ba da “yardar” talikai ba. An haife mu bayi ga zunubi da ɓatanci, ba mu da na yi a batun nan. Amma Jehovah cikin jinƙansa ya ƙyale Adamu da Hauwa’u su yi rayuwa su haifi ’ya’ya. Ko da yake mu ’ya’yansu an ƙasƙantar da mu zuwa banza na zunubi da mutuwa, muna da zarafin mu yi abin da Adamu da Hauwa’u suka kasa yi. Za mu iya sauraron Jehovah kuma mu koyi cewa ikon mallakarsa na adalci ne kuma mai kyau, yayin nan kuma sarautar ’yan Adam bare da Jehovah tana kawo azaba, baƙin ciki, da banzanci. (Irmiya 10:23; Ru’ya ta Yohanna 4:11) Kuma tasirin Shaiɗan sai daɗa sa abubuwa su yi muni yake yi. Tarihin ’yan Adam ya tabbatar da gaskiyar nan.—Mai-Wa’azi 8:9.

16. (a) Me ya sa za mu tabbata cewa Jehovah ba shi da alhakin wahala da muke gani a duniya yau? (b) Wane bege Jehovah cikin ƙauna ya yi wa mutanensa masu aminci tanadinsa?

16 A bayyane yake, cewa Jehovah yana da dalilai masu kyau na ƙasƙantar da mutane zuwa banza. To, wannan yana nufin cewa Jehovah ne tushen banzanci da wahala da kowannenmu ke sha a yau? To dai, ka yi tunanin wani alƙali ya zartar da hukunci a kan wani mai laifi. Mai laifin yana iya wahala lokacin da yake kurkuku, amma daidai ne ya ga laifin alƙalin cewa shi ya jawo masa wahala? Sam babu! Ban da haka, ba Jehovah ne tushen mugunta ba. Yaƙub 1:13 ta ce: “Allah ba shi jarabtuwa da mugunta, shi kuwa da kansa ba shi jarabci kowa ba.” Bari kuma mu tuna cewa Jehovah ya zartar da wannan hukunci domin samun “bege” ne. Cikin ƙauna, an yi wa ’ya’yan Adamu da Hauwa’u masu aminci shiri su ga ƙarshen banzanci kuma su yi murna wajen “ ’yanci na darajar ’ya’yan Allah.” A dukan dawwama, ’yan Adam masu aminci ba sa bukatar damuwa cewa dukan talikai za su sake fāɗawa cikin yanayin azaba na banzanci ba. Yadda Jehovah yake bi da abubuwa a hanya ta adalci na tabbatar da dacewar ikon mallakarsa ta dukan lokaci.—Ishaya 25:8.

17. Yaya ya kamata maimaita dalilan wahala ta duniya yau ya shafe mu?

17 Da muka maimaita waɗannan dalilan shan wahala ta mutane, akwai wani dalili ne na ganin laifin Jehovah game da mugunta ko kuma da za mu ƙi dogara gare shi? Ba haka ba, irin binciken nan yana sa mu yarda da waɗannan kalmomin Musa: “Fa ne shi, aikinsa cikakke ne; gama dukan tafarkunsa shari’a ne: Shi Allah mai-aminci ne, marar-mugunta, kuma, mai-adalci ne shi mai-gaskiya.” (Kubawar Shari’a 32:4) Ta yin bimbini a kan waɗannan al’amura, bari mu maimaita fahiminmu a wasu lokaci. Haka nan, sa’ad da muke fuskantar gwaji, za mu tsayayya wa ƙoƙarce-ƙoƙarcen Shaiɗan ya shuka shakka a zukatanmu. Mataki na biyu da aka ambata a farko fa? Dogara ga Jehovah ta ƙunshi menene?

Abin da Yake Nufi a Dogara ga Jehovah

18, 19. Da waɗanne kalmomi Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu, amma wane ra’ayi na kuskure mutane suke da shi?

18 Kalmar Allah ta aririce mu: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.” (Misalai 3:5, 6) Waɗannan kalmomi masu daɗi ne masu tabbatarwa. Hakika babu wani a dukan sararin halitta da za mu tabbata da shi fiye da Ubanmu mai ƙauna na samaniya. Amma waɗannan kalmomi na Misalai suna da sauƙin a karanta amma da wuya a yi amfani da su.

19 Mutane da yawa suna kuskure a ra’ayinsu game da abin da yake nufin a dogara ga Jehovah. Wasu suna tunanin cewa irin wannan dogara tsotsuwar zuciya ce kawai da muke da ita. Wasu kuma kamar sun gaskata cewa dogara ga Allah na nufin ya kāre mu daga kowacce wahala, ya yi maganin damuwarmu, ya bi da gwajinmu na yau da kullum yadda muke zato—nan da nan! Amma irin ra’ayin nan ba daidai ba ne. Dogara ta fi tsotsuwar zuciya kawai, gaskiya ce. Ga manya, dogara ta ƙunshi tsai da shawara, ta tunanin kirki.

