Ka Yi Ƙoƙari Ka Ɗauki Wasu Yadda Jehovah Yake Ɗaukansu
“Ganin Ubangiji ba kamar na mutum ba ne.”—1 SAMU’ILA 16:7.
1, 2. Ta yaya yadda Jehovah ya ga Eliyab ya bambanta da yadda Sama’ila ya gan shi, menene za mu iya koya daga wannan?
AƘARNI na 11 K.Z., Jehovah ya aiki annabi Sama’ila ya yi wani aiki a ɓoye. Ya umarci annabin ya tafi gidan wani mutum mai suna Jesse ya naɗa ɗaya cikin ’ya’yan Jesse ya zama sarkin Isra’ila na gaba. Sa’ad da Sama’ila ya ga Eliyab, ɗan Jesse, ya tabbata cewa ya sami wanda Allah ya zaɓa. Amma Jehovah ya ce: “Kada ka dubi fuskarsa, ko kuwa tsawon jikinsa: gama na ƙi shi: gama ganin Ubangiji ba kamar na mutum ba ne: gama mutum yana duban aini, amma Ubangiji yana duban zuciya.” (1 Samu’ila 16: 6, 7) Sama’ila ya kasa ganin Eliyab yadda Jehovah ya gan shi.a
2 Yana da sauƙi mutane su yi kuskure a yadda suke ganin wasu! A gefe ɗaya, mutane da suke da kyan gani suna iya ruɗinmu amma a ciki ba su da ƙa’idodin ɗabi’a. A wani ɓangare kuma, muna iya kasance da zafin hali da aniya a yadda muke ganin sahihan mutane waɗanda ba ma son halayensu.
3, 4. (a) Idan matsala ta taso tsakanin Kiristoci biyu, menene kowanne ya kamata ya ƙudura niyyar yi? (b) Waɗanne tambayoyi ya kamata mu yi wa kanmu sa’ad da muke jayayya mai tsanani da ɗan’uwa mai bi?
3 Matsaloli suna iya tasowa sa’ad da muke saurin hukunta wasu—har ma waɗanda muka daɗe da saninsu. Wataƙila husuma mai tsanani ya taso tsakaninka da wani Kirista da dā amini ne. Za ka so ku sulhunta matsalar? Menene zai taimaka maka ka cim ma wannan?
4 Me ya sa ba za ka dubi ɗan’uwanka ko ’yar’uwarka Kirista da dā amininka ne da kyau ba? Kuma ka yi haka ta wajen la’akari da kalmomin Yesu: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” (Yohanna 6:44) Sai ka tambayi kanka: ‘Me ya sa Jehovah ya jawo wannan mutumin zuwa ga Ɗansa? Waɗanne halaye masu kyau mutumin yake da su? Ina ƙyaliya ko kuma ba na ɗaukan waɗannan halaye da muhimmanci? Me ya sa ma muka zama abokai dama? Me ya jawo ni kusa da wannan mutumin?’ Da farko zai yi wuya ka yi tunanin halayensa masu kyau, musamman idan ka riƙe shi a zuciya. Amma, wannan muhimmin mataki ne na mai da abokantaka da ke tsakaninku. Don a kwatanta yadda za a yi wannan, bari mu dubi halaye kyawawa na mutane biyu da a wani lokaci ake ɗaukansu bisa kasawarsu. Mutanen annabi Yunana ne da manzo Bitrus.
Ganin Yunana Yadda Ya Kamata
5. Wane aiki aka ba Yunana, amma me ya yi?
5 Yunana ya yi hidimar annabi ga masarautar arewa ta Isra’ila a zamanin Sarki Jeroboam na II, ɗan Jehoash. (2 Sarakuna 14:23-25) Wata rana, Jehovah ya umarci Yunana ya bar Isra’ila ya je Nineba, babban birnin Daular Assuriya. Wane aiki zai yi? Ya faɗakar da mazaunan cewa za a halaka babban birninsu. (Yunana 1:1, 2) Maimakon ya bi umurnin Allah, Yunana ya gudu! Ya shiga jirgin ruwa da ke zuwa Tarshish, yana da nisa daga Nineba.—Yunana 1:3.
6. Me ya sa Jehovah ya zaɓi Yunana ya tafi Nineba?
6 Menene yake faɗowa zuciyarka sa’ad da aka yi zancen Yunana? Kana tunani cewa annabi ne mai rashin biyayya? Ganinsa sama sama zai iya sa ka yi tunani haka. Amma Allah ya naɗa Yunana ya zama annabi domin yana rashin biyayya ne? Ko kaɗan! Yunana yana da wasu halaye masu kyau. Yi la’akari da labarinsa na annabi.
7. A wane yanayi ne Yunana ya yi wa Jehovah hidima a Isra’ila, ta yaya sanin wannan ya shafi ra’ayinka game da shi?
7 Yunana ya yi aiki tuƙuru da aminci a Isra’ila, yanki da ba masu saurara. Annabi Amos, wanda ya rayu kusan lokaci ɗaya da Yunana, ya kwatanta Isra’ilawa na lokacin masu son annashuwa.b Miyagun abubuwa suna faruwa a ƙasar, amma Isra’ilawa sun ƙyale waɗannan abubuwa. (Amos 3:13-15; 4:4; 6:4-6) Duk da haka, Yunana cikin aminci ya yi aikinsa na yi musu wa’azi a kai a kai. Idan kai mai shelar bishara ne, ka san yadda yake da wuya a yi wa mutane da suke da kome da ba sa son su ji saƙon magana. Saboda haka, bayan mun yarda da kasawar Yunana, kada mu manta da halayensa na aminci da jimiri sa’ad da ya yi wa Isra’ilawa marasa bangaskiya wa’azi.
8. Wane ƙalubale yake jiran annabi Ba’isra’ile a Nineba?
8 Aiki ya je Nineba ƙalubale ne mai wuya. Don ya isa birnin, Yunana zai yi tafiya na mil 500 a ƙar—tafiya mai wuya da za ta ɗauki misalin wata guda. In ya isa birnin, annabin zai yi wa Assuriyawa da aka san su da zalunci wa’azi. Gana wa mutane azaba ɓangare ne na yaƙe-yaƙensu. Suna ma alfahari da zaluncinsu. Ba abin mamaki ba ne da aka kira Nineba “birni mai-jini”!—Nahum 3:1, 7.
9. Sa’ad da hadari mai tsanani ya razane matuƙan jirgin, wane hali Yunana ya nuna?
9 Da yake ba ya son ya yi biyayya ga umurnin Jehovah, Yunana ya shiga jirgin ruwa da ya kai shi da nisa daga wajen aikinsa. Duk da haka, Jehovah bai fid da rai daga annabinsa ba ko kuma ya shirya wani ya ɗauki matsayinsa. Maimako, Jehovah ya yi ƙoƙari ya taimaki Yunana ya ga muhimmancin aikinsa. Allah ya sa hadari ya taso a tekun. Raƙumin ruwa ya soma jujjuya jirgin ruwa da Yunana ke ciki. Mutane marasa laifi suka kusa su halaka, domin Yunana! (Yunana 1:4) Yaya Yunana zai yi? Tun da yake ba ya son matuƙan jirgin su yi hasarar rayukansu dominsa, Yunana ya gaya musu: “Ku ɗauke ni, ku jefa ni cikin teku; da hakanan teku za ya yi muku sauƙi ya kwanta.” (Yunana 1:12) Sa’ad da a ƙarshe matuƙan jirgin suka jefa shi cikin ruwa, ba shi da dalilin tunanin cewa Jehovah zai cece shi daga tekun. (Yunana 1:15) Amma, Yunana a shirye yake ya mutu don kada matuƙan jirgin su mutu. Ba mu ga halin gaba gaɗi, tawali’u da ƙauna ba a nan?
10. Menene ya faru bayan da Jehovah ya sake ba Yunana aiki?
10 A ƙarshe, Jehovah ya ceci Yunana. Abin nan da Yunana ya yi ya sa ne bai cancanci bauta wa Allah kuma a matsayin wakilinsa ba? A’a, Jehovah cikin jinƙai da ƙauna ya sake ba wa annabin aikin wa’azi ga mutanen Nineba. Sa’ad da Yunana ya isa Nineba, da gaba gaɗi ya gaya wa mazaunan cewa Allah ya lura da muguntarsu kuma za a halaka birninsu cikin kwana 40. (Yunana 1:2; 3:4) Bayan sun saurari saƙon da Yunana ya bayar kai tsaye, mutanen Nineba suka tuba, kuma ba a halaka birninsu ba.
11. Menene ya nuna cewa Yunana ya koyi darasi mai kyau?
11 Yunana har ila ra’ayinsa bai dace ba. Amma ta wurin darasi Jehovah cikin haƙuri ya taimaki Yunana ya koyi cewa yana duba fiye da yadda mutum yake a waje. Yana bincika zuciya. (Yunana 4:5-11) An ga cewa Yunana ya koyi darasi mai kyau daga labari na gaskiya da ya rubuta da kansa. Rubuta kasawarsa haɗe da abubuwar kunyatarwa ya ƙara ba da tabbaci na tawali’unsa. Yana bukatar gaba gaɗi don mutum ya amince da kuskurensa!
12. (a) Ta yaya muka sani cewa Yesu yana ganin mutane yadda Jehovah yake ganinsu? (b) An ƙarfafa mu mu kasance da wane ra’ayi wajen mutane da muke musu wa’azin bishara? (Dubi akwati a shafi na 12)
12 Ƙarnuka bayan haka, Yesu Kristi ya yi furci mai ƙarfafawa game da abin da ya faru a rayuwar Yunana. Ya ce: “Kamar yadda Yunana yana cikin cikin babban kifi na teku yini uku da kwana uku; hakanan kuma Ɗan mutum za ya yi yini uku da kwana uku cikin zuciyar ƙasa.” (Matta 12:40) Bayan Yunana ya tashi daga matattu, zai koyi cewa Yesu ya gwada lokacin da yake cikin kabari da lokacin da annabin ba ya aiki a rayuwarsa. Ba ma farin cikin bauta wa Allah da ba ya ƙin bayinsa sa’ad da suka yi kuskure? Mai Zabura ya rubuta: “Kamar yadda uba ya kan yi juyayin ’ya’yansa, hakanan Ubangiji yana juyayin masu-tsoronsa. Gama ya san tabi’ammu; Ya kan tuna mu turɓaya ne.” (Zabura 103:13, 14) Hakika, wannan “turɓaya”—haɗe da mutane ajizai a yau—za su iya cim ma abu mai yawa da taimakon ruhu mai tsarki na Allah!
Daidaitaccen Ra’ayi Game da Bitrus
13. Waɗanne halayen Bitrus za mu iya tuna da su, amma me ya sa Yesu ya zaɓe shi manzo?
13 Yanzu bari mu ɗan bincika misali na biyu, manzo Bitrus. Idan an ce ka kwatanta Bitrus, za ka yi saurin cewa mai aikata abu ne bisa motsin rai, har ma mai girman kai? Bitrus ya nuna irin waɗannan halaye a wasu lokatai. Amma, da Yesu zai zaɓi Bitrus ya kasance ɗaya cikin manzanninsa 12 idan Bitrus da gaske mai zafin rai ne, da yake aikata abu bisa motsin rai, ko kuma mai girman kai? (Luka 6:12-14) Ko kaɗan! Yesu ya ƙyale waɗannan kasawa kuma ya lura da halayen Bitrus masu kyau.
14. (a) Me zai yi bayanin abin da ya sa Bitrus ne yake fara yin magana? (b) Me ya sa za mu yi godiya cewa Bitrus yana tambayoyi a kai a kai?
14 Bitrus wani lokaci mai magana ne a madadin sauran manzannin. Wasu za su ɗauki wannan cewa rashin filako ne. Amma haka ne? Wasu mutane sun ce Bitrus ya girme wasu manzanni—wataƙila ma ya girme Yesu kansa. Idan haka ne, wannan zai iya taimaka a bayyana dalilin da ya sa Bitrus sau da yawa shi yake fara magana. (Matta 16:22) Duk da haka, akwai wani abu da za a bincika. Bitrus mutumi ne mai ruhaniya. Yadda yake son ya sami sani ne yake motsa shi ya yi tambayoyi. Mun amfana daga tambayoyinsa. Yesu ya yi furci masu tamani wajen amsa tambayoyin Bitrus, kuma an yi ajiyar waɗannan cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, da yake amsa tambayar da Bitrus ya yi ne Yesu ya yi maganar “wakili mai-aminci.” (Luka 12:41-44) Ka yi tunanin tambayar da Bitrus ya yi: “Mun bar abu duka, mun bi ka; me za mu samu fa?” Wannan ya sa Yesu ya yi alkawari mai ƙarfafawa: “Kowanene ya bar gidaje, ko ’yan’uwa maza, ko ’yan’uwa mata, ko uba, ko uwa, ko ’ya’ya, ko ƙasashe, sabili da sunana, za ya sami riɓi ɗari; za ya kuma gāji rai na har abada.”—Matta 15:15; 18:21, 22; 19:27-29.
15. Me ya sa za a ce Bitrus mai aminci ne da gaske?
15 Bitrus yana da wani hali mai kyau—mai aminci ne. Sa’ad da almajiran da yawa suka daina bin Yesu domin ba su fahimci wata koyarwarsa ba, Bitrus ne ya yi magana babu ɓata lokaci a madadin manzanni 12 ya ce: “Ubangiji, a wurin wa za mu tafi? kai ne da maganar rai na har abada.” (Yohanna 6:66-68) Lallai waɗannan kalmomin sun daɗaɗa wa Yesu rai! Bayan haka, sa’ad da taron suka zo su kama Ubangijin, yawancin manzannin suka gudu. Amma, Bitrus ya bi taron da ɗan nisa kuma ya shiga har cikin farfajiyar babban firist. Gaba gaɗi, ba tsoro ba ne ya sa ya je wajen. Sa’ad da ake yi wa Yesu tambayoyi, Bitrus yana tare da Yahudawa da suke ɗuma kansu kusa da wuta. Ɗaya cikin bayin babban firist ya gane shi kuma tuhume shi da cewa yana tare da Yesu. Hakika, Bitrus ya musanci sanin Ubangijinsa, amma kada mu manta cewa aminci ne kuma ya damu da Yesu ya sa Bitrus cikin wannan mummunar yanayi, yanayi da yawancin manzannin ba su da gaba gaɗin fuskantarsa.—Yohanna 18:15-27.
16. Domin wane dalili ne muka bincika halayen Yunana da Bitrus masu kyau?
16 Halayen Bitrus masu kyau sun fi kasawarsa. Haka wannan yake game da Yunana. Yadda muka lura da Yunana da Bitrus da kyau fiye da yadda dama za mu yi, haka nan ma dole mu koyar da kanmu mu kasance da ra’ayi mai kyau a yadda muke ganin ’yan’uwanmu na ruhaniya na zamani. Yin haka zai sa mu kasance da nasaba mai kyau da su. Me ya sa ake bukatar wannan?
Amfani da Darasin a Yau
17, 18. (a) Me ya sa jayayya za ta taso tsakanin Kiristoci? (b) Wane gargaɗi na Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu warware matsaloli da ’yan’uwa masu bi?
17 Maza, mata, da yara daga dukan matsayi na tattalin arziki da ƙabila suna bauta wa Jehovah cikin haɗin kai a yau. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10) Muna da mutuntaka dabam dabam a cikin ikilisiyar Kirista a yau! Da yake muna bauta wa Allah tare, babu makawa cewa jayayya za ta taso a wasu lokatai.—Romawa 12:10; Filibbiyawa 2:3.
18 Ko da yake muna ganin kasawar ’yan’uwanmu, ba ma nacewa a kansu. Mu yi ƙoƙari mu yi koyi da Jehovah, game da wanda mai Zabura ya rera: “Idan kai, ya Ubangiji, za ka ƙididdiga laifofi, wa za ya tsaya, ya Ubangiji?” (Zabura 130:3) Maimakon mai da hankali a kan halaye da zai raba mu, mu “bi waɗannan abu fa da ke nufa wajen salama, da abubuwa waɗanda za mu gina junanmu da su.” (Romawa 14:19) Muna ƙoƙari mu ga mutane yadda Jehovah yake ganinsu, muna ƙyale kasawarsu mu mai da hankali a kan halayensu masu kyau. Sa’ad da muka yi haka, zai taimaka mana mu yi “haƙuri da juna.”—Kolossiyawa 3:13.
19. Ka faɗi wasu matakai masu kyau da Kirista zai ɗauka ya warware jayayya mai tsanani.
19 Idan jayayyar da ba za mu iya manta ba a zuciyarmu ta taso fa? (Zabura 4:4) Wannan ya taɓa faru a tsakaninka da wani ɗan’uwa mai bi? Me ya sa ba za ka yi ƙoƙari ka warware batun ba? (Farawa 32:13-15) Na farko, ka yi wa Jehovah addu’a, ka nemi ja-gorarsa. Sa’an nan da halayen mutumin masu kyau a zuciyarka, ka je wajensa “cikin tawali’u na hikima.” (Yaƙub 3:13) Ka gaya masa kana son ku sulhunta. Ka tuna da huraren gargaɗi: “Yi hanzarin ji, shi yi jinkirin yin magana, shi yi jinkirin yin fushi.” (Yaƙub 1:19) Gargaɗi ka “yi jinkirin yin fushi” na nuna cewa wani zai iya yin wani abu ko ya faɗi wani abin da zai sa ka fushi. Idan hakan ya faru, ka nemi taimakon Jehovah ka kame kanka. (Galatiyawa 5:22, 23) Ka bari ɗan’uwanka ya faɗi ɓacin ransa, kuma ka saurara da kyau. Kada ka katse masa hanzari, ko ma ba ka yarda da dukan abin da ya ce ba. Wataƙila ra’ayinsa ba daidai ba ne, amma duk da haka ra’ayinsa ke nan. Ka yi ƙoƙari ka ga matsalar yadda yake gani. Wannan na nufin bincika kanka daga ra’ayin ɗan’uwanka.—Misalai 18:17.
20. Sa’ad da muke warware jayayya, waɗanne matakai suke taimaka ga sulhuntawa?
20 Sa’ad da ya kai lokacin da za ka yi magana, ka yi magana mai zaƙi. (Kolossiyawa 4:6) Ka gaya wa ɗan’uwanka abin da kake so game da shi. Ka nemi gafara a duk abin da ka yi da ya jawo jayayyar. Idan ƙoƙarinka cikin tawali’u ya sa kuka sulhunta, ka gode wa Jehovah. Idan ba haka ba, ka ci gaba da neman ja-gorar Jehovah yayin da kake neman zarafin sulhuntawa.—Romawa 12:18.
21. Ta yaya wannan darasi ya taimaka maka ka ɗauki wasu yadda Jehovah yake ɗaukansu?
21 Jehovah yana ƙaunar dukan bayinsa. Yana farin cikin yin amfani da dukanmu cikin hidimarsa duk da ajizancinmu. Yayin da muka ƙara koya game da yadda yake ganin wasu, ƙaunarmu game da ’yan’uwanmu za ta ƙaru. Idan ƙaunarmu ga Kirista mai bi ta yi sanyi, za a iya somawa kuma. Za mu sami albarka mai yawa idan mun ƙudura niyya mu yi ƙoƙari mu nuna ra’ayi mai kyau game da wasu—hakika, muna ɗaukansu yadda Jehovah yake ɗaukansu!
[Hasiya]
a Daga baya ya bayyana cewa kyakkyawa Eliyab ba shi da halaye da ake bukata don sarki da ya dace na Isra’ila. Sa’ad da Bafilisti Goliath ya ƙalubalanci Isra’ilawa a yaƙi, Eliyab, da sauran mazan Isra’ila suka tsorata.—1 Samu’ila 17:11, 28-30.
b Domin wasu muhimman yaƙi da aka ci nasara da maido da yanki na dā da kuma haraji da aka tara ta haka, Jeroboam na ll babu shakka ya ƙara arzikin masarauta ta arewa.—2 Samu’ila 8:6; 2 Sarakuna 14:23-28; 2 Labarbaru 8:3, 4; Amos 6:2.
Ta Yaya Za Ka Amsa?
• Yaya Jehovah yake ɗaukan kasawar bayinsa masu aminci?
• Waɗanne halaye masu kyau na Yunana da Bitrus za ka iya lissaftawa?
• Wane ra’ayi ne game da ’yan’uwanka Kiristoci ka ƙudura niyyar ka riƙe?
[Akwati a shafi na 12]
Ka Yi Tunanin Yadda Allah Yake Ɗaukan Wasu
Yayin da kake bimbini a kan labarin Yunana na Littafi Mai Tsarki, ka ga kana bukatar ka sake duban mutane da kake yi wa wa’azin bishara a kai a kai? Za su bayyana sun gamsu ko ba sa son saƙon kamar Isra’ilawa, ko kuma su yi hamayya da saƙon Allah. Duk da haka, yaya Jehovah Allah yake ɗaukansu? Har wasu mutane ma da suka shahara a wannan zamani wata rana za su juya wurin Jehovah, yadda sarkin Nineba ya tuba domin wa’azin Yunana.—Yunana 3:6, 7.
[Hoto a shafi na 9]
Kana ɗaukan wasu yadda Jehovah yake ɗaukansu?
[Hoto a shafi nas 10, 11]
Yesu ya ga abu mai kyau da zai ce game da labarin Yunana