DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ISHAYA 58-62
‘Ku Yi Shelar Shekara ta Alherin’ Jehobah
“Shekara ta alherin” Jehobah ba shekara ta zahiri ba ce
61:1, 2
Lokaci ne da Jehobah ya ba wa mutane masu tawali’u su soma bauta masa
A ƙarni na farko, shekarar alherin ta soma a shekara ta 29 bayan haihuwar Yesu kuma ta ƙare a “ranar sakaiya” ta Jehobah, wato sa’ad da aka halaka Urushalima a shekara ta 70
A zamaninmu, shekarar ta soma sa’ad da aka naɗa Yesu sarki a sama a shekara ta 1914 kuma zai ƙare a lokacin ƙunci mai girma
Jehobah ya ba mu kyautar manyan “itatuwa na adalci”
61:3, 4
Itatuwa masu tsayi sosai ba sa kasancewa su kaɗai amma suna girma tare da wasu itatuwa a cikin daji
Jijiyoyinsu masu girma suna haɗuwa da juna kuma hakan na taimaka musu sa’ad da ake iska mai ƙarfi
Manyan itatuwa suna kāre ƙananan itatuwa daga zafin rana kuma ganyayensu da ke faɗiwa a ƙasa suna zama taki
Dukan ikilisiyoyi a faɗin duniya suna amfana daga kāriya da kuma taimakon da manyan “itatuwa na adalci” suke mana, wato shafaffun Kiristocin da suka rage a duniya