Itatuwa Da Suke Jimrewa na Dogon Lokaci
WATAƘILA GANGARA NA DUWATSU BA WURI BA NE MAI KYAU DON KA GINA GIDANKA, MUSAMMAN MA IDAN DUWATSUN SUNA DA TSAWO. KO DA MUTANE BA ZA SU IYA ZAMA A IRIN WAƊANNAN WURAREN BA DOMIN WAHALARSU, WASU IRIN ITATUWA SUKAN MANNE WA DUWATSUN, SUNA JIMRE WA SANYIN HUNTURU DA KUMA FARI NA RANI.
IRIN waɗannan itatuwa ba kyawawa ba ne kamar ’yan’uwansu da suke ƙasa. Wataƙila jikin itatuwan ba a miƙe ba ne kuma gajeru ne. Yanayi mai tsananin da kuma rashin ƙasa a inda suke girma ne yake kawo haka.
Tun da yake suna jimre wa yanayi mafi tsanani haka a duniya, kana iya cewa, ai waɗannan itatuwa ba za su daɗe ba. Amma ba haka ba ne. Wasu sun ce Methuselah, wani irin itace da ba ya bushewa, wanda yake girma wajen kafa 10,000 na White Mountains na California, shekarunsu 4,700 ne. The Guinness Book of Records 1997 ya faɗi cewa wannan ne ya fi daɗewa a duniya. Edmund Schulman, wanda ya yi nazari a kan waɗannan itatuwa na dā, ya bayyana haka: “Wannan itacen pine . . . kamar ya fi tsira domin wahala. Sauran irin itatuwan nan da suke kan White Mountains ana samunsu kusan mil 3,000 a hamada, cike da duwatsu.” Schulman ya kuma gano cewa mafi daɗewa a cikin irin itatuwan da suke girma a yanayi mai tsanani ma sun yi girma ne a irin wannan yanayi mai tsanani.
Ko da yake dole ne su jimre wa wahala, waɗannan abin koyi a jimrewa suna amfani da abubuwa biyu da suke da su. Wuraren da suke, inda babu tsiro, yana kāre su daga wutar daji, haɗari mai girma ga manyan itatuwa. Kuma tsaiwarsu ta kama duwatsu gam gam da girgizar ƙasa ce kawai za ta iya motsa su.
A cikin Littafi Mai Tsarki an gwada bayin Allah masu aminci da itatuwa. (Zabura 1:1-3; Irmiya 17:7, 8) Su ma suna fuskantar wahala domin yanayi da suka sami kansu ciki. Tsanantawa, rashin lafiya, ko kuma fatara sukan gwada bangaskiyar mutum ƙwarai, musamman ma idan gwajin ya ci gaba na shekaru. Duk da haka, Mahaliccinsu, wanda ya sifanta itatuwa da suke jimre wa wahala, ya tabbatar wa bayinsa cewa zai toƙara musu. Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari wa waɗanda suke tsaya da aminci: “Shi kafa ku, shi ƙarfafa ku kuma.”—1 Bitrus 5:9, 10.
‘Mutum ya yi tsayin daka, tsaya da aminci, ko kuma nacewa’ shi ne abin da aikatau na Helenanci da ake yawar fassara shi “jimrewa” yake nufi cikin Littafi Mai Tsarki. Yadda itacen da muka ambata da farko yake, yadda yake mannewa gam ne yake taimaka masa wajen jimrewa. Kiristoci, suna bukatar su dasu ƙwarai cikin Yesu Kristi don su tsaya kafaffu. “Tun da shi ke kuka karɓi Kristi Yesu Ubangiji,” in ji Bulus, “sai ku yi tafiya a cikinsa hakanan, dasassu, ginannu kuma cikinsa, kafaffu cikin bangaskiyarku, kamar yadda aka koya maku, kuna yalwata cikin godiya.”—Kolossiyawa 2:6, 7.
Bulus ya fahimci bukatar tsaiwa mai ƙwari na ruhaniya. Shi kansa ya yi fama da “masuki cikin jiki,” ya kuma jimre wa tsanani na ƙwarai duk cikin hidimarsa. (2 Korinthiyawa 11:23-27; 12:7) Amma ya zo ga fahimtar cewa cikin ƙarfin Allah zai iya ci gaba. Ya ce: “Na iya yin abu duka a cikin wannan da ya ke ƙarfafata.”—Filibbiyawa 4:13.
Yadda misalin Bulus ya nuna, nasarar jimrewa ta Kirista ba ta dangana bisa yanayi mai kyau ba. Kamar itacen nan da ya jimre wa yanayi masu tsanani cikin ƙarnuka da yawa, za mu iya tsayawa tsayin daka idan muka kahu cikin Kristi kuma muka dangana ga ikon da Allah ke bayarwa. Bugu da ƙari, idan muka jimre zuwa ƙarshe, za mu yi zaton ganin cikar alkawarin nan na Allah: “Kamar yadda kwanakin itace su ke, hakanan kwanakin mutanena za su zama.”—Ishaya 65:22; Matta 24:13.