Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 6/1 pp. 4-7
  • Bayarwa Da Ke Faranta Wa Allah Rai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bayarwa Da Ke Faranta Wa Allah Rai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Ku Bada Sadaka”
  • Motsawa da ta Dace Tana da Muhimmanci
  • Gudummawa da Aka Shirya Fa?
  • Bayarwa da Take da Amfani Mafi Kyau
  • Ka Bi Misalin Yesu Kuma Ka Nuna Damuwa Ga Matalauta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Bauta wa Jehobah da Iya Karfinka Zai Sa Ka Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Bayarwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 6/1 pp. 4-7

Bayarwa Da Ke Faranta Wa Allah Rai

YESU da almajiransa sun mori cin abinci tare a Bait’anya da wasu abokai, da Maryamu, Martha, da kuma Li’azaru da aka ta da daga matattu lokacin. Sa’ad da Maryamu ta ɗauko mai mai tsada kuma ta shafa a ƙafafun Yesu, sai Yahuda Iskariyoti ya yi fushi kuma ya furta ra’ayinsa. “Me ya sa ba a sayar da man nan a bakin sule ɗari uku [watau kuɗin aiki na shekara ke nan] ba, a ba fakirai?” in ji shi. Nan da nan wasu ma suka yi gunaguni haka.—Yohanna 12:1-6; Markus 14:3-5.

Amma Yesu ya amsa: “Ku bar ta . . . Gama kuna da fakirai kullum tare da ku, lokacin da ku ke so duka kuma kuna da zarafi ku yi musu alheri: amma ba ku da ni kullum ba.” (Markus 14:6-9) Shugabannan addini na Yahudawa suna koyar da cewa ba da sadaka ba kawai abin kirki ba amma cewa zai iya yin kafarar zunubai. A wata sassa, Yesu ya nuna cewa bayarwa da ke faranta wa Allah rai ba ta wurin ba da kyautar sadaka kawai ba ce ga fakirai.

Idan muka bincika yadda ake bayarwa a cikin ikilisiyar Kirista ta farko zai bayyana wasu hanyoyi da za mu iya nuna damuwarmu kuma mu faranta wa Allah rai ta wurin bayarwarmu. Zai kuma nuna wata irin bayarwa da take dabam, da ke aikata nagarta mafi kyau.

“Ku Bada Sadaka”

Yesu ya ƙarfafa almajiransa a lokatai da yawa su “bada sadaka,” kuma yadda wasu fassara suka ce, “ba da kyautar alheri” ko kuma a “ba da ta sadaka.” (Luka 12:33; New English Bible; A Translation in the Language of the People, na Charles B. Williams) Yesu ya faɗakar game da alfarmar banza don kawai a girmama mai bayarwar maimakon Allah. “Sa’anda fa ka ke yin sadaka,” in ji shi, “kada ka busa ƙaho a gabanka, kamar yadda masu-riya ke yi cikin majami’u da hanyoyi, domin su sami daraja a wurin mutane.” (Matta 6:1-4) Domin sun yi amfani da wannan gargaɗin, Kiristoci na farko suka guje wa alfarmar banza na shugabannan addini na zamaninsu kuma suka zaɓi su taimaka wa waɗanda suke da bukata ta wurin yi musu hidima ko kuma ba su kyauta da kansu.

Alal misali, a Luka 8:1-3, an gaya mana cewa Maryamu Magadaliya, Yuwanna, Susannatu, da wasu sun yi amfani da “dukiyarsu” da ba a sani ba, suka yi wa Yesu hidima tare da manzanninsa. Ko da yake waɗannan maza ba tsiyayyu ba ne, amma domin sun ba da kansu wajen hidima sun ƙyale neman abin duniya. (Matta 4:18-22; Luka 5:27, 28) Ta wurin taimakonsu su cika aikin da Allah ya ba su, hakika, waɗannan mata sun ɗaukaka Allah. Kuma Allah ya nuna godiyarsa gare su ta wurin adana labarin karimcinsu na alheri cikin Littafi Mai Tsarki domin tsararraki na nan gaba su karanta.—Misalai 19:17; Ibraniyawa 6:10.

Wata mace mai alheri ita ce Dokas “cike ta ke da ayyukan nagarta da bayebayen.” Tana ɗinka wa gwauraye mata tufafi a garinta na kusa da teku a Yafa. Ko ita take sayan yaɗin ta yi ɗinkinsu, ko kuma ɗinkin kawai take yi musu, ba mu sani ba. Duk da haka, nagargarun ayyukanta sun jawo waɗanda ta iya taimaka musu kusa da ita, kuma jawo ta wurin Allah wanda ya albarkace alherinta.—Ayukan Manzanni 9:36-41.

Motsawa da ta Dace Tana da Muhimmanci

Me ya motsa waɗannan mutane su bayar? Ba zai zama wani motsin rai kawai ba da tsosuwar zuciya take sa mutum ya so ya taimaka. Sun ga ya dace su yi abin da za su iya kowacce rana su taimaka wa waɗanda suke talauci, shan wahala, rashin lafiya, ko kuma wasu wahala. (Misalai 3:27, 28; Yaƙub 2:15, 16) Irin wannan bayarwa ce take faranta wa Allah rai. Ainihi ƙauna ce mai zurfi ga Allah da sha’awar yin koyi da alherinsa da karimcinsa ke motsa mutum.—Matta 5:44, 45; Yaƙub 1:17.

Manzo Yohanna ya nanata wannan muhimmin sashe na bayarwa sa’ad da ya yi tambayar nan: “Amma wanda shi ke da dukiyar duniya, yana kuwa ganin ɗan’uwansa da tsiya, ya hana masa tausayi, ƙaƙa ƙaunar Allah tana zaune a cikinsa?” (1 Yohanna 3:17) Ba sai an ba ka amsar ba. Ƙaunar Allah ce take motsa mutane su ba da sadaka. Allah yana godiya kuma yana yi wa waɗanda kamarsa suke nuna halin karimci albarka. (Misalai 22:9; 2 Korinthiyawa 9:6-11) Muna ganin irin karimcin nan a yau? Ga wani abin da ya faru a wata ikilisiyar Shaidun Jehovah ba da daɗewa ba.

Gidan wata Kirista tsohuwa ya lalace sosai. Tana zama ita kaɗai ba ta da iyalin da suke kula da ita. Shekaru da yawa, a cikin gidanta ake yin taron Kirista, kuma sau da yawa sai ta gayyaci waɗanda za su iya zuwa su ci abinci a gidanta. (Ayukan Manzanni 16:14, 15, 40) Da suka ga matsalarta, waɗanda suke cikin ikilisiya suka yi gudummawa don su taimake ta. Wasu sun ba da kuɗi, wasu kuma suka yi aikin. Cikin makonni kaɗan, ma’aikatan suka ɗora sabuwar jinka, suka gina wajen wanka, suka yi shafe kuma shafa wa gidan fenti, aka gina mata sabon kabat a cikin kicin. Sakamakon bayarwa da suka yi ba kawai ya gamsar da bukatar matar ba amma kuma ya jawo ikilisiyar su yi kurkusa da juna kuma ya burge maƙwabta su ga misalin bayarwa ta Kirista ta gaskiya.

Da akwai hanyoyi da yawa da za mu taimaka wa wasu mu kanmu. Za mu iya ba da lokaci wa maraya ko marainiya? Za mu iya zuwan cefane wa gwauruwa tsohuwa da muka sani? Za mu iya dahuwa ko kuma ba wani da yake bukata kuɗi? Ba sai muna da arziki za mu iya taimakawa ba. Manzo Bulus ya rubuta: “Idan nufi yana nan, abin karɓa ne gwargwadon abin da ke wurin mutum, ba gwargwadon abin da ba shi da shi” ba. (2 Korinthiyawa 8:12) Amma irin wannan bayarwa ce kaɗai Allah ke wa albarka? A’a.

Gudummawa da Aka Shirya Fa?

Wasu lokatai ƙoƙarce-ƙoƙarcen kanmu bai isa ba. Hakika, Yesu da manzanninsa sun yi ajiya domin matalauta, kuma suna karɓan wasu kuɗaɗe daga mutanen da suka iske a lokatan aikinsu na hidima. (Yohanna 12:6; 13:29) Haka ma, ikilisiyoyi na ƙarni na farko suka tattara kuɗi lokacin da bukata ta taso kuma aka shirya gudummawa mai girma.—Ayukan Manzanni 2:44, 45; 6:1-3; 1 Timothawus 5:9, 10.

Ɗaya cikin lokatan nan ya taso a shekara ta 55 A.Z., ne. Ikilisiyoyi da suke Yahudiya sun shiga talauci, wataƙila saboda yunwa da ta auku ne a lokacin. (Ayukan Manzanni 11:27-30) Domin kullum yana damuwa da matalauta, manzo Bulus ya jera sunayen ikilisiyoyi da ake bukatar taimakonsu har da Makidoniya. Shi kansa ya shirya a tattara kuɗi kuma ya aiki maza da suka dace su kai kuɗin. (1 Korinthiyawa 16:1-4; Galatiyawa 2:10) Da shi da waɗanda suka yi aikin ba wani cikinsu da aka biya domin hidimar da suka yi ba.—2 Korinthiyawa 8:20, 21.

A yau ma Shaidun Jehovah suna hanzarin su taimaka yayin da bala’i ya auku. Alal misali, a rani na shekara ta 2001, aka yi hadari da ya hadassa rigyawa mai yawa a Houston, Texas, U.S.A. Duka duka, gidaje 723 na Shaidun suka lalace, da yawa cikinsu sun lalace sosai. Aka kafa kwamiti na wannan bala’i da ƙwararrun dattawa Kiristoci suke ciki, nan da nan suka bincika bukatun kowanne mutum kuma aka ba su gudummawa da ya dace a taimaka wa Shaidu a yankin su jimre da yanayin kuma a yi musu gyaran gidajensu. Waɗanda suka ba da kansu daga ikilisiyoyi na yankin suka yi dukan aikin. Wata Mashaidiya ta yi murna ƙwarai game da taimakon da aka yi mata har bayan da kwamfanin ishora suka biyata kuɗin bala’in don ta gyara gidanta, nan da nan ta ba da kuɗin don gudummawa ga wasu da suke da bukata.

Idan ya zo ga ba da sadaka ga wata ƙungiya, muna bukatar mu mai da hankali da irin sanarwan da ake yi. Wasu ƙungiyoyi suna da ma’aikata da yawa da suke biya da kuma kuɗin biyan talla, sai kuɗin ya rage kaɗan kawai don ainihin manufar tattara sadakar. Misalai 14:15 ta ce: “Marar-wayo yana gaskata kowacce magana: amma mai-hankali ya kan lura da al’amuransa da kyau.” Saboda haka, hikima ce a bincika matakin sosai.

Bayarwa da Take da Amfani Mafi Kyau

Da akwai wata irin bayarwa da ta fi muhimmanci da sadaka. Yesu ya yi nuni ga wannan, lokacin da wani masarauci matashi ya yi tambayar abin da zai yi don ya samu rai na har abada. Yesu ya ce masa: “Sai ka tafi, ka sayarda abin da ka ke da shi, ka ba fakirai, za ka sami wadata a sama: ka zo kuma, ka biyo ni.” (Matta 19:16-22) Ka lura cewa Yesu bai ce, ‘Ka ba fakirai, za ka sami rai’ ba. Maimako, ya daɗa cewa, “Ka zo kuma, ka biyo ni.” A wata sassa, yadda ake yaba wa ba da kyautar sadaka kuma yake da amfani, almajiranci na Kirista yana da ƙarin wasu abubuwa.

Manufar Yesu na musamman taimaka wa wasu a ruhaniya ne. Bai daɗe ba kafin mutuwarsa, ya gaya wa Bilatus: “Domin wannan an haife ni, domin wannan kuma na zo cikin duniya, domin in bada shaida ga gaskiya.” (Yohanna 18:37) Ko da yake ya yi jagabanci a taimaka wa matalauta, warkar da masu ciwo, ya ciyar da masu yunwa, ainihi Yesu ya koyar da almajiransa su yi wa’azi ne. (Matta 10:7, 8) Hakika, koyarwarsa na ƙarshe ta ƙunshi umurnin nan: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai.”—Matta 28:19, 20.

Babu shakka, wa’azi ba zai warware dukan matsalolin duniya ba. Duk da haka, sa hannu a bisharar Mulkin Allah ga dukan ire-iren mutane na ɗaukaka Allah, domin wa’azi yana cim ma nufin Allah kuma na buɗe hanyar fa’idodi masu dawwama ga waɗanda suka karɓi saƙon Allah. (Yohanna 17:3; 1 Timothawus 2:3, 4) Me ya sa ba za ka saurara abin da Shaidun Jehovah za su gaya maka a ziyararsu a nan gaba ba? Suna tafe da kyauta ta ruhaniya. Kuma sun sani cewa wannan ne hanya mafi kyau da za su nuna maka.

[Hotuna a shafi na 6]

Da akwai hanyoyi da yawa da za mu iya nuna muna damuwa

[Hoto a shafi na 7]

Yin wa’azin bishara na faranta wa Allah rai kuma na buɗe hanyar fa’idodi masu dawamma

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba