Ka Nuna Ƙauna Ta Alheri Ga Waɗanda Suke Da Bukata
“Ku nuna [ƙauna ta alheri, “NW”] . . . kowane mutum zuwa ga ɗan’uwansa.”—ZECHARIAH 7:9.
1, 2. (a) Me ya sa za mu nuna ƙauna ta alheri? (b) Waɗanne tambayoyi za mu bincika?
KALMAR Jehovah Allah ta aririce mu mu yi ƙauna “[ƙauna ta alheri].” (Mikah 6:8, hasiya ta NW ) Kuma ta ba mu dalili da ya sa za mu yi haka. Abu ɗaya shi ne, “mai [ƙauna ta alheri] ya kan yi ma ransa alheri.” (Misalai 11:17) Hakika! Nuna ƙauna ta alheri ko kuma ƙauna ta aminci, tana ƙulla dangantaka mai jimrewa da wasu. Sakamakon haka, za mu samu amintattun abokane—lada mai tamani.—Misalai 18:24.
2 Bugu da ƙari, Nassosi ya gaya mana: “Wanda ya bi adalci da [ƙauna ta alheri, NW ] rai yake samu.” (Misalai 21:21) Hakika, bin ƙauna ta alheri za ta jawo mu kusa da Allah kuma ta sa mu a layin masu samun albarka, har da rai madawwami. Amma ta yaya za mu nuna ƙauna ta alheri? Ga wa za mu nuna ta? Kuma ta yaya ƙauna ta alheri ta bambanta da alheri na mutane na kullum ko kuma alheri galibinsa?
Alheri na Mutane da Ƙauna ta Alheri
3. Ta yaya ƙauna ta alheri ta bambanta da alheri na mutane?
3 Alheri na mutane da ƙauna ta alheri sun bambanta a hanyoyi da yawa. Alal misali, waɗanda suke nuna alheri sau da yawa suna yin haka ne ba tare da wata dangantaka ba ta kusa ko kuma nasaba da mutumin da suke yi wa alheri. Idan muka nuna ƙauna ta alheri ga wani, to, cikin ƙauna mun ɗaure kanmu da wannan mutumin. A cikin Littafi Mai Tsarki, nuna ƙauna ta alheri tsakanin mutane zai dangana ne a kan nasaba da ta riga tana wanzuwa. (Farawa 20:13; 2 Samu’ila 3:8; 16:17) Ko kuma za ta kasance ne bisa wani alheri da aka yi a dā. (Joshua 2:1, 12-14; 1 Samu’ila 15:6; 2 Samu’ila 10:1, 2) Domin mu kwatanta wannan bambanci, bari mu gwada misalai biyu na Littafi Mai Tsarki, ɗaya na alheri ɗayan kuma na ƙauna ta alheri da mutane suka nuna.
4, 5. Ta yaya misalan Littafi Mai Tsarki biyu da aka nuna sun bambanta tsakanin alheri na mutane da ƙauna ta alheri?
4 Misali ɗaya na alheri na mutane ya shafi rukunin mutane da suka yi haɗari a jirgin ruwa, har da manzo Bulus. Ruwa ya tura su zuwa tsibirin Malita. (Ayukan Manzanni 27:37–28:1) Ko da yake mutanen Malita ba su da wajibi da farko ga waɗannan mutane da suka ɓata ko kuma dangantaka da take tsakaninsu, mutanen tsibirin suka marabce su, “suka nuna musu alheri irin da ba a kan saba yi ba.” (Ayukan Manzanni 28:2, 7, NW ) Marabtarsu alheri ne, amma domin tsautsayi ne kuma sun nuna wa baƙi. Saboda haka, alheri ne na mutane.
5 Ka gwada alheri da Sarki Dauda ya yi wa Mephibosheth, ɗan Jonathan. Dauda ya gaya wa Mephibosheth: “Za ka ci abinci a [teburi] nawa kullayaumin.” Da yake bayani abin da ya sa yake wannan tanadi, Dauda ya gaya masa: “Hakika zan gwada maka [ƙauna ta alheri] sabili da Jonathan ubanka.” (2 Samu’ila 9:6, 7, 13) Alherin Dauda marar ƙarewa an ce da shi nuna ƙauna ta alheri, ba alheri ba kawai, domin tabbacin amincinsa ne ga dangantaka da aka ƙulla. (1 Samu’ila 18:3; 20:15, 42) Hakanan a yau, bayin Allah suna nuna wa galibin mutane alheri. Duk da haka, suna nuna ƙauna ta alheri, ko kuma ƙauna ta aminci, ga waɗanda suke da yardaddiyar dangantaka da Allah.—Matta 5:45; Galatiyawa 6:10.
6. Waɗanne halaye ne tattare da ƙauna ta alheri da aka nuna tsakanin mutane suka fita sarai a cikin Kalmar Allah?
6 Domin mu ga wasu halaye da suke tattare da ƙauna ta alheri, za mu bincika tarihi uku na Littafi Mai Tsarki da ya nuna wannan hali. Daga waɗannan za mu lura cewa ƙauna ta alheri da mutane suka nuna an yi ta ne (1) da takamammun ayyuka, (2) da son rai, da kuma (3) an nuna ta ne musamman ga waɗanda suke da bukata. Bugu da ƙari, waɗannan tarihi sun nuna cewa mu ma za mu iya nuna ƙauna ta alheri a yau.
Uba Ya Nuna Ƙauna ta Alheri
7. Menene baran Ibrahim ya gaya wa Bethuel da Laban, kuma wane batu ne baran ya kawo?
7 Farawa 24:28-67 sun ba da sauran labarin baran Ibrahim, da aka faɗa a talifi da ya gabata. Bayan ya sadu da Rifkatu, an gayyace shi ya shiga gidan ubanta, Bethuel. (Ayoyi 28-23) A nan baran ya feɗe biri har wutsiya game da yadda yake neman mace ga ɗan Ibrahim. (Ayoyi 33-47) Ya nanata cewa yana ganin nasara da ya yi alama ce daga Jehovah, “wanda ya bishe ni cikin tafarkin da ke daidai da zan ɗauki ’yar ɗan’uwan ubangidana ta zama matar ɗansa.” (Aya ta 48) Baran babu shakka ya yi begen cewa ba su labarin zai huɗubantar da Bethuel da ɗansa Laban cewa Jehovah ya albarkaci dalilin zuwansa. A ƙarshe, baran ya ce: “Idan za ku aika [ƙauna ta alheri] da aminci game da ubangidana, ku faɗa mini; in kuma ba haka ba, ku faɗa mini; domin in juya ko dama ko hagu.”—Aya ta 49.
8. Mecece amsar Bethuel ga al’amarin da ya shafi Rifkatu?
8 Jehovah ya riga ya nuna ƙauna ta alheri ga Ibrahim. (Farawa 24:12, 14, 27) Bethuel zai yi hakan ya ƙyale Rifkatu ta bi baran Ibrahim? Za a cika ƙauna ta alheri ta Allah da ƙauna ta alheri ta mutane? Ko kuma dai doguwar tafiya ta baran za ta kasance aikin banza? Hakika zai kasance da ban ƙarfafa da baran Ibrahim ya ji Laban da Bethuel suka ce: “Al’amarin nan daga wurin Ubangiji ya ke.” (Aya ta 50) Sun fahimci nufin Jehovah a al’amarin kuma sun karɓa ba tare da gardama ba. Sai Bethuel ya nuna ƙaunarsa ta alheri ta wajen daɗa cewa: “Ga Rifkatu, a gabanka, ka ɗauke ta, ta tafi, ta zama matar ɗan ubangidanka, kamar yadda Ubangiji ya faɗi.” (Aya ta 51) Rifkatu ta bi baran Ibrahim da son rai, ba da daɗewa ba ta zama mowar Ishaƙu.—Ayoyi 49, 52-58, 67.
Yaro Ya Nuna Ƙauna ta Alheri
9, 10. (a) Menene Yakubu ya roƙi ɗansa Yusufu ya yi ma shi? (b) Ta yaya Yusufu ya nuna ƙauna ta alheri ga ubansa?
9 Jikan Ibrahim Yakubu an nuna masa ƙauna ta alheri. Kamar yadda Farawa sura 47 ta nuna, Yakubu yana zama a ƙasar Masar, “lokaci ya yi kusa kuwa da [za] ya mutu.” (Ayoyi na 27-29) Ya damu domin ba zai mutu ba a ƙasar da Allah ya yi wa Ibrahim alkawari. (Farawa 15:18; 35:10, 12; 49:29-32) Yakubu ba ya so a binne shi a ƙasar Masar, saboda haka, ya yi tanadin a kai gawarsa ƙasar Kan’ana. Wa zai kasance a matsayin da ya dace ya tabbata cewa an cika wasiyyarsa fiye da ɗansa mai rinjaya, Yusufu?
10 Tarihin ya ce: “[Yakubu] ya kirayi ɗansa Yusufu, ya ce masa, Idan dai na sami tagomashi a gabanka, . . . ka aika [ƙauna ta alheri, NW ] da aminci gareni kuma; ina roƙonka, kada ka binne ni cikin Masar: amma sa’anda ina barci tare da ubannina, sai ka ɗauke ni daga cikin ƙasar Masar, ka binne ni a wurin makushaitansu.” (Farawa 47:29, 30) Yusufu ya yi alkawari zai cika wannan roƙon, ba da daɗewa ba bayan haka Yakubu ya mutu. Yusufu da kuma wasu ’ya’yan Yakubu suka ɗauki gawarsa zuwa “ƙasar Kan’ana, suka binne shi cikin kogon dutse na saurar Machpelah, wanda Ibrahim ya saya.” (Farawa 50:5-8, 12-14) Ta haka Yusufu ya nuna ƙauna ta alheri ga ubansa.
Ƙauna ta Alheri Daga Surkuwa
11, 12. (a) Ta yaya Ruth ta nuna ƙauna ta alheri ga Naomi? (b) A wace hanya ce ƙauna ta alheri da Ruth ta nuna a “ƙarshe” ta fi ta “fari”?
11 Littafin Ruth ya nuna yadda gwauruwa Naomi ta samu ƙauna ta alheri daga wajen surkuwarta Ruth wadda ita ma gwauruwa ce. Sa’ad da Naomi ta shawarta ta koma Baitalahmi Yahudiya, Ruth ta nuna ƙauna ta alheri da kuma ƙuduri, tana cewa: “Inda za ki tafi duka, nan za ni; inda za ki sauka, nan zan sauka: danginki za su zama dangina, Allahnki kuma Allahna.” (Ruth 1:16) Ruth daga baya ta nuna ƙauna ta alheri sa’ad da ta nuna son ranta ta auri dangin Naomi da ya manyanta, Boaz.a (Kubawar Shari’a 25:5, 6; Ruth 3:6-9, 10) Ya gaya wa Ruth: “Wannan [ƙauna ta alheri] na ƙarshe da ki ka nuna, ya fi na fari, da shi ke ba ki maida hankali ga samari, ko masu arziki, ko masu-talauci ba.”—Ruth 3:10.
12 Lokaci na “fari” da Ruth ta nuna ƙauna ta alheri yana nuni ne da lokacin da ta bar mutanenta ta manne wa Naomi. (Ruth 1:14; 2:11) Wannan aikin ma ya wuce lokaci na “fari” na ƙauna ta alheri—yardar Ruth ta auri Boaz da son rai. Yanzu Ruth za ta iya ta haifi wa Naomi magaji, wadda ta riga ta wuce lokacin haihuwa. Aka ɗaura aure, kuma sa’ad da daga baya Ruth ta haihu, matan Baitalahmi suka ce: “An haifa ma Naomi ɗa.” (Ruth 4:14, 17) Hakika Ruth “macen kirki ce,” wadda kuma Jehovah ya yi mata albarka da gata mai ban sha’awa na kasancewa kakar Yesu Kristi.—Ruth 2:12; 3:11; 4:18-22; Matta 1:1, 5, 6.
Ana Nuna ta Cikin Ayyuka
13. Ta yaya Bethuel, Yusufu, da kuma Ruth suka nuna nasu ƙauna ta alheri?
13 Ka lura da yadda Bethuel, Yusufu, da kuma Ruth suka nuna ƙaunarsu ta alheri? Ba su yi haka ba da kalmomi masu daɗi kawai amma sun yi hakan da takamammun ayyuka. Bethuel bai ce ba kawai, “Ga Rifkatu” amma a hakikanci “suka yi sallama da Rifkatu.” (Farawa 24:51, 59) Yusufu bai ce ba kawai, “ni yi yadda ka faɗi” amma shi da ’yan’uwansa suka yi “masa bisa yadda ya umurce su.” (Farawa 47:30; 50:12, 13) Ruth ba ta ce, “inda za ki tafi duka, nan za ni” ba kawai, amma ta bar mutanenta ta bi Naomi, “su biyu fa suka yi ta tafiya har suka zo Baitalahmi.” (Ruth 1:16, 19) A Yahudiya, Ruth ta sake yin “kamar yadda surkuwarta ta faɗa mata duka.” (Ruth 3:6) Hakika, ƙauna ta alheri ta Ruth, kamar ta wasu, an nuna ta cikin ayyuka.
14. (a) Ta yaya bayin Allah na zamani suke nuna ƙauna ta alheri ta wajen ayyuka? (b) Waɗanne ayyukan ƙauna ta alheri ka sani a tsakanin Kiristoci a yankinku?
14 Abin daɗaɗawa ne mu ga yadda bayin Allah a yau suke nuna ƙauna ta alheri ta wajen ayyuka. Alal misali, ka yi tunanin waɗanda suke ba da taimako ga naƙasassu, waɗanda suka raunana a zuciya, da kuma ’yan’uwa waɗanda suke makoki. (Misalai 12:25) Ko kuma ka yi la’akari da Shaidun Jehovah waɗanda cikin aminci suke jan tsofaffi zuwa Majami’ar Mulki su halarci taron ikilisiya na mako. Anna, ’yar shekara 82 tana fama da ƙaba, ta yi magana game da wasu sa’ad da ta ce: “Kai ni taro, albarka ce daga Jehovah. Ina yi masa godiya daga zuciya da ya ba ni waɗannan ’yan’uwa.” Kana saka hannu a irin waɗannan ayyuka a ikilisiyarku? (1 Yohanna 3:17, 18) Idan kana yi, ka tabbata cewa ana godiya ƙwarai domin ƙaunarka ta alheri.
Ana Nuna ta da Son Rai Ne
15. Waɗanne halayen ƙauna ta alheri aka ƙara nanaci a cikin labarai uku na Littafi Mai Tsarki da muka bincika?
15 Labarai na Littafi Mai Tsarki da muka bincika ya nuna cewa ƙauna ta alheri ana nuna da son rai ne ba don dole ba. Bethuel da son rai ya ba wa baran Ibrahim haɗin kai, kuma haka ma Rifkatu ta yi. (Farawa 24:51, 58) Yusufu ya nuna ƙaunarsa ta alheri ba tare da wani rinjaya daga waje ba. (Farawa 50:4, 5) Ruth “ta ƙalafa ranta za ta tafi tare da [Naomi].” (Ruth 1:18) Sa’ad da Naomi ta shawarci Ruth ta tuntuɓi Boaz, ƙauna ta alheri ta motsa ’yar Mowabawa ta ce: “Dukan abin da kika faɗi, sai in yi.”—Ruth 3:1-5.
16, 17. Menene ya sa ƙauna ta alheri na Bethuel, Yusufu, da kuma Ruth musamman suke da muhimmanci, kuma menene ya motsa su su nuna wannan hali?
16 Ƙauna ta alheri da Bethuel, Yusufu, da kuma Ruth suka nuna, tana da muhimmanci domin Ibrahim, Yakubu, da kuma Naomi ba su da daman su rinjaye su. Ban da haka ma, bai wajaba ba ga Bethuel ya rabu da ’yarsa. Da zai iya ce wa baran Ibrahim: ‘A’a, ina son ’yata mai ƙwazo ta kasance kusa da ni.’ (Farawa 24:18-20) Hakanan Yusufu yana da ’yancin ya yi abin da babansa yake so ko a’a, domin Yakubu ya mutu ba zai iya ya matsa masa ba ya bi maganarsa. Naomi kanta ta ce Ruth tana da ’yancin ta zauna a Mowab. (Ruth 1:8) Ruth kuma tana da ’yancin ta auri ɗaya daga cikin ‘samari’ maimakon Boaz da ya manyanta.
17 Bethuel, Yusufu, da Ruth sun nuna ƙauna ta alheri da son rai, zuciyarsu ce ta motsa su su yi haka. Sun ji suna da hakkin su nuna wannan hali ga waɗanda suke da dangantaka da su, kamar yadda Sarki Dauda ya ji daga baya cewa ya wajaba ya nuna wannan ga Mephibosheth.
18. (a) Da wane hali ne dattawa Kiristoci suke ‘kiwon tumaki’? (b) Ta yaya wani dattijo ya nuna motsin ransa game da taimakon wani ɗan’uwa mai bi?
18 Ƙauna ta alheri har ila alama ce ta mutanen Allah, har da mutane da suke kiwon tumakin Allah. (Zabura 110:3; 1 Tassalunikawa 5:12) Irin waɗannan dattawa, ko masu kula suna jin hakkinsu ne su yi daidai da abin da aka ɗanka musu ta wajen naɗa su. (Ayukan Manzanni 20:28) Duk da haka, aikinsu na kiwo da kuma wasu ayyukan ƙauna ta alheri domin ikilisiya suna yi ne “ba kamar na tilas ba, amma da yardan rai.” (1 Bitrus 5:2) Dattawa suna yin kiwon tumakin domin suna da hakkin haka kuma suna da muradin su yi haka. Suna nuna ƙauna ta alheri ga tumakin Kristi domin ya kamata su yi kuma suna son su yi haka. (Yohanna 21:15-17) “Ina son ziyartar gidajen ’yan’uwa ba domin wani dalili ba fiye da in nuna musu ina tunaninsu,” in ji wani dattijo. “Taimakon ɗan’uwa tushe ne na farin ciki da gamsuwa a gare ni!” Dattawa da suke kula a ko’ina da dukan zuciyarsu sun yarda da haka.
Ka Nuna Ƙauna ta Alheri ga Waɗanda Suke da Bukata
19. Wace gaskiya ce game da ƙauna ta alheri aka nuna a cikin wannan labaran Littafi Mai Tsarki da aka tattauna a cikin wannan talifin?
19 Labaran Littafi Mai Tsarki da muka tattauna sun nuna cewa ƙauna ta alheri ya kamata a nuna ta ga waɗanda suke da bukatar da ba za su iya biyanta ba da kansu. Domin ya ci gaba da zuriyarsa, Ibrahim yana bukatar haɗin kan Bethuel. Domin a kai gawarsa Kan’ana, Yakubu yana bukatar taimakon Yusufu. Kuma domin ta samu magaji, Naomi tana bukatar taimakon Ruth. Babu wanda zai iya cika waɗannan bukatar ba tare da taimako ba tsakanin Ibrahim, Yakubu da kuma Naomi. Hakanan a yau, ƙauna ta alheri ya kamata a nuna ta, musamman ga waɗanda suke da bukata. (Misalai 19:17) Muna bukatar mu yi koyi da uban iyali Ayuba, wanda yake mai da hankalinsa ga “talakan da ya yi kuka, maraya kuma wanda ba shi da mai-taimakonsa” har da wanda “ya ke bakin mutuwa.” Ayuba kuma ya ‘faranta wa gwauruwa rai’ kuma ya zama ‘ido ga makaho sawu kuma ga gurgu.’—Ayuba 29:12-15.
20, 21. Su waye suke da bukatar mu nuna musu ƙaunarmu ta alheri, kuma menene kowannenmu ya kamata ya ƙuduri aniyar yi?
20 Hakika, da akwai ‘talakawa masu kukar taimako’ a kowane ikilisiya ta Kirista. Wannan zai kasance ne domin dalilai kamarsu kaɗaita, kasala, jin rashin amfani, da kuma yin abin ƙuna na wasu, cuta mai tsanani, ko kuma mutuwar wanda ake ƙauna. Ko menene dalilin, dukan irin waɗannan ƙaunatattu suna da bukata da za a iya kuma ya kamata a biya ta wajen ayyukanmu na ƙauna ta alheri da son rai.—1 Tassalunikawa 5:14.
21 Saboda haka, bari mu ci gaba da koyi da Jehovah Allah, wanda “mai-yalwar [ƙauna ta alheri]” ne. (Fitowa 34:6; Afisawa 5:1) Za mu iya yin haka ta wajen yin takamammun aiki, musamman ma a maimakon waɗanda suke da bukata. Kuma babu shakka za mu daraja Jehovah kuma mu samu farin ciki mai yawa sa’ad da muka “nuna [ƙauna ta alheri, NW ] . . . kowane mutum zuwa ga ɗan’uwansa.”—Zechariah 7:9.
[Hasiya]
a Domin bayani game da irin aure da ya kasance a nan, duba Littafi na 1, shafi na 370, na Insight on the Scriptures, Shaidun Jehovah ne suka buga.
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya ƙauna ta alheri ta bambanta da alheri na mutane?
• A wace hanya ce Bethuel, da Yusufu, da Ruth suka nuna ƙauna ta alheri?
• Da wane hali za mu nuna ƙauna ta alheri?
• Waye suke bukatar ƙaunarmu ta alheri?
[Hoto a shafi na 15]
Ta yaya Bethuel ya nuna ƙauna ta alheri?
[Hoto a shafi na 18]
Ƙauna ta aminci ta Ruth albarka ce ga Naomi
[Hotuna a shafi na 20]
Ƙauna ta alheri na mutane ana nuna ta ne da son rai, ta wajen takamaiman aiki, kuma ana nuna ta ne ga waɗanda suke da bukata