Menene Jehovah Yake Bukata A Gare Mu?
“Me ne Ubangiji ya ke biɗa gareka kuma, sai aikin gaskiya, da son jinƙai, ka yi tafiya da tawali’u tare da Allahnka?”—MIKAH 6:8.
1, 2. Me ya sa wasu bayin Jehovah suke yin sanyin gwiwa, amma me zai taimake su?
VERA ’yar shekara 75, Kirista ce mai aminci kuma ba ta da isashen lafiya. “Wani lokaci,” in ji ta, “Nakan duba ta taga sai na ga ’yan’uwana Kirista maza da mata suna wa’azi gida gida. Yakan sa ni hawaye domin ina son na kasance tare da su, amma rashin lafiya ya rage hidimata ga Jehovah.”
2 Ka taɓa jin haka nan? Hakika, dukan waɗanda suke ƙaunar Jehovah suna son su yi tafiya cikin sunansa kuma su cika farillansa. To, idan muna rashin lafiya, ko mun tsufa, ko muna da hakki na iyali fa? Za mu iya sanyin gwiwa domin irin wannan yanayi zai iya hana mu yin dukan abin da zuciyarmu za ta so ta yi a hidimar Allah. Idan haka yanayinmu yake, babu shakka bincika Mikah surori 6 da 7 za su kasance da ban ƙarfafa. Waɗannan surorin sun nuna cewa farillan Jehovah ya yi su da sanin ya kamata kuma za a iya cika su.
Yadda Allah Yake Bi da Mutanensa
3. Yaya Jehovah ya bi da Isra’ilawa ’yan tawaye?
3 Bari mu fara bincika Mikah 6:3-5 kuma mu lura da yadda Jehovah ya bi da mutanensa. Ka tuna cewa a zamanin Mikah Isra’ilawan ’yan tawaye ne. Duk da haka, Jehovah ya yi musu magana cikin juyayi da waɗannan kalmomi, “Ya ku mutanena.” Ya yi roƙo: “Ya ku mutanena, ku tuna.” Maimako ya zarge su cikin fushi, ya yi ƙoƙari ya taɓa zuciyarsu ta wajen tambaya, “Me na yi muku?” Har ya ƙarfafa su su ba da “shaida,” game da shi.
4. Yaya ya kamata misalin Allah na juyayi ya shafe mu?
4 Lallai Allah ya kafa mana misali! Cikin juyayi ya kira har mutanen Isra’ila da Yahuda ’yan tawaye na zamanin Mikah “mutanena” kuma ya yi musu ‘roƙo.’ Saboda haka, ya kamata mu nuna juyayi da kuma halayen kirki a yadda muke bi da waɗanda suke cikin ikilisiya. Hakika, wasu ba su da sauƙi a yi sha’ani da su, ko kuma sun raunana a ruhaniya. Duk da haka, idan suna ƙaunar Jehovah za mu so mu taimake su kuma mu yi juyayinsu.
5. Wane muhimmin darasi aka nuna a Mikah 6:6, 7?
5 Bari yanzu mu juya zuwa Mikah 6:6, 7. Mikah ya yi wasu tambayoyi, yana cewa: “Da me zan zo a gaban Ubangiji, in yi sujjada a gaban Allah Maɗaukaki? zan zo gareshi da ƙonannun hadayu, da ’yan maruƙa bana ɗaya? Ubangiji za ya ji daɗin dubban raguna, ko kogunan mai har zambar goma? zan bada ɗan fārina domin laifina, zuriyar jikina domin zunubin raina.” A’a, ba zai yiwu ba a faranta wa Jehovah rai da “dubban raguna, ko kogunan mai har zambar goma.” Amma da akwai abin da zai faranta masa rai. Menene wannan?
Dole Mu Yi Gaskiya
6. Waɗanne farillai uku na Allah aka nuna a Mikah 6:8?
6 A Mikah 6:8, mun koya abin da Jehovah yake bukata a gare mu. Mikah ya yi tambaya: “Me ne Ubangiji ya ke biɗa gareka kuma, sai aikin gaskiya, da son jinƙai, ka yi tafiya da tawali’u tare da Allahnka?” Waɗannan farillai uku sun ƙunshi yadda muke ji, yadda muke tunani, da kuma yadda muke ayyuka. Dole mu motsa mu nuna halayen nan, mu yi tunanin yadda za mu nuna su, kuma mu aikata daidai haka. Bari mu bincika waɗannan farillai uku bi da bi.
7, 8. (a) Menene yake nufi a yi “aikin gaskiya”? (b) Waɗanne rashin gaskiya yake ko’ina a zamanin Mikah?
7 “Aikin gaskiya” yana nufin mu yi abin da yake daidai. Yadda Allah yake abubuwa shi ne mizanin aikin gaskiya. Amma, mutanen zamanin Mikah ba su yi aikin gaskiya ba sai na rashin gaskiya. A waɗanne hanyoyi? Ka duba Mikah 6:10. A ƙarshen wannan ayar, an kwatanta ’yan kasuwa da cewa suna amfani da “mudun ƙoro” watau, wanda ya yi ƙarami sosai. Aya ta 11 ta ƙara da cewa suna amfani da “ma’aunonin rikici.” Kuma in ji aya ta 12, suna “faɗi ƙarerayin harshensu.” Saboda haka, mudunsu na ƙarya, ma’auninsu na ƙarya, da kuma maganganunsu na ƙarya sun yi yawa a kasuwa ta zamanin Mikah.
8 Ayyukan rashin gaskiya ba su tsaya a kasuwa ba. Haka suka kasance ruwan dare gama gari a kotu. Mikah 7:3 ta nuna cewa “ɗan sarki yana roƙon toshi, alƙali kuma a shirye ya ke ya karɓa.” Ana ba wa alƙalai toshiya domin su yi hukunci marar gaskiya ga marasa laifi. “Babban mutum,” ko kuma mutane masu rinjaya sun saka hannu cikin wannan laifin. Mikah ya ce ɗan sarki, alƙali, da kuma babban mutum suna “aika” ko kuma suna ja-gorar miyagun ayyukansu.
9. Yaya rashin gaskiya da miyagu suke yi ya shafi Yahuda da Isra’ila?
9 Rashin gaskiya da miyagun shugabannan suke aikatawa ya shafi dukan Yahuda da Isra’ila. Mikah 7:5 ta ce rashin gaskiya ya kai ga rashin yarda tsakanin abokane, aminai, har da ma’aurata. Aya ta 6 ta nuna cewa wannan ya kai ga tashin hankali tsakanin dangi na kusa kamar ɗa da ubansa, ’ya da uwarta suna rena juna.
10. A yanayin rashin gaskiya na zamanin yau, ta yaya Kiristoci suke bi da kansu?
10 Yau kuma fa? Ba ma ganin yanayi ne da ya yi kama da wannan? Kamar Mikah, mu ma rashin gaskiya ne ya kewaye mu, yanayin rashin yarda, da kuma tashin hankali tsakanin mutane da na iyali. Duk da haka, tun da mu bayin Allah ne a tsakanin wannan duniya marar adalci, ba za mu ƙyale halin wannan duniya na rashin gaskiya ya shigo cikin ikilisiyar Kirista ba. Maimakon haka, ya kamata mu yi ƙoƙari mu ɗaukaka mizanin gaskiya da aminci, muna nuna wannan a rayuwarmu ta yau da kullum. Hakika, “mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.” (Ibraniyawa 13:18) Ba ka yarda ba cewa ta wajen yin aikin gaskiya muna morar albarka da take zuwa daga ’yan’uwantaka da ta kasance a kan yarda?
Ta Yaya Mutane Suke Jin “Muryar Ubangiji”?
11. Yaya Mikah 7:12 take cika?
11 Mikah ya yi annabci cewa duk da wannan yanayin rashin gaskiya, aikin gaskiya zai kai ga dukan ire-iren mutane. Annabin ya annabta cewa za a tara mutane “daga teku zuwa teku, daga dutse har zuwa dutse” su zama masu bauta wa Jehovah. (Mikah 7:12) A yau, a cikar ƙarshe na wannan annabci, ba wata al’umma ba ce, amma mutane ɗaɗɗaya daga dukan al’ummai suna amfana daga aikin gaskiya na Allah na rashin son zuciya. (Ishaya 42:1) Ta yaya wannan ya zama gaskiya?
12. Ta yaya ake jin “muryar Ubangiji” a yau?
12 Domin ka sami amsar, ka bincika kalmomin Mikah na farko. Mikah 6:9 ta ce: “Muryar Ubangiji tana kiran birni, mutumin hikima kuma za ya ga sunanka.” Ta yaya mutanen dukan al’ummai suke jin “muryar Ubangiji,” kuma yaya wannan yake da nasaba da yin gaskiya? Hakika, mutane a yau ba sa jin muryar Allah a zahiri. Ta wajen aikinmu na wa’azi a dukan duniya, mutane ɗaɗɗaya na dukan ƙabilu ko yaya matsayinsu yake a rayuwa suna jin muryar Jehovah. Domin haka, waɗanda suke saurara ‘suna tsoron sunan Allah,’ suna kuma daraja ta. Muna aikata a hanyar da ta yi daidai cikin ƙauna ta hidima na masu shelar Mulki da himma. Ta wurin sanar da sunan Allah ga kowa ba tare da son zuciya ba, “aikin gaskiya” muke yi.
Dole Mu So Alheri
13. Menene bambanci tsakanin ƙauna ta alheri da so?
13 Bari mu bincika farilla ta biyu da aka ambata a Mikah 6:8. Jehovah yana bukata mu ‘so alheri.’ Kalmar Ibrananci da aka fassara “alheri” an kuma saka ta “ƙauna ta alheri,” ko kuma “ƙauna ta aminci.” Ƙauna ta alheri aiki ne na juyayi na damuwa da kuma yin la’akari da wasu. Ƙauna ta alheri ta bambanta da so. Ta yaya? So yana da ma’ana mai faɗi wanda ana iya amfani da shi ga abubuwa da kuma ra’ayi. Alal misali, Nassosi ya yi maganar mutumin da yake “son ruwan anab da mai” da kuma mutumin da yake “ƙaunar hikima.” (Misalai 21:17; 29:3) A wata sassa, ƙauna ta alheri a dukan lokaci ta shafi mutane ne, musamman waɗanda suke bauta wa Allah. Mikah 7:20 ta yi magana, game da [“ƙauna ta alheri, NW ] ga Ibrahim”—mutum wanda ya bauta wa Jehovah Allah.
14, 15. Yaya ake nuna ƙauna ta alheri, kuma wane misali aka ambata?
14 In ji Mikah 7:18, annabin ya ce Allah “yana jin daɗin [ƙauna ta alheri, NW ].” A Mikah 6:8, ba a gaya mana ba kawai mu nuna ƙauna ta alheri amma cewa mu so wannan halin. Menene muka koya daga waɗannan nassosi? Ana nuna ƙauna ta alheri da son rai domin muna so mu nuna ta. Kamar Jehovah, muna jin daɗi wajen nuna ƙauna ta alheri ga waɗanda suke da bukata.
15 A yau, irin wannan ƙauna ta alheri alama ce ta mutanen Allah. Ga misali guda kawai. A Yuni na shekara ta 2001, hadari da ya jawo ambaliya mai yawa a Texas na Amirka, ya lalace dubban gidaje, haɗe da gidaje ɗarurruwa na Shaidun Jehovah. Domin su taimaki ’yan’uwansu Kiristoci da suke cikin bukata, Shaidu 10,000 sun ba da lokacinsu da kuma ƙarfinsu da son zuciya. Waɗanda suka ba da kansu sun yi aiki na kusan rabin shekara babu tsayawa, sun yi amfani da dare da rana, da kuma ƙarshen mako su sake gina Majami’un Mulki 8 da gidaje fiye da 700 domin ’yan’uwansu Kiristoci. Waɗanda ba su iya wannan aikin ba sun ba da gudummawa ta abinci, kayayyaki, da kuma kuɗi. Me ya sa waɗannan Shaidu dubbai suka taimaki ’yan’uwansu? Domin suna ‘son alheri.’ Kuma yana daɗaɗa zuciya mu sani cewa ’yan’uwanmu a dukan duniya suna nuna irin waɗannan ayyuka na ƙauna ta alheri! Hakika, cika farillar mu ‘so alheri’ ba kaya ba ne, amma abin farin ciki ne!
Ka Yi Filako a Yin Tafiya da Allah
16. Wane misali ya nanata bukata mu kasance da filako a yin tafiya da Allah?
16 Farilla ta uku da aka samu a Mikah 6:8 ita ce “ka yi tafiya da [filako] tare da Allahnka.” Wannan yana nufin mu fahimci kasawarmu kuma mu dogara da Allah. Alal misali: Ka yi tunanin yarinya ƙarama ta riƙe hannun babanta gam gam yayin da suke tafiya cikin guguwa. Yarinyar ta sani cewa ƙarfinta kaɗan ne, amma ta dogara ga babanta. Mu ma dole mu san kasawarmu amma mun dogara ga Ubanmu na samaniya. Ta yaya za mu riƙe wannan dogara? Hanya ɗaya, ita ce muna tuna abin da ya sa hikima ce mu kusaci Allah. Mikah ya tuna mana dalilai uku: Jehovah shi ne Mai Cetonmu, Mai Ja-Gorarmu, kuma shi ne Mai Kāre mu.
17. Ta yaya Jehovah ya yi ceto, ya yi ja-gora, kuma ya kāre mutanensa na lokatan dā?
17 In ji Mikah 6:4, 5, Allah ya ce: “Ni na fishe ku daga ƙasar Masar.” Hakika, Jehovah ne Mai Ceton Isra’ila. Jehovah ya ƙara cewa: “A gabanku kuma na aike Musa, da Haruna da Maryamu.” An yi amfani da Musa da Haruna wajen ja-gorar al’ummar, Maryamu kuma ta ja-goranci matan Isra’ila wajen rawar nasara. (Fitowa 7:1, 2; 15:1, 19-21; Kubawar Shari’a 34:10) Jehovah ya ba da ja-gora ta wajen bayinsa. A aya ta 5, Jehovah ya tuna wa al’ummar Isra’ila cewa shi ya kāre su daga Balak da Balaam kuma shi ya kāre Isra’ilawa a ƙarshen tafiyarsu daga Shittim a Mowab zuwa Gilgal a Ƙasar Alkawari.
18. Ta yaya Allah yake aikata shi Mai Ceto, Mai Ja-Gora, da Mai Kāre mu a yau?
18 Yayin da muke tafiya da Allah, ya cece mu daga duniyar Shaiɗan, yana mana ja-gora ta Kalmarsa da ƙungiyarsa, kuma yana kāre mu a rukuni sa’ad da ’yan adawa suka kawo mana faɗa. Saboda haka, muna da dalilai masu yawa na riƙe hannun Ubanmu na samaniya gam gam sa’ad da muke tafiya na ƙarshe cikin guguwa zuwa wurin da ya fi Ƙasar Alkawari na dā girma—sabuwar duniya ta adalci na Allah.
19. A wace hanya filako yake da nasaba da kasawarmu?
19 Kasance da filako a yin tafiya da Allah na taimaka mana mu ga yadda yanayinmu yake da gaske. Wannan haka yake domin kasance da filako ya ƙunshi sanin kasawarmu. Tsufa da ciwo suna iya kafa iyaka ga abin da za mu iya yi a hidimar Jehovah. Maimakon mu yarda wannan ya sa mu sanyin gwiwa, yana da kyau mu tuna cewa Allah yana amince da ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu da sadaukarwa ‘na abin da muke da shi, ba abin da ba mu da shi ba.’ (2 Korinthiyawa 8:12) Hakika, Jehovah yana bukata mu bauta masa da dukan zuciyarmu, muna yin dukan abin da yanayinmu ya ƙyale. (Kolossiyawa 3:23) Yayin da muke yin dukan abin da za mu iya da himma a hidimarsa, Allah zai yi mana albarka.—Misalai 10:22.
Halin Jira na Kawo Albarka
20. Sanin menene ya kamata ya taimake mu mu kasance da irin halin jira na Mikah?
20 Samun albarkar Jehovah yana motsa mu mu yi koyi da halin Mikah. Ya ce: “Zan jira Allah na cetona.” (Mikah 7:7) Ta yaya waɗannan kalmomin suka shafi yin tafiyarmu da filako tare da Allah? Kasancewa da halin jira, ko kuma haƙuri, na taimakonmu mu guji kasalar cewa ranar Jehovah ba ta zo ba tukuna. (Misalai 13:12) Hakika, dukanmu muna da muradin ganin ƙarshen wannan muguwar duniya. Duk da haka, kowane mako mutane dubbai suna fara tafiya da Allah. Sanin wannan ya ba mu kyakkyawan dalili na nuna halin jira. Wani Mashaidi da ya daɗe ya ce game da wannan: “Ganin shekara 55 na aikin wa’azi, na tabbata cewa ban yi hasarar kome ba wajen jiran Jehovah. Akasin haka, an kāre ni daga baƙin ciki da yawa.” Kai ma ka shaida wannan?
21, 22. Ta yaya Mikah 7:14 ta cika a zamaninmu?
21 Yin tafiya da Jehovah tana ba mu albarka mai yawa. Yayin da muka karanta Mikah 7:14, Mikah ya kwatanta mutanen Allah da tumaki da suke kwanciya cikin kwanciyar hankali tare da makiyayinsu. A yau, a cika mai girma ta wannan annabcin, raguwar Isra’ila ta ruhaniya da kuma “waɗansu tumaki” suna da kwanciyar hankali da Makiyayinsu abin dogara, Jehovah. Suna zama ‘su kaɗai a cikin daji, a cikin kurmi a tsakiyar Karmel,’ da ta rabu a ruhaniya da wannan duniya da ta cika da masifa.—Yohanna 10:16; Kubawar Shari’a 33:28; Irmiya 49:31; Galatiyawa 6:16.
22 Mutanen Jehovah suna more ni’ima, kamar yadda ma Mikah 7:14 ta annabta. Da yake magana game da tumakin Allah, ko kuma mutane, Mikah ya ce: “Bar su su yi kiwo cikin Bashan da Gilead.” Kamar yadda tumaki a Bashan da Gilead suke kiwo a waje mai ni’ima, haka mutanen Allah a yau suke more ni’ima ta ruhaniya—ƙarin albarka ne ga waɗanda suke tafiya cikin filako da Allah.—Litafin Lissafi 32:1; Kubawar Shari’a 32:14.
23. Wane darasi za mu koya daga bincika Mikah 7:18, 19?
23 A Mikah 7:18, 19, annabin ya taƙaita muradin Jehovah ya gafarta wa waɗanda suka tuba. Aya ta 18 ta ce Jehovah yana “gafarta mugunta” kuma yana “rufe laifi.” Aya ta 19 ta ce, zai “zubarda zunubansu duka cikin zurfin teku.” Wane darasi ɗaya za mu koya daga wannan? Za mu iya tambayar kanmu ko muna yin koyi da Jehovah a wannan. Muna gafarta zunuban da wasu suke yi mana? Sa’ad da waɗannan suka tuba suka yi gyara, hakika za mu so mu yi koyi da gafartawa gaba ɗaya da son rai na Jehovah.
24. Ta yaya ka amfana daga annabcin Mikah?
24 Ta yaya muka amfana daga bincika annabcin Mikah? Ya tuna mana cewa Jehovah ya ba da bege na gaske ga waɗanda suka matsa kusa da shi. (Mikah 2:1-13) An ƙarfafa mu mu yi dukan abin da zai yiwu domin mu ɗaukaka bauta ta gaskiya domin mu yi tafiya cikin sunan Allah har abada. (Mikah 4:1-5) Kuma an tabbatar mana cewa ko yaya yanayinmu yake, za mu iya cika farillan Jehovah. Hakika, annabcin Mikah ya ƙarfafa mu da gaske mu yi tafiya cikin sunan Jehovah.
Yaya Za Ka Amsa?
• Bisa ga Mikah 6:8, menene Jehovah yake bukata a gare mu?
• Menene wajibi idan za mu yi “aikin gaskiya”?
• Ta yaya za mu nuna cewa muna ‘son alheri’?
• Menene ‘kasancewa da filako a yin tafiya da Allah’ ya ƙunsa?
[Hotuna a shafi na 15]
Duk da yanayin mugunta a zamaninsa, Mikah ya bi farillan Jehovah. Saboda haka kai ma za ka iya
[Hoto a shafi na 17]
Ka yi aikin gaskiya ta yi wa dukan mutane wa’azi
[Hotuna a shafi na 17]
Ka nuna kana son alheri ta biyan bukatun wasu
[Hoto a shafi na 17]
Ka yi abin da za ka iya ta amince da kasawarka cikin filako