“Idan Allah Ke Wajenmu, Wa Ke Gāba Da Mu?”
“Me za mu ce da waɗannan al’amura fa? Idan Allah ke wajenmu, wa ke gāba da mu?”—ROMAWA 8:31.
1. Su wanene suka bar Masar tare da Isra’ilawa, kuma me ya sa suka yi haka?
LOKACIN da Isra’ilawa suke kan hanyarsu zuwa ’yanci bayan sun yi shekara 215 a Masar, yawancin shekarun cikin bauta, “taron tattarmuka kuma suka tafi tare da su.” (Fitowa 12:38) Waɗannan mutane da ba Isra’ilawa ba ne sun ga annoba masu ban tsoro guda goma da suka yi halaka a Masar kuma suka mai da allolinsu na ƙarya abin dariya. A wannan lokacin, sun lura da yadda Jehovah ya kāre mutanensa—musamman daga annoba ta huɗu zuwa sama. (Fitowa 8:23, 24) Ko da yake ba su da cikakken sanin nufe-nufen Jehovah, sun tabbata da abu guda: Allolin Masar sun kasa kāre Masarawa, amma Jehovah ya tabbatar da kansa mai ƙarfi domin Isra’ilawa.
2. Me ya sa Rahab ta tallafa wa Isra’ilawa masu leƙen asiri, kuma me ya sa dogarar ta ga Allahnsu ba kuskuri ba ne?
2 Shekara 40 daga baya, kusan shigar Isra’ilawa Ƙasar Alkawari, Joshua, wanda ya gāji Musa, ya aikar da mutane biyu su leƙi asirin ƙasar. A can suka haɗu da Rahab, ’yar Jericho. Daga abin da ta ji game da ayyuka masu girma na Jehovah na kāre Isra’ilawa na shekara 40 tun lokacin da suka bar ƙasar Masar, ta san cewa idan tana son albarkar Allah, dole ne ta tallafa wa mutanensa. Domin shawararta ta hikima, ita da iyalinta an ƙyale su lokacin da Isra’ilawa suka ci birnin a yaƙi daga baya. Hanya ta mu’ujiza da aka cece su kanta ma tabbaci ne a fili cewa Allah yana tare da su. Saboda haka, dogara da Rahab ta yi ga Allahn Isra’ilawa ba kuskuri ba ne.—Joshua 2:1, 9-13; 6:15-17, 25.
3. (a) Wane mu’ujiza Yesu ya yi a kusa da birnin Jericho da aka sake ginawa, kuma me shugabannan addinin Yahudawa suka yi? (b) Menene wasu Yahudawa, daga baya kuma waɗanda ba Yahudawa ba suka fahimta?
3 Ƙarnuka 15 daga baya, Yesu ya warkar da makaho mai bara kusa da birnin Jericho da aka sake ginawa. (Markus 10:46-52; Luka 18:35-43) Wannan mutumin ya roƙi Yesu ya jiƙansa, hakan ya nuna cewa ya san Yesu yana da goyon baya daga wurin Allah. Shugabannan addinin Yahudawa da mabiyansu, a ɓangare ɗaya, sun ƙi su yarda da mu’ujizar da Yesu ya yi a kan tabbaci ne na cewa yana yin aikin Allah. Maimakon haka, suka nemi laifi a gare shi. (Markus 2:15, 16; 3:1-6; Luka 7:31-35) Har ma bayan an tunƙare su da gaskiyar cewa an tashi Yesu daga matattu bayan sun kashe shi, ba su yarda su gaskata cewa wannan yin Allah ne ba. Maimakon haka, suka ja-goranci tsananta wa mabiyan Yesu, suka yi ƙoƙari su hana aikin “wa’azin Ubangiji Yesu.” Amma wasu Yahudawa, daga baya kuma waɗanda ba Yahudawa ba, suka lura da waɗannan abubuwa suka bincika su daidai. A gare su a bayyane yake cewa Allah ya ƙi shugabannan Yahudawa waɗanda suke nuna kansu masu adalci ne, kuma yana goyon bayan mabiyan Yesu Kristi masu tawali’u.—Ayukan Manzanni 11:19-21.
Waye Yake da Goyon Bayan Allah a Yau?
4, 5. (a) Yaya wasu mutane suke ji game da zaɓan addini? (b) Wajen gano addini na gaskiya, mecece ce muhimmiyar tambaya?
4 Game da tambayar addini na gaskiya, wani limami a wani ganawa da aka yi a telibijin a baya bayan nan, ya ce: “Zan nace cewa addini na gaskiya ne idan ya mayar da mutum mai ɗabi’a, idan shi ko ita tana rayuwa bisa ƙa’idodinsa.” Hakika, addinin gaskiya yana mai da mutane masu ɗabi’a. Amma gaskiyar cewa addini yana yin mutane masu ɗabi’a yana tabbatar da cewa Allah yana goyon bayan addinin ne? Wannan shi ne ainihin abin da yake nuna addinin gaskiya?
5 Kowa yana son ya yi zaɓe da kansa, har da zaɓan addini. Amma kasance da ’yancin yin zaɓe ba tabbaci ba ne cewa mutum zai yi zaɓe mai kyau. Alal misali, wasu mutane suna zaɓan addini bisa girmansa, ko arzikinsa, bukukuwa masu kyan gani, ko kuma saboda dangantakar iyali. Babu ko ɗaya cikin waɗannan da zai tabbatar da addinin cewa na gaskiya ko na ƙarya ne. Muhimmiyar tambaya a wannan batu ita ce: Wane addini ne yake ariritar mabiyansa su yi nufin Allah kuma su ba da tabbaci mai ƙarfi na goyon bayan Allah, domin mabiyansa su iya cewa “Allah ke wajenmu”?
6. Waɗanne kalmomin Yesu ne suka ba da ƙarin haske a batun addini na gaskiya da na ƙarya?
6 Yesu ya kafa ƙa’idodin bambance addinin gaskiya daga addinin ƙarya lokacin da ya ce: “Ku yi hankali da masu-ƙaryan annabci, masu-zuwa wurinku da fatar tumaki, amma daga ciki kerketai ne masu-hauka. Bisa ga ’ya’yansu za ku sansance su.” (Matta 7:15, 16, tafiyar tsutsa tamu ce; Malachi 3:18) Bari mu duba wasu cikin “ ’ya’yansu” ko kuma alamar gano addini na gaskiya, saboda bisa gaskiya mu tabbatar da wanda yake da goyon bayan Allah a yau.
Alamar Gano Waɗanda Suke da Goyon Bayan Allah
7. Menene yake nufi a koyar da abin da yake da tushe cikin Littafi Mai Tsarki kawai?
7 Koyarwarsu tana da tushe cikin Littafi Mai Tsarki. Yesu ya ce: “Abin da ni ke koyarwa ba nawa ba ne, amma nasa ne wanda ya aiko ni. Idan kowane mutum yana da nufi shi aika nufin Allah, shi za ya sani ko abin da ni ke koyarwa na Allah ne, ko domin kaina ni ke magana.” Kuma: “Wanda shi ke na Allah, yana jin maganar Allah.” (Yohanna 7:16, 17; 8:47) Don a samu goyon bayan Allah dole ne mutum ya koyar da abin da Allah ya bayyana kawai a Kalmarsa; suna ƙin koyarwa da suke bisa hikima ko kuma al’adar mutane.—Ishaya 29:13; Matta 15:3-9; Kolossiyawa 2:8.
8. Me ya sa yake da muhimmanci a yi amfani da sunan Allah wajen bauta?
8 Suna amfani da sunan Allah, Jehovah, kuma suna yaɗa shi. Ishaya ya annabta: “A cikin ranan nan kuma za ku ce, Ku yi ma Ubangiji godiya, ku furta da sunansa, ku bayyana ayyukansa a wurin al’ummai, ku ambata sunansa maɗaukaki ne. Ku yi rairawa ga Ubangiji; gama ya aika al’amura mafifita; bari wannan ya zama sananne cikin dukan duniya.” (Ishaya 12:4, 5) Yesu ya koyar da mabiyansa su yi addu’a: “Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka.” (Matta 6:9) Saboda haka, ko Yahudawa ko waɗanda ba Yahudawa ba, Kiristoci za su kasance mutane “domin sunan [Allah].” (Ayukan Manzanni 15:14) A bayyane yake cewa Allah yana farin ciki ya goyi bayan waɗanda suke alfahariya su kasance mutane “domin sunansa.”
9. (a) Me ya sa farin ciki yake nuna waɗanda suke cikin addini na gaskiya? (b) Ta yaya Ishaya ya gwada addinin gaskiya da na ƙarya?
9 Suna nuna halin Allah na farin ciki. Tun da shi ne mai “bishara,” Jehovah ‘Allah mai farin ciki’ ne. (1 Timothawus 1:11) To, yaya kuwa masu bauta masa za su zama marasa farin ciki ko kuma ko yaushe da tararren fuska? Duk da masifa ta duniya da damuwarmu, Kiristoci suna riƙe ruhun farin ciki domin suna cin abinci mai yawa na ruhaniya a kai a kai. Ishaya ya gwada su da waɗanda suke yin addinin ƙarya: “Domin wannan in ji Ubangiji Yahweh, Ga shi, bayina za su ci, amma ku za ku ji yunwa: ga shi, bayina za su sha, amma ku za ku ji ƙishi; ga shi, bayina za su yi farinciki, amma ku za ku ji kunya: ga shi kuma, bayina za su yi rairawa domin murna a zuci, amma ku za ku yi kuka domin ɓacin zuciya, za ku yi ihu domin karyawar ruhu.”—Ishaya 65:13, 14.
10. Ta yaya waɗanda suke da addini na gaskiya suke guje wa koyo ta fāɗi-ka-tashi?
10 Halinsu da kuma shawararsu bisa mizanan Littafi Mai Tsarki ne. Marubucin Misalai ya ba mu shawara: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: a cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.” (Misalai 3:5, 6) Allah yana goyon bayan waɗanda suke biɗansa domin ya yi musu ja-gora maimakon su dogara ga hasashe masu saɓa da juna na mutanen da suka ƙi hikimar Allah. Yadda mutum ya daidaita rayuwarsa ta jitu da Kalmar Allah, haka nan zai guje wa koyo ta fāɗi–ka-tashi.—Zabura 119:33; 1 Korinthiyawa 1:19-21.
11. (a) Me ya sa waɗanda suke yin addini na gaskiya ba za su rabu su zama ajin malamai da kuma masu bi ba? (b) Wane misali waɗanda suke ja-gora tsakanin mutanen Allah suke kafa wa garken?
11 An tsara su kamar ikilisiyar Kirista na ƙarni na farko. Yesu ya kafa ka’ida: “Kada a kira ku Malam: gama malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa ’yan’uwa ne. Kuma kada ku ce da kowane mutum a duniya ubanku: gama ɗaya ne Ubanku, shi na sama. Kada kuwa a ce da ku iyayengiji: gama ɗaya ne Ubangijinku, Kristi. Amma wanda shi ke mafi girma a cikinku shi zama mai-hidimanku.” (Matta 23:8-11) Ikilisiyar ’yan’uwa bai ƙunshi ajin malamai ba mai fahariya da yake ɗaukaka kansa da manyan laƙabi kuma da ɗaga kansa bisa sauran masu bi. (Ayuba 32:21, 22) Waɗanda suke kiwon tumakin Allah za su yi haka “ba kamar na tilas ba, amma da yardan rai, bisa ga nufin Allah; ba kuwa domin riba mai ƙazanta, amma da karsashin zuciya; ba kuwa kamar masu-nuna sarauta bisa abin kiwo da aka sanya a hannunku ba, amma kuna nuna kanku gurbi ne ga garken.” (1 Bitrus 5:2, 3) Kiristoci makiyaya na gaskiya suna guje wa mai da kansu iyayengiji kan bangaskiyar wasu. Yadda suke abokan aiki a hidimar Allah, suna ƙoƙari ne su kafa misali mai kyau.—2 Korinthiyawa 1:24.
12. Wane daidaicaccen ra’ayi ne game da gwamnatin mutane, Allah yake bukata daga waɗanda suke son su sami goyon bayansa?
12 Suna miƙa kai ga gwamnatin mutane amma duk da haka suna kasancewa da tsakatsaki. Wanda ya ƙi ya yi “zaman biyayya da ikon masu-mulki” ba zai yi tsammanin samun goyon bayan Allah ba. Me ya sa? Domin “ikokin da ke akwai kuma sanyayyu ne na Allah. Wanda ya yi tsayayya da iko fa, yana tsayayya da umurnin Allah ke nan.” (Romawa 13:1, 2) Duk da haka, Yesu ya fahimci ƙila a iske bambancin ra’ayi lokacin da ya ce: “Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar, Allah kuma abin da ke na Allah.” (Markus 12:17) Waɗanda suke da muradin su samu goyon baya daga wurin Allah dole ne su ci gaba da “biɗan mulkin [Allah da farko], da adalcinsa,” har ila kuma su riƙa yin biyayya ga dokokin ƙasa da suka jitu da babban hakkinsu ga Allah. (Matta 6:33; Ayukan Manzanni 5:29) Yesu ya nanata batun tsakatsaki lokacin da ya ce game da almajiransa: “Ba na duniya su ke ba, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.” Daga baya ya daɗa: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne.”—Yohanna 17:16; 18:36.
13. Wane aiki ƙauna take yi wajen gano mutanen Allah?
13 Ba sa wariya wajen aikata nagarta “ga dukan mutane.” (Galatiyawa 6:10) Ƙauna ta Kiristoci ba ta san wariya ba, tana karɓan dukan mutane ko yaya launin fatarsu, arziki ko kuma ilimin mutum, ƙasarsa, ko kuma yare ba. Aikata nagarta ga dukan mutane tun ba waɗanda suke cikin iyalin imani ba yana taimakawa wajen gano waɗanda suke da goyon baya daga wurin Allah. Yesu ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.”—Yohanna 13:35; Ayukan Manzanni 10:34, 35.
14. Mutanen da suke da yardar Allah dole ne mutane duka su karɓe su? Ka ba da bayani.
14 Suna shirye su sha tsanani domin yin nufin Allah. Yesu ya yi wa mabiyansa gargaɗi: “Idan suka yi mani tsanani, su a yi maku tsanani kuma; idan suka kiyaye maganata, su a kiyaye taku kuma.” (Yohanna 15:20; Matta 5:11, 12; 2 Timothawus 3:12) Waɗanda suke da goyon bayan Allah ko da yaushe ba a yarda da su, kamar yadda yake da Nuhu, wanda ya hukunta duniya ta wajen bangaskiyarsa. (Ibraniyawa 11:7) A yau, waɗanda suke son su sami goyon bayan Allah kada su surka kalmar Allah ko kuma su karya ƙa’idodin Allah domin su guje wa tsanani. Muddin suka ci gaba da bauta wa Allah, sun sani cewa mutane za su yi ‘mamaki kuma suna aibatanku.’—1 Bitrus 2:12; 3:16; 4:4.
Lokaci da Ya Kamata a Bincika Gaskiya
15, 16. (a) Waɗanne tambayoyi ne za su taimake ka ka fahimci addini da yake more goyon bayan Allah? (b) Wane kammalawa mutane miliyoyi suka kai, kuma me ya sa?
15 Ka tambayi kanka, ‘Wane addini ne aka sani da manne wa Kalmar Allah, ko ma koyarwarta ta bambanta da imanin yawancin mutane? Su waye ke nanata muhimmancin sunan Allah, har ma suna amfani da shi wajen sansance kansu? Waye yake nuna cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai magance matsalolin ’yan adam? Su wa ke bin mizanan ɗabi’a na Littafi Mai Tsarki, cikin haɗarin kiransu ’yan ƙauye? Wane rukuni aka sani da cewa ba su da rukunin malamai da ake biyansu, kuma dukan mabiyan masu wa’azi ne? Su wa ake yaba musu domin bin dokar ƙasa, ko da yake ba sa saka hannu ciki siyasa? Su wa cikin ƙauna suke ɓatar da lokaci da kuma kuɗi wajen taimakon wasu su koyi game da Allah da kuma nufe-nufensa? Kuma duk da waɗannan abubuwa masu kyau, su wa ake ƙi, ake yi wa ba’a, kuma ake tsananta musu?’
16 Miliyoyin mutane a dukan duniya suna bincika waɗannan gaskiya kuma sun huɗubantu cewa Shaidun Jehovah ne kaɗai suke yin addini na gaskiya. Sun zo ga wannan ra’ayi ne bisa abin da Shaidun Jehovah suka koyar da kuma yadda suke da ɗabi’a, har kuma da amfani da addininsu ya kawo. (Ishaya 48:17) Miliyoyin mutane suna cewa, kamar yadda aka annabta a Zechariah 8:23: “Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.”
17. Me ya sa ba ɗaga kai ba ne Shaidun Jehovah suke a nuna cewa su kaɗai ke da addini na gaskiya?
17 Ɗaga kai ne Shaidun Jehovah suke a cewa su kaɗai ne suke da goyon bayan Allah? Hakika, da’awarsu daidai ce da ta Isra’ilawa a Masar da suka yi da’awar suna da goyon bayan Allah duk da imanin Masarawan, ko kuma Kiristoci na ƙarni na farko da suka yi da’awar suna da goyon bayan Allah ban da Yahudawa masu addini. Gaskiya ta tabbatar da gaskiyar da’awar. A ƙasashe 235 Shaidun Jehovah suna yin aikin da Yesu ya annabta cewa mabiyansa na gaskiya za su yi a kwanaki na ƙarshe: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.”—Matta 24:14.
18, 19. (a) Me ya sa babu wani dalilin da zai sa Shaidun Jehovah su daina aikinsu na wa’azi, duk da hamayyar da suke fuskanta? (b) Ta yaya Zabura 41:11 ta yarda da gaskiyar cewa Shaidu suna da goyon baya daga wurin Allah?
18 Shaidun Jehovah za su ci gaba da bin wannan umurnin, ba za su bar tsanantawa ko hamayya ta hana su ayyukansu ba. Dole ne a yi aikin Jehovah kuma za a yi. Duk wani ƙoƙarin da wasu suka yi a ƙarni da ya shige su hana Shaidu daga cika aikin Allah ya faɗi banza, domin Jehovah ya yi alkawari: “Babu alatun da aka halitta domin ciwutanki da za ya yi albarka; iyakar harshe kuma da za shi tashi gaba da ke, a shari’a za ki kayar da shi. Gadōn bayin Ubangiji ke nan, adalcinsu wanda shi ke daga wurina.”—Ishaya 54:17.
19 Gaskiyar cewa Shaidun Jehovah sun fi ƙarfi kuma suna ƙwazo yanzu fiye da dā—wannan duk a fuskar hamayya ta duniya—tabbaci ne cewa Jehovah ya yarda da abin da muke yi. Sarki Dauda ya ce: “Da hakanan na sani kana jin daɗina, da shi ke maƙiyina ba ya yi mini ƙashimba ba.” (Zabura 41:11; 56:9, 11) Maƙiyan Allah ba za su taɓa ihun nasara bisa mutanen Jehovah ba, domin Shugabansu, Yesu Kristi, yana ci gaba zuwa nasara ta ƙarshe!
Za Ka Iya Amsawa?
• Waɗanne misalan dā ne na mutanen da suka sami goyon bayan Allah?
• Menene waɗansu alamun gano addini na gaskiya?
• Me ya sa ka tabbata cewa Shaidun Jehovah suna da goyon bayan Allah?
[Hoto a shafi na 21]
Waɗanda suke son samun goyon baya daga wurin Allah dole ne koyarwarsu ta fito daga cikin Kalmarsa kaɗai
[Hoto a shafi na 23]
Dattawa Kiristoci suna kasancewa abin koyi ne ga tumaki