20, 21. Mecece dogara ga Jehovah ta ƙunsa? Ka ba da misali.

20 Ka sake lura da abin da Misalai 3:5 ta ce. Ta bambanta dogara ga Jehovah da dogara ga namu fahimi, ta nuna cewa ba za mu iya yin su biyun ba. Wannan yana nufin cewa ba a yarda ne mu yi amfani da namu fahimi? A’a, domin Jehovah ya ba mu hankalin nan yana son mu yi amfani da shi. (Romawa 12:1) Amma a kan me muke dangana ko kuma dogara? Idan tunaninmu bai yi daidai da na Jehovah ba, muna yarda da hikimarsa—cewa ita ta fi tamu? (Ishaya 55:8, 9) Mu dogara ga Jehovah na nufin mu yarda wa tunaninsa ya yi mana ja-gora.

21 Ga misali: Ka yi tunanin ƙaramin yaro na zaune a kujerar baya ta ƙaramar mota da iyayensa a gaba. Babansa na tuƙi. Lokacin da suka soma shakkar hanyar da za a bi—ko matsalar hadari ko hanyar ba ta da kyau—yaya yaro mai biyayya, da ke dogara zai yi? Zai yi ihu ne daga wajen zamansa, yana gaya wa babansa yadda zai tuƙa motar? Zai yi shakkar shawarar iyayensa ko kuma ya ƙi sa’ad da suka tuna masa ya sha ɗamara da bel na kujerarsa? A’a, alhali ya tabbata da iyayensa su bi da al’amura daidai, ko da su ajizai ne. Jehovah Ubanmu ne kamili. Bai kamata mu dogara gare shi ƙwarai, sa’anda muke fuskantar yanayi mai wuya ba?—Ishaya 30:21.

22, 23. (a) Me ya sa ya kamata mu dogara ga Jehovah sa’ad da muka fuskanci matsala, kuma ta yaya za mu yi haka? (b) Me za a tattauna cikin talifi na gaba?

22 Amma Misalai 3:6 ta nuna cewa ya kamata mu ‘shaida Jehovah a dukan al’amuranmu,’ ba a lokacin da muke fuskantar yanayi mai wuya kawai ba. Shawarwari da muke yi yau da kullum ya kamata su nuna muna dogara ga Jehovah. Sa’anda matsala ta taso, bai kamata mu ji tsoro mu yi rawan jiki ko mu ƙi da ja-gorar Jehovah game da bi da al’amura a hanya mafi kyau ba. Muna bukatar mu ɗauki gwaji cewa zarafi ne na goyon bayan ikon mallakar Jehovah, mu nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne, mu kuma koyi biyayya da wasu halaye da ke faranta wa Jehovah rai.—Ibraniyawa 5:7, 8.

23 Za mu iya nuna dogararmu ga Jehovah duk da irin tangarɗa da za ta iya razanar da mu. Muna yin haka cikin addu’o’inmu kuma ta yadda muke dogara ga Kalmar Jehovah da ƙungiyarsa don ja-gora. Amma, ta yaya za mu nuna dogara ga Jehovah sa’ad da muka fuskanci matsaloli da ke tasowa a duniyar yau? Talifi na gaba a kan wannan batun ne.

[Hasiya]

a Kalmar Helenanci da Bulus ya yi amfani da ita wa “banza” ita ce aka yi amfani da ita a Septuagint na Helenanci a fassara furcin da Sulemanu ya yi amfani da shi sau da sau a littafin Mai-Wa’azi, a furcin nan ‘dukan abu banza ne!’—Mai-Wa’azi 1:2, 14; 2:11, 17; 3:19; 12:8.

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya Dauda ya nuna ya sa Jehovah madogararsa?

• Waɗanne dalilai uku ne ke sa mutane su wahala a yau, kuma me ya sa yake da kyau mu maimaita su a wasu lokaci?

• Wane hukunci Jehovah ya yi wa ’yan Adam, kuma me ya sa hukuncin na adalci ne?

• Me dogara ga Jehovah ta ƙunsa?

[Hotuna a shafi na 20]

Dauda ya sa Jehovah ya zama madogararsa

[Hoto a shafi na 22]

Yesu ya nuna cewa sa’ad da wata hasumiya ta fāɗi a Urushalima ba Jehovah ke da alhakinsa ba

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba