Neman Gafara—Hanya Ce Mai Kyau na Samun Salama
“NEMAN gafara yana da kyau. Yana warware matsala ba tare da faɗa ba, gyara wariya tsakanin al’ummai, kuma yana sa gwamnati ta yarda da wahalar talakawanta, kuma ta daidaita dangantaka.” Haka Deborah Tannen ta rubuta, mawallafiya da ake yawan sayan littattafanta kuma masaniyar rayuwar jama’a a Jami’ar Georgetown a Washington D.C.
Littafi Mai Tsarki ya tabbatar da cewa neman gafara da gaske sau da yawa shi ne hanyar gyara dangantaka da ta lalace. Alal misali, a almarar Yesu na ɗa almubazzari, sa’ad da ɗan ya dawo gida ya nemi gafara, ubansa ya yi matuƙar farin cikin karɓansa. (Luka 15:17-24) Hakika, mutum bai kamata ya kasance mai yawan fahariya ba, ya tattake fahariyarsa ya ba da haƙuri, ya kuma nemi gafara. Ga mutane masu gaskiya masu tawali’u, neman gafara ba abu ba ne mai wuya.
Matsayin Neman Gafara
Abigail, mace mai hikima a Isra’ila ta dā, ta nuna misalin matsayin neman gafara, ko da yake ta nemi gafara ne domin laifin da mijinta ya yi. Sa’ad da suke da zama cikin daji, Dauda, wanda daga baya ya zama sarkin Isra’ila, tare da dakarunsa suka kāre tumakin Nabal, mijin Abigail. Duk da haka, da samarin Dauda suka nemi gurasa da ruwa, Nabal ya kore su da baƙar magana. Domin Dauda ya fusata, ya je da mutane wajen 400 ya tare wa Nabal da gidansa. Da ta fahimci yanayin, Abigail ta fita ta tare Dauda. Da ta gan shi, ta durƙusa a gabansa. Sai ta ce: “Ya ubangijina laifin nan a kaina ya ke, a kaina: ina roƙonka kuma ka bar baiwarka ta yi magana a kunnenka, ka ji maganar baiwarka kuma.” Sai Abigail ta yi bayani game da yanayin kuma ta ba wa Dauda kyautar abinci da abin sha. Bayan haka, ya ce: “Ki isa gidanki lafiya: ga shi, na saurari muryarki, na kuwa dubi girmanki.”—1 Samu’ila 25:2-35.
Halin tawali’u na Abigail da kuma kalmominta na neman gafara domin mugun halin mijinta ya ceci gidanta. Dauda har ya yi mata godiya domin kāre shi da ta yi daga ɗaukan alhakin jini. Ko da yake ba Abigail ba ce ta yi wa Dauda mugun hali, ta ɗauki laifin iyalinta kuma ta nemi yin salama da Dauda.
Wani mutum kuma da ya san lokacin da ya kamata ya nemi gafara manzo Bulus ne. Akwai lokacin da dole ne ya kāre kansa daga Majalisa, babban kotun Yahudawa. Da Ananiyas babban firist ya fusata domin kalmomi masu gaskiya na Bulus, ya ba da umurni ga waɗanda suke kusa da Bulus su mari bakinsa. Sai Bulus ya ce masa: “Allah za ya buge ka, kai farantacen bango: kana zaune garin yi mini shari’a bisa ga Attaura, kana kuwa umurta a buge ni saɓanin Attaura?” Da ’yan kallo suka tuhume shi cewa yana zagin babban firist, manzon bai ɓata lokaci ba ya ɗauki laifinsa, yana mai cewa: “Ban san shi ne babban malamin ba, ’yan’uwa: gama an rubuta, Kada ka ambaci shugaban jama’arka da mugunta.”—Ayukan Manzanni 23:1-5.
Abin da Bulus ya faɗa—cewa wanda aka naɗa alƙali bai kamata ya koma yana nuna ƙarfi ba—daidai ne. Duk da haka, ya nemi gafara daga maganar da ya yi wa babban firist da za a iya ɗauka rashin ladabi ne.a Neman gafara da Bulus ya yi ya ba da zarafin da Majalisar ta saurari abin da zai faɗa. Tun da Bulus yana sane da jayayya da take tsakanin ’yan majalisar, ya ce musu ana tuhumarsa ne domin imaninsa ga tashin matattu. Daga baya, rashin jituwa ya auko, Farisawa suka goyi bayan Bulus.—Ayukan Manzanni 23:6-10.
Me za mu koya daga waɗannan misalai biyu na Littafi Mai Tsarki? A dukan yanayi biyun, furci na tuba da gaske sun ba da zarafin tattaunawa. Saboda haka kalmomin neman gafara za su iya taimakonmu mu samu salama. Hakika, yarda da kurakuranmu da kuma neman gafara domin laifi da muka yi zai iya ba da zarafi domin tattaunawa.
‘Amma Babu Laifi da Na Yi’
Idan muka lura cewa wani ya yi fushi domin abin da muka ce ko kuma muka yi, muna iya ɗaukan cewa mutumin ya cika fahariya ko kuma ya cika damuwa. Duk da haka, Yesu Kristi ya shawarci almajiransa: “Idan fa kana cikin miƙa baiwarka a wurin bagadi, can ka tuna ɗan’uwanka yana da wani abu game da kai, sai ka bar baiwarka can a gaban bagadi, ka yi tafiyarka, a sulhuntu da ɗan’uwanka tukuna, kāna ka zo ka miƙa baiwarka.”—Matta 5:23, 24.
Alal misali, ɗan’uwa zai ga cewa ka yi masa laifi. A irin wannan yanayin, Yesu ya ce kai za ka je ka “sulhuntu da ɗan’uwanka,” ko kana ganin ka yi masa laifi ko babu. Bisa ga ayar a Helenanci, kalmar da Yesu ya yi amfani da ita a nan ‘na nufin sulhunta bayan an yi gāba.’ (Vine’s Expository Dictionary of Old and New Testament Words) Hakika, idan mutane biyu ba su jitu da juna ba, zai kasance dukansu suna da ɗan laifi, tun da dukansu ajizai ne kuma suna iya yin laifi. Wannan hakika yana bukatar sulhu.
Wannan batun ba waye yake da laifi, waye ba shi da laifi ba, amma waye zai yi amfani da zarafi ya nemi salama. Sa’ad da manzo Bulus ya lura cewa Kiristoci a Koranti suna ƙarar ’yan’uwansu bayin Allah a kotu, a kan wasu rashin jituwa game da kuɗi, ya yi musu gyara: “Ba gwamma a yi haƙuri da zalunci ba? Ba gwamma ku jimre da ƙwace ba?” (1 Korinthiyawa 6:7) Ko da yake Bulus ya yi gargaɗi ne game da Kiristoci kada su riƙa ƙarar juna a kotu, ƙa’idar a bayyane take sarai: Salama tsakanin ’yan’uwa masu bi ta fi muhimmanci da tabbatar wannan ne mai laifi wannan ne ba shi da laifi. Tuna wannan mizanin zai sa ya yi sauƙi a nemi gafara domin laifi da wani ya yi tunanin an yi masa ko kuma mata.
Ana Bukatar Sahihanci
Wasu mutane kuma, suna amfani da kalmomin da ake amfani da su domin neman gafara. Alal misali, a Japan, kalmar nan sumimasen, ana amfani da ita wajen ba da haƙuri, an ji ta sau dubbai. Ana iya amfani da ita wajen furta godiya, tana nuna rashin farin ciki domin ba za a iya saka alheri da aka yi ba. Domin yanayin ta, wasu za su iya jin cewa ana yawan amfani da wannan kalmar kuma suna mamaki ko waɗanda suke amfani da ita da gaske suke. Wasu kalmomin neman gafara za su iya kasancewa ana yawan amfani da su a wasu al’adu ma.
A kowanne harshe, yana da muhimmanci mu ba da haƙuri da gaske. Furci da kuma murya ya kamata su nuna sahihancinmu. Yesu Kristi ya koyar da almajiransa a Huɗuba bisa Dutse cewa: “Bari zancenku ya zama, I, i; da A’a, a’a: abin da ya wuce waɗannan duka daga wurin Mugun ne.” (Matta 5:37) Idan ka ba da haƙuri, ka yi shi da gaske! Alal misali: Wani mutum da yake layi a kantar masu shigowa a tashar jirgin sama ya ba wa wata mata da take bayansa haƙuri domin kayansa ya ture ta. Bayan wasu ’yan mintoci, bayan layin ya yi gaba, jakarsa ta sake taɓa matar. Mutumin ya sake ba da haƙuri. Sa’ad da abin ya sake faruwa, abokin tafiyar matar ya ce wa mutumin ko ya tabbata da gaske yake, ya tabbata cewa jakarsa kar ta sake taɓa matar. Hakika, ƙudurin kada a sake yin wannan laifi ya kamata ya biyo bayan neman gafara.
Idan da gaske muke, ba da haƙuri zai haɗa da yarda da laifinmu, neman gafara, da kuma ƙoƙarin mu gyara abin da muka ɓata yadda zai yiwu. Hakanan kuma, wanda aka yi wa laifi ya kamata ya gafarci mai laifin. (Matta 18:21, 22; Markus 11:25; Afisawa 4:32; Kolossiyawa 3:13) Tun da dukan mutane ajizai ne, sulhu ba zai tafi sumul ba ko da yaushe. Duk da haka, kalmomin neman gafara suna da iko a neman salama.
Sa’ad da Bai Dace a Nemi Gafara Ba
Ko da yake neman gafara yana iya kawo salama, mutum mai hikima yana guje wa yin amfani da kalmomi sa’ad da bai dace a yi haka ba. Alal misali, a ce, batun ya shafi aminci ga Allah. Sa’ad da Yesu yake duniya, “ya ƙasƙantarda kansa, ya zama yana biyayya har da mutuwa, i, har mutuwa [a kan gungumen azaba].” (Filibbiyawa 2:8) Amma bai ba da haƙuri ba game da imaninsa domin a kawar da wahalarsa. Kuma Yesu bai ba da haƙuri ba sa’ad da babban firist ya bukaci haka: “Na gama ka da Allah mai-rai, ka faɗa mana, ko kai Kristi ne Ɗan Allah.” Maimakon ya ba da haƙuri, Yesu ya amsa cikin gaba gaɗi: “Ka faɗi: amma ina ce muku, Gaban nan za ku ga Ɗan mutum a zaune ga hannun dama na iko, yana zuwa kuma bisa gizagizan sama.” (Matta 26:63, 64) Bai taɓa mai da hankali ga neman salama da babban firist sa’an nan ya ƙyale aminci ga Ubansa, Jehovah ba.
Kiristoci suna ladabi ga waɗanda suke da iko. Duk da haka, ba sa ba da haƙuri domin biyayyarsu ga Allah da kuma domin ƙaunar ’yan’uwansu.—Matta 28:19, 20; Romawa 13:5-7.
Babu Cikas ga Salama
A yau, muna yin kuskure ne domin mun gaji ajizanci daga wajen kakanmu Adamu. (Romawa 5:12; 1 Yohanna 1:10) Yanayin ajizanci na Adamu domin tawayensa ne ga Mahalicci. Ko da yake, a asali, Adamu da Hauwa’u kamilai ne, kuma Allah ya yi alkawari zai mai da mutane zuwa wannan yanayi na kamilcewa. Zai kawar da zunubi da kuma abin da yake jawowa.—1 Korinthiyawa 15:56, 57.
Ka yi tunanin abin da wannan yake nufi! A gargaɗinsa game da yin amfani da harshe, ɗan’uwan Yesu Yaƙub ya ce: “Idan wani ba ya yi tuntuɓe ga wajen magana ba, wannan cikakken mutum ne, mai-ikon sarrafa dukan jiki kuma.” (Yaƙub 3:2) Mutum kamili zai iya kame bakinsa da ba zai bukaci neman gafara domin kuskure da harshensa ba. Zai iya ‘sarrafa dukan jikinsa.’ Lallai zai kasance da ban sha’awa sa’ad da muka zama kamilai! Sannan, ba zai zama tangarɗa ga salama tsakanin mutane ba. Amma a yanzu, neman gafara da gaske domin laifi da muka yi zai iya kawo salama.
[Hasiya]
a Zai iya kasance domin yanayin idanun Bulus ne ya sa bai gane babban firist ɗin ba.
[Hoto a shafi na 5]
Menene za mu koya daga misalin Bulus?
[Hoto a shafi na 7]
Sa’ad da kowa ya zama kamili, babu cikas ga salama