Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 1/1 pp. 3-4
  • Mugunta Ta Fi Nagarta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mugunta Ta Fi Nagarta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mugunta Tana Ƙaruwa
  • Yadda Nagarta Za Ta Yi Nasara Bisa Mugunta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Menene Yake Faruwa da Ba da Sadaka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 1/1 pp. 3-4

Mugunta Ta Fi Nagarta

ADUNIYAR yau, mutane kaɗan ne kawai suka yarda su ba da kansu. Wasu kuwa suna son su “nuna bambanci” ta wurin yi wa wasu kirki. A kowace shekara, mutane masu ɗimbin yawa suna ba da biliyoyin Dala ga abin da suke ganin shi ne sanadin abu mai kyau. Alal misali, a ƙasar Britaniya, gudummawa da ake bayarwa ga ƙungiyoyin mutane marasa galihu ta kai Dala biliyan 13 a shekara ta 2002. Tun a shekara ta 1999, mutane goma masu taimakon matalauta sun ba da fiye da Dala biliyan 38 don taimaka wa gajiyayyu.

Wani aiki mai kyau da wasu ma’aikata masu taimako suka yi nasara a kai ya ƙunshi biyan kuɗin asibiti na iyalan masu karɓan ƙaramin albashi, taimaka wa yara marayu, taimaka wa shirye-shiryen rigakafi a ƙasashe masu tasowa, ba wa yara ilimin firamare, samar da dabbobi masu haihuwa ga manoma da suke ƙasashe marasa arziki, da kuma ba da agaji ga mutanen da bala’i ya shafa.

Wannan gaskiyar ta nuna cewa ’yan adam za su iya yin abu mai kyau ga wasu. Abin baƙin ciki shi ne, akwai wasu mutane da suke aikata miyagun abubuwa.

Mugunta Tana Ƙaruwa

Tun daga ƙarshen yaƙin duniya na biyu, an rubuta aukuwa kusan 50 na kisan ƙare-dangi da kuma na mutanen da aka yi wa kisan kiyashi domin siyasa. “Waɗannan kashe-kashen,” in ji jaridar American political science Review, “sun yi sanadin mutuwar sojoji aƙalla miliyan 12 da kuma farar hula miliyan 22, wanda hakan ya fi adadin mutanen da aka kashe a yaƙe-yaƙen cikin gida da na waje tun daga shekara ta 1945.”

A ƙarshen rabin ƙarni na ashirin, an kashe mutane miliyan biyu da dubu dari biyu a Kambodiya saboda siyasa. A ƙasar Ruwanda ƙiyayya da ke tsakanin ƙabilu ta jawo kisan mutane 800,000 maza da mata da yara ƙanana. A ƙasar Boswana an kashe mutane fiye da 200,000 saboda addini da siyasa.

Sa’ad da yake ambatar ayyukan mugunta na baya bayan nan a shekara ta 2004, sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce: “A ƙasar Iraƙi an yi wa mutane farar hula kisan gilla, kuma an kama ma’aikata masu taimako, ’yan jarida, da wasu farar-hula, aka yi musu kisan wulaƙanci. Sa’an nan kuma an yi wa fursunan Iraƙi ƙeta. A ƙasar Dafur an ta da dukan mutanen gari, an ƙoƙƙone gidajensu, kuma an yi wa mata fyaɗe da gangan. A arewacin ƙasar Yuganda, an yi wa yara lahani kuma an tilasta musu su azabtar da mutane. A ƙasar Beslan an kama yara an yi musu kisa na rashin imani.”

Har a ƙasashen da suka bunƙasa, laifuffukan da aka yi don wasu sun tsani wasu sun ƙaru. Alal misali, jaridar Independent News ta ba da rahoto cewa a shekara ta 2004 a ƙasar Britaniya an ga “ƙarin yawan mutanen da aka yi wa ƙeta saboda bambancin launin fata a shekarun da suka shige.”

Me ya sa mutane da suke iya yin abu mai kyau suke yin mugunta? Mugunta za ta taɓa ƙarewa kuwa? Kamar yadda talifi na gaba ya nuna, Littafi Mai Tsarki ya ba da kyakkyawar amsa ga waɗannan tambayoyin.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba