Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 8/1 pp. 3-4
  • Kana Da Ikon Ka Gaskata

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Da Ikon Ka Gaskata
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ra’ayi da Gaskiya
  • Me Ya Sa Ka Gaskata Abin Da Ka Gaskata?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Shaidun Jehobah Kiristoci Ne na Gaske?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Shin Shaidun Jehobah Suna Hada Bautarsu da Mutanen da Imaninsu ba Daya Ba?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Mai Sauƙin Kai Jarumi Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 8/1 pp. 3-4

Kana Da Ikon Ka Gaskata

Wataƙila kana daraja iko da ka ke da shi ka gaskata ko menene da ka so ka gaskata. Kusan kowa ma haka ne. Ta wajen nuna wannan iko, mazauna duniya mutane biliyan shida sun fito da ra’ayoyi dabam dabam masu ban mamaki. Kamar yadda muke samun launi, siffa, hali, ɗanɗano, ƙanshi, da sauti dabam dabam a halitta, ra’ayoyi dabam dabam sau da yawa suna daɗa ga abin da muke so, farin ciki da jin daɗinmu a rayuwa. Hakika, irin wannan bambanci, yana sa rayuwa ta zama da daɗi.—Zabura 104:24.

AMMA ya kamata a mai da hankali. Wasu ra’ayoyi ba kawai dabam suke ba amma suna da haɗari. Alal misali, da farko a cikin ƙarni na 20, wasu mutane sun gaskata cewa Yahudawa da wasu Rukunin Asiri suna shirin “hana al’adar Kirista kuma su kafa jiha ta duniya a ƙarƙashin nasu iko.” Tushen wannan ra’ayi shi ne wata warƙar Yahudawa mai jigo Protocols of the Learned Elders of Zion. Warƙar ta ce shirin ya haɗa da ɗaukaka haraji mai yawa, da cin gaba wajen yin makamai, ƙarfafa kamfani guda ya sarrafa dukan ayyukan kasuwanci don ‘a halaka arzikin ’yan Al’umma farat ɗaya.’ Ƙagen ya haɗa da a juya tsarin ilimantarwa don a ‘mai da ’yan Al’umma su zama sauna da ba sa tunani,’ da kuma gina hanyar jirgin ƙasa a ƙarƙashin ƙasa da zai haɗa manyan birane domin dattawan Yahudawa su ‘halaka duk wani ɗan hamayya.’

Amma waɗannan ƙarya ne—an shirya ne don a ji haushin Yahudawa. ‘Wannan ƙage na rashin hankali,’ in ji Mark Jones na ma’adanar kayayyakin tarihi na Britaniya, ‘ta yaɗu daga Rasha,’ inda ta bayyana da farko a wani talifin jarida a shekara ta 1903. Ta kai jaridar nan The Times ta London a ranar 8 ga Mayu, 1920. Bayan fiye da shekara guda, jaridar The Times ta fallasa rubutun cewa ƙarya ne. Amma a lokacin, an riga an yi ɓarna. ‘Ƙaryace-ƙaryace kamar irin waɗannan,’ in ji Jones, ‘na da wuya a rufe su.’ Muddin mutane sun amince da su, suna kawo ƙiyayya, dafi, da ra’ayoyi masu haɗari—sau da yawa da sakamako na bala’i, yadda tarihi na ƙarni na 20 ya nuna.—Misalai 6:16-19.

Ra’ayi da Gaskiya

Hakika, ba sai an yi ƙarya ba da gangan kafin a samu ra’ayoyi da ba daidai ba. Wasu lokatai, muna iya fahimtar wasu abubuwa da muka karanta a hanyar da ba daidai ba. Mutane nawa ne suke mutuwar kadangatse domin sun yi abin da suke jin daidai ne? Amma kuma, sau da yawa muna gaskata aba kawai domin muna so mu gaskata ne. Wani shehun malami ya ce ’yan kimiyya ma “sau da yawa suna ɗaukaka nasu hasashen da kuma abin da suka kammala.” Ra’ayoyinsu ya sa ba sa iya bincika al’amura ba tare da son nasu ba. Suna iya ba da rayuwarsu a ƙoƙarin goyon bayan ra’ayoyi da ƙarya ne.—Irmiya 17:9.

Irin waɗannan abubuwa sun faru da ra’ayoyi na addinai—inda aka samu saɓani da yawa. (1 Timothawus 4:1; 2 Timothawus 4:3, 4) Wani mutum yana da bangaskiya mai ƙarfi ga Allah. Wani kuma ya ce mutane ba su da tabbaci da zai goyi bayan bangaskiyarsu ga Allah. Wani ya ce kana da kurwa da ba ta mutuwa tana tsira wa mutuwa. Wani ya gaskata cewa in ka mutu ka daina wanzuwa gabaki ɗaya. Babu shakka, irin waɗannan ra’ayoyi da sun saɓa da juna ba duka ba ne za su zama gaskiya. Ba hikima ba ce, ka tabbata cewa abin da ka gaskata gaskiya ce ba kawai abin da ka ke son ka gaskata ba? (Misalai 1:5) Yaya za ka yi hakanan? Talifi na gaba zai bincika wannan batun.

[Hoto a shafi na 3]

Talifin da ke fallasa “Protocols of the Learned Elders of Zion” na shekara ta 1921

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba