Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 6/1 pp. 9-14
  • Amfana Daga Ƙauna Ta Alheri Ta Jehovah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amfana Daga Ƙauna Ta Alheri Ta Jehovah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Bambancinta Daga So da Aminci
  • Ceto—Nuna Ƙauna ta Alheri Ce
  • Ƙauna ta Alheri da Kuma Ja-Gorar Jehovah
  • Ƙauna ta Alheri Tana Kawo Sauƙi da Kāriya
  • Ƙauna ta Alheri ta Allah Ba ta Ƙarewa
  • Allah Ya Yi wa Bayinsa Tagomashi
  • Ka Nuna “Ka’idar Ƙauna Ta Alheri” A Furcinka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ka Nuna Ƙauna Ta Alheri Ga Waɗanda Suke Da Bukata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Jehovah—Mafificin Misali Na Nagarta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 6/1 pp. 9-14

Amfana Daga Ƙauna Ta Alheri Ta Jehovah

“Wanda ya ke da hikima duka za ya lura . . . kuma da [ƙauna ta alheri, “NW”] na Ubangiji.”—ZABURA 107:43.

1. Yaushe aka yi amfani da furcin nan “ƙauna ta alheri” da farko a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma waɗanne tambayoyi game da wannan halin za mu bincika?

SHEKARA 4,000 da ta gabata, ɗan wan Ibrahim Lutu ya ce game da Jehovah: “Ka ɗaukaka [ƙaunarka ta alheri, NW ].” (Farawa 19:19) Wannan shi ne lokaci na farko da wannan furcin “ƙauna ta alheri” ya bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki a harshe na asali. Yakubu, Naomi, Dauda, da wasu bayin Allah sun yi magana game da wannan hali na Jehovah. (Farawa 32:10; Ruth 1:8; 2 Samu’ila 2:6) Hakika, wannan furcin “ƙauna ta alheri” da kuma “ƙauna ta aminci” sun bayyana wajen sau 250 a cikin Nassosin asali na Ibrananci. Amma menene ƙauna ta alheri na Jehovah? Ga su wa ya nuna shi a dā? Ta yaya muke amfana a gare shi a yau?

2. Me ya sa kalmar Ibrananci da aka fassara “ƙauna ta alheri” take da wuyar ba da ma’anar, kuma wace fassara ce ta dace da wannan furcin da aka fassara da shi?

2 A cikin Nassosi, “ƙauna ta alheri” fassara ce ta kalmar Ibrananci da take cike da ma’ana da harsuna da yawa ba su da kalma guda da za ta ba da cikakkiyar ma’anarta. Saboda haka, fassara kamar su “ƙauna,” “jinƙai,” da kuma “aminci” ba su ba da cikakkiyar ma’anarta ba. Amma, cikakkiyar fassara “ƙauna ta alheri” ma “bai kai cikakkiyar ma’anar kalmar ba,” in ji Theological Wordbook of the Old Testament. New World Translation of the Holy Scriptures—With References ya sa “ƙauna ta aminci” cewa wata hanya ce ta fassara kalmar Ibrananci da aka fassara ta “ƙauna ta alheri.”—Fitowa 15:13; Zabura 5:7; hasiya.

Bambancinta Daga So da Aminci

3. Ta yaya ƙauna ta alheri ta bambanta daga so?

3 Ƙauna ta alheri, ko kuma ƙauna ta aminci, tana da nasaba ta kusa da so da kuma aminci. Duk da haka, ta bambanta daga so a wata hanya muhimmiya. Ka yi la’akari game da yadda ƙauna ta alheri da kuma so suka bambanta. A wasu harsuna za a iya amfani da so ga abubuwa kuma ga ra’ayi. Littafi Mai Tsarki ya yi maganar “son ruwan anab da mai” da kuma “ƙaunar hikima.” (Misalai 21:17; 29:3) Amma ƙauna ta alheri ga mutane take, ba ga ra’ayi ba ko kuma abubuwa marasa rai. Alal misali, Fitowa 20:6, (NW ) ta ce Jehovah yana, “nuna ƙauna ta alheri ga dubbai,” wannan ya shafi mutane ne.

4. Ta yaya ƙauna ta alheri ta bambanta daga aminci?

4 Kalmar Ibrananci da aka fassara ta “ƙauna ta alheri” tana da ma’ana mai zurfi fiye da kalmar nan “aminci.” A wasu harsuna, “aminci” sau da yawa ana amfani da shi ga hali da wani zai nuna ga na gaba da shi wajen aiki. Amma kamar yadda wani manazarci ya lura, a matsayin Littafi Mai Tsarki, ƙauna ta alheri “sau da yawa tana nufin saɓa wa nasabar ce: mai iko ya kasance da aminci ga mai raunana, mai bukata ko kuma mai dangana.” Saboda haka sarki Dauda ya roƙi Jehovah: “Ka sa fuskarka ta haskaka wajen bawanka: ka cece ni cikin ƙaunarka ta alheri.” (Zabura 31:16) Jehovah mai iko, an roƙe shi ya nuna ƙauna ta alheri, ko kuma ƙauna ta aminci, ga mabukaci, Dauda. Tun da mabukaci ba shi da iko bisa mai iko, ƙauna ta alheri da aka nuna a wannan al’amari an yi ta ne da son rai, ba don dole ba.

5. (a) Waɗanne ayyukan ƙauna ta alheri ta Allah ne suka bayyana a cikin Kalmarsa? (b) Waɗanne hanyoyi ne da Jehovah ya nuna ƙauna ta alheri za mu bincika?

5 “Wanda ya ke da hikima” in ji mai Zabura, “za ya . . . lura kuma da [ƙauna ta alheri, NW ] ta Ubangiji.” (Zabura 107:43) Ƙauna ta alheri ta Jehovah za ta iya kai wa ga tsira da kuma ceto. (Zabura 6:4; 119:88, 159) Abar kāriya ce kuma aba ce mai kawo sauƙi daga masifu. (Zabura 31:16, 21; 40:11; 143:12) Domin wannan halin, tuba daga zunubi tana iya yiwu. (Zabura 25:7) Ta wajen maimaita wasu tarihin Littafi Mai Tsarki, za mu gani cewa ƙauna ta alheri ta Jehovah (1) an nuna ta cikin ayyuka takamammu da kuma (2) bayinsa masu aminci sun shaida haka.

Ceto—Nuna Ƙauna ta Alheri Ce

6, 7. (a) Ta yaya Jehovah ya ɗaukaka ƙaunarsa ta alheri a batun Lutu? (b) Yaushe ne Lutu ya yi maganar ƙauna ta alheri na Jehovah?

6 Wataƙila hanya mafi kyau na sanin zurfin ƙauna ta alheri ta Jehovah ita ce bincika tarihin Nassosi da suka ƙunshi wannan halin. A Fitowa 14:1-16, mun ga cewa Lutu, ɗan wan Ibrahim, abokan gaba sun kama shi. Amma Ibrahim ya ceci Lutu. Ran Lutu yana cikin haɗari sa’ad da Jehovah ya yanke shawara ya halaka mugun birnin nan Saduma, inda Lutu da iyalinsa suke da zama.—Farawa 18:20-22; 19:12, 13.

7 Kafin a halaka Saduma, mala’ikun Jehovah suka raka Lutu da iyalinsa bayan garin. A wannan lokacin, Lutu ya ce: “Bawanka ya sami tagomashi a gabanka, ka ɗaukaka [ƙauna ta alheri, NW ] kuma, wanda ka nuna mini da ka ceci raina.” (Farawa 19:16, 19) Da waɗannan kalmomi Lutu ya fahimci cewa Jehovah ya nuna masa ƙauna ta alheri mai yawa da ya cece shi. A wannan batun ƙauna ta alheri ta Allah an nuna ta cikin ceto da kuma tsira.—2 Bitrus 2:7.

Ƙauna ta Alheri da Kuma Ja-Gorar Jehovah

8, 9. (a) Menene umurnin da aka ba baran Ibrahim? (b) Me ya sa baran ya yi wa Allah addu’a domin ƙauna ta alheri, kuma menene ya faru sa’ad da yake addu’ar?

8 A Farawa sura 24, mun karanta game da wani nunin ƙauna ta alheri ta Allah ko kuma ƙauna ta aminci. Tarihin ya nuna cewa Ibrahim ya umurci baransa ya tafi ƙasar dangin Ibrahim ya nema wa ɗansa Ishaƙu mata. (Ayoyi na 2-4) Aikin yana da wuya, amma an tabbatar wa baran cewa mala’ikan Jehovah zai yi masa ja-gora. (Aya ta 7) A ƙarshe baran ya isa wata rijiya a bayan “birnin Nahor” (ko Haran ko kuma wani wuri da yake kusa) daidai lokacin da mata suke zuwa ɗiban ruwa. (Ayoyi na 10, 11) Sa’ad da ya ga matan sun yi kusa, ya sani cewa lokaci mai muhimmanci na aikinsa ya zo. Amma ta yaya zai gane matar da ta dace?

9 Da ya fahimci cewa yana bukatar taimakon Allah baran Ibrahim ya yi addu’a: “Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim ubangidana ina roƙonka, ka aiko mini da arziki yau, ka gwada [ƙauna ta alheri, NW ] kuma ga ubangidana Ibrahim.” (Aya ta 12) Shin Jehovah zai nuna ƙaunarsa ta alheri ne? Baran ya roƙi alama takamammiya da zai gane yarinyar da Allah ya zaɓa. (Ayoyi na 13, 14) Mace ɗaya ta yi daidai abin da ya roƙi Jehovah. Hakika, kamar dai ta ji addu’arsa! (Ayoyi na 15-20) Cikin mamaki, baran “ya kafa mata duba.” Duk da haka, wasu gaskiya masu muhimmanci suna bukatar a bincika su. Wannan kyakkyawar mace dangin Ibrahim ce? Ba ta yi aure ba ne tukuna? Saboda haka baran ya yi “shuru, domin shi sakankance ko Ubangiji ya arzuta tafiyarsa, ko ba ya yi ba.”—Ayoyi na 16, 21.

10. Me ya sa baran Ibrahim ya kammala da cewa Jehovah ya nuna wa ubangidansa ƙauna ta alheri?

10 Ba da daɗewa ba bayan haka, yarinyar ta gabatar da kanta ta ce “ni ’yar Bethuel ce, ɗan Milcah, wanda ta haifa ma [ɗan’uwan Ibrahim] Nahor.” (Farawa 11:26; 24:24) Da jin haka baran ya fahimci cewa Jehovah ya amsa addu’arsa. Da ya cika, sai ya yi sujjada ya ce: “Mai-albarka ne Ubangiji, Allah na ubangidan Ibrahim, wanda ba ya fasa [ƙaunarsa ta alheri, NW ] da amincinsa zuwa ga ubangidana: ni fa, Ubangiji ya bishe ni cikin tafarki har gidan ’yan’uwan ubangidana.” (Aya ta 27) Ta wajen yi masa ja-gora, Allah ya nuna ƙauna ta alheri ga ubangidan baran, Ibrahim.

Ƙauna ta Alheri Tana Kawo Sauƙi da Kāriya

11, 12. (a) A lokacin wane gwaji ne Yusufu ya shaida ƙauna ta alheri ta Jehovah? (b) Ta yaya aka nuna ƙauna ta alheri a batun Yusufu?

11 Bari mu bincika Farawa sura 39. Batun tattaɓa kunnuwan Ibrahim ne, Yusufu, wanda aka sayar da shi zuwa bauta a ƙasar Masar. Duk da haka, “Ubangiji kuwa yana tare da Yusufu.” (Ayoyi na 1, 2) Hakika, har ubangidan Yusufu na ƙasar Masar, Potiphar, ya gane cewa Jehovah yana tare da Yusufu. (Aya ta 3) Amma, Yusufu ya fuskanci gwaji mai tsanani. An tuhume shi da yi wa matar Potiphar fyaɗe kuma aka ɗaure shi a fursuna. (Ayoyi 7-20) A cikin “kurkuku” suke “ciwuci ƙafafunsa da mari; aka sa shi cikin baƙin ƙarfe.”—Farawa 40:15; Zabura 105:18.

12 Menene ya faru a wannan lokacin gwaji? “Ubangiji yana tare da Yusufu ya gwada masa [ƙauna ta alheri, NW ] kuma.” (Aya ta 21a) Wata ƙauna ta alheri ta musamman aka fara ta abubuwa daki-daki da daga baya zai kawo sauƙi daga masifun da Yusufu ya fuskanta. Jehovah ya ga Yusufu ya samu “tagomashi a wurin mai-tsaron kurkuku.” (Aya ta 21b) A ƙarshe, ma’aikacin ya bai wa Yusufu matsayi. (Aya ta 22) Daga baya, Yusufu ya sadu da mutumin da ya sa ya sada da Fir’auna mamallakin ƙasar Masar. (Farawa 40:1-4, 9-15; 41:9-14) A ƙarshe, sarkin ya fifita Yusufu zuwa matsayi na biyu a ƙasar Masar, da ya kai ga yin aikin ceton rai a ƙasar Masar da fari ya addaba. (Farawa 41:37-55) Wahalar Yusufu ta fara ne lokacin da yake shekara 17 kuma ta kai wajen shekaru 12! (Farawa 37:2, 4; 41:46) Amma a cikin dukan waɗannan shekaru na wahala da bala’i, Jehovah Allah ya nuna ƙaunarsa ta alheri ga Yusufu ta wajen kāre shi daga masifa mai tsanani kuma ta wajen kiyaye shi domin matsayi a cika ƙudurin Allah.

Ƙauna ta Alheri ta Allah Ba ta Ƙarewa

13. (a) Waɗanne nuna ƙauna ta alheri ne na Jehovah aka samu a Zabura 136? (b) Yaya ƙauna ta alheri take?

13 Jehovah ya nuna ƙauna ta alheri ga mutanensa Isra’ilawa a kai a kai. Zabura 136 ta nuna cewa a cikin ƙaunarsa ta alheri, ya cece su (Ayoyi na 10-15), da ja-gora (Aya ta 16), da kuma kāriya. (Ayoyi na 17-20) Allah kuma ya nuna ƙaunarsa ta alheri ga mutane ɗai-ɗai. Mutumin da ya nuna ƙauna ta alheri ga ɗan’uwansa ɗan Adam ya yi haka ne da son rai domin ya biya muhimmiyar bukata. Game da ƙauna ta alheri, wani littafin bayani na Littafi Mai Tsarki ya ce: “Aiki ne da yake kiyaye ko kuma ɗaukaka rayuwa. Saka hannu ne domin wani da yake wahala daga masifa.” Wani manazarci ya kwatanta ta da cewa “ƙauna ce da aka nuna cikin aiki.”

14, 15. Me ya sa za mu tabbata cewa Lutu bawan Allah ne, abin yardarsa?

14 Tarihin Farawa da muka bincika ya nuna cewa Jehovah ba ya fasa nuna ƙauna ta alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa. Lutu, Ibrahim, da Yusufu sun yi rayuwa a yanayi dabam dabam kuma sun fuskanci gwaji iri dabam dabam. Mutane ne ajizai, amma bayin Jehovah ne da suka samu yardarsa, kuma suna bukatar taimakon Allah. Mun samu ƙarfafa daga gaskiyar cewa Ubanmu na samaniya ya nuna ƙauna ta alheri ga waɗannan mutane.

15 Lutu ya yi shawara marar hikima kuma wannan ta kai ga wahala. (Farawa 13:12, 13; 14:11, 12) Duk da haka, ya nuna halaye da za a yaba wa. Sa’ad da mala’iku biyu na Allah suka isa Saduma, Lutu ya yi musu alheri. (Farawa 19:1-3) Cikin bangaskiya ya yi wa surukansa biyu gargaɗi game da halaka ta Saduma da ta yi kusa. (Farawa 19:14) An samu ra’ayin Allah game da Lutu a 2 Bitrus 2:7-9, a inda mun karanta: “[Jehovah] ya kuma ceci Lutu adalin, sa’anda ransa ya ɓaci ƙwarai domin zaƙuwa ta masu-mugunta gama wannan mai-adalci da ya ke zaune a tsakiyarsu, yana gani yana ji, yau da gobe ya azabatadda ransa mai-adalci domin ayyukansu marasa-shari’a: Ubangiji ya san yadda za ya ceci masu-ibada daga cikin jaraba.” Hakika, Lutu adalin mutum ne, kuma kalmomin a nan sun nuna cewa mutum ne mai ibada. Kamar sa, mu ma muna more ƙauna ta alheri ta Allah sa’ad da muke yin “tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma.”—2 Bitrus 3:11, 12.

16. A waɗanne kalmomi masu kyau Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da Ibrahim da Yusufu?

16 Tarihin da yake Farawa sura 24 bai bar wata shakka ba game da dangantakar Ibrahim da Jehovah. Aya ta fari ta ce “Ubangiji kuwa ya rigaya ya albarkaci Ibrahim cikin dukan al’amura.” Baran Ibrahim ya kira Jehovah “Allah na ubangidana Ibrahim.” (Ayoyi na 12, 27) Kuma almajiri Yaƙub ya ce Ibrahim “ya barata” kuma “aka ce da shi abokin Allah.” (Yaƙub 2:21-23) Haka yake da Yusufu ma. Dangantaka ta kusa da ta kasance tsakanin Jehovah da Yusufu an nanata ta a cikin dukan sura 39. (Ayoyi na 2, 3, 21, 23) Bugu da ƙari, game da Yusufu, almajiri Istafanus ya ce: “Allah yana tare da shi.”—Ayukan Manzanni 7:9.

17. Menene za mu koya daga misalan Lutu, Ibrahim, da kuma Yusufu?

17 Waɗanda suka samu ƙauna ta alheri ta Allah waɗanda muka bincika, mutane ne waɗanda suke da dangantaka mai kyau da Jehovah Allah kuma suka cika nufin Allah a wasu hanyoyi. Sun fuskanci tangarɗa da ba za su iya nasara bisansu ba da kansu. Ceton ran Lutu yana cikin haɗari, ci gaba da zuriyar Ibrahim, da kuma kāre matsayin Yusufu. Jehovah ne kawai zai iya ya biya bukatun waɗannan mutane masu ibada, kuma ya yi haka ta wajen saka hannu da ayyuka na ƙauna ta alheri. Idan za mu mori ƙauna ta alheri ta Jehovah har abada, mu ma dole ne mu kasance da dangantaka ta kusa da shi kuma mu ci gaba da yin nufinsa.—Ezra 7:28; Zabura 18:50.

Allah Ya Yi wa Bayinsa Tagomashi

18. Menene ayoyi na Littafi Mai Tsarki da yawa suka nuna game da ƙauna ta alheri ta Jehovah?

18 Ƙauna ta alheri ta Jehovah ta cika “duniya,” kuma muna son wannan hali na Allah! (Zabura 119:64) Mun amsa waƙar mai Zabura da dukan zuciyarmu: “Da dai mutane suka yarda su yabi Ubangiji domin [ƙaunarsa ta alheri, NW ], da al’ajabansa da ya ke yi ma ’yan adam kuma.” (Zabura 107:8, 15, 21, 31) Muna farin ciki cewa Jehovah ya ba da ƙaunarsa ta alheri ga bayinsa abin yarda—ko ɗai-ɗai ko kuma a rukuninsu. A cikin addu’a, annabi Daniel ya ce wa Jehovah “ya Ubangiji, babban Allah mai-ban razana kuma, wanda ya kiyaye alkawari da [ƙauna ta alheri, NW ] ga masu-ƙaunarsa da masu-kiyaye dokokinsa.” (Daniel 9:4) Sarki Dauda ya yi addu’a: “Ka lizamta rahamarka ga waɗanda sun san ka.” (Zabura 36:10) Muna godiya cewa Jehovah yana nuna ƙauna ta alheri ga bayinsa!—1 Sarakuna 8:23; 1 Labarbaru 17:13.

19. Waɗanne tambayoyi za mu bincika a talifi na gaba?

19 Hakika, an yi mana tagomashi mu mutanen Jehovah! Ƙari ga amfana daga ƙaunar Allah da yake nuna wa dukan mutane, muna moran albarka ta musamman da take zuwa daga ƙauna ta alheri ko kuma ƙauna ta aminci ta Ubanmu na samaniya. (Yohanna 3:16) Musamman ma a lokacin bukata muke amfana daga wannan hali na musamman na Jehovah. (Zabura 36:7) Amma ta yaya za mu yi koyi da ƙauna ta alheri na Jehovah Allah? Kowannenmu yana nuna wannan hali mai ban sha’awa? Waɗannan da wasu tambayoyi da suka shafi wannan za a bincika a talifi na gaba.

Ka Tuna?

• Wane furci ne za a iya amfani da shi a maimakon “[ƙauna ta alheri, NW ]”?

• Ta yaya ƙauna ta alheri ta bambanta da so da kuma aminci?

• Ta wace hanya ce Jehovah ya nuna ƙauna ta alheri ga Lutu, Ibrahim, da kuma Yusufu?

• Wane tabbaci za mu samu daga nuna ƙauna ta alheri ta Jehovah ta dā?

[Hoto a shafi na 10]

Ka san yadda Allah ya nuna ƙauna ta alheri ga Lutu?

[Hotuna a shafi na 12]

A cikin ƙaunarsa ta alheri, Jehovah ya yi wa baran Ibrahim ja-gora

[Hotuna a shafi na 13]

Jehovah ya nuna ƙauna ta alheri ta wajen kāre Yusufu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba