15-21 GA YUNI, 2026
WAƘA TA 122 Mu Tsaya Daram, Babu Tsoro!
Abin da Zai Taimaka Mana Saꞌad da Muke Fama da Matsaloli
“Masifa da damuwa suna matsa ni, [amma] umarnanka su ne farin cikina.”—ZAB. 119:143.
ABIN DA ZA MU KOYA
Idan muna ɗaukan matsalolinmu kamar yadda Jehobah yake so mu ɗauke su, hakan zai taimaka mana mu riƙe amincinmu kuma mu yi farin ciki.
1-2. Mene ne zai iya taimaka mana mu jimre saꞌad da muka fuskanci matsaloli? (Ka kuma duba hoton.)
SHIN, kana fama da rashin adalci ne, ko danginka ba sa son yadda kake bauta wa Jehobah, ko kuma wasu suna tsananta maka don imaninka? Kana fama da rashin lafiya ko tsufa? Ko wani abu marar daɗi ya same ka, kamar wani naka ya rasu? Idan haka ne, ba kai kaɗai ba ne. Bayin Jehobah da yawa ma suna fama da matsaloli iri-iri.—Zab. 90:10.
2 Idan muna fama da matsaloli, zai dace mu kasance da raꞌayin Jehobah game da matsalolinmu, hakan zai taimaka mana mu iya jimrewa. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Domin idan ba mu kasance da raꞌayin da ya dace game da matsalolinmu ba, ba za mu san abin da ya kamata mu yi don mu iya jimre matsalolinmu ba. Za mu iya kwatanta hakan da tuƙa mota. Idan gilashin gaban motar yana da datti, ba za mu iya ganin hanya da kyau ba. Amma idan yana da tsabta, za mu iya ganin hanya da kyau. A wannan talifin, za mu tattauna (1) yadda Jehobah yake so mu riƙa ɗaukan matsalolinmu, (2) abin da zai iya faruwa idan ba mu ɗauki matsalolinmu yadda Jehobah yake so mu yi ba, da kuma (3) abin za mu iya yi saꞌad da wani abu marar kyau ya faru da mu.
Idan mun kasance da raꞌayin da ya dace game da matsalolinmu, hakan zai sa mu iya jimrewa (Ka duba sakin layi na 2)
YADDA JEHOBAH YAKE SO MU RIƘA ƊAUKAN MATSALOLINMU
3. Me ya sa ba za mu iya guje wa matsaloli a wannan duniyar ba?
3 Ba za mu iya guje wa matsaloli a wannan muguwar duniyar ba. Da yake Shaiɗan ne yake iko da duniyar nan kuma mu ajizai ne, ba za mu iya guje wa matsaloli ba. Ƙari ga haka, yayin da ƙarshen duniyar nan yake gabatowa, matsalolinmu za su daɗa muni, kuma da alama cewa balaꞌoꞌi za su daɗa ƙaruwa. (Mat. 24:8; 2 Tim. 3:13) Idan Jehobah ya magance matsalolin nan yanzu, hakan zai zama kamar yana taimaka wa Shaiɗan ya yi mulkin wannan duniyar. Tun da Shaiɗan ne yake mulkin wannan duniyar, dole ne mu yi fama da matsaloli.—M. Wa. 9:12.
4. Wane dalili ne kuma yake sa mabiyan Yesu su sha wahala?
4 Muna kuma shan wahala domin mu mabiyan Yesu ne. Sau da yawa Yesu ya gaya wa almajiransa cewa za a tsananta musu domin su mabiyansa ne. (Mat. 24:9; Yoh. 16:2) Sanin hakan yana taimaka mana mu riƙe amincinmu saꞌad da ake tsananta mana. (1 Tas. 3:3, 4) Kuma idan muka riƙe amincinmu saꞌad da muke fama da matsaloli, za mu iya kasance da tabbaci cewa Jehobah da Yesu za su yi mana albarka. Ƙari ga haka, hakan zai nuna cewa mun zaɓi mu bauta wa Jehobah domin shi ne ya cancanci ya zama sarkinmu, kuma muna nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Ɗaya daga cikin ƙaryace-ƙaryacen da Shaiɗan yake yaɗawa shi ne, ꞌyanꞌadam ba sa ƙaunar Allah da zuciya ɗaya. Suna yin hakan ne domin abin da Allah yake ba su. Shi ya sa Shaiɗan yake kai wa bayin Jehobah hari don ya nuna cewa ba za su iya riƙe amincinsu ba a mawuyacin hali. (Ayu. 1:9-11) Amma idan muka jimre don muna ƙaunar Jehobah, hakan zai sa shi farin ciki sosai.—K. Mag. 27:11.
5. Me za mu iya koya daga Mai-Waꞌazi 7:13, 14? (Ka kuma duba hotunan.)
5 Jehobah yakan ƙyale wasu matsaloli. Jehobah ba ya mana mugunta ko kuma ya jarrabce mu. (Yak. 1:13) Amma me ya sa Sarki Sulemanu ya rubuta cewa, Allah ne ya yi “kwanakin wahala”? (Karanta Mai-Waꞌazi 7:13, 14.) Hakan ba ya nufin cewa Jehobah ne yake sa abubuwa marasa kyau su faru, amma yana ƙyale su ne kawai. Me za mu iya koya daga abin da Sulemanu ya rubuta a Mai-Waꞌazi 7:13, 14? Ga abubuwa biyu. Na ɗaya, zai dace mu san cewa akwai lokacin da abubuwa za su yi tafiya sumul, da kuma lokacin da za mu fuskanci matsaloli, domin muna duniyar Shaiɗan. Saboda haka, idan abubuwa suna tafiya sumul, ya kamata mu gode wa Jehobah, domin shi ne yake ba mu abubuwa masu kyau. Na biyu, Sulemanu ya tuna mana cewa ꞌyanꞌadam ba za su iya sanin “abin da zai faru nan gaba ba,” ko da mai kyau ne ko marar kyau. Hakan yana nufin cewa, abubuwa marasa kyau za su iya samun masu adalci da marasa adalci.
Zai dace mu san cewa akwai lokacin da za mu ji daɗi da lokacin da ba za mu ji daɗi ba a wannan duniyar Shaiɗan (Ka duba sakin layi na 5)
6. Mene ne wataƙila zai iya sa Jehobah ya ƙyale mu mu sha wahala? (Ibraniyawa 12:7, 11)
6 Saꞌad da muke fuskantar matsaloli, Jehobah zai iya koya mana yadda za mu dogara gare shi, maimakon kanmu. A duk lokacin da muke fama da matsaloli, Jehobah yana gani kuma zai taimaka mana. Ko da ya ƙyale wani abu mai tsanani ya same mu, yakan taimaka mana mu san abin da ya kamata mu yi. Ƙari ga haka, yana tabbatar mana cewa yana ƙaunar mu kuma yana ba mu ƙarfin jimrewa. (Zab. 23:4) Wani abu kuma shi ne, idan muna fuskantar matsaloli, hakan zai iya sa mu ga wasu halayen da muke bukatar mu kasance da su. Kuma da taimakon Jehobah za mu iya kasancewa da irin halayen. (Karanta Ibraniyawa 12:7, 11.) Alal misali, akwai lokacin da Ayuba ya bukaci ya kasance da sauƙin kai. Ba Jehobah ne ya jawo wa Ayuba matsalolin da ya fuskanta ba, amma ya ƙyale shi ya sha wahala, kuma Jehobah ya yi amfani da yanayin don ya taimaka wa Ayuba ya koyi darussa. (Ayu. 42:1-6) Muna da tabbaci cewa, idan Jehobah ya ƙyale wani yanayi mai wuya ya same mu, zai taimaka mana mu riƙe amincinmu kuma zai albarkace mu.—Rom. 8:35-39.
7. Me ya sa za mu iya yin farin ciki saꞌad da ake tsananta mana don imaninmu?
7 Za mu iya yin farin ciki saꞌad da ake tsananta mana. Idan ana tsananta maka saboda imaninka, kada ka ɗauka cewa Jehobah ya yi watsi da kai ko kuma ba ya tare da kai. A maimakon haka, ka tuna cewa ana tsananta maka ne domin kana yi wa Jehobah biyayya. Babu shakka, hakan na faranta masa rai kuma zai albarkace ka. (Mat. 5:10-12) Idan muka kasance da raꞌayin Jehobah game da matsaloli, za mu yi farin ciki saꞌad da ake tsananta mana don imaninmu, kamar yadda mazannin Yesu suka yi. (A. M. 5:40-42) Ƙari ga haka, idan muka riƙe amincinmu saꞌad da ake tsananta mana, hakan zai sa mu taimaka wa mutane su koyi gaskiya game da Jehobah kuma “su ɗaukaka” sunansa. (1 Bit. 2:12) Ka yi laꞌakari da abin da ya faru da Yusufu. Jehobah ya taimaka masa kuma ya yi masa albarka saꞌad da yake kurkuku, da kuma lokacin da ya bar wurin. Hakan ya tabbatar mana cewa Jehobah zai iya taimaka mana kuma ya albarkace mu saꞌad da muke shan wahala.—Far. 39:3, 23.
8. Mene ne kuma zai taimaka mana mu ci-gaba da jimrewa saꞌad da muke fuskantar matsaloli?
8 Matsalolinmu za su ƙare. Labarin Ayuba ya tabbatar mana cewa matsalolinmu za su ƙare. Littafi Mai Tsarki ya ce, Jehobah “ya albarkaci Ayuba a ƙarshen kwanakinsa fiye da na farko.” (Ayu. 42:12) Mu ma Jehobah ya yi mana alkawari cewa, zai ba mu rai na har abada a sabuwar duniya. Ba za mu iya kwatanta rayuwar da muke yi a yanzu da wanda za mu yi a nan gaba ba. Bari dukanmu mu ci-gaba da jimrewa har ƙarshe don mu sami albarkun!—Mat. 24:13.
YADDA RAꞌAYINMU ZAI IYA SA YANAYINMU YA DAƊA MUNI
9. Ta yaya kasancewa da raꞌayin da bai dace ba zai iya sa yanayinmu ya daɗa muni?
9 Yayin da muke fama da matsaloli, za mu iya sa yanayinmu ya daɗa muni idan muka kasance da raꞌayin da bai dace ba. Alal misali, za mu iya gani kamar Jehobah ne ya jawo mana matsalolin. Abin da ya faru da Ayuba ke nan. Akwai lokacin da ya ɗauka cewa Jehobah ne ya jawo masa matsaloli. Har ma “ya nace a kan adalcinsa fiye da adalcin Allah.” (Ayu. 32:2) Akwai lokacin da Naomi ma ta kasance da irin raꞌayin nan. Da farko ta ɗauka cewa Jehobah ne yake jawo mata matsaloli. (Rut 1:13, 20, 21) Da a ce Ayuba da Naomi sun ci-gaba da kasancewa da raꞌayin nan, da sun ɓata dangantakarsu da Jehobah. (K. Mag. 19:3) Amma Jehobah ya taimaka musu su fahimci cewa ba shi ne yake jawo musu matsaloli ba. Kuma ya albarkace su don sun riƙe amincinsu.
10. Saꞌad da muke fama da matsaloli, wane raꞌayi ne za mu iya kasancewa da shi?
10 Ko da muna da tabbaci cewa ba Jehobah ne yake jawo matsalolinmu ba, za mu iya yin shakka ko ya damu da mu da gaske. Irin raꞌayin nan zai iya sa mu sanyin gwiwa, kuma ya yi mana wuya mu ci-gaba da bauta wa Jehobah. (K. Mag. 24:10) Sarki Dauda da annabi Habakkuk sun fuskanci matsaloli da yawa a rayuwarsu. Hakan ya sa a wasu lokuta, sun yi shakka ko Jehobah yana jin adduꞌoꞌinsu. (Zab. 10:1; Hab. 1:2) Duk da haka, ba su daina yin adduꞌa ba. Jehobah ya amsa adduꞌoꞌinsu kuma ya ci-gaba da taimaka musu. Kai ma zai ci-gaba da taimaka maka.—Zab. 10:17.
11. Mene ne zai iya faruwa da mu idan ba mu kasance da raꞌayin da ya dace game da matsalolinmu ba?
11 Idan ba mu kasance da raꞌayin da ya dace game da matsalolinmu ba, za mu iya ganin kamar bai kamata Jehobah ya bar mu mu sha wahala ba. Don haka, za mu iya jin wani iri idan wani abu marar kyau ya same mu. (1 Bit. 4:12) Ya yi wa almajiran Yesu wuya su fahimci cewa Yesu zai sha azaba kuma za a kashe shi. (Luk. 18:33, 34) Alal misali, duk da cewa Yesu ya riga ya gaya wa almajiransa abin da zai faru da shi, Bitrus ya ɗauka cewa Jehobah ba zai bar hakan ya faru ba. Yesu ya san cewa irin raꞌayin Bitrus ɗin nan, zai iya hana shi cika nufin Jehobah. Shi ya sa ya yi wa Bitrus gyara. (Mar. 8:31-33) Kuma har bayan mutuwar Yesu, almajiransa ba su yi saurin fahimtar dalilin da ya sa aka kashe shi ba. Amma Yesu ya nuna ya damu da su kuma ya ci-gaba da taimaka musu. Bayan da aka ta da Yesu daga mutuwa, ya taimaka wa almajiransa ta wurin bayyana musu Nassosi don su fahimci dalilin da ya sa ya sha wahala kuma aka kashe shi. (Luk. 24:25-27, 32, 44-48) Saꞌad da suka yi tunani a kan abin da Yesu ya koya musu, hakan ya taimaka musu su iya jimre matsalolin da suka fuskanta a gaba. Mu ma za mu iya yin tunani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da tsanantawa da kuma matsaloli don mu iya jimrewa.
12. Yaya za mu iya ji idan ba mu kasance da raꞌayin da ya dace game da yanayinmu ba?
12 Idan ba mu kasance da raꞌayin da ya dace game da yanayinmu ba, za mu iya gani kamar matsalolinmu sun fi yadda suke. Yesu ya nuna yadda hakan zai iya faruwa da mu a misalin da ya bayar na maꞌaikatan gonar inabi. Wasu daga cikin maꞌaikatan sun yi ta gunaguni don suna ganin ba a biya su yadda ya kamata ba. Amma maigidan ya gaya wa ɗaya daga cikinsu cewa: “Abokina, ai ban cuce ka ba.” (Mat. 20:10-13) Maꞌaikatan suna ganin maigidan ya yi musu rashin adalci ne, amma ba haka ba ne. Suna so ya biya su fiye da yadda suka shirya. A yau ma, wasu ꞌyanꞌuwa suna fama da irin yanayin nan. Alal misali, za su iya ganin kamar rashin adalci ne aka yi musu don ba su sami irin hidimar da suke so ba. To, me zai taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace idan muna fama da wani yanayi mai wuya?
ABIN DA ZA MU IYA YI IDAN MUNA FAMA DA MATSALOLI
13. Mene ne zai iya faruwa saꞌad da muke fama da matsaloli?
13 Bayin Allah sun san abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da matsalolinmu. Har ma sukan yi amfani da nassosi don su ƙarfafa mutane da suke fama da matsaloli. Amma idan kai ne kake fama da matsaloli, yana yi maka sauƙi ka kasance da raꞌayin da ya dace ne? Alal misali, kana ganin kamar Jehobah yana maka horo ne, ko kuma ba ya amsa adduꞌoꞌinka? Idan haka ne kake ji, mene ne zai taimaka maka ka kasance da raꞌayin da ya dace?
14. Mene ne za mu iya roƙan Jehobah ya yi mana saꞌad da muke fama da matsaloli? (Filibiyawa 4:13)
14 Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka. Ka gaya wa Jehobah game da yanayin da kake ciki da kuma yadda kake ji. Ka gaya masa ainihin abin da kake so ya yi maka. Ka roƙe shi ya ba ka ruhu mai tsarki don ka iya kasance da ƙarfi da kuma hikimar da kake bukata don ka ci-gaba da jimrewa. Amma ka tuna cewa Jehobah zai iya amsa adduꞌoꞌinka a hanyoyin da ba ka yi tsammani ba. (Afis. 3:20) Zai iya amfani da malaꞌiku da kuma ꞌyanꞌuwa maza da mata don su taimaka maka. (Zab. 34:7) Saboda haka, ka lura da yadda Jehobah yake taimaka maka, kuma ka gode masa. Babu shakka, yana so ya ba ka ruhunsa mai tsarki don ka iya jimre kowace irin matsala.—Karanta 2 Korintiyawa 4:7.
15. Mene ne za mu iya yi don mu iya jimre wahala? (Ka kuma duba hoton.)
15 Ka ci-gaba da yin ayyukan ibada. Ka ci-gaba da yin iya ƙoƙarinka, ko da abin da kake yi yanzu bai kai na dā ba. Ka riƙa yin tunani a kan abubuwan da za su taimaka maka ka kasance da raꞌayin Jehobah, musamman a lokacin “masifa da damuwa.” (Zab. 119:143) Ka riƙa karanta Kalmar Allah, da yin nazari, da kuma yin tunani mai zurfi a kai. Ka ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo, da halartan taro, da kuma yin kalami. Ƙari ga haka, ka riƙa yin cuɗanya da ꞌyanꞌuwa maza da mata. Ban da haka ma, ka guji ware kanka.—K. Mag. 18:1.
Ka yi iya ƙoƙarinka don ka ci-gaba da ayyukan ibada (Ka duba sakin layi na 15)
16. Saꞌad da kake fama da matsaloli, mene ne ya kamata ka daina yi, kuma me zai taimaka maka ka yi hakan? (2 Korintiyawa 10:4, 5)
16 Ka daina shakka. Saꞌad da kake fama da matsaloli, kana bukata ka “rusa abubuwa da suka tsaya da ƙarfi kamar katanga.” Hakan ya ƙunshi yin shakka game da kanmu da kuma Jehobah. (Karanta 2 Korintiyawa 10:4, 5.) Wani abin da zai taimaka mana mu daina irin shakkar nan shi ne, bincika Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu. Alal misali, idan kana ganin cewa Jehobah bai yarda da kai ba, me za ka iya yi? Ka bincika labarin manzo Bulus. Duk da matsalolin da manzo Bulus ya fuskanta, ya ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo. Kuma ya kasance da tabbaci cewa Jehobah da Yesu suna jin daɗin abin da yake yi. (2 Kor. 11:23-27) Shin, kana shakka ko Jehobah ya gafarta maka zunuban da ka yi a dā? Idan haka ne, ka rubuta nassosi dabam-dabam da suka nuna cewa lallai Jehobah yana gafarta mana. (Isha. 43:25) Bayan haka, ka karanta su, sai ka yi tunani mai zurfi a kansu. (Zab. 119:97) Shin, akwai wani abu marar kyau da ya taɓa faruwa da ya sa ka ga kamar Jehobah ba ya kāre bayinsa ne? Ka yi amfani da littattafanmu ka yi bincike don ka ga dalilin da ya sa Allah ya ƙyale mu mu sha wahala. (Zab. 91:9-12) Ƙari ga haka, ka karanta labaran ꞌyanꞌuwan maza da mata da suka fuskanci matsaloli a rayuwarsu, da kuma abubuwan da suka yi don su ci-gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki.a
17. Me ya kamata mu yi idan muna fama da matsaloli?
17 Wataƙila a yanzu ba ka fama da wasu matsaloli masu tsanani. Idan haka ne, ka gode wa Jehobah sosai don abubuwan da kake mora yanzu. (M. Wa. 7:14) Amma idan ka soma fama da matsaloli, ka kasance da raꞌayin da ya dace kuma ka ci-gaba da dogara ga Jehobah da dukan zuciyarka. Babu shakka, idan ka yi hakan, Jehobah ‘zai buɗe maka hanya don ka iya jimrewa.’ (1 Kor. 10:13) Amma ta yaya za mu iya taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu idan wani abu marar kyau ya same su? Abin da za mu tattauna a talifi na gaba ke nan.
WAƘA TA 150 Mu Bi Allah Don Mu Sami Ceto
a Alal misali, ka karanta labarin nan mai jigo: “Ka Ci gaba da Bauta wa Jehobah a ‘Miyagun Kwanaki’” da ke Hasumiyar tsaro ta 15 ga Yuli, 2015, shafi na 12-13.