“Ku Yi Tsayayya Da Iblis”
“Ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya fa guje muku.”—YAƘUB 4:7.
1. Me za a ce game da wannan duniyar, kuma me ya sa shafaffu tare da abokansu suke bukatar su kasance a farke?
“ALLAH ya ɓāce Iblis ne yake nan.” Waɗannan kalmomi na mawallafi ɗan Faransa, André Malraux sun dace da duniyar da muke cikinta a yau. Ayyukan mutane suna nuna dabarun Iblis fiye da na nufin Allah. Shaiɗan yana ɓatar da mutane “da dukan iko da alamu da al’ajabai na ƙarya, da dukan ruɗami na rashin adalci domin waɗanda su ke halaka.” (2 Tassalunikawa 2:9, 10) Amma a waɗannan “kwanaki na ƙarshe,” a kan bayin Allah da suka keɓe kansu, Kiristoci shafaffu, “waɗanda su ke kiyaye da dokokin Allah, suna riƙe da shaidar Yesu” ne, Shaiɗan yake mai da hankali da ƙoƙarce-ƙoƙarcensa. (2 Timothawus 3:1; Ru’ya ta Yohanna 12:9, 17) Waɗannan Shaidu tare da abokansu da suke da begen rayuwa a duniya suna bukatar su kasance a farke.
2. Ta yaya Shaiɗan ya ruɗi Hauwa’u, kuma tsoro game da menene manzo Bulus ya furta?
2 A kowacce hanya dai, Shaiɗan mai ruɗi ne. Ya yi amfani da maciji, ya ruɗi Hauwa’u ta yi tunanin cewa za ta samu farin ciki mai yawa ta wajen neman ’yancin kai daga Allah. (Farawa 3:1-6) Shekara 400 bayan haka, manzo Bulus ya furta tsoronsa kada Kiristoci shafaffu a Koranti su jarabtu ta dabarar Shaiɗan. Bulus ya rubuta: “Ina jin tsoro, kamar yadda maciji ya ruɗi Hauwa’u da wayonsa, hakanan kuma azancinku ya ɓaci da ko ƙaƙa daga sahihanci da tsabta da ke wajen Kristi.” (2 Korinthiyawa 11:3) Shaiɗan yana ɓata azantan mutane kuma ya dagula tunaninsu. Kamar yadda ya ruɗi Hauwa’u, zai iya sa Kiristoci su yi tunanin da ba na kirki ba kuma su yi tsammanin cewa za su samu farin ciki daga yin abin da Jehovah da Ɗansa ba su yarda da shi ba.
3. Wace kāriya daga Iblis Jehovah yake tanadinta?
3 Za a iya gwada Shaiɗan da mafaraucin tsuntsu da ya ɗana tarko da zai kama marar lura. Domin mu guji tarkunan Shaiɗan, muna bukatar mu ‘zauna cikin sitiran Maɗaukaki,’ wajen kāriya ta alama da Jehovah ya yi tanadinsa wa waɗanda suka miƙa kai ga ikonsa na mallaka a abin da suke yi. (Zabura 91:1-3) Muna bukatar dukan kāriya da Allah yake tanadinsa ta wurin Kalmarsa, ruhunsa, da kuma ƙungiyarsa domin mu “sami ikon da za [mu] yi tsayayya da dabarun Shaiɗan.” (Afisawa 6:11) Babu shakka, Iblis yana amfani da dabaru da yawa a ƙoƙarinsa ya kama bayin Jehovah.
Tarkunan da Shaiɗan Ya Ɗana wa Kiristoci na Farko
4. A wace irin duniya ce Kiristoci na farko suka rayu?
4 Kiristoci da suka rayu a ƙarnuka na farko da na biyu A.Z., sun rayu ne a lokacin da Daular Roma ta kai ƙolin bunƙasarta. Pax Romana (Salamar Romawa) ta sa kasuwanci ya bunƙasa ƙwarai. Wannan ni’imar ta sa masu mulki su samu sukuni, kuma suka ga ya dace jama’a su samu nishaɗi da yawa domin kada su yi tawaye. A wasu shekaru ma, kwanakin hutu suna da yawa kamar kwanakin da ake zuwa aiki. Shugabannan suka buɗe wa jama’a wuraren liyafa, suna shafa wa jama’a mai a leɓa, sa’an nan su ɗimauce hankalinsu.
5, 6. (a) Me ya sa bai dace ba Kiristoci su dinga zuwa ɗakunan wasanni ko kuma filin wasanni na Romawa? (b) Wace dabara ce Shaiɗan ya yi amfani da ita, kuma ta yaya Kiristoci za su guji wannan?
5 Irin wannan yanayin haɗari ne kuwa ga Kiristoci na farko? Daga rubuce-rubucen gargaɗi da marubuta bayan manzanni suka rubuta, kamarsu Tertullian, yawancin ayyukan nishaɗi a lokacin sun cika da haɗari na ruhaniya da kuma na ɗabi’a ga Kiristoci na gaskiya. Mafi muni ma, yawancin bukukuwan jama’a da kuma wasanni, ana yin su ne domin su girmaman allolin arna. (2 Korinthiyawa 6:14-18) A manyan ɗakunan wasa, har ma da akwai wasannin da wai na al’adu, idan ba na lalata tsantsa na zubar da jini ba ke nan. Da shigewar lokaci, jama’a ta daina marmarin wasannin al’adun, sai aka sake su da wasannin kwaikwayo na lalata tsantsa. A cikin littafinsa Daily Life in Ancient Rome, ɗan tarihi Jérôme Carcopino ya ce: “A cikin waɗannan wasannin ana yarda wa ’yan wasa su tuɓe su yi tsindir . . . Ana zubar da jini sosai. . . . [Wasannin] sun ɗauki wuri mai yawa ƙwarai har da ya sha kan jama’ar daular. Ba sa ƙyamar irin waɗannan kwaikwayon domin zubar da jini da ake yi cikin ɗakunan wasan, da daɗewa ya taurara su kuma sun sangarta a tunaninsu.”—Matta 5:27, 28.
6 A cikin ɗakunan wasa, mafāɗa suna fāɗa da juna har mutuwa, ko kuma su yi fāɗa da dabbobin daji, su kashe dabbobin ko dabbobin su kashe su. Masu laifi da aka yi musu hukuncin kisa, da kuma Kiristoci da yawa ana zuba su ga dabbobin daji. Har a lokatan farko ma, dabarar Shaiɗan ta taurarar da ƙyamar da mutane suke wa lalata da nuna ƙarfi har waɗannan abubuwa suka gama gari mutane suka fara biɗansu. Hanyar da za su guji wannan tarkon ita ce su guji zuwan ɗakunan wasannin da kuma filin wasannin.—1 Korinthiyawa 15:32, 33.
7, 8. (a) Me ya sa zai zama wauta Kirista ya je wajen sukuwa? (b) Ta yaya Shaiɗan ya yi amfani da wankan Romawa don ya kama Kiristoci?
7 Sukuwa da ake yi a filayen sukuwa lallai sun kasance da kayatarwa, amma Kiristoci ba su amince da su ba saboda sau da yawa jama’a sukan ta da fāɗa. Marubuci na ƙarni na uku ya rubuta cewa wasu ’yan kallo sai su soma fāɗa, Carcopino kuma ya ce “masu duba da taurari da karuwai suna da wurin kasuwancinsu” a wasu ƙananan rumfa a filin wasan. Hakika, filayen sukuwar Romawa ba waje ba ne na Kiristoci.—1 Korinthiyawa 6:9, 10.
8 Me za a ce game da sanannen wankan Romawa? Hakika, wanka domin a kasance da tsabta ba laifi ba ne. Amma yawancin wajen wanka na Romawan manyan gine-gine ne da suke da ɗakunan matsa jiki, ɗakunan wasannin motsa jiki, ɗakunan caca, da kuma wuraren ci da sha. Ko da yake, yadda ya kamata, akwai lokatai da mata suke nasu wanka maza kuma su yi nasu, amma sau da yawa ana ƙyale maza da mata suna wanka tare. Clement na Iskandariya ya rubuta: “Maza da mata suna wanka tare ba ji ba gani; tsiraru yadda za su yi lalata.” A ta haka, wajen da aka kafa da izinin gwamnati, Shaiɗan ya mai da shi tarko ga Kiristoci. Masu hikima sun guji wurin.
9. Waɗanne tarkuna Kiristoci na farko suke bukatar su guje wa?
9 Caca hanyar shaƙatawa ce tsakanin mutanen sa’ad da Daular Roma take kan martabarta. Kiristoci na farko za su iya guje wa caca da ake yi a filayen sukuwa idan sun ƙi zuwa filayen. Ana caca ma a wasu ƙananan mahuta da kuma masauƙi. Masu wasan dara da duwatsu ko kuma ƙasusuwa da suke ɓoye wa abokan dararsu, suna zuba kuɗin cacar. Caca ta daɗa farin ciki ga rayuwar jama’ar, domin tana sa su yi zaton samun kuɗi hankali kwance. (Afisawa 5:5) Ban da haka, masu sayar da abin sha a waɗannan mashaya sau da yawa karuwai ne, wannan ya daɗa haɗarin lalata. Wasu ke nan cikin tarkunan da Shaiɗan ya sa wa Kiristoci da suke cikin biranen Daular Roma. Abubuwa sun bambanta ne a yau?
Tarkunan Shaiɗan a Yau
10. Yaya yanayi na yau ke kama da yanayin da ke a Daular Roma?
10 Galibi, dabarun Shaiɗan ba su canja ba a cikin dukan ƙarnuka. Domin kada “Shaiɗan ya ci ribar” Kiristoci da suke cikin birnin Koranti da ya cika da lalaci, manzo Bulus ya ba su gargaɗi mai tsanani. Ya ce: “Ba mu cikin rashin sanin makiɗan [Shaiɗan] ba.” (2 Korinthiyawa 2:11) A ƙasashe da yawa da suka bunƙasa, yanayin ya yi kama da wanda ya kasance cikin Daular Roma a kwanakinta na bunƙasa. Mutane suna da lokacin shaƙatawa fiye da dā. Wuraren caca na gwamnati suna ba da bege har ga matalauta. Da akwai nishaɗi da yawa da suke cin lokacin mutane. Filayen wasan kwallo suna cika da mutane, mutane suna yin caca, jama’a sai su ta da fāɗa wani lokaci, har da ’yan wasan ma suna haka. Kaɗe-kaɗe marasa daraja suna cika kunnuwan mutane, wasan tsiraru suna cika manyan ɗakunan wasa da kuma siliman da telibijin. A wasu ƙasashe, mata da maza suna wanka tare a gidajen wanka, da kuma maɓulɓulan ruwa mai ɗumi, kada ma a yi maganar wanka tsirara a bakin tekunan ke nan. Kamar yadda yake a ƙarni na farko na Kiristanci, Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya jarabi bayin Allah ta wurin ayyukan shaƙatawa na duniya.
11. Waɗanne tarkuna suke cikin son a sami hutu kuma a shaƙata?
11 A cikin duniya da take cike da wahala, yana da sauƙi mutum ya so ya samu wuri ya huta ko ya gudu ma gabaki ɗaya. Kamar yadda wanka na Romawa ya ƙunshi abubuwan da suke da haɗari ga Kiristoci na farko, wasu wuraren da ake zuwa hutu ko kuma wurin shaƙatawa sun zama tarkon da Shaiɗan ya yi amfani da su ya jawo Kiristoci na zamani zuwa ga lalata ko kuma maye. Bulus ya rubuta zuwa ga Kiristoci cikin Koranti: “Kada ku yaudaru: zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki. Ku farka daga magagi zuwa adalci, ku bar zunubi; gama waɗansu ba su da sanin Allah.”—1 Korinthiyawa 15:33, 34.
12. Waɗanne dabaru ne Shaiɗan yake amfani da su don ya jarabi bayin Jehovah?
12 Mun gani a zancen Hauwa’u yadda Shaiɗan ya yi amfani da wayo ya dagula tunaninta. (2 Korinthiyawa 11:3) A yau, ɗaya cikin tarkunan Iblis shi ne ya jarabi Kiristoci su yi tunanin cewa za su iya yin iyakacin ƙoƙarin nuna cewa Shaidun Jehovah ba su bambanta ba da sauran mutane, don su iya jawo wasunsu zuwa gaskiyar Kirista. Wasu lokatai suna dulmuya da zurfi, har ba za su iya ba da taimakon ba. (Haggai 2:12-14) Wani cikin dabarar Shaiɗan kuma shi ne ya motsa Kiristoci da suka keɓe kai, manyan da yara, suna rayuwa iri biyu suna ‘fusata ruhu mai tsarki na Allah.’ (Afisawa 4:30) Wasu sun fāɗa cikin tarkon ta wajen amfani da Intane.
13. Wane tarkon ɓoye lahani ne ɗaya cikin dabarun Iblis, kuma wane gargaɗin da ke Misalai ya dace a nan?
13 Wani tarkon Shaiɗan shi ne ɓoye lahanin rukuni na asiri. Babu Kirista na gaskiya da zai shiga Shaiɗanci ko kuma sihiri da saninsa. Amma, wasu ba da saninsu ba suna ƙyale kome idan ya zo ga siliman, tsarin wasan telibijin, wasan bidiyo, har da littattafan yara da wasannin ban dariya da ake nuna ƙarfi ko kuma wasu ayyukan sihiri. Duk abin da yake da alamar sihiri ya kamata a guje shi. Karin magana mai hikima ta ce: “Ƙayayuwa da tarkuna suna kan hanyar mai-gamtsin baki: wanda ya kiyaye ransa za ya yi nisa da su.” (Misalai 22:5) Tun da Shaiɗan ne “allah na wannan zamani,” duk abin da jama’a ta karɓa mai yiwuwa ne akwai tarkonsa a ɓoye ciki.—2 Korinthiyawa 4:4; 1 Yohanna 2:15, 16.
Yesu Ya Yi Tsayayya da Iblis
14. Ta yaya ne Yesu ya yi tsayayya da jarrabar Iblis ta farko?
14 Yesu ya yi tanadin misali mai kyau na yin tsayayya da Iblis da kuma sa shi ya rabu da shi. Bayan an yi masa baftisma da azumi na kwana 40, Shaiɗan ya jarabi Yesu. (Matta 4:1-11) A gwaji na farko ya yi amfani da yunwa da Yesu yake ji ne bayan azuminsa. Shaiɗan ya ce Yesu ya yi mu’ujizarsa ta farko don ya gamsar da bukata ta jiki. Ya yi ƙaulin Kubawar Shari’a 8:3, Yesu ya ƙi ya yi amfani da ikonsa ya nuna son kai kuma ya sa abinci na ruhaniya gaba da na jiki.
15. (a) Wane muradi ne Shaiɗan ya yi amfani da shi ya jarrabi Yesu? (b) Wacce ce dabara ta musamman na Iblis wajen bayin Allah a yau, amma ta yaya za mu yi tsayayya da shi?
15 Abin lura game da wannan gwajin shi ne Iblis bai jarabi Yesu ya yi zunubin lalata ba. Yunwa da take ta da muradin abinci shi ne sha’awa mafi ƙarfi da zai yi amfani da ita ya jarrabi Yesu a wannan misali. Waɗanne jarabobbi Iblis yake amfani da su a yau don ya ruɗi mutanen Allah? Suna da yawa kuma sun bambanta, amma ya fi yin amfani da jima’i wajen ƙoƙarin karya amincin mutanen Jehovah. Ta wurin yin koyi da Yesu, za mu iya tsayayya da Iblis kuma mu yi tsayayya da jarrabarsa. Kamar yadda Yesu ya kawar da ƙoƙarin Shaiɗan ta wurin tuna nassosi da suka dace, yayin da muka jarabtu za mu iya tuna nassosi kamar su Farawa 39:9 da 1 Korinthiyawa 6:18.
16. (a) Ta yaya ne Shaiɗan ya jarrabi Yesu a lokaci na biyu? (b) A waɗanne hanyoyi ne Shaiɗan zai yi ƙoƙarin ya jarrabe mu mu jarrabi Jehovah?
16 Ban da haka, Iblis ya ƙalubalanci Yesu ya yi tsalle daga saman haikali don ya gwada ko Allah zai cece shi ta wurin mala’ikunsa. Yesu ya ƙi ya gwada Ubansa ta wurin yin ƙaulin Kubawar Shari’a 6:16. Shaiɗan ba zai jarrabe mu cewa mu yi tsalle daga saman haikali ba, amma zai iya jarrabar mu mu jarrabi Jehovah. Ana jarrabar mu mu zo kurkusa da yin koyi da salon duniya a yin ado da sa tufafi ba tare da an yi mana gargaɗi ba? Muna fuskantar jarraba a zancen nishaɗi marar kyau ne? Zai zama muna jarraba Jehovah. Idan muna da irin nufin nan, maimakon ya gudu daga wajenmu, Shaiɗan sai ya yi ta matso wajenmu, yana nacewa a ƙoƙarin sa mu bi nasa ra’ayi.
17. (a) Ta yaya Iblis ya jarrabi Yesu a lokaci na uku? (b) Ta yaya Yaƙub 4:7 za ta kasance gaskiya a gare mu?
17 Lokacin da Shaiɗan ya ba Yesu dukan mulkokin duniya a bakin sujjada sau ɗaya tak, Yesu ya sake tsayayya da shi ta ɗaukan Nassi, ya tsaya tsayin daka ga bautar Ubansa shi kaɗai. (Kubawar Shari’a 5:9; 6:13; 10:20) Shaiɗan ba zai ba mu mulkokin duniya ba, amma kullum yana jarrabar mu da son abubuwan duniya, har ma mu ji kamar za mu iya samun sarauta ta kanmu. Muna iya amsawa yadda Yesu ya yi, ta ba da bautarmu ga Jehovah shi kaɗai? Idan haka ne, abin da ya faru wa Yesu zai faru da mu. Labarin Matta ya ce: “Shaiɗan ya rabu da shi.” (Matta 4:11) Shaiɗan zai bar mu idan mun yi tsayin daka ta wurin tuna da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da suka dace kuma ta yin amfani da su. Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya fa guje muku.” (Yaƙub 4:7) Wani Kirista ya rubuta zuwa reshe na Shaidun Jehovah a Faransa: “Shaiɗan yana da wayo ƙwarai. Duk da ƙoƙarina, ya yi mini wuya ainun na sarrafa tunanina da kuma muradina. Amma tare da gaba gaɗi, haƙuri, kuma fiye da kome, da taimakon Jehovah na kasance da aminci kuma ina riƙe da gaskiya.”
Shiryayyu Sosai don Yin Tsayayya da Iblis
18. Wane makami na ruhaniya ne ke shirya mu mu yi tsayayya da Iblis?
18 Jehovah ya ba mu makamai na ruhaniya don mu yi “tsayayya da dabarun Shaiɗan.” (Afisawa 6:11-18) Ƙaunarmu ga gaskiya za ta ɗaure ɗamara, ko kuma shirya mu, don ayyuka na Kirista. Ƙudurinmu mu manne wa mizanan adalci na Jehovah zai zama sulke da ke kāre zuciyarmu. Idan mun ɗaura wa sawayenmu bishara, a kai a kai za su dinga kai mu zuwa aikin wa’azi, kuma wannan zai ƙarfafa kuma ya ba mu kāriya ta ruhaniya. Bangaskiyarmu za ta zama kamar garkuwa, tana kāre mu daga “jefejefe masu-wuta na mugun,” farmakinsa na yaudara da kuma jarraba. Begen da muke da shi da gaba gaɗi a cikar alkawuran Jehovah zai kasance kwalkwali da ke kāre tunaninmu kuma ke ba mu salamar zuci. (Filibbiyawa 4:7) Idan muka ƙware a yin amfani da Kalmar Allah, za ta zama kamar takobi da za mu iya amfani da shi a taimakon mutane su ’yantu daga bautar Shaiɗan. Za mu iya amfani da shi mu kāre kanmu, kamar yadda Yesu ya yi lokacin da aka jarrabe shi.
19. Me ake bukata kuma, ban da ‘yin tsayayya da Iblis’?
19 Ta wurin yafa wannan “dukan makamai na Allah” kuma da yin addu’a a kai a kai, za mu iya kasancewa da gaba gaɗi cewa Jehovah zai kāre mu yayin da Shaiɗan ya kawo mana hari. (Yohanna 17:15; 1 Korinthiyawa 10:13) Amma Yaƙub ya nuna cewa ‘tsayayya da Iblis’ kawai bai isa ba. Fiye da haka, dole ne mu kuma ‘ba da kanmu ga Allah,’ wanda yake kula da mu. (Yaƙub 4:7, 8) Yadda za mu yi haka za a tattauna cikin talifi na gaba.
Yaya Za Ka Amsa?
• Waɗanne tarkuna na Shaiɗan Kiristoci na farko suka bukaci su guje wa?
• Waɗanne dabaru Shaiɗan yake amfani da su don ya kama bayin Jehovah a yau?
• Ta yaya Yesu ya yi tsayayya da jarrabar Iblis?
• Waɗanne makamai na ruhaniya ne ke taimakonmu mu yi tsayayya da Iblis?
[Hoto a shafi na 9]
Yesu ya yi tsayayya da Iblis ƙwarai
[Hotuna a shafi na 10]
Kiristoci na ƙarni na farko sun ƙi nishaɗi na nuna ƙarfi na lalata
[Inda aka Dauko]
The Complete Encyclopedia of Illustration/J. G. Heck