Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 4/1 p. 3
  • Menene Jibin Maraice Na Ƙarshe?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Menene Jibin Maraice Na Ƙarshe?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Makamantan Littattafai
  • Jibin Maraice Na Ubangiji Yana da Ma’ana Mai Muhimmanci Gare Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Idin Ketarewa na Karshe da Yesu Ya Yi
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Taron da Bai Kamata A Ba Ka Labari Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Me Ya Sa Yadda Shaidun Jehobah Suke Yin Jibin Ubangiji Ya Bambanta da Na Sauran Addinai?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 4/1 p. 3

Menene Jibin Maraice Na Ƙarshe?

ME YAKE faɗowa zuciyarka sa’ad da ka ji wannan furcin “jibin maraice na ƙarshe”? Mutane da yawa za su tuna wani zane a Milan ta Italiya, wanda mai zane Leonardo da Vinci suka zana (1452-1519). Hakika, wannan jibin maraice na ƙarshe abin da masu zane, marubuta, da mawaƙa a dukan ƙarnuka suke magana a kai ne.

Amma, menene ne Jibin Maraice na Ƙarshe, kuma menene ma’anar sa ga mutane da suke raye a wannan ƙarni na 21? Kundin sani da ƙamus za su gaya maka cewa Jibin Maraice na Ƙarshe, ana kiransa Jibin Maraice na Ubangiji ma, abinci ne da Yesu Kristi ya ci da manzanninsa da yamma kafin mutuwarsa ta hadaya. Tun da yake wannan jibi na ƙarshe ne da Yesu ya ci da mabiyansa masu aminci ana kiransa Jibin Maraice na Ƙarshe. Kuma tun da Ubangiji Yesu Kristi ne da kansa ya kafa shi, Jibin Maraice na Ubangiji daidai ne.

A cikin dukan ƙarnuka, mutane da yawa sun sadaukar da rayukansu domin abin da suka gaskata ya cancanta. Wasu cikin waɗannan mutuwa ta amfani wasu mutane na ɗan lokaci. Amma, idan aka gwada, babu ko ɗaya cikin waɗannan da ta yi kusa wajen muhimmanci da mutuwar Yesu Kristi. Bugu da ƙari, babu mutuwa a dukan tarihin ’yan Adam da ta shafi dukan duniya kamar wannan. Me ya sa?

Domin a amsa wannan tambayar kuma a taimaka maka ka fahimci abin da Jibin Maraice na Ubangiji yake nufi a gare ka, muna masu gayyatarka ka karanta talifi na gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba