Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 6/1 p. 19
  • An Gamsar da Bukatarsa ta Ruhaniya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • An Gamsar da Bukatarsa ta Ruhaniya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Makamantan Littattafai
  • Ba Mu Ji Tsoro Ba Don Jehobah Yana Tare Da Mu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 6/1 p. 19

Rahoto Daga Masu Shelar Mulki

An Gamsar da Bukatarsa ta Ruhaniya

ƘUBRUS wata tsibiri ce a arewa maso gabashin Bahar Maliya. A lokatan Littafi Mai Tsarki, an san Ƙubrus domin tagulla da kuma katakonta masu kyau. Bulus da Barnaba sun yi shelar bisharar Mulki a wajen lokacin tafiyarsu ta farko ta wa’azi. (Ayukan Manzanni 13:4-12) A yau, bisharar har ila tana amfana rayukan mutanen Ƙubrus da yawa. Babu shakka wannan gaskiya ce a zancen Lucas, ɗan shekara 40. Ya ba da labari:

“An haife mu mu bakwai, a dajin kiwon tumaki. Tun ina yaro, ina da marmarin karatu. Littafin da na fi so shi ne Nassosin Kiristoci na Helenanci daidai aljihu. Lokacin da na ke da shekara goma, ni da wasu abokanena kuma muka kafa wani ƙaramin rukuni na nazarin Littafi Mai Tsarki. Ko da yake, bai daɗe ba domin wasu tsofaffi a ƙauyen suna kiranmu ’yan shirka.

“Daga baya, da nake makaranta a Amurka, na saɗu da mutane daga addinai dabam dabam. Wannan ya sake ta da muradina na abubuwan ruhaniya. Na yi kwanaki da yawa a cikin laburare na jami’a ina nazarin addinai dabam dabam. Kuma na halarci coci da yawa, amma duk da ƙoƙarina, ban gamsu ba a ruhaniya.

“Bayan na gama karatuna, na koma Ƙubrus na samu aikin darektan ɗakin bincike na likitoci. Wani dattijo mai suna Antonis, Mashaidin Jehovah ne, yakan ziyarce ni a wajen aikina. Cocin Greek Orthodox sun lura da ziyararsa.

“Ba da daɗewa ba, wani ɗan tauhidi ya ziyarce ni ya ce kada na yi magana da Shaidun Jehovah. Tun da an koya mini tun ina yaro cewa Cocin Greek Orthodox sune ke da gaskiya, na ji maganarsa na daina taɗi da Antonis na fara tattauna batun Littafi Mai Tsarki da ɗan tauhidin. Na ziyarci gidan zaman zuhudu da yawa a Ƙubrus. Har ma na tafi arewacin Helas na ziyarci Mount Athos, inda ake gani shi ne dutse da ya fi tsarki a addinin Orthodox. Duk da haka, tambayoyina game da Littafi Mai Tsarki suna nan ba a ba da amsar ba.

“Sai na yi wa Allah addu’a ya taimake ni na sami gaskiya. Ba da daɗewa ba, Antonis ya sake zuwa ya ziyarce ni kuma a wajen aikina, kuma na ji cewa wannan amsa ce ga addu’ata. Sai na daina ziyarar ɗan tauhidin na fara nazarin Littafi Mai Tsarki da Antonis. Na ci gaba da cin gaba, a Oktoba na shekarar 1997, na nuna keɓe kaina ga Jehovah wajen baftisma cikin ruwa.

“Matata da manyan ’ya’yana mata biyu, shekarunsu 14 da kuma 10, a farko sun yi hamayya. Amma domin halina mai kyau, matata ta shawarta ta halarci taro a Majami’ar Mulki. Kirkin Shaidun ya burge ta ƙwarai da gaske da kuma damuwa da suka nuna game da ita. Abin da ya fi burge ta ma yadda suke amfani da Littafi Mai Tsarki ne. Domin haka, matata da manyan ’ya’yana mata suka yarda su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehovah. Ka yi tunanin farin cikina lokacin da dukansu uku suka yi baftisma a taron gunduma na “Kalmomin Annabci na Allah” a shekara ta 1999!

“Hakika, gaskiya da na nema na samu. A yanzu iyalina duka, haɗe da matata da ’ya’ya huɗu, duk sun haɗa kai wajen bauta mai tsarki na Jehovah.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba