Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 11/1 pp. 3-4
  • Me Ya Sa Yake da Wuya a Nemi Gafara?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Yake da Wuya a Nemi Gafara?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Ya Dace In Nemi Gafara?
    Tambayoyin Matasa
  • Neman Gafara—Hanya Ce Mai Kyau na Samun Salama
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Me Zan Yi Idan Na Taka Dokar Iyayena?
    Tambayoyin Matasa
  • Idan Zuciyata Tana Damu Na, Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Min?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 11/1 pp. 3-4

Me Ya Sa Yake da Wuya a Nemi Gafara?

A YULI na shekara ta 2000, Majalisar dokoki na Jihar California a Amirka ta miƙa doka da aka tsara ta domin ta sauƙaƙa wa mutane idan suka nuna tausayi ga mutumin da ya ji rauni a haɗarin motar da su suke cikinta. Me ya sa aka kafa dokar? Kamar yadda aka lura yayin da haɗari ya jawo rauni ko kuma hasara, mutane sau da yawa suna jinkirin neman gafara domin kada a ce sune da laifi idan suka je kotu. A wani ɓangaren kuma, waɗanda suke jin ya kamata a nemi gafara a wurinsu babu ɓata lokaci sai su yi fushi, sai ka ga ɗan haɗari ya jawo babbar magana.

Hakika, ba dole ba ne ka nemi gafara a kan haɗarin da ba laifinka ba ne. Kuma da akwai lokatai da abin da ya fi shi ne ka mai da hankali game da abin da kake faɗa. Wani tsohon karin magana ya ce: “A cikin yawan maganganu ba a rasa saɓo ba: amma wanda ya iya ma bakinsa aikin hikima ya ke yi.” (Mis. 10:19; 27:12) Duk da haka, za ka iya kasancewa mai gaba gaɗi da ban taimako.

Amma ba gaskiya ba ne cewa mutane da yawa sun daina neman gafara, ko ma idan babu batun da ya shafi kotu? A gida, mace wataƙila ta ce, ‘Mijina ba ya neman gafara.’ A wurin aiki wataƙila homan ya ce, ‘Ma’aikatana ba sa yarda da kuskurensu, da ƙyar suke neman gafara.’ A makaranta malami wataƙila ya ba da rahoton cewa, “Ba a koyar da yara su nemi izini ba.”

Dalilin da ya sa mutane suke jinkirin neman gafara shi ne suna tsoron kada a ƙi su. Tunanin za a ware shi yana damunsa, ba zai iya ya furta yadda yake ji ba. Hakika, mutumin da aka yi wa laifi wataƙila ya guji mai laifin, ya sa sulhuntawa ta yi wuya ƙwarai.

Halin babu ruwana shi ne wani dalilin da ya sa wasu suke jinkirin su nemi gafara. Wataƙila su sa ka a zuciyarsu, ‘Neman gafara ba zai gyara kuskure da na riga na yi ba.’ Har ila, wasu suna jinkirin neman gafara domin sakamakon hakan. Zai ce, ‘Za a ɗora mini laifi ne kuma a ce in biya diyya?’ Amma, babban matsalar ƙin laifi ita ce fahariya. Mutumin da fahariya ta yi masa yawa ba zai iya cewa “a gafarce ni ba” domin zai yi tunanin cewa, ‘ba na son in yar da darajata, ta ɗaukan nauyin kuskure da na yi. Wannan zai rage mini girma.’

Ko dalilin menene ne, mutane da yawa suna iske shi da wuya su furta kalmomin neman gafara. Amma ya wajaba ne mutane su nemi gafara? Wane amfani neman gafara yake da shi?

[Hoto a shafi na 3]

“Ba a koyar da yara su nemi izini ba”

[Hoto a shafi na 3]

“Ma’aikatana ba sa yarda da kuskurensu”

[Hoto a shafi na 3]

“Mijina ba ya neman gafara”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba