Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 9/1 p. 32
  • Taimako na Gaske ga Matalauta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Taimako na Gaske ga Matalauta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 9/1 p. 32

Taimako na Gaske ga Matalauta

YAYIN da Ɗan Allah, Yesu Kristi, yake duniya, ya nuna yana son ya taimaka wa matalauta da gaske. Shaidu da suka ga hidimar Yesu suka ce: “Makafi suna karɓan ganin gari, guragu suna tafiya, kutare suna tsarkaka, kurame suna ji, ana tada matattu, ana yi ma talakawa wa’azin bishara.” (Matta 11:5) Amma, miliyoyin matalauta a yau fa? Akwai bishara dominsu ne? E, da akwai saƙon bege!

Ko da yake sau da yawa mutane galiba suna banza da matalauta, Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari: “Gama ba kullum za a manta da matalauta ba, begen talakawa kuma ba za shi taɓe har abada ba.” (Zabura 9:18) Waɗannan kalmomi na ta’aziyya za su cika lokacin da Mulkin Allah, gwamnati ta samaniya, ta sake dukan sarautar ’yan Adam. (Daniel 2:44) Domin shi ne Sarkin gwamnatin samaniya, Yesu “za ya nuna tausayi ga matalauci da mai-mayata, za ya kuwa ceci rayukan fakirai. Za ya fanshi ransu daga zalunci da ƙwace; a ganinsa kuma jininsu mai-daraja ne.”—Zabura 72:13, 14.

Yaya yanayin zama zai kasance sa’ad da Kristi ya soma sarauta bisa duniya? Waɗanda suke ƙarƙashin sarautar Kristi bisa duniya za su mori amfanin aikin hannuwansu. Littafi Mai Tsarki ya ce a Mikah 4:3, 4: “Kowa za ya zauna a ƙarƙashin kuringar anab nasa da itacen ɓaurensa; ba kuwa wani mai-tsoratadda su; gama bakin Ubangiji mai-runduna ya faɗi.” Mulkin Allah ma zai yi maganin matsalolin ciwo da mutuwa. (Ishaya 25:8) Lallai duniyar za ta zama dabam! Za mu iya tabbata da waɗannan alkawura na Littafi Mai Tsarki domin Allah ne kansa ya hure su.

Ban da ba da saƙon bege, Littafi Mai Tsarki na taimaka a bi da matsaloli na yau da kullum, irinsu a sha kan rashin mutunci, da talauci ke iya jawowa. Kirista wanda mabukaci ne ya sani ta wurin nazarinsa na Littafi Mai Tsarki cewa yana da tamani a idanun Allah yadda Kirista mawadaci ke da tamani. Littafin Ayuba cikin Littafi Mai Tsarki ya lura game da Allah cewa “ba ya kuwa fi ganin darajar masu-arziki da masu-talauci ba.” (Ayuba 34:19) Dukansu Allah na ƙaunarsu daidai.—Ayukan Manzanni 10:34, 35.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba