Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 11/1 pp. 13-18
  • Jehovah Yana Kula Da Kai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehovah Yana Kula Da Kai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jehovah Yana Son Ya Taimake Mu
  • Jehovah Yana Jawo Mutanensa Wurinsa
  • Akwai Bukatar Biɗan Jehovah
  • Dole ne Jehovah Ya Kasance da Gaske a Gare Mu
  • Ka Fahimci Kula ta Jehovah Kuwa?
  • Ka Ci Gaba da Biɗan Jehovah
  • Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Ta Yaya Za Ka Iya Zama Aminin Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Sa Zuciya ga Yahweh”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 11/1 pp. 13-18

Jehovah Yana Kula Da Kai

“Kuna zuba dukan alhininku a bisa [Allah], domin yana kula da ku.”—1 BITRUS 5:7.

1. A wane muhimmin azanci ne Jehovah da Shaiɗan suka saɓa ƙwarai?

JEHOVAH da Shaiɗan sun saɓa ƙwarai da juna. Duk wanda ya matsa kusa da Jehovah zai guji Iblis. Wani bincike ya nuna wannan saɓawar. Game da ayyukan Iblis da aka nuna a littafin Ayuba na Littafi Mai Tsarki, Encyclopædia Britannica (1970) ya ce: ‘Aikin Shaiɗan ne ya yi yawo a cikin dukan duniya yana neman ayyuka ko kuma mutanen da za su yi mugunta; aikinsa ya saɓa da na “idanun Ubangiji,” da suke yawo cikin dukan duniya suna ƙarfafa dukan abin da ke nagari (II Lab. 16:9). Shaiɗan bai yarda ba da nagartar ’yan Adam marar son kai kuma an ƙyale shi ya jarraba wannan a ƙarƙashin ikon Allah da mallakarsa cikin iyakar da Allah ya kafa masa.’ Hakika, saɓawa ce ƙwarai!—Ayuba 1:6-12; 2:1-7.

2, 3. (a) Yaya ma’anar kalmar nan “Iblis” ta bayyana ƙwarai a cikin abin da ya faru da Ayuba? (b) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Shaiɗan yana ci gaba da zargin bayin Jehovah a duniya yau?

2 Kalmar nan “Iblis” ta fito ne daga kalmar Helenanci da ke nufin “maƙaryaci,” “mai tsegumi.” Littafin Ayuba ya bayyana cewa Shaiɗan ya zargi Ayuba bawa mai aminci na Jehovah cewa yana bauta Masa domin son kai, yana cewa: “A banza ne Ayuba ya ke tsoron Allah?” (Ayuba 1:9) Labarin nan cikin littafin Ayuba ya nuna cewa duk da jarabobbi da kuma gwaji, Ayuba ya jawo kurkusa da Jehovah. (Ayuba 10:9, 12; 12:9, 10; 19:25; 27:5; 28:28) Bayan wahalarsa, ya ce wa Allah: “Na ji labarinka ta wurin ji na kunne; amma yanzu idona ya gan ka.”—Ayuba 42:5.

3 Shaiɗan ya daina zargin bayi masu aminci na Allah ne tun lokacin Ayuba? A’a. Littafin Ru’ya ta Yohanna ya nuna cewa a wannan lokaci na ƙarshe, Shaiɗan ya ci gaba da zargin shafaffun ’yan’uwan Kristi kuma hakika tare da abokansu masu aminci. (2 Timothawus 3:12; Ru’ya ta Yohanna 12:10, 17) Abin da ya sa ke nan, bukata ta ƙwarai ta dukanmu Kiristoci na gaskiya ita ce mu ba da kanmu ga Allahnmu mai kula, Jehovah, mu bauta masa da ƙauna ta ƙwarai muna tabbatar da cewa zargin Shaiɗan ƙarya ne. A ta haka, za mu faranta zuciyar Jehovah.—Misalai 27:11.

Jehovah Yana Son Ya Taimake Mu

4, 5. (a) Ba kamar Shaiɗan ba, menene Jehovah yake nema cikin duniya? (b) Idan za mu samu tagomashin Jehovah, menene ake bukata a gare mu?

4 Iblis yana yawo cikin duniya yana neman ya zargi kuma ya halaka wani. (Ayuba 1:7, 9; 1 Bitrus 5:8) Akasarin haka, Jehovah yana son ya taimake waɗanda suke bukatar ƙarfinsa. Annabi Hanani ya gaya wa Sarki Asa: “Idanun Ubangiji suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.” (2 Labarbaru 16:9) Da bambanci tsakanin mugun bincike da Shaiɗan yake yi da kulawa ta ƙauna na Jehovah!

5 Jehovah ba ya yi mana ganganima don ya ga kowanne laifi da kasawarmu. Mai Zabura ya rubuta: “Idan kai, ya Ubangiji, za ka ƙididdiga laifofi, wa za ya tsaya, ya Ubangiji?” (Zabura 130:3) Amsarta, ita ce: babu mutum ko guda. (Mai-Wa’azi 7:20) Idan muka matsa kusa da Jehovah da zuciya ɗaya, idanunsa suna kanmu, ba domin ya hukunta mu ba, amma domin ya ga ƙoƙarinmu kuma yana amsa addu’o’inmu don ya taimaka kuma ya gafarta mana. Manzo Bitrus ya rubuta: “Idanun Ubangiji suna bisa masu-adalci, kunnuwansa kuma suna buɗe ga jin roƙonsu: amma fuskar Ubangiji tana gāba da waɗanda ke aika mugunta.”—1 Bitrus 3:12.

6. Ta yaya ne yanayin Dauda ya zama abin ta’aziyya da kuma gargaɗi a gare mu?

6 Dauda ajizi ne kuma ya yi zunubi ƙwarai. (2 Samu’ila 12:7-9) Ya buɗe wa Jehovah zuciyarsa kuma ya matsa kusa da shi cikin addu’a. (Zabura 51:1-12) Ko da yake Dauda ya sha azabar sakamako masu muni na zunubinsa, Jehovah ya ji addu’arsa kuma ya gafarta masa. (2 Samu’ila 12:10-14) Ya kamata wannan ya zama mana abin ta’aziyya da kuma gargaɗi. Abin farin ciki ne mu sani cewa Jehovah a shirye yake ya gafarta mana zunubanmu idan muka tuba da gaske, amma abin baƙin ciki ne mu ga mummunar sakamakon da zunubin ya jawo. (Galatiyawa 6:7-9) Idan muna so mu matsa kusa da Jehovah, ya kamata mu yi ƙoƙari sosai mu guji wani abin da zai baƙanta masa rai.—Zabura 97:10.

Jehovah Yana Jawo Mutanensa Wurinsa

7. Waɗanne irin mutane Jehovah yake nema, kuma ta yaya yake jawo su ga kansa?

7 Dauda ya rubuta cikin wata zaburarsa: “Ubangiji maɗaukaki ne, ya kan lura da masu tawali’u: Amma masu-girman kai daga nesa ya fishe su.” (Zabura 138:6) Haka kuma, wata zabura ta ce: “Wanene kinin Ubangiji Allahnmu, wanda ya ke da kursiyinsa cikin ɗaukaka, Wanda ya kan ƙasƙantarda kansa domin ya duba abubuwan da ke cikin sama da duniya? Ya kan tada matalauci daga cikin turɓaya.” (Zabura 113:5-7) Hakika, Mahaliccin dukan sararin samaniya yana ƙasƙantar da kansa zuwa duniya, kuma idanunsa na ganin “masu-tawali’u,” “matalauci,” mutane da suke “ajiyar zuci, suna kuwa kuka saboda dukan ƙazanta da a ke yi.” (Ezekiel 9:4) Ya jawo waɗannan ta wajen Ɗansa. Lokacin da yake duniya Yesu ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi . . . Ba wanda ya iya zuwa gareni ba, sai ko Uba ya ba shi.”—Yohanna 6:44, 65.

8, 9. (a) Me ya sa dukanmu ke bukatar mu zo wurin Yesu? (b) Menene yake ba da sha’awa game da shirin fansa?

8 Ya kamata dukan mutane su zo wurin Yesu kuma su kasance da bangaskiya cikin hadayar fansa domin an haife su masu zunubi, bare daga Allah. (Yohanna 3:36) Suna bukatar su sulhunta da Allah. (2 Korinthiyawa 5:20) Allah bai jira masu zunubi su roƙe shi domin ya yi tanadi da za su kasance da salama tare da shi ba. Manzo Bulus ya rubuta: “Allah yana shaidar ƙaunatasa garemu, da shi ke, tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu. . . . Gama idan tun muna maƙiya muka sulhuntu da Allah ta wurin mutuwar Ɗansa, balle, sulhuntattu, za mu tsira ta wurin ransa.”—Romawa 5:8, 10.

9 Manzo Yohanna ya tabbatar da fahimin gaskiya, Allah yana sulhunta mutane ga kansa, ya ce: “Inda aka bayyana ƙaunar Allah garemu ke nan, Allah ya aike Ɗansa haifaffensa kaɗai cikin duniya, domin mu rayu ta wurinsa. Nan akwai ƙauna, ba cewa mu ne muka yi ƙaunar Allah ba, amma shi ne ya ƙaunace mu, ya aike Ɗansa kuma shi zama kafara ta zunubanmu.” (1 Yohanna 4:9, 10) Allah ne ya ɗauki matakin ba mutane ba. Ba ka jin kana so ka matsa wajen Allahn da ya nuna irin yawan ƙaunar nan ga “masu-zunubi,” “maƙiya” ba?—Yohanna 3:16.

Akwai Bukatar Biɗan Jehovah

10, 11. (a) Menene dole mu yi don mu biɗi Jehovah? (b) Yaya ya kamata mu ɗauki zamanin Shaiɗan?

10 Babu shakka, Jehovah ba ya tilasa mana mu zo wurinsa. Dole ne mu biɗe shi, “a lallaba [a] same shi, ko da shi ke ba shi da nisa da kowanne ɗayanmu ba.” (Ayukan Manzanni 17:27) Dole ne mu fahimci dacewar Jehovah mu ba da kanmu gare shi. Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Ku zama fa masu-biyayya ga Allah amma ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya fa guje muku. Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gareku. Ku tsabce hannuwanku, ku masu zunubi; ku tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.” (Yaƙub 4:7, 8) Ya kamata mu tsaya tsayin daka wajen gāba da Iblis domin Jehovah.

11 Wannan yana nufin za mu yi nisa daga zamanin Shaiɗan. Yaƙub kuma ya rubuta: “Ku mazinata, ba ku sani ba abutar duniya magabtaka ce da Allah? Dukan wanda ya ke so shi zama abokin duniya fa yana maida kansa magabcin Allah.” (Yaƙub 4:4) Babu shakka, idan muna son mu zama abokan Jehovah, dole mu zaci cewa duniyar Shaiɗan za ta ƙi mu.—Yohanna 15:19; 1 Yohanna 3:13.

12. (a) Waɗanne kalmomin ta’aziyya Dauda ya rubuta? (b) Wane gargaɗi ne Jehovah ya bayar ta wurin annabi Azariya?

12 Yayin da duniyar Shaiɗan ta yi hamayya da mu a wata hanya, muna bukatar mu kusaci Jehovah musamman cikin addu’a, muna neman taimakonsa. Dauda, wanda ya shaida ceton Jehovah a lokatai da yawa, ya rubuta domin ta’aziyyarmu: “Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda su ke kira bisa gareshi, ga dukan waɗanda su ke kira gareshi da gaskiya. Za ya biya muradin waɗanda ke tsoronsa; Za ya kuma ji kukarsu, ya cece su. Ubangiji yana kiyayadda dukan waɗanda ke ƙaunarsa; Amma za ya halaka dukan miyagu.” (Zabura 145:18-20) Wannan zaburar ta nuna cewa Jehovah zai iya cetonmu yayin da an gwada kowannenmu kuma cewa zai ceci mutanensa gabaki ɗaya a lokacin “babban tsananin.” (Ru’ya ta Yohanna 7:14) Jehovah zai kasance kusa da mu idan mun kasance kusa da shi. Tare da ja-gorar “ruhun Ubangiji” annabi Azariya ya ambaci abin da za mu iya la’akari da shi, gaskiya a yadda take: “Ubangiji yana tare da ku, muddar kuna tare da shi; idan kun neme shi, yā samu a gareku; amma idan kun yashe shi, shi kuma za ya yashe ku.”—2 Labarbaru 15:1, 2.

Dole ne Jehovah Ya Kasance da Gaske a Gare Mu

13. Ta yaya za mu nuna cewa Jehovah ya kasance da gaske a gare mu?

13 Manzo Bulus ya rubuta game da Musa cewa “ya jimre, kamar yana ganin wanda ba shi ganuwa.” (Ibraniyawa 11:27) Babu shakka, Musa bai ga Jehovah da idanunsa ba. (Fitowa 33:20) Amma Jehovah ya kasance da gaske a gare shi kamar yana ganin Sa. Hakanan ma, bayan gwajinsa, idanun Ayuba na bangaskiya sun ga Jehovah sarai, Allah wanda ya ƙyale bayinsa masu aminci su sha gwaji amma ba ya taɓa yashe su. (Ayuba 42:5) An yi zancen Ahnuhu da Nuhu cewa sun yi ‘tafiya da Allah.’ Sun yi hakan ta yin ƙoƙarin faranta wa Allah rai da kuma yi masa biyayya. (Farawa 5:22-24; 6:9, 22; Ibraniyawa 11:5, 7) Idan a gare mu Jehovah yana da gaske kamar yadda ya kasance da Ahnuhu, Nuhu, Ayuba, da kuma Musa, za mu “shaida shi” a duk hanyoyinmu, kuma zai “daidaita hanyoyin[mu].”—Misalai 3:5, 6.

14. Menene yake nufi a “manne” wa Jehovah?

14 Lokacin da Isra’ilawa suke goshin shiga Ƙasar Alkawari, Musa ya yi musu gargaɗi: “Za ku bi Ubangiji Allahnku, ku ji tsoronsa, ku kiyaye dokokinsa, ku ji muryatasa, za ku bauta masa kuma, ku manne masa.” (Kubawar Shari’a 13:4) Suna bukatar su bi Jehovah, su ji tsoronsa, su yi masa biyayya, kuma su manne masa. Game da kalmar nan da aka fassara “manne,” wani manazarcin Littafi Mai Tsarki ya ce “kalmar tana nuna dangantaka ta kurkusa.” Mai Zabura ya ce: “Asirin Ubangiji ga masu-tsoronsa ya ke.” (Zabura 25:14) Wannan dangantaka mai tamani, na kurkusa da Jehovah za ta zama tamu idan ya kasance gaskiya a gare mu kuma idan muna ƙaunarsa sosai da za mu ji tsoron mu baƙanta masa a kowacce hanya.—Zabura 19:9-14.

Ka Fahimci Kula ta Jehovah Kuwa?

15, 16. (a) Yaya Zabura ta 34 ta nuna yadda Jehovah yake kula da mu? (b) Me ya kamata mu yi idan mun iske shi da wuya mu tuna da wasu ayyukan nagarta na Jehovah dominmu?

15 Ɗaya cikin kissoshin Shaiɗan shi ne yana ƙoƙarin ya sa mu manta cewa Allahnmu Jehovah, koyaushe yana kula da bayinsa masu aminci. Sarki Dauda na Isra’ila ya fahimci kāriyar Jehovah har ma a lokatai mafi wuya. Lokacin da ya nuna ya haukace a gaban Sarki Achish na Gath, ya shirya waƙa, wata zabura mai kyau, da ta haɗa da wannan furcin bangaskiya: “Ku girmama Ubangiji tare da ni, bari kuma mu ɗaukaka sunansa tare. Na biɗi Ubangiji, ya amsa mini, ya kuma tsamarda ni daga dukan yawan tsorona. Mala’ikan Ubangiji yana kafa sansani a kewaye da masu-tsoronsa, yana tseradda su kuma. Ku ɗanɗana, ku duba, Ubangiji nagari ne: mai-albarka ne mutum wanda ya ke dogara gareshi. Ubangiji yana kusa da masu-karyayyar zuciya, yana ceton irin waɗanda su ke da ruhu mai-tuba. Masifu na mai-adalci dayawa su ke: amma Ubangiji ya kan tsamarda shi daga cikinsu duka.”—Zabura 34:3, 4, 7, 8, 18, 19; 1 Samu’ila 21:10-15.

16 Ka tabbata da ikon ceto na Jehovah? Ka fahimci kāriyarsa ta wurin mala’iku? Kai kanka ka taɓa shaida kuma ka ga cewa Jehovah nagari ne? Yaushe ne kai musamman ka tuna cewa Jehovah ya yi maka nagarta? Yi ƙoƙari ka tuna. A gida na ƙarshe da ka je wa’azi ne, da kake jin ba za ka iya ci gaba ba? Wataƙila daga baya ka ji daɗin taɗi da maigidan. Ka tuna ka gode wa Jehovah don ya ƙara maka ƙarfi da kake bukata kuma ya albarkace ka? (2 Korinthiyawa 4:7) A wata sassa, wataƙila ya kasance da wuya ka tuna wata nagarta da Jehovah ya yi maka. Ƙila ya kamata ka yi tunanin zuwa baya na mako guda, wata guda, shekara guda, ko ma fiye da haka. Idan haka ne, me ya sa ba za ka yi ƙoƙari da saninka ka jawo kurkusa da Jehovah kuma ka ga yadda yake kāriya kuma yake maka ja-gora ba? Manzo Bitrus ya gargaɗi Kiristoci: “Ku ƙasƙantarda kanku . . . ƙarƙashin hannu mai-iko na Allah, . . . kuna zuba dukan alhininku a bisansa, domin yana kula da ku.” (1 Bitrus 5:6, 7) Hakika, za ka yi mamakin yawan yadda yake kula da kai!—Zabura 73:28.

Ka Ci Gaba da Biɗan Jehovah

17. Menene wajibi ne idan za mu ci gaba da biɗan Jehovah?

17 Adana dangantakarmu da Jehovah aba ce da za ta zama ta kullum. Yesu ya faɗa cikin addu’a ga Ubansa: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” (Yohanna 17:3) Samun sanin Jehovah da na Ɗansa yana bukatar ƙoƙarinmu na kullum. Muna bukatar taimako ta addu’a da kuma ruhu mai tsarki don mu fahimci abubuwa “zurfafa na Allah.” (1 Korinthiyawa 2:10; Luka 11:13) Muna kuma bukatar ja-gorar “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” su ciyar da zukatanmu da abinci na ruhaniya da ke zuwa a “lotonsa.” (Matta 24:45) Ta wurin wannan magudana, Jehovah yana mana gargaɗi mu karanta Kalmarsa kowacce rana, mu halarci taron Kirista a kai a kai, kuma mu sa hannu a wa’azin “bisharar mulki.” (Matta 24:14) Ta yin haka, za mu ci gaba da biɗan Allahnmu mai kula, Jehovah.

18, 19. (a) Menene ya kamata mu ƙudiri niyyar yi? (b) Wace albarka za mu samu idan muka tsaya tsayin daka wajen gāba da Iblis, kuma muka ci gaba da biɗan Jehovah?

18 Shaiɗan yana iyakacin ƙoƙarinsa don ya kawo tsanani, hamayya, da kuma matsi daga kowanne fanni a kan mutanen Jehovah. Yana ƙoƙarin ya lalata salamarmu kuma ya halaka matsayinmu mai kyau wajen Allahnmu. Ba ya son mu ci gaba da aikinmu na neman masu zuciyar kirki muna taimakonsu su zo gefen Jehovah a al’amarin ikon mallaka. Amma dole ne mu ƙudiri niyyar mu kasance da aminci, muna dogara gare shi ya cece mu daga wannan mugun. Idan mun yarda wa Kalmar Allah ta yi mana ja-gora kuma mu tsaya da ƙwazo cikin ƙungiyarsa da ake gani, mu tabbata cewa kullum yana nan don ya goyi bayanmu.—Ishaya 41:8-13.

19 Saboda haka, bari dukanmu mu tsaya tsayin daka gāba da Iblis da ayyukansa na dabara, muna biɗan Allahnmu abin ƙauna, Jehovah, da ba zai kasa ‘kafa mu, yana ƙarfafa mu’ kuma. (1 Bitrus 5:8-11) Ta haka, za mu ‘ajiye kanmu cikin ƙaunar Allah, muna sauraron jinƙan Ubangijinmu Yesu Kristi zuwa rai na har abada.’—Yahuda 21.

[Hoto a shafi na 15]

Duk da gwajinsa, Ayuba ya fahimci cewa Jehovah yana kula da shi

[Hotuna a shafuffuka na 16, 17]

Karatun Littafi Mai Tsarki na kowacce rana, halartan taron Kirista, da kuma sa hannu da ƙwazo a aikin wa’azi na tunasar da mu cewa Jehovah yana kula da mu

[Hoto a shafi na 18]

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene kalmar nan “Iblis” take nufi, kuma yaya Iblis ya jitu da wannan sunan?

• Ta yaya Jehovah ya bambanta da Iblis a hanyar da Yake duba mazaunan duniya?

• Me ya sa dole ne mutum ya amince da fansa don ya kusaci Jehovah?

• Menene yake nufi a “manne” wa Jehovah, kuma ta yaya za mu ci gaba da biɗansa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba