Jibin Maraice Na Ubangiji Yana da Ma’ana Mai Muhimmanci Gare Ka
SHIN Jibin Maraice na Ubangiji yana da wata ma’ana mai muhimmanci a gare ka? Domin mu fahimci wannan, bari da farko mu fahimci ma’ana da Yesu Kristi kansa ya liƙa wa wannan abin na musamman.
Da maraice a ranar 14 ga Nisan, shekara ta 33 A.Z., Yesu ya tara manzanninsa 12 a wani gidan bene a Urushalima domin su yi bikin Ƙetarewa na shekara shakara. Bayan sun ci jibin bikin Ƙetarewan, Yahuda maci amana ya fita ya bar ɗakin domin ya ci amanar Yesu. (Yohanna 13:21, 26-30) Ga sauran manzanni 11, Yesu ya gabatar da “Jibin Ubangiji.” (1 Korinthiyawa 11:20) Ana kuma kiransa Bikin Tuna Mutuwar Yesu, tun da Yesu ya umurci mabiyansa su: “Yi wannan abin tunawa da ni.” Wannan shi ne kawai bikin da aka umurci Kiristoci su riƙa yi.—1 Korinthiyawa 11:24.
In ji ƙamus na Webster’s, tuna wani abu, abu ne da yake taimakawa wajen “adana abin” ko kuma “yake sa a riƙa tuna abin.” A wurare da yawa, mutane sukan kafa wani abu na tuni ko kuma su keɓe wasu ranaku domin su tuna da wani da ya mutu ko kuma wani abu mai muhimmanci. A wannan batun Yesu ya kafa jibi na tunawa da shi—jibi da zai taimaka wajen tunani, ya taimaka wa almajiransa su tuna da abu mai muhimmanci ƙwarai na wannan babbar rana. Domin tsararraki masu zuwa, wannan jibin zai tuna wa masu bikin ma’ana mai zurfi na abin da Yesu ya yi a wannan daren, musamman ma abubuwa da ya yi amfani da su. Waɗanne abubuwa ne Yesu ya yi amfani da su, kuma menene suke nufi? Bari mu bincika Littafi Mai Tsarki mu tuna da abin da ya faru a wannan daren na shekara ta 33 A.Z.
Abin da Suke Nufi
“Ya ɗauki gurasa kuma, sa’anda ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba su, ya ce, Wannan jikina ne wanda an bayar domin ku: ku yi wannan abin tunawa da ni.”—Luka 22:19.
Sa’ad da Yesu ya ɗauki gurasar ya ce, ‘Wannan yana nufin jikina ne,’ yana nufi ne cewa wannan gurasa marar yisti tana wakiltar, ko kuma alama ce na jikinsa marar zunubi, wanda ya bayar “sabili da ran duniya.” (Yohanna 6:51) Ko da yake wasu fassarar Littafi Mai Tsarki sun ce “Wannan [Helenanci, es·tin] jikina ne,” Thayer’s Greek-English Lexicon of the New Testament ya ce wannan kalmar aikatau sau da yawa na nufin “nuna, muhimmanci.” Yana da ma’anar ta wakilta.—Matta 26:26.
Haka kuma yake ga ƙoƙon ruwan inabi. Yesu ya ce: “Wannan ƙoƙo sabon alkawari ne cikin jinina, wanda an zubar dominku.”—Luka 22:20.
A cikin tarihi na Matta, Yesu ya ce game da ƙoƙon: “Wannan jinina ne na alkawari, wanda an zubar domin mutane dayawa zuwa gafarar zunubai.” (Matta 26:28) Yesu ya yi amfani da ruwan inabi da yake cikin ƙoƙo ya wakilci jininsa. Jininsa da aka zubar ne tushen “sabon alkawari” domin almajirai waɗanda aka shafa su da ruhu, waɗanda za su yi sarauta da kuma aikin firist tare da shi a samaniya.—Irmiya 31:31-33; Yohanna 14:2, 3; 2 Korinthiyawa 5:5; Ru’ya ta Yohanna 1:5, 6; 5:9, 10; 20:4, 6.
Ruwan inabin cikin ƙoƙo kuma za ta kasance da tunasarwa cewa jinin Yesu da aka zubar shi ne tushen samun “gafarar zunubai,” saboda haka ya buɗe hanya domin a kira masu ci zuwa rayuwa a samaniya su zama magada tare da Kristi. Saboda haka, waɗanda aka kira su zuwa sama—adadinsu ƙalilan ne—su ne kawai suke cin wannan gurasa kuma su sha ruwan inabi a lokacin Bikin Tuna Mutuwar Yesu.—Luka 12:32; Afisawa 1:13, 14; Ibraniyawa 9:22; 1 Bitrus 1:3, 4.
To, yaya kuma game da dukan sauran mabiyan Yesu da ba sa cikin wannan sabon alkawari? Waɗannan su ne “waɗansu tumaki” na Ubangiji, waɗanda suke sauraron, ba sarauta da Kristi ba a samaniya, amma su more rai madawwami a aljanna a duniya. (Yohanna 10:16; Luka 23:43; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Wannan “taro mai-girma” na Kiristoci masu aminci “suna yi ma [Allah] bauta kuma dare da rana,” suna farin cikin su kiyaye wannan jibin maraice na Ubangiji. Kalmominsu da kuma ayyukansu watau yana cewa ne: “Ceto ga Allahnmu ne wanda ya zauna bisa kursiyin, ga Ɗan ragon kuma.”—Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10, 14, 15.
Sau Nawa?
“Ku yi wannan abin tunawa da ni.”—Luka 22:19.
Sau nawa ya kamata a yi bikin Tuna Mutuwar domin a adana wannan bikin na tuna mutuwar Kristi? Yesu bai faɗa ba. Duk da haka, tun da ya kafa Jibin Maraice na Ubangiji a ranar 14 ga Nisan, a maraicen bikin Ƙetarewa, wanda Isra’ilawa suke yi kowacce shekara, a bayyane yake cewa Yesu yana so ne a yi bikin a wannan hanyar. Sa’ad da Isra’ilawa suke biki kowacce shekara domin ’yancinsu daga bauta a ƙasar Masar, Kiristoci kowacce shekara za su yi bikin ’yancinsu daga bauta ga zunubi da mutuwa.—Fitowa 12:11, 17; Romawa 5:20, 21.
Ra’ayin tunawa da abu shekara shekara ba sabo ba ne. Alal misali, ka yi la’akari da sa’ad da ma’aurata za su yi bikin tuna ranar aurensu ko kuma al’umma za ta yi bikin wani abu mai muhimmanci a tarihinta. Bikin babu shakka sau ɗaya ake yi a shekara idan ranar wannan abin ta kewayo. Ƙarnuka da yawa bayan Kristi, da yawa da suke da’awar su Kiristoci ne ana kiransu, “ ’yan sha huɗu,” domin suna bikin mutuwar Yesu sau ɗaya a shekara, a ranar 14 ga Nisan.
Biki Mai Sauƙi Amma Mai Muhimmanci
Manzo Bulus ya yi bayani cewa kiyaye Jibin Maraice na Ubangiji zai sa almajiran Yesu su ci gaba da “shelar mutuwar Ubangiji har ya zo.” (1 Korinthiyawa 11:26) Saboda haka, wannan bikin zai mai da hankali ne a kan matsayin Yesu mai wuya, da mutuwarsa, ta cika cikin nufin Allah.
Ta wajen kasancewa da aminci har mutuwarsa, Yesu Kristi ya ɗaukaka Jehovah Allah Mahalicci mai hikima da ƙauna da Mamallakin dukan halitta mai adalci. Ba kamar yadda Shaiɗan ya yi da’awa ba, ba kamar Adamu ba, Yesu ya tabbatar cewa yana yiwuwa ga mutane su kasance da aminci ga Allah, har a lokaci mai tsanani.—Ayuba 2:4, 5.
Jibin Maraice na Ubangiji yana sa a tuna a yi godiya da ƙauna ta sadaukar da kai na Yesu. Duk da gwaji mai tsanani, Yesu ya kasance da cikakkiyar biyayya ga Ubansa. Saboda haka ya ba da kamiltaccen ransa na mutum domin ya rufe zunubin Adamu mai yawa. Kamar yadda Yesu da kansa ya yi bayani, ya zo ya ba da “ransa kuma abin fansar mutane dayawa.” (Matta 20:28) Saboda haka, dukan waɗanda suka ba da gaskiya ga Yesu za a gafarta musu zunubansa kuma su sami rai madawwami cikin jituwa da ainihin nufin Jehovah domin mutane.—Romawa 5:6, 8, 12, 18, 19; 6:23; 1 Timothawus 2:5, 6.a
Dukan wannan ya nanata nagarta mai yawa na Jehovah da kuma ƙauna ta aminci wajen yi wa mutane tanadin ceto. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Inda aka bayyana ƙaunar Allah garemu ke nan, Allah ya aike Ɗansa haifaffensa kaɗai cikin duniya, domin mu rayu ta wurinsa. Nan akwai ƙauna, ba cewa mu ne muka yi ƙaunar Allah ba, amma shi ne ya ƙaunace mu, ya aike Ɗansa kuma shi zama kafara ta zunubanmu.”—1 Yohanna 4:9, 10.
Hakika, yin bikin Tuna Mutuwar Yesu abu ne mai kyau ƙwarai da gaske! Yana da sauƙi da za a iya yin bikin a dukan duniya a cikin yanayi dabam dabam, duk da haka yana da ma’ana wajen tunasarwa na lokaci mai tsawo.
Ma’anarsa a Gare Ka
Mutuwar hadaya ta Ubangijinmu Yesu Kristi ya yi masa zafi da kuma Ubansa, Jehovah. Shi kamilin mutum Yesu, bai fuskanci mutuwa da ya gada ba kamar yadda muke fuskanta. (Romawa 5:12; Ibraniyawa 7:26) Da zai ci gaba da rayuwa har abada. Ba za a iya kashe shi ba ba tare da ya ƙyale ba. Ya ce: “Ba wanda ya ke ƙwace mini [raina], amma don kaina ina ba da shi.”—Yohanna 10:18.
Duk da haka, Yesu da son rai ya ba da kamiltaccen ransa na mutum, domin hadaya saboda ta “wurin mutuwa shi wofinta wanda yake da ikon mutuwa, watau Shaiɗan; shi kuma sake dukan waɗanda ke ƙarƙashin bauta muddar ransu saboda tsoron mutuwa.” (Ibraniyawa 2:14, 15) Ƙaunar Kristi ta sadaukar da kai ta bayyana kuma cikin irin mutuwa da ya miƙa kansa. Yana sane da irin azaba da zai sha da kuma mutuwa da zai yi.—Matta 17:22; 20:17-19.
Bikin Tuna Mutuwar Yesu kuma yana tunasar da mu ƙauna mafi yawa da aka taɓa nuna mana daga Ubanmu na samaniya, Jehovah. Lallai ya dame shi, shi mai “tausayi mai-jinƙai,” ya ji kuma ya ga “kuka mai-zafi da hawaye” na Yesu a cikin lambun Jathsaimani, da kuma bulala ta mugunta, da azabar ƙeta, da kuma mutuwa a sannu sannu mai ƙuna ƙwarai. (Yaƙub 5:11; Ibraniyawa 5:7; Yohanna 3:16; 1 Yohanna 4:7, 8) Tunanin wannan a yanzu ma bayan ƙarnuka da yawa, yana damun mutane da yawa.
Ka yi tunanin yadda Jehovah Allah da Yesu Kristi suka biya irin wannan fansa mai tsada dominmu masu zunubi! (Romawa 3:23) Kowacce rana, muna fuskantar gaskiyar yanayinmu na zunubi da kuma ajizancinmu. Duk da haka, bisa ga bangaskiya cikin hadayar fansa na Yesu, muna iya roƙon Allah ya gafarta mana. (1 Yohanna 2:1, 2) Wannan ya sa yana yiwuwa mu more ’yancin magana da Allah da kuma lamiri mai kyau. (Ibraniyawa 4:14-16; 9:13, 14) Bugu da ƙari, za mu sami begen rayuwa a aljanna a duniya mu dawwama. (Yohanna 17:3; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Wannan da kuwa wasu albarka duka suna kasancewa ne domin sadaukar da kai mai girma da Yesu ya yi.
Nuna Godiya ga Jibin Maraice na Ubangiji
Jibin Maraice na Ubangiji babu shakka nuni ne na “mafificin alherin Allah.” Kuma tanadin da Jehovah Allah ya yi domin hadayar fansa—da sadaukar da kai ta Yesu ta sa ya yiwu—hakika “ta fi gaban magana.” (2 Korinthiyawa 9:14, 15) Shin wannan nagarta da Allah ya nuna ta wurin Yesu Kristi bai motsa godiya da ƙauna ba a cikinka?
Mun tabbata ya yi hakan. Saboda haka, muna gayyatarka ka haɗu da Shaidun Jehovah domin bikin Tuna Mutuwar Yesu. Wannan Shekarar za a yi bikin ranar Laraba, 16 ga Afrilu, bayan faɗuwar rana. Shaidun Jehovah a yankinku za su yi farin cikin gaya maka ainihin lokacin da kuma wurin da za a yi wannan bikin mai muhimmanci.
[Hasiya]
a Domin cikakken bayani na fansa, don Allah ka dubi littafin nan Sanin da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada, Shaidun Jehovah ne suka buga.
[Box/Hotuna a shafi na 6]
“WANNAN JIKINA NE” KO KUMA “WANNAN YANA NUFIN JIKINA” WANNE CIKI?
Sa’ad da Yesu ya ce, “Ni ne ƙofa” da kuma “Ni ne guringar anab,” babu wanda ya yi tunanin cewa shi ne ƙofa ta zahiri ko kuma kuringar anab na zahiri. (Tafiyar tsutsa tamu ce; Yohanna 10:7; 15:1.) Hakazalika, sa’ad da The New Jerusalem Bible ya yi ƙaulin Yesu yana cewa: “Wannan ƙoƙon ne sabon alkawari,” ba ma cewa ƙoƙon ne a zahiri sabon alkawari ba. Haka nan, sa’ad da ya ce gurasar ne jikinsa, babu shakka cewa gurasar tana nufin, ko kuma tana wakiltar jikinsa ne. Saboda haka, fassarar Charles B. Williams ta ce: “Wannan tana wakiltan jikina.”—Luka 22:19, 20.
[Hoto a shafi na 5]
Gurasa marar yisti da kuma ruwan inabi alamu ne da suka dace domin jikin Yesu marar zunubi da kuma jininsa da aka zubar
[Hoto a shafi na 7]
Bikin Tuna Mutuwar Yesu abin tunasarwa ce mai kyau na ƙauna da Jehovah Allah da kuma Yesu Kristi suka nuna