Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 8/15 pp. 21-25
  • Ka Nuna “Ka’idar Ƙauna Ta Alheri” A Furcinka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Nuna “Ka’idar Ƙauna Ta Alheri” A Furcinka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ƙauna ta Aminci Ce Take Sa a Yi Alheri
  • Bimbini da Addu’a Suna da Muhimmanci
  • Ta Kasance a Furcin Abokan Aure
  • Ka Nuna Ƙauna ta Aminci ga ’Yan’uwa Masu Bi
  • Mutumin da ke Nuna “Ƙauna ta Alheri” Zai Samu Rai
  • Amfana Daga Ƙauna Ta Alheri Ta Jehovah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka Nuna Ƙauna Ta Alheri Ga Waɗanda Suke Da Bukata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Dole Mutanen Allah Su So Alheri
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 8/15 pp. 21-25

Ka Nuna “Ka’idar Ƙauna Ta Alheri” A Furcinka

“Ta kan buɗe bakinta da hikima: ka’idar nasiha kuma tana kan harshenta.”—MIS. 31:26.

1, 2. (a) Wane hali ne aka ƙarfafa masu bauta wa Jehobah su koya? (b) Menene za a tattauna a wannan talifi?

SAƘO mai muhimmanci da Sarki Lemuel na zamanin dā ya samu daga wurin mahaifiyarsa ya ƙunshi wani abu mai muhimmanci da ke nuna matar kirki. Ta gaya masa: “Ta kan buɗe bakinta da hikima: Ka’idar nasiha kuma tana kan harshenta.”a (Mis. 31:1, 10, 26) Yana da kyau mace mai hikima da kuma dukan waɗanda suke son su faranta wa Jehobah Allah rai su yi magana da ƙauna ta alheri. (Karanta Misalai 19:22.) Ya kamata ƙauna ta alheri ta bayyana a furcin dukan masu bauta ta gaskiya.

2 Menene ƙauna ta alheri? Su waye ne za a nuna wa ƙauna ta alheri? Menene zai taimaka mana mu nuna “ƙa’idar nasiha” a furcinmu? Yaya yin hakan zai shafi tattaunawarmu da waɗanda suke cikin iyalinmu da kuma ’yan’uwa masu bi?

Ƙauna ta Aminci Ce Take Sa a Yi Alheri

3, 4. (a) Menene ƙauna ta alheri? (b) Yaya ƙauna ta alheri ta bambanta da ƙauna ta yau da kullum ko alheri ta mutane?

3 Kamar yadda kalmar ta nuna, ƙauna ta alheri ta ƙunshi halayen ƙauna da alheri. Ta ƙunshi alheri, wato, nuna son mutane da kuma nuna hakan ta wajen yin ayyuka na taimako da kuma yin kalamai masu ƙarfafawa. Tun da yake akwai ƙauna a ciki, nuna ƙauna ta alheri yana bukatan son zaman lafiyar mutane don muna ƙaunarsu. Amma, kalmar yare na ainihi da aka fassara ƙauna ta alheri tana nufin fiye da alheri da aka nuna don ƙauna. Ƙauna ta alheri tana nufin mutum ya nuna alheri tare da aminci cikin son rai har sai ya cim ma nufinsa na nuna alherin ga mutumin.

4 Ƙauna ta alheri ta bambanta da alheri a wani azanci kuma. Mutane suna iya nuna alheri ga baƙi. Mazauna tsibirin Malita sun nuna irin wannan alherin ga manzo Bulus da mutane 272 da jirginsu ya ragargaje, duk da cewa ba su taɓa haɗuwa ba. (A. M. 27:37–28:2) A wani ɓangare kuma, ƙauna ta alheri tana nuni ga mutanen da suka riga suka ƙulla dangantaka kuma suka manne wa juna cikin aminci.b Irin wannan alherin ne Keniyawa suka nuna wa “dukan ’ya’yan Isra’ila lokacin da suka fito daga cikin Masar.”—1 Sam. 15:6.

Bimbini da Addu’a Suna da Muhimmanci

5. Menene zai taimaka mana mu kame harshenmu?

5 Nuna ƙauna ta alheri a furcinmu ba ta da sauƙi. Da yake magana game da harshe, almajiri Yaƙub ya rubuta: “Babu mutum wanda ya ke da iko ya hore shi; mugunta ne shi marar-hutu, cike da guba mai-matarwa.” (Yaƙ. 3:8) Menene zai taimaka mana mu kame wannan gaɓa na jiki da yake da wuyan kamewa? Kalaman Yesu ga shugabannin addinai na zamaninsa sun ba mu ƙarin haske. Ya ce: “Daga cikin yalwar zuciya baki ya kan yi magana.” (Mat. 12:34) Idan muna son mu nuna ƙauna ta alheri a furcinmu, dole ne mu gina wannan halin a zuciyarmu, wato, muradinmu. Bari mu ga yadda bimbini da addu’a za su taimaka mana mu yi hakan.

6. Me ya sa za mu yi bimbini a kan ayyukan Jehobah na ƙauna ta alheri?

6 Jehobah Allah “mai-yalwar jinƙai” ne, in ji Littafi Mai Tsarki. (Fit. 34:6) Mai zabura ya rera waƙa: “Duniya cike ta ke da jinƙanka, ya Ubangiji.” (Zab. 119:64) Nassosi suna ɗauke da labarai masu yawa game da yadda Jehobah ya nuna ƙauna ta alheri ga masu bauta masa. Ɗaukan lokaci don mu yi bimbini cikin godiya a kan ‘aikin Jehobah’ zai sa mu yi sha’awar koyan wannan hali da Allah yake nunawa.—Karanta Zabura 77:12.

7, 8. (a) Wace ƙauna ta alheri ce Jehobah ya nuna ga Lutu da iyalinsa? (b) Yaya Dauda ya ji game da samun ƙauna ta alheri na Allah?

7 Alal misali, ka yi tunanin yadda Jehobah ya ceci Lutu ɗan yayan Ibrahim da iyalinsa sa’ad da ya halaka Saduma, birnin da suke zaune. Yayin da lokacin yake ƙara kusatowa, mala’ikun da suka zo wurin Lutu suka aririce shi ya kwashe iyalinsa kuma ya bar birnin da sauri. Sa’ad da ya ci gaba da “jinkiri,” in ji Littafi Mai Tsarki, “[Mala’ikun] fa suka kama hannunsa, da hannun matatasa, da hannuwan ɗiyansa su biyu mata; gama Ubangiji yana jinƙansa: suka fitar da shi, suka ajiye shi bayan birnin.” Sa’ad da muka yi bimbini a kan wannan aikin ceto, hakan ya motsa mu mu fahimci cewa lalle wannan nuna ƙauna ce ta alheri daga Allah, ko ba haka ba?—Far. 19:16, 19.

8 Ka yi la’akari da misalin Sarki Dauda na Isra’ila ta dā, wanda ya rera waƙa: “[Jehobah] da ke gafarta dukan laifofinka; Mai-warkar da dukan cututtukanka.” Babu shakka, Dauda ya yi godiya sosai ga Jehobah don gafarta masa zunubin da ya yi da Bath-sheba! Ya ɗaukaka Jehobah, yana cewa: “Kamar yadda sama ta yi nisa birbishin duniya, haka nan kuma jinƙansa yana da girma zuwa ga masu-tsoronsa.” (Zab. 103:3, 11) Yin bimbini a kan waɗannan da wasu labaran da ke cikin Nassi yana cika zukatanmu da godiya don ƙauna ta alheri na Jehobah, kuma hakan ya motsa mu mu yabe shi kuma mu gode masa. Yayin da muke ƙara godiya a zuciyarmu, za mu ƙara so mu zama masu koyi da Allah na gaskiya.—Afis. 5:1.

9. Wane dalili ne mai girma ya sa masu bauta wa Jehobah za su nuna ƙauna ta alheri a rayuwarsu ta yau da kullum?

9 Misalan da ke cikin Nassi sun nuna cewa Jehobah yana nuna ƙaunarsa ta alheri, wato, ƙaunarsa ta aminci ga waɗanda suka ƙulla dangantaka da shi. Waɗanda ba su da irin wannan dangantaka na kud da kud da Allah mai rai kuma fa? Jehobah yana tsananta musu ne ko kuma yana nuna musu rashin alheri? Ko kaɗan. “[Allah] mai-alheri ne ga marasa-godiya da miyagu,” in ji Luka 6:35. “Ya kan sa ranatasa ta fito ma miyagu da nagargaru, ya kan aiko da ruwa bisa masu-adalci da marasa-adalci.” (Mat. 5:45) Kafin mu koyi gaskiya da kuma yin amfani da ita, Allah ya nuna mana alheri, ko kuma alheri da yake nuna wa dukan mutane. Amma, a matsayin masu bauta masa, ya nuna mana ƙaunarsa ta aminci, wato, ƙaunarsa ta alheri da yake ci gaba da nunawa. (Karanta Ishaya 54:10.) Muna godiya don hakan! Wannan dalili ne mai girma na nuna ƙauna ta alheri a furcinmu da kuma wasu fannoni na rayuwarmu ta yau da kullum!

10. Me ya sa addu’a take da amfani sosai wajen sa ƙauna ta alheri ta kasance sashe na halinmu?

10 Addu’a tana da muhimmanci wajen taimaka mana mu koyi nuna ƙauna ta alheri. Domin ƙauna da alheri, waɗanda sashe ne na ƙauna ta alheri, fannoni ne na ’yar ruhu mai tsarki na Jehobah. (Gal. 5:22) Muna iya nuna ƙauna ta alheri ta wajen ƙyale wannan ruhun ya yi mana ja-gora. Hanyar da za mu fi samun ruhu mai tsarki na Jehobah ita ce mu roƙe shi ta wurin addu’a. (Luk 11:13) Ya dace mu riƙa yin addu’a a kai a kai don samun ruhun Allah kuma mu karɓi ja-gorarsa. Hakika, yin bimbini da addu’a suna da muhimmanci idan za mu nuna ƙa’idar ƙauna ta alheri a furcinmu.

Ta Kasance a Furcin Abokan Aure

11. (a) Yaya muka sani cewa Jehobah yana bukatan magidanta su nuna ƙauna ta alheri ga matansu? (b) A wace hanya ce ƙa’idar ƙauna ta alheri take taimaka wa miji ya kame harshensa?

11 Manzo Bulus ya ƙarfafa magidanta: “Ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya bada kansa dominta.” (Afis. 5:25) Bulus ya kuma tuna musu abin da Jehobah ya gaya wa Adamu da Hauwa’u. Manzon ya rubuta: “Mutum za ya rabu da ubansa da uwatasa, ya manne ma matatasa; su biyu kuma za su zama ɗaya.” (Afis. 5:31) A bayyane yake cewa Jehobah yana bukatan magidanta su manne wa matansu cikin aminci, a koyaushe suna nuna musu ƙauna ta alheri. Mijin da yake yin magana cikin ƙauna ta aminci ba ya fallasa laifofin matarsa a fili ko kuma ya ƙasƙantar da ita. Yana farin cikin yabonta. (Mis. 31:28) Idan don wasu dalilai matsala ta taso a cikin dangantakar, ƙauna ta alheri za ta motsa mijin ya kame harshensa daga wulakanta matarsa.

12. Ta yaya matar aure za ta nuna ta furcinta cewa ƙa’idar ƙauna ta alheri tana yi wa harshenta ja-gora?

12 Ya kamata ƙa’idar ƙauna ta alheri ta kuma yi wa harshen matar ja-gora. Bai kamata ruhun duniya ya yi wa furcinta ja-gora ba. Ta wajen ganin “kwarjinin mijinta,” tana magana mai kyau game da shi a fili kuma tana ƙara darajar da mutane suke ba shi. (Afis. 5:33) Domin ba ta son ta rage darajar da yaran suke ba babansu, ba ta yin gardama da shi ko kuma ta tuhumi ra’ayinsa a gabansu. Tana magance irin waɗannan batutuwa sa’ad da suke su biyu kawai. “Kowace mace mai-hikima ta kan gina ɗakinta,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Mis. 14:1) Gidanta wuri ne na farin ciki da kwanciyar hankali ga dukan iyalin.

13. A ina ne musamman ya kamata ƙa’idar ƙauna ta alheri ta yi ja-gora, yaya za ta yi hakan?

13 Har a cikin gidansu, dole ne ma’aurata su ci gaba da yin amfani da harshensu a hanyar da ke nuna cewa suna daraja juna. Bulus ya rubuta: “Ku kawar da dukan waɗannan; fushi, hasala, ƙeta, tsegumi, alfasha daga cikin bakinku.” Ya daɗa: “Ku yafa zuciya ta tausayi, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa . . . ku yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.” (Kol. 3:8, 12-14) Idan yara suka saba da jin furcin ƙauna da alheri a gida, za su yi nasara kuma suna iya yin koyi da yadda iyayensu suke magana.

14. A wace hanya ce magidanta za su yi amfani da harshensu su ƙarfafa waɗanda suke ƙarƙashin kulawarsu?

14 Mai zabura ya rubuta game da Jehobah: ‘Bari jinƙanka ya zama abin ta’aziya a gareni, ina roƙonka.’ (Zab. 119:76) Hanya ta musamman da Jehobah yake yi wa mutanensa ta’aziyya ita ce ta wajen ƙarfafa su da kuma yi musu ja-gora. (Zab. 119:105) Ta yaya magidanta za su amfana daga misalin Ubanmu na samaniya kuma su yi amfani da harshensu su ƙarfafa waɗanda suke ƙarƙashinsu? Za su iya yin hakan ta wajen yin tanadin ja-gora da ƙarfafawa da ake bukata. Bauta ta Iyali da yamma zarafi ne mai kyau na koyan batutuwa masu tamani na ruhaniya!—Mis. 24:4.

Ka Nuna Ƙauna ta Aminci ga ’Yan’uwa Masu Bi

15. Ta yaya dattawa da wasu da suka manyanta a ruhaniya za su yi amfani da harshensu su kāre waɗanda suke cikin ikilisiya?

15 Sarki Dauda ya yi addu’a: “Ƙaunarka da amincinka za su kiyaye lafiyata kullum.” (Zab. 40:11) Ta yaya dattawa Kiristoci da wasu da suka manyanta a ruhaniya a cikin ikilisiya za su yi koyi da Jehobah a wannan batun? Yin amfani da harshenmu mu jawo hankalin mutane ga bayanin da ke cikin Nassi zai nuna ƙauna ta alheri.—Mis. 17:17.

16, 17. A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna cewa ƙa’idar ƙauna ta alheri ce take yi wa furcinmu ja-gora?

16 Menene ya kamata mu yi idan muka lura cewa wani Kirista yana bin tafarkin rayuwar da ta saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki? Bai kamata ƙauna ta alheri ta motsa mu mu yi amfani da harshenmu don yi masa gyara ba? (Zab. 141:5) Idan muka san cewa wani ɗan’uwa mai bi ya yi wani zunubi mai tsanani, ƙauna ta aminci za ta motsa mu mu ƙarfafa mai laifin ya “kira dattiɓan ikilisiya” domin “su yi addu’a a bisansa, suna shafe shi da mai cikin sunan Ubangiji.” (Yaƙ. 5:14) Idan mai laifin ya ƙi zuwa wajen dattawa, ba za mu nuna ƙauna ta alheri ba idan ba mu kai ƙarar batun ba. Wasu a cikinmu suna iya yin sanyin gwiwa, jin kaɗaici, jin rashin cancanta, ko kuma baƙin ciki ya sha kansu. Hanya mai kyau da za mu nuna cewa ƙa’idar ƙauna ta alheri tana harshenmu ita ce mu “ƙarfafa masu-raunanan zukata.”—1 Tas. 5:14.

17 Yaya ya kamata mu aikata sa’ad da magabtan Allah suke yaɗa jita-jita game da ’yan’uwa masu bi? Maimakon mu soma shakkar amincin ’yan’uwanmu, ya kamata mu ƙi irin wannan magana ba tare da mai da martani ba ko kuma mu tambayi mai tuhumar ko ya san abin da yake cewa, ko kuma ya tabbata cewa abin da yake faɗa yana da tushe. Idan maƙiyan mutanen Allah suka nemi su san inda ’yan’uwanmu Kiristoci suke don su yi musu lahani, ƙauna ta aminci ga ’yan’uwanmu za ta hana mu gaya musu.—Mis. 18:24.

Mutumin da ke Nuna “Ƙauna ta Alheri” Zai Samu Rai

18, 19. Me ya sa bai kamata ƙa’idar ƙauna ta alheri ta fice daga harshenmu ba a yin sha’ani da ’yan’uwa masu bi?

18 Ya kamata mu nuna ƙauna ta aminci a dukan sha’aninmu da ’yan’uwa masu bauta wa Jehobah. Har ma a yanayi mai wuya, bai kamata ƙa’idar ƙauna ta alheri ta fice daga harshenmu ba. Sa’ad da ƙauna ta alheri na ’ya’yan Isra’ila ta zama “kamar raɓa da ta kan watse tun da wuri,” Jehobah ya yi baƙin ciki. (Hos. 6:4, 6) A wani ɓangare kuma, Jehobah yana farin ciki idan ana nuna ƙauna ta alheri a kai a kai. Ka yi la’akari da yadda ya albarkaci waɗanda suke biɗan ta.

19 Misalai 21:21 ta ce: “Wanda ya bi adalci da jinƙai rai ya ke samu, da adalci, da girma.” Ɗaya daga cikin albarka mai yawa da irin wannan mutumin zai samu ita ce rai, ba na ɗan lokaci ba amma rai na har abada. Jehobah zai taimaka masa ya samu “rai wanda ya ke hakikanin rai.” (1 Tim. 6:12, 19) Saboda haka, bari mu “nuna [ƙauna ta alheri, NW] kowane mutum zuwa ga ɗan’uwansa.”—Zech. 7:9.

[Hasiya]

a An fassara kalma ta asali ta “ƙauna ta alheri” a cikin Littafi Mai Tsarki na Hausa a matsayin “nasiha,” “alheri” da “jinƙai.”

b Don ƙarin bayani na yadda ƙauna ta alheri ta bambanta daga aminci, so, da alheri, ka duba fitowar Hasumiyar Tsaro na 1 ga Yuni, 2002, shafuffuka na 9-10, 15-16.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Yaya za ka ba da ma’anar ƙauna ta alheri?

• Menene zai taimaka mana mu kasance da ƙa’idar ƙauna ta alheri a kan harshenmu?

• Ta yaya abokan aure za su nuna ƙauna ta aminci a furcinsu?

• Menene zai nuna cewa ƙa’idar ƙauna ta alheri tana kan harshenmu a sha’aninmu da ’yan’uwa masu bi?

[Hoton da ke shafi na 23]

Dauda ya ɗaukaka ƙauna ta alheri na Jehobah

[Hoton da ke shafi na 24]

Kuna yin Bauta ta Iyali da yamma a kai a kai?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba