Me Ya Sa Ka Gaskata Abin Da Ka Gaskata?
An ba da ma’anar gaskatawa cewa “amincewa ne da abu cewa gaskiya ce, tabbatacce, ko kuma na ainihi.” Rubutun Universal Declaration of Human Rights na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce kowanne mutum yana da “ikon ’yancin tunani, lamiri da addini.” Wannan ikon ya haɗa da ’yancin “canja addininsa ko kuma ra’ayi,” in yana so ya yi haka.
AMMA, me ya sa wani zai so ya canja addininsa ko ra’ayi? Ra’ayi da ake da shi a ko’ina shi ne “Ina da nawa imanin, kuma ina farin ciki da shi.” Mutane da yawa suna jin cewa, imanin ƙarya ba shi da wani lahani ga kowa. Alal misali, wanda ya gaskata cewa duniya lebur ce, wataƙila ba zai cuci kansa ba ko kuma wani. Wasu sun ce, “ya kamata mu yarda cewa ra’ayoyinmu sun bambanta.” Wannan koyaushe ne yake da kyau? Likita haka kawai zai yarda da ra’ayoyin abokan aikinsa idan ɗaya yana da ra’ayin cewa ya je nan da nan bayan ya yi aiki a kan gawa a gidan ajiye gawa sa’an nan ya ci gaba da bincika majiyyata?
In ya zo ga addini, ra’ayoyi da ba daidai ba sun yi ɓarna mai girma cikin tarihi. Ka yi tunanin bala’i da ta biyo baya sa’ad da shugabannan addinai suka “zuga rukunin masu himma na Kirista su yi mugunta babu tausayi” a lokacin Jihadi na Zamanin Jahiliyya. Ko kuma ka yi tunanin “Kirista” ’yan bindiga daɗi na zamani a yaƙin basasa, “kamar mayaƙan zamanin jahiliyya da suke da sunayen waliyai a kan takobansu, suka liƙa hotunan Maryamu a gindin bindigarsu.” Duka waɗannan masu himma sun gaskata cewa abin da suka yi daidai ne. Duk da haka, a bayyane yake cewa a waɗannan da wasu jayayya da yaƙe-yaƙe na addinai, akwai abin da ba daidai ba.
Me ya sa akwai tashin hankali da kuma hargitsi haka? Amsar Littafi Mai Tsarki ita ce cewa Shaiɗan Iblis yana “ruɗin dukan duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9; 2 Korinthiyawa 4:4; 11:3) Manzo Bulus ya yi kashedi cewa mutanen addinai da yawa za su ‘halaka’ domin Shaiɗan zai ruɗe su, wanda zai yi ‘mu’ujizai da abubuwa masu girma don ruɗu.’ Irin waɗannan, in ji Bulus za su ‘ƙi ƙaunar gaskiya da zai sa su samu ceto’ da haka ‘za a ruɗe su ga gaskata ƙarya.’ (2 Tassalunikawa 2:9-12) Yaya za ka rage gaskata ƙarya? Me ya sa ka ke gaskatawa yadda ka ke yi?
An Yi Rainonka Ka Gaskata?
Wataƙila an yi rainonka cikin imanin iyalinka. Wannan mai yiwuwa abu ne mai kyau. Allah yana son iyaye su koyar da yaransu. (Kubawar Shari’a 6:4-9; 11:18-21) Alal misali, saurayi Timothawus, ya amfana ƙwarai daga saurarar mamarsa da kakarsa. (2 Timothawus 1:5; 3:14, 15) Nassosi sun ƙarfafa a daraja abin da iyaye suka gaskata. (Misalai 1:8; Afisawa 6:1) Amma Mahaliccinka ya nufe ka da gaskata abubuwa domin kawai iyayenka sun gaskata su ne? Manne wa abin da tsararraki na dā suka gaskata kuma suka yi, ba tare da yin tunani a kansu ba, zai zama da haɗari.—Zabura 78:8; Amos 2:4.
Basamariya da ta sadu da Yesu Kristi an raine ta ta gaskata addininta na Samariyawa. (Yohanna 4:20) Yesu ya daraja ’yancin ta ta zaɓi abin da take son ta gaskata, amma kuma ya nuna mata: “Ku kuna yin sujjada ga abin da ba ku sani ba.” Hakika, da yawa cikin imanin addininta kuskure ne, kuma ya gaya mata cewa ya kamata ta canja ra’ayoyinta idan Allah zai yarda da sujjadarta—“cikin ruhu da cikin gaskiya.” Maimakon manne wa abin da babu shakka ra’ayoyi da suke so, ita da wasu kamar ta sun “yi biyayya ga imanin” da aka bayyana ta Yesu Kristi.—Yohanna 4:21-24, 39-41; Ayukan Manzanni 6:7.
An Koyar da Su Su Gaskata?
Malamai da gwanaye a fannonin ilimi na musamman da yawa sun cancanci a daraja su sosai. Duk da haka, tarihi ya cika da misalan sanannun malamai da abin da suka koyar ba daidai ba ne. Alal misali, game da littattafai biyu a kan batutuwan kimiyya da ɗan falsafa na Helenanci Aristotle ya rubuta, ɗan tarihi Bertrand Russell ya ce “da kyar a amince da layi guda cikin littattafan nan a kimiyya ta zamani.” Gwanaye na zamani ma sau da yawa suna kai wa ga kammala da ba daidai ba. Ɗan kimiyya na Britaniya Lord Kelvin a 1895 da gaba gaɗi ya ce, “na’ura mai tashi da ta fi iska nauyi ba zai yiwu ba.” Saboda haka, mutum mai hikima, ba zai gaskata cewa aba gaskiya ce ba domin kawai wani gwani ne ya faɗe ta.—Zabura 146:3.
Hakanan ma ana bukatar mai da hankali in ya zo ga ilimin addini. Manzo Bulus yana da ilimi sosai ta wajen malamansa na addini kuma yana da “himma domin tadodin ubannin[sa]” ƙwarai. Amma himmarsa domin ra’ayoyin kakaninsa, ya jawo masa matsaloli. Ya sa shi ‘tsananta wa ikilisiyar Allah da lalatar da ita.’ (Galatiyawa 1:13, 14; Yohanna 16:2, 3) Mafi muni, na dogon lokaci, Bulus ya ci gaba da “harbi a masuka,” yana ƙin rinjayar da za ta kai shi ga gaskata da Yesu Kristi. Ya bukaci Yesu kansa ya sa hannu ya motsa Bulus ya gyara ra’ayoyinsa.—Ayukan Manzanni 9:1-6; 26:14.
Hanyoyin Sadarwa Sun Rinjaye Ka?
Mai yiwuwa hanyar sadarwa ta shafe ra’ayoyinka sosai. Yawancin mutane suna farin ciki cewa akwai ’yancin magana a hanyoyin sadarwa, yana ba su hanyar jin labarai da za su iya amfani da su. Amma, akwai iko masu ƙarfi da za su iya kuma a kai a kai su rinjayi hanyoyin wasa labarai. Abin da ake gabatarwa sau da yawa ƙarya ne da za ta iya shafan tunaninka.
Ƙari ga haka, don a jawo ko kuma su faranta wa mutane da yawa rai, hanyoyin sadarwa suna sanar ga jama’a abin da zai motsa da kuma abin ban mamaki. Abin da da kyar a faɗa ko kuma a buga wa jama’a shekaru kaɗan da suka shige yana gama gari a yau. Sannu a hankali, mizanan ɗabi’a da aka kafa suna lalacewa. A hankali ana lalata tunanin mutane. Sun soma gaskata cewa “mugunta nagarta; nagarta kuma mugunta.”—Ishaya 5:20; 1 Korinthiyawa 6:9, 10.
Samun Tushe Mai Kyau don Gaskatawa
Gini a kan ra’ayoyi da falsafan mutane kamar gini ne a kan yashi. (Matta 7:26; 1 Korinthiyawa 1:19, 20) To, a kan menene da gaba gaɗi za ka kafa ra’ayoyinka? Tun da yake Allah ya ba ka iyawa na bincika duniya da ta kewaye ka kuma ka yi tambayoyi game da al’amura na ruhaniya, ba tunani mai kyau ba ne cewa zai kuma yi tanadin hanyoyin samun amsoshi da daidai ne ga tambayoyinka? (1 Yohanna 5:20) E, zai yi! To, yaya za ka san aba gaskiya ce, tabbaccaciya, ko ta ainihi game da batutuwa na sujjada? Ba ma ɓata lokaci a cewa Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki ne kaɗai ke tanadin tushe na yin haka.—Yohanna 17:17; 2 Timothawus 3:16, 17.
Amma wani zai ce, “ka daƙanta, ba mutane da suke da Littafi Mai Tsarki ba ne suke haddasa yawanci hargitsi da rikici a harƙoƙin duniya?” To, gaskiya ce cewa shugabannan addinai da suke da’awa suna bin Littafi Mai Tsarki sun kawo rikici da suka saɓa wa juna. Wannan domin ra’ayoyinsu ba daga Littafi Mai Tsarki ba ne. Manzo Bitrus ya kwatanta su “masu-ƙaryan annabci” da “masu-ƙaryan malamta” da za su shigo da “wayo.” A sakamakon ayyukansu, in ji Bitrus, “za a yi kushen hanyar gaskiya.” (2 Bitrus 2:1, 2) Har ila, Bitrus ya rubuta, “muna kuwa da maganar annabci wadda an fi tabbatarda ita; wadda ya yi muku kyau ku lura da ita, kamar da fitilla mai-haskakawa cikin wuri mai-duhu.”—2 Bitrus 1:19; Zabura 119:105.
Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu bincika imaninmu da abin da yake koyarwa. (1 Yohanna 4:1) Miliyoyi da suke karanta wannan jarida za su shaida cewa yin haka ya daɗa ga manufar da kuma ƙarfin rayuwarsu. Saboda haka, ka zama kamar mutanen Biriya da suke da yardan rai. ‘Ka bincika Nassosi kowacce rana’ kafin ka tsai da abin da za ka gaskata. (Ayukan Manzanni 17:11) Shaidun Jehovah za su yi farin ciki su taimaka maka domin ka yi haka. Amma, shawarar taka ce ga abin da ka ke son ka gaskata. Duk da haka, hikima ce ka tabbata cewa ra’ayoyinka, ba hikimar ’yan Adam da sha’awoyinsu ne suke mulmula su ba, amma Kalmar gaskiya ta Allah da aka bayyana ne.—1 Tassalunikawa 2:13; 5:21.
[Hotuna a shafi na 6]
Da gaba gaɗi za ka iya kafa ra’ayoyinka a kan Littafi Mai Tsarki