Menene Yake Faruwa da Ba da Sadaka?
BAYAN farmaki na 11 ga Satumba 2001, a New York City da Washington, D.C., abin mamaki ne a ga yadda mutane suka tallafa wa waɗanda suke shan wahalar aukuwar. Ƙungiyar karɓan sadaka sun yi mamaki da suka sami fiye da dala biliyan biyu da rabi don a taimaki iyalai da suke wahala. Domin yadda bala’in yake da girma, mutane a ko’ina suna son su yi taimako.
Bai daɗe ba sai wasu cikin jama’a suka yi fushi da jin tuhumar da aka yi wa ƙungiyoyin karɓan sadaka cewa ba sa amfani da kuɗaɗen yadda ya dace. An yi hasala ƙwarai da jin cewa wata ƙungiyar sadakar tana son ta riƙe kusan rabin kuɗi dala miliyan 546 da aka ba su domin ba da taimako. Ko da yake ƙungiyar daga baya ta bar shawarar kuma ta nemi gafara, wata manemar labarai ta ce: “ ’Yan sūka sun ga cewa wannan shawarar ta makara a mai da wa ƙungiyoyin riƙon amana” da mutane suke yi musu kafin farmakin. Kai kuma fa? A baya bayan nan amincinka game da ba da sadaka ga ƙungiyoyi ya ragu ne?
Ba da Sadaka Yana da Amfani ne ko Kuma Babu?
Ana ɗaukan ba da kyauta ga ƙungiyar sadaka kirki ne. Amma, ba kowa ne ke ɗaukansa haka ba. Fiye da shekaru 200 da suka shige, Samuel Johnson, marubucin insha’i a Ingilishi, ya rubuta: “Za ka fi tabbatawa cewa kana nagarta idan ka ba da kuɗi ga waɗanda suka yi aiki, maimakon ba da kuɗi kawai ga ƙungiyar ba da sadaka.” Haka ma wasu a yau suke shakka, kuma labaran yadda ƙungiyoyin kyautar sadaka suke ɓata kuɗi ba ya ƙarfafa jama’a sam. Ga misalai biyu.
An kore wani darektan ƙungiyar kyautar sadaka ta addini a San Francisco domin an tuhume shi da cewa ya biya kuɗin cin abincinsa da kowanne mako dala 500 da kuma na jinyarsa na sake-kama na shekara biyu. A Britaniya, waɗanda suke shirya kyautar sadaka a telibijin sun sha kunya da aka gano cewa dala miliyan 10 na kuɗin Amirka da aka bayar domin a taimaka a gina gidajen marayu a Romania, an gina gidaje 12 ne kawai da ba su dace ba, kuma dubban dala ba a san inda suka bi ba. Irin munanan labaran nan suna sa waɗanda suke ba da kyautar su daɗa mai da hankali game da yawan kuɗin da suke bayarwa da kuma wanda za su ba wa.
A Bayar ko Kuma Kada a Bayar
Abin baƙin ciki ne mu yarda abin da wasu mutane ko kuma ƙungiyoyi suka yi ya kashe mana damuwa na gaske da kuma yi wa wasu juyayi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Addini mai-tsarki marar-ɓāci a gaban Allah Ubanmu ke nan, mutum shi ziyarci marayu da gwauraye cikin ƙuncinsu.” (Yaƙub 1:27) Hakika, damuwa da matalauta da tsiyayyu sashe ne na musamman na Kiristanci.
Har ila, kana iya tunani, ‘Ya kamata na ci gaba da ba da kyauta ga ƙungiyar sadaka ko kuma ya kamata na taimaka kawai ta ba wa mutanen kansu kyauta? Wace irin bayarwa Allah yake bukata? Talifi na gaba zai tattauna waɗannan tambayoyi.