Bauta ta Gaskiya Tana Haɗa Kan Iyali
MARIA ’yar shekara 13 ce lokacin da ita da ƙanwarta, Lucy, suka ji game da Jehovah daga wajen wani danginsu wanda kuma ya bayyana musu begen Aljanna a duniya. Domin abin ya kwashi hankalinsu, suka bi shi zuwa Majami’ar Mulki na Shaidun Jehovah. Bayanin da Maria ta ji ya burge ta. Dabam yake sosai da na coci, inda kusan waƙa kawai ake yi! Ba da daɗewa ba yaran suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehovah.
Yayansu Hugo yana son ussan ilimi da ra’i na bayyanau. Yana da’awar cewa bai yarda da akwai Allah ba. Amma lokacin da yake aikin soja, ya karanta littafin nan Life—How Did It Get Here? By Evolution or by Creation? a Ya sami amsoshin da ba zai samu ba daga wani addini. Da ya gama aikin soja, ya soma ƙarfafa sabon imaninsa ga Allah ta yin nazarin Littafi Mai Tsarki da halartar taro da ƙannensa mata. Maria da Lucy sun yi baftisma a shekara ta 1992, shekara biyu bayan da suka sami gaskiya, yayansu kuma ya yi nasa bayan shekara biyu.
Yayin nan kuma iyayensu da suke da imanin al’adu na Katolika, ba sa son gaskiyar. Suna jin haushin Shaidun Jehovah, ko da suna son hali da ado mai kyau na matasa Shaidu waɗanda yaransu suke gayyata zuwa gidansu. A lokacin cin abinci, sa’ad da yaran suke taɗin abubuwan da suka koya daga taron, iyayensu suna son su sani.
Duk da haka, iyayen suna son maita. Babansu mashayi ne da yake dūkan mamarsu. Iyalin ta kusa ta rabu. Sai kuma baban ya yi mako biyu a kurkuku don mummunar hali na yawan shan giya. Da yake cikin kurkuku, ya soma karanta Littafi Mai Tsarki. Yayin da yake karatun, ya lura da wurin da Yesu ya yi magana game da alamar kwanaki na ƙarshe. Saboda suna son su sani, baban da mamar suka je Majami’ar Mulki kuma suka yarda a soma nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Da suka koyi gaskiya, suka halaka dukan littattafansu na maita kuma suka samu ’yanci daga farmaki na aljanu ta wurin kiran sunan Jehovah. Suka soma yin gyara a halayensu.
Za ka iya tunanin irin farin ciki da Maria da Lucy suka yi da suke kallon Hugo yake wa iyayensu baftisma a wani taron gunduma da aka yi a Bolivia a shekara ta 1999? Wannan ya faru shekara tara bayan da Maria da Lucy suka ji game da Jehovah da alkawuransa. Suna hidima ta cikakken lokaci yanzu tare da Hugo. Lallai suna farin ciki da bauta ta gaskiya ta kawo haɗin kai ga iyalinsu!
[Hasiya]
a Shaidun Jehovah ne suka buga